• ZURFIN CIKI KASHI NA 2 TWO BY BABA MONO
    ZURFIN CIKI KASHI NA 2 TWO BY BABA MONO
  • Download Now ZURFIN CIKI KASHI NA 2 BIYU
    :-2**** ta dafa kafadata tana cewa kayi haquri mubarak na sani kana son nabeelah sannan itama tana sonka,sai dai kuma kayi kuskuren rashin bayyana soyayyarka gareta a sanda ta bukaci hakan,nayi kokarin dai- daita tsakaninku amma naji tsoron kada mutane suyi tunanin na aurar da nabeelah ga d'ana ba bisa son ranta ba sai dai bisa dole kasancewar ta girma a hannuna.......haka kuma yanzu bazan saka kaina cikin wannan matsalar taku ba amma zan goya muku baya bisa dukkan shawarar da kuka yanke,idan kuna nemana ku sameni a fallow*** na kalli nabeelah idona cike da hawaye na fara magana kamar haka'nabeelah ina sonki,kuma ina kaunarki, sai dai na kasance cikin irin mutane da sukan boye sirrin zuciyarsu,kiyi haquri ki gafarceni,nasan nayi miki laifi...nagode ki tashi ki tafi allah ya bada zaman lafia sannan allah yasa shine mafi alkhairi gareki........na miqe zan fita daga motar,ta kamo hannuna ta zaunar dani tana magana hade da wani kuka mai tsuma zuciya gami da sa tausayi kamar haka'yamubarak da farko na yarda kana sona amma yanzu na gane cewar soyayyar batayi tasiri a zuciyarka ba tunda har ka yarda zaka haqura dani kan wani ya aura,lallai na yarda baka kishina baka tausayina irin zaman da zanyi tare da wani namiji wanda ba kaiba,ka sani cewar zuciya ba zata aminci rabuwa da kaiba,jikina na haramtashi ga dukkan wani d'a namiji idan ba kaiba dan haka na qudiri niyyar mallakarka ka ta wane hali,yamubarak kayi kokari ka soni kamar yanda nake sonka,yamubarak kada ka bani kunya'*** na share hawayen dake zuba kan kuncinta,na kama hannayenta na kwantar da ita bisa kirjina,nabeela h ki amince da soyayyata gareki kada ki zargeni da komi sai alkhairi,nabeelah ina sonki kuma nine mijinki da yardar allah,da sauri ta tashi daga kan kirjina ta dafa kafaduna tana kallon fuskata,ta sumbaci goshina sannan ta rungumeni kan kirjinta tana cewa hakika farincikina ya karu,burina ya cika sannan alheri ya tabbata gareni.....amma *menene mafita? *da wane zance zamu tunkari abba? *sannan kuma lokaci yana da karanci garemu.... Na kalli nabeelah dake kan kirjina nace zaifi sauki muje wurin kawu aminu mu shaida masa halinda muke ciki...ni nasan me zan fada masa kuma zai yarda. *kai tsaye na tuka motar zuwa gidan kawu na tarar ya gama cin abinci yana gindin bishiya yana hutawa..bayan mun gaisa ya cigaba da magana kamar haka'lallai daga ganinku akwai matsala dan naga alamun damuwa gareku, shin ko baki son auren ne? Ya tambaya' na fara da cewa gaskiya kawu ita nabeelah ba wanda take son za'a bata ba,kawu yace wannan zancen banza ne dama shi yasa suke boye min to wallahi wannan maganar babu ita,ku tashi mu tafi gidan.... Na tuka mota har kofar gidan muka shiga shi kuwa kawu tun daga kofar gida yake ta fada..yana shiga su mama suka fito suna gaisuwa amma ko amsawa bayyiba ya cigaba da cewar'maganar auren nabeelah babu na soketa yanzu zata fada mana wanda take so kuma goben zan daura mata aure dashi...nabeelah ta kada baki tace'ya mubarak nake so' kawu yayi dariya yace au to ai shikenan ta kwana gidan sauki kuda dan iskanci abin na gidane ma kuke bata lokaci,to ai ni yanxu xan daura auren idan yaso kuje chan kuyi ta bikinku,sannan baba ya shigo yaji meke faruwa amma ba yanda zaiyi da kawu dan yasan halins doe qura ya zama waliyina shi kuma waliyin yamubarak aka daura auren*** take yamubarak ya daukeni muka tafi gidan kunshi daga nan ya kaini nayi kitso muka wuce gidan aunty nafeesat nayi wanka na saka rigar atamfa kaina ba dankwali na fito gareshi,wow nabeelah amma kinyi kyau,ya kamo hannu daga inda yake zaune gefen gadon,ya sumbaceni har saida numfashina ya dauke,ya kwantar dani kan gadon ya fara cire kayan dake.......hakika ban taba sanin haka yamubarak ya iya soyayyaba sai yau,lallai da tuni nayi asar miji,haka muka kasance cikin nuna kaunar juna har zuwaN CIKI book 2 part 1
    ZURFIN CIKI book 2 part 1
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:05
    Abba kwance kan gado,dare yayi nisa amma shi
    ya kasa bacci sam.saboda matsalar da yake ciki
    yanzun. domin kuwa matar shi in yaga bazai iya
    ba sai ya sawwake mata,amma maganar auran
    ummi koda Alhaji bai goya mishi ba bazai iya guje
    mata ba. "yanzun menene mafita?"ya tambayi
    kansa,wata zuciyar ta ce, "kayi shiru tamkar baka
    ga wannan takarda ba,tunda ba wanda yasan ka
    gani." a fili ya ce,"haka ne." ya ci gaba da
    tunanin kila ma yanxun ya janye kudirinshi,tunda
    yaga ummin bata da kan gado. don yaga rubutun
    yayi shi ne tun ranar da aka haifi ummi,ko kuma
    ranar sunanta. tunda gashi har da sunan ummi a
    jiki.mafita kenan yayi shiru.wata zuciyar ta ce,"in
    ko kayi haka kayiwa Alhaji da ummanka adalci?
    koda yar su ba yar adam ba ce bai kamata ka
    gujeta ba.ko don albarkacin son da suka nuna
    maka. shin da ummi ta kasance mai jin magana
    da nutsuwa,kuma mai tsananin kyau zaka
    gujeta? Kada kayi zaton Alhaji yayi kudurin aura
    maka yarsa ne don yasan zata zama mara ji,kayi
    nazari. haka Abba yayi ta tunani har asubah
    tayi,amma hukuncin da ya yanke shine yayi shiru.
    sai dai ya janye batun rabuwa da matar shi,don
    yasan yana sakinta zai zama mijin ummi,kai
    batun nan hadiye ma cikinshi shine mafi dacewa.
    dunkuna masu kyau yayi wa matarshi saboda cin
    suna.haka yayi wa dan siyayya daidai karfinshi,ya
    kawo ma umma. Taji dadi sosai nan ahj ya iske
    su, shima ya shiga dakin umman ya xauna ya ce
    a dauko masa abinci nan xai ci yau.ya dubi abba,
    babana nayi sautun raguna xuwa qauye nace xa
    a siyo nmanya.abba ya ce biyu?umma tace
    hakan yayi.abba ai tuwan girma miyarsa nama,
    aja rago daya xiqal a shiga wannan gida da shi?
    abba yace,me xai hana tunda ban musu qaryar
    arxiki ba sun san mu talakawa ne.ahj yace
    xancanka dutse bacna,amma maganar ummanka
    ita xa a bi, sannan xa a sai buhun shinkafa da
    cefane a kai musu.ana gobe suna abba da
    abokansa suka dira gidan da ragunan da kayan
    mai jego da na yaro sannan ga kayan abinci. sun
    samu anty a gidan,ta musu tarbar mutunci.da
    yake abba xana waya da ita,ya fada mata komai
    ta sani.hjy zainu da taji kukan raguna ta fito,anty
    tace dan Allah momy kada ki musu magana,kin
    ga shi da abokansa ne.da qar ta samu ta turata
    sashin ahj,shi kuma murna yayi yace aje a daure
    su.zainu tace ahj menene na numa farin ciki sai
    kace ba ma cin nama?can ba xa a ka kada ba
    dan kawai shagalin sunan, sannan tace harda
    shinkafa suka kawo sai kace muna yunwa? nana
    take ya hade rai tare da cewa,zainu kada dai ki ce
    min kin sa an dawo da yarinyar nan gidan ne dan
    ki kashe mata aure?tace haba dai. ya ce to hir
    dinki dan bansan in kuma jin irin xantukan nan
    yayi ma matarsa daidai arxikinsa. mu kuma mu
    ma yarmu da jikanmu gwargwadan arxikinmu,in
    ya fito daga gun mai jegon ki turo min shi,sbd mu
    ji in da xa a yi sa sunan.tace ina xa ayi in ba nan
    ba?ya dube ta an taba haka?ki dai turo minshi.ta
    taba baki sannan ta wuce.lkcn da ta leqa dakin
    abba da abokansa suna xaune,abba yana ta fama
    da danne dannen waya,domin tun da suka shiga
    ya qi ko kallan inda bishira take bare danta.tace
    bishira ki eada musu in sun fito ahj na san
    magana da su.ta wuce ba tare da jiran jin amsa
    ba,ko amsa gaisuwan da abokan abba suke mata
    bata yiba.bishira ta kalli abba wanda tana
    hankalce da shariyan da yayi mata,tace kaji abin
    da momy tace?sai lkcn ya dubeta me tace? yayi
    maganar ne cikin tsare gida.dadynmu yana san
    ganin ku. bai amsa ba,sai kurun ya tura mata
    jakar kayanta,ki duba,ta xaxxage dinkuna ne na
    gani na fada masu kyau,duk da xannuwan ba
    masu tsada ba ne kala uku atamfa daya shaea
    daya sai kuma leshi.sai ko kayan yaron.ta dube
    shh an riga an sai mana kayan fitar
    sunanmu.ahmad ya dube ta wannan din baki so?
    tace ni bance ba.abba yace ku tashi muje.tace
    ina san magana da kai.ya ce kiyi
    maganarki.muktar yace kuxo mu fita ta dauki
    yaran tare da miqa mashi ta ce ina lura da kai
    rabon da ka dauke shi tun randa aka
    haifeshi,alhalin mu kuma yana nan yana hana mu
    baccin dare.kai kana can kana baccin ka.ta fadi
    haka ne cikin sanyin murya.ya amshi dan tare da
    cewa ai gara ya hanaku bacci tunda kunqi ku
    kaishi gurin babanshi.ya tsura ma yaran ido,wata
    qaunan dan ce take shigarsa.ta matso
    jikinshi.abba ya kalli furkarta,ita ma kallansa
    take,ta ce yanxu ko dan murmushin ka bana
    gani.yace,in da kina san gani da baki dawo ghda
    ba.yaci gaba da cewa na sha mamakinki
    bishira,da har xa ki yarda ki dawo gidanku ba da
    ixinina ba. kuma tun kafin ki haihu sai da na fada
    miki ba za ki zo gida ba.Ta ce To Abba mony ce
    ta ce sai an zo. Ya ce shi kenan ku zauna. ya
    mike mata yaron ta amshe shi ta kwantar ta
    kama mishi hannu. Abba wane suna ka sa masa?
    ya ce Sunan Alhj babba. Da sauri ta saki
    Hannushi . Sunan 'yan da? ya kalle ta Na zaci
    zaki ce suna mara ma'ana,tund da ne da sauki.
    ya fice. Haushin hali irin na Bishira ya ke ji.dn
    son shi yasan tana matukar sonshi,amma bata
    son yin biyayya ga abn d yake so. Ya samu su
    Mktr sannan suka shiga gurin Alhj ya tambaye su
    in d za a sa sunan,Abba ya ce a masallaci kusa d
    gidn babnshi ne za a yi addu a. Amma tuni an sa
    wa yaro suna Sulaiman.sunan babana. Alhj ya ce
    Madalla Allah ya raya mana shi, ba sai mun zo
    ba dn yanayin sanyi ne. Nan dai Abba d
    abokansa suka tafi suna yabn Alhjn. An ci sunan
    shima Abba shi d abokansa sun yi walima da
    Azahar. matar abokinshi Bala ita ce suka bai wa
    girkin ta yi masu. Mai jego taci gaba d wnk. Abba
    kan leka su lkc zuwa lkc,kusan dk lkcn d yaje ba
    su cika rabuwa d dadi ba sbd mgnr d hjy zainu kn
    datsa mishi. Umma shi ma bata yi fushi ba tana
    leka su dk d rashin sakar mata fuska d mai jegon
    tare d mahaifiyar keyi. Ummi tana tafe tana 'yan
    tsince-tsincenta,kmr yadda ta saba,sai ko taga
    sim,take ta yarda dk wani abu d t samu t dauki
    Sim din. Gefen zaninta t samu ta kulle,sannan ta
    tafi,cikin jakr mkrntrta t saka.wata rana ta dauki
    wayar umma ta shige daki,ta bude wayar ta cire
    sim din ta saka wanda ta tsinto a cikin zani ta
    soke wayar ta fito soro.Jikin dakin yaya Abba a
    bakin kofar ta dauki lamar Abba da ya rbt sbd
    masu zuwa nemanshi tana kira taji wayr tana
    ringing. Ta kashe tana ta dry,hk tayi ta yi wa
    Abba Flashing dg nan tayi gidn du Amina
    kawarta,tana ba wa Amina lbrn abn d ta ke wa
    Abba. Ta ce Amina nsn yanzun hk yana cn yana
    jin haushi,shi yasa ki ka ga ina murna.Ta ce in ya
    gane fa?Ummi ta ce Ai tsintar sim din nayi,Umma
    kuwa ba za ta san na dauki wayarta ba,domin
    yaya Abba da Alhjnmu kawai suke kiranta. Amina
    ta ce Yadda za a yi ki kira shi ne in ya dauka sai
    ki make murya ki canza suna. Ummi ta ce Tab,dn
    in ci duka. Amina ta ce Dalla cn gane ki zai yi?
    suka kira ya daga ummi ta sirantr d muryarta
    tana fadin "Hello! Abba ya ce Ke wace ce ki ke
    kiran layina? Ta ce Sunana '"Suhaila. ya ce
    Menene ki ke kirana?Ina ma ki ka samu lambata?
    Ta ce Gani nayi ni ma a cikin wayr. Tsaki yaja
    Sannan ya kashe.Suka dinga tsuntsira dry. Amina
    ta ce Sake kiranshi ki ce ma ke a kaduna ki ke.
    Ummi ta ce Kai yin waya akwai dadi ni ina son
    buga waya. Ta sake kira cikin Zafin rai ya ce Ke
    lfy??kin dame ni fa!Ummi ta ce To tsaya mana
    kaji ina son mu gaisa ne ni ina kaduna ne. Ya ce
    To na gode. Sai ma ya kashe wayar gaba daya
    suka yi ta kira a kashe. Tun daga ranar Ummi ta
    samu in umma tana aiki ko tana bacci sai ta sace
    wayar ta cire sim tasa nata ta kira Abba. Tun
    yana kyararta hr ya daina ya koma rokon ta
    daina kiranshi,dk a banza. Daga baya sai Abba ya
    soma sauraronta, ranar kuma ta kira shi ne
    misalin dayan dare,ranar taki zuwa dakin
    Tsohuwa ta kwanta a dakin umma. umma kuma
    dama dakin Alhj take kwana. A dai-dai lkcn ya
    kwanta kadaici ya dame shi,ga garin yanayin
    sanyi. wayar ta katse tunaninshi d yake yi na
    matarshi zuwa yanzu ya haddace lambar Suhaila.
    Ya daga ya ce "Hello ya ce Ke wai me ya hana ki
    bacci?Ta ce Ni ba sunana ke ba,Ni sunana
    Suhaila,kai fada min sunanka. Ya ce Abba Ta
    danne dryr d taso kwace mata ta ce Abba ba
    suna bane,Fada mn sunanka n gsky. Ya ce "Idris
    Yadda ya fadi sunan sai da ta dage kwarai
    sannan ta maida dryrta. Ya katseta d cewa Ina
    ku ke a kaduna?tayi dim,dn dai bata san ko ina
    ba a garin kaduna ba,ba ta ma ta6a zuwa ba.
    Take ta tuno Amina sun ta6a zuwa unguwar
    Sarki,dn hk ta ce "Unguwar Sarki. Ya ce, wai
    shekaranki nawa? Ta ce Sha takwas. Ta sheka
    masa karya.Ya ce Amma shi ne a ka ba kiwaya?
    ta ce ta ka san wanene Babana? Ya ce A"a ta ce,
    To shi ne mai bawa Gwamna shawara a jihar
    kaduna. Abba ya ce Lallai, ki ce in nazo kawo
    miki ziyara ba zan samun ganinki ba? Ta ce za
    ka ganni mana. Ya ce To zan zo. Ta ce To, Ya
    ce,Amma fa ina d mata ta haihu ne ta tafi
    wankan gida. . Ummi ta ce Lallai to sai da safe.
    Ya ce, Wa ke zuba miki kudi ne cikin waya?Ta ce
    Babana mana. ita sai lkcn ne ma ta tuna cewa
    ana saka kudi tunda ta ke kira bai taba kin zuwa
    ba,aranta ta ce kila wannan ba a sa kudi. Sunyi
    Sallama babu dadewa,wayar ta sake daukar
    tsuwwa. Ga zaton Ummi Abba ne sai da ta daga
    sannan taji muryar wani. Ya ce Da wa nake
    waya? ta ce wa ka ke nema?Ya ce Me wayr. ta
    ce Ummata ce kuma tayi bacci. Ya ce Yallabai
    nake nema. Ta ce Ban san wani yallabai ba,kada
    ka dame ni Ta kashe wayar tare da jan tsaki.
    Sannan ta cire layin ta maida na umma Wasa-
    wasa cikin kwanakin Abba ya soma damuwa da
    lamarin Suhaila kaduna, lokuta da dama ya kan
    kira layinta amma sai ya ji shi a kashe. Sam ba
    ya samunta sai lkcn d ta kira shi,ko da ya yi
    mata korafin hk,sai ta ce "Eh ita ce ke kashe
    layin sbd ana damunta. Sun yi jarabawar (J. S.
    C.E.)sakamako suke jira. dn hk yanzu tana gida
    ko yaushe tsokana kuwa bata fasa ba. Kullum ita
    d Amina cikin shirya yadda za su yi wa Abba
    waya suke, kudin cikin layin ya kare,Abba shi ke
    tura kati yanzun. Duk lkcn d Abba yazo gidansu d
    ya ga ummi ya hade rannan yana muzurai,ita km
    sai ta yi ta sheka dry,dmn tana tuno yadda yake
    kwantat d murya a waya. Wata rana hr duka ya yi
    mata sbd dryr d ta dinga yi daga sallamrshi a
    gdn. Tsohuwa kam ranar yini tayi fada,wai ita za
    ta bar gidan.Cin kashin d ake yi wa ummi ya yi
    yawa. A ce rashin 'yancin yakai ko dry ba a son
    tayi. Da kyar umma ta sha kanta t hkr. Wannan
    ta kaicin dukn yasa ummi tace ita kam sa tasa
    shi wahala. dn hk ranar gdn su Amina taje. suka
    shirya yadda in ta kira shi zata ce yaxo Kd ta
    ganshi, ummi ta ce mugu dama in yaje ya 6ace in
    huta. Hakn kuwa ta fada mishi, a ranar d suna
    waya. Ta ce '"Idris.dn Allah yaushe za ka zo ne?
    Ya ce Tun yaushe Suhaila nake cewa zan zo
    amma kin ki,to yanzun yaushe zanzo? ta ce kazo
    Juma'a ya ce A"a zan dai zo Asabar,Juma'a
    rabin rana ce. Ta ce,To sai kazo.Nan d kwana 4
    kenan?ya ce Insha Allah,sannan ina son ki toro
    min da adireshin dn gdnk,sannan ranar d zan zo
    ki bar wayarki a kunne. Ta ce To." Ranar Asabar
    misalin goma na safe Abba ya shigo cikin sabbin
    kaya,ya yi matukar kyau tamkar sabon Ango.
    Umma ta ce za ka je gurin su Maigida ne?Ya ce
    A"a umma koda yake zan bi ta can.Kd zan je.
    Umma ta rike baki "Kd,? Me a ke yi?ya ce sai na
    dawo za ki ji.Ummi d ke wanke-wanke ta kwashe
    da dry. Umma ta dirma mata dundu tare d
    cewa,Ke wai ciwon dry ne y kama ki?Abba ya
    dubeta cike da tsana. Ummi ba za ki shiga
    hnklnki da ni ba?ta sunkuyar da kai tare d maida
    dryrta ciki. Sannan ta ce Yaya Abba dn Allah ka
    siyo min biredi,wlh biredin Kd dadi ne da shi.
    Lkcn d Amina suka dawo ta sammin. Ya galla
    mata harara,tare d fadin an ce miki nima bakauye
    ne irinki?In ma ki ka sake min mgn sai na gabje
    ki. . Ya kalli Umma Kada ki ce ma Alhj nayi tafiya
    amma in na dawo zan fada masa. ta ce ,To" Allah
    ya tsare. Abba ya fita. Ummi tana gama wanke-
    wanke ta shige daki dn yin gyaran gado. Umma
    na shiga kicin itama ta fito falo ta ciri wayr a caji
    taje ta saka sim. Take kuwa kiranshi ya shigo, ta
    daga ta matse murya kamar yadda ta saba, ka
    taso ne? ya ce Ina mota mun kusa tasowa. Ki
    turo mn adireshin. Ta ce Ba fa wahala,d kun
    sauka tasha sai ka ce a kawo ka unguwar sarki
    gidn mai ba Gwamna shawara. Ya ce Suhaila ma
    su ba Gwamna shawara d yawa Ta ce Um to ai a
    nan unguwar Sarki shi daya ne. Ya ce Ya sunan
    layin?ta ra sa me zata ce,gabnta y shiga
    faduwa.Ta samu kanta da cewa, Abuja Ya ce
    Abuja kuma Suhaila?ko dai Abuja road? Ta ce Eh
    gida mai lamba 6. ya ce To zan ci gaba da kiran
    layin. ummi ta ce To," Ta zauna tana sauke
    numfashi. Tab da ya dogata d ta bani,Sannan ta
    saka dry murna take yau yaya Abba zai sha
    wahala. Jefi-jefi ya kan kira ya ce sun zo gari,dk
    lkcn d ya kira in ta ji ringing sai tayi bayi da
    gudu, har Tsohuwa da suke zaune tare ta ce, ke
    takwara gudawa ki ke ko atini ne? Ta yamutsa
    fuska, sannan ta ce Bacin ciki ne. Tsohuwa ta ce,
    To taso uwarki ta baki magani. Ummi ta ce ya yi
    min sauki ma. Can kuma masu kiran layin suka
    kara kira. Ummi tayi kofar gida ta daga wayar a
    ka ce ke ina ki ka samu wannan wayar? Ta ce
    Oho 'yan rainin wayau kada ku sake kirana. Ta
    kashe wayar ta koma gida. Lokacin da Abba ya
    ce sun shiga KD har ma sun kusa sauka, sai ta
    cire layin ta ci gaba da harkokin gabanta ta
    manta ma da labarin wani yaya Abba. KADUNA
    Abba suna sauka a tashar kawo, ya sauka ya
    shiga raba ido yana kallon garin kaduna. Yau ce
    rana ta 2 d ya ta6a zuwa KD, daman sun zo
    daurin auran wani abokin su bara waccan. Ya
    kalli wani dan aca6a sannan ya yafito shi da
    hannu. Ya iso yana cewa Ina za ka? ya ce
    Unguwar Sarki. Dan aca6a ya ce Wane layi? Abba
    ya ce Abuja Road. Ya dubi Abba Rigasa kenan,
    unguwar Sarki babu layi mai wannan sunan.
    Abba ya ce, Ina zuwa, bari dai in kirata. Koda ya
    kira layin Ummi sai ya ji shi a kashe, yana ta kira
    a kashe. Ya dubi dan aca6a ya ce, Kasan gidn
    Mai ba Gwamna shawara? Dan aca6a ya ce, Hau
    dai muje sai mu tambaya. Abba ya hau mashin
    yana mai ci gaba da nemn layin Suhaila. Sun
    zagaye unguwar Sarki layi-layi suna tambayar
    masu gadi da 'yan dai-daikun mutanen da ke
    giftawa kasancewar unguwa ce ta manyan
    mutane, daga karshe dan aca6a yaba Abba
    shawar ya tafi gida kawai. Don haka sun gama
    zagayen unguwar Sarki har da makotanta, amma
    ba su samu ba. Gida daya ne aka ce musu da
    akwai Suhaila, amma yarinya ce ta goye. Kusan
    karfe 3 sannan suka koma tasha,ya biya dan
    aca6a, sannan yaje ya yi sallah. Zuciyarsa cike
    da takaici sai yanzu yake Sallah. gashi ya kasa
    samun layin Suhaila. kila ma tana sane ta kashe
    wayr dn kawai ta tazarta shi. Ya tuna d zagin d
    wani mu2m ya masa lkcn d suka tambaye shi ko
    ya san ina ne gidan mai ba wa Gwamna
    shawara? Mutuminya ce,mai ba Gwamna
    shawara a kan me? Ma su ba da shawara suna
    da yawa, ya sunan layin da ka zo? ya sunan mai
    gidan? kama ina lambarsu? Abba ya ce, Lambr
    kadai gare ni,km taki shiga.Mutumn ya ce,"Amma
    kai soko ne,gashi kmar wayayye.Ya ja tsaki ya
    wuce. Shi kanshi sai yanzu yaga wautarshi. ko
    me ya kawo shi gurin yarniyar?Shida dai ba za
    ya ce sonta ya keba,km ba ya ce ba sonta yake
    ba. Wani ma ya zaci dn kudi ubanta yazo,shi kam
    in ya koma shiru zai yi ko abokanshi zai ce musu
    bai gane ba kawai,dn yabi ya fada musu lbrn
    Suhaila,sun km san d batun zuwanshi gurinta
    sarai,km yasan hlinsu za su maida abn na
    tsokanarshi. Cikin matukar takaici suke tafe cikin
    motar kaduna zuwa kani,sun zo kwanar Dangora
    tsautsayi ya akfa musu. in da tayar motarsu guda
    ta fashe. . Nan take motar ta bar hannunta ta
    mulmula da su suna ta salati,nan aka kwashe su
    xuwa asibiti.wasu sun mutu take,wasu sun yi
    dogon suma.masu waya ta cikin wayarsu aka yi
    ta kiran yan uwansu,shi ma abba a cikin wayarsa
    aka kira lambar ummanshi da alhj da sauran su
    aka shaida musu cewa mai wannan layin sun
    samu hadari,kuma an kawo su asibitin mlm
    aminu kano yanxu.iyakan rudewa su umma sun
    rude,tsohuwa kam take cikinta ya kada ta soma
    xagawa bandaki tana kuka tana face
    majina.ummi bata gidan tana can gidan su amina
    suna ta hira suna cin dariya ,tace bari in je in
    qara sa layin in ya kira sai ince wayata chaji ne
    sai yanxu nayi.sadaf sadaf ta shige daki,kan
    kujera taga wayar,ta dauka ta saka sim din ta
    cire wancan. tana kunnawa sakuna suka soma
    shigowa. kafin ta bude ta duba sai ta jiyo muryar
    tsohuwa cikin kuka tana cewa wannan yaro ashe
    ajalh ne ya kira shi,ko me xashi yi kaduna?ni ban
    sani ba.ummi ta fito da sauri tana cewa,tsohuwa
    me ya faru?tace ba kina can gun yawanki na
    tsiya ba.Mai sunan mlm da ya tafi kd sun tafka
    hadari, yanxun haka suna asibitin mlm. ana xatan
    shi ma ya mutu.ummi ta saki ihu,sam bata san
    ta damu da dan uwan ta abba ba sai yau,ko tana
    kukan ita ce sila?oho.kafin kice haka,lbr ya watsu
    a unguwa abba ya mutu.cikin kuka ummi ta
    tambayi tsohuwa ina ummata? tace tare suka
    nufi asibitin da ummarku.taqi yarda ta jira
    su.ummi tana jiyo ihun kukan umman bashir ta
    xaga gidan.gidan ya rincabe da kuka,ummi fa
    hankalinta ya qara tashi.matarsa ta iso da kuka
    da yan uwanta a motoci.yayyantamaza suka nufa
    asibitin.can kusan qarfe takwas su alhj suka
    shigo.alhj ya ba mutane haquri,ya ce bai mutu ba
    dogm suma yayi.kuma Allah yayi taimako ba
    karaya.likitocin sunce xast duba shi xuwa gobe
    su gani.nan ko jama'a suka dinga fadin
    alhamdulillah.ummi ma tadan ji dadi a
    ranta,sanna fa kowa ya tafi dama wasu sunce xa
    stje yin sallah su dawo.saida suka koma sannan
    suka taho da umma,ummi cikin kuka tace umma
    da gaske bai mutu ba, umma tace eh bai mutu
    ba,muyi magana dashi. . Umma tace in sha Allah
    gobennan xai dawo gida. ummi tace to,umma
    tace kinga wayata? gaban ummi ya fadi ta tashi
    da sauri ta shiga neman waya,taci sa'ar ganin
    wayar,sai dai bata san inda ta saka sim din ba
    sai wanda ta tsinto ne a ciki.ummi dai tayi shiru
    ta miqa ma umma waya. kusan qarfe goma sha
    daya wayar abba da umma ta taho da ita ta
    soma qara,umma ta dauka.alhj ne ya ce ina
    wayarki ina ta kira ana cemin a kashe?una tace,
    a ku6e take gata ma a hannuna.yace to inata
    kira.tace qila faduwan da tayi daxu ne ta samu
    matsala.yace to dama zance ne ki dafa masa
    ruwan xafi a xuba a flask dan uwan matansa xai
    kawo mu yanxun a mota xai amsa ya kai.ta ce to
    alhj wayn xai kwana gunsa?yace bashir na nan
    kuma matarsa anyi anyi ta qi tafiya shi yasa na
    haqura xan dawo dan ba na xauna gun su ba ko?
    umma tace amma yaya jikin nashi?ya ce da sauqi
    yanxu ma yana son shan tea ne.tace to xan hada
    harda wayar tasa inya so ma dunga kiran shi
    kafin gari ya waye.ya ce yauwa ki
    bada.Alhamdulillah abba jiki ba matsala. Don hk a
    ka sallamo shi zuwa gd.kai tsaye gdn su umma a
    ka wuce d shi. A salin dakinsa a ka gyara a cikin
    kwana nan 3 ya yi ras sannan ya koma shago.
    Bishira kuwa lkcn mahaifinta ya ce maza ta koma
    dakinta,tunda ga abn d ya samu mijinta.Sun
    dawo hr da tafkeken injin Janareto wai yaron ba
    ya son duhu. Sannan ga kayan kallo d
    saraunsu.TabbasAbba ya ji dadin dawowar
    iyalanshi,dn dama yana cike d bukatarsu. Ranar
    yini suka yi gyaran gd ita da 'yan uwanta,sai byn
    magrib sannan ya shigo d tsarabobi.madara
    tatacciya da kaji. Ya dauki dansa cikin jin dadi
    yana kallonta cike da so da kauna,Nayi missing
    din ku da yawa.URFIN CIKI book 2 part 3
    ZURFIN CIKI book 2 part 3
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:08
    Ai bama shiri. shi ne fa ya kawo ni mkrntr kwana
    dn kawai baya son ganina. Suka yi ta mamaki.
    Can jimawa ya dawo, sun fito rakiyar 'yan
    uwansu Safiyya da na Khadija, suka ganshi tsaye
    yana danne- dannen waya. Ya taho ya gaida
    iyayensu duka,sannan suka koma gefe d ummi,
    ya ce Ni ma zan tafi. Ta ce, Ya Abba ko fa
    gaisawa ba mu yi ba. Ta karkatar da kai,Cikin
    raunin murya tamkar mai shawagaba,ta ci ga ba
    da cewa Ya Abba su Umma ba wanda ya ce a
    gaishe ni? Sai hawaye suka soma zuba.
    Hankicinshi da ke hannunta tasa tana sharar
    kwalla.Abba yana da matukar tausayin mace. Don
    haka duk da tsanar da ya yi wa Ummi sai da ya
    tausaya mata.Ya tausasa Murya. Sun ce in
    gaishe ki sosai, za ki ga gyada mai gishiri,
    Tsohuwa ta ce a ba ki.Umma ta miki miya, ta
    kuma daka miki yaji. Ta ce Na gode, Alhj me
    yasai min?ya ce kayan tea ne da lemun kwali. Ta
    ce Na gode. Tana ci gaba da share hawaye. Ya
    mike Zan tafi. yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi
    ya mika mata, ta ce A'a ya Abba ka bar kudinka.
    Ya ce Ba ni ne na baki ba,Alhj Karami ne ya ce in
    ba ki. Ta sa hannu 2 ta amsa tare d godiya.Sun
    raka shi kusa da Gate ita da su khadija,sai kuka
    Ummi ke yi. Bayan sun dawo dakinsu ne ta zauna
    tana duba kayan da ya lissafo mata,duk ta gani.
    Sai kuma saitin sabulun wanka da manshi da
    turaransa da hodarsa duk na (Aloe vera.) Shi
    kuma bai fada mata ko daga wa ba,ko ba komai
    ta dai yi murna sobada tana da 'yan kuraje a
    fuska,tasan kuma za su mutu. Sai kuma audagar
    mata,tayi dan murmushi. . Tunda Umma taji
    sallamar Abba ya shigo dakin ta bar komai tazo
    ta zauna tana son jin lbrn Ummi. Abba ya fahimci
    Haka,dn haka sai ya boye mata cewa, Ummi na
    kuka hr yanzun. Ya nuna mata ai Ummi ta
    kwantar da Hankalinta,km tayi hnkl dn ya bincika
    ya ji ana ta yabonta. Umma taji dadi Sosai,Sai da
    ya fara zuwa gurin Ummu,sannan ya je gida.Ya
    samu Bishira tana zaune tana aikin nata,wato
    Kallo. Tun da ta dawo daga wankan gida tazo da
    janareto da kayan kallo,shi kenan ta sanu abn
    yi.Kullum tana gabn (TV)da ta shi da safe in ta
    kokarta shi ne ta dafa ruwan tea ko wanka ba za
    ta yi wa dan ba,sai lkcn d man injin ya kare. Ya
    nufi gurin injin ya kashe,dif din da ta ji komai ya
    tsaya shi ne yasa ta zabura ta mike tana fadin
    Ba dai har man nan ya kare ba? Ta fito da niyar
    dubawa.Abba ta gani tsaye gabn injin yana bn
    tsakar gidan da kallo cikin takaici. Ta ce Baban
    Walid kashe min injin kayi??Ya ce Eh na kashe dn
    Allah dubi gidanki?kalli wanke-wanke kuda na bi
    dubi tulin wankin kayan Fitsarin yaronki. Dubi
    kicin dinki,kuma ko da bn shiga dakinki da
    wannan falon da ki ke kallo ba.na tabbata da
    wanda ki ka dauke ko tsinkw a cikin sa.Kila ma
    ba ki yi Sallah ba. Ta ce Dan karashe ne fa ya
    rage min in gama kallon in zo in yi aikin.Haushi
    ya sake kana shi,Sai kurum ya shige daki.
    Tsakuwar da ya dora kafa a kai tasa tsigar
    jikinshi tashi,sam ya tsani ya shiga daki ya dora
    kafa kan datti. Ya dawo yasa takalmanshi ya
    shiga da su,Walid yana kwance tun kayan da ya
    bar shi da su da safe sune a jikinshi yana ta
    bacci cikin fitsarin da ya shafka wanda ba wata
    leda da zata hana katifar ta jike. Ko wankan safe
    ma ba a mishi ba kenan.A fili ya ce,",Inna lillahi
    wa'inna ilaihinr raji'un. ya juya ya nufi shagi. Ita
    kam sai ta kunna injinta ta karasa kallonta,
    sannanta tashi ta dora girki.sai lkcn ta ma Walid
    wanka. Ta dan dauraye kwanukan da za su ci
    abnci,wai ta gaji sauran wanke-wanken sai gobe.
    Fati ta shigo,Bishira ta ce Yauwa Fatima naji
    dadin zuwanki.shuga dakina ki gyara min gado,ki
    dan yo min shara. Fati ta ce To. Ta shiga ita ma
    duk shegiyar darin ce gurin kuiyar aikin,dn haka
    ta dan birbira ta fito ta ce ta gama. Bishira ta ce
    Yauwa dan dauraye min kaya can na Walid. Nan
    ma tasan sama ta shanya. Bishira ta ce Yauwa
    ta ga abnci nan kici.sai ki dauki na Ummarku ki
    kai mata. Har Fati ta kai waje,Bishira ta kwala
    mata kira. ta ce,Zo ki tafi da wannan galan din
    na man fetir kije shagon Babn Walid kice ya taho
    mana da shi,dn man ya kare. Koda Fati ta same
    shi da galan ta fada mishi sako ya ce Ba zan siya
    ba,Maida mata galan din. Ta tafi,Shi kuma ya ci
    gaba da mita a zcyrshi. Yana fadin Na daina
    sayan man tunda ba za a bari sai dare a kunnan
    ba.Gidan Ummanshi yaje,ba ta nan ma taje
    barkar Haihuwa. Ko dakin Tsohuwa bai shiga
    ba,ya zauna nan falonta.Ya za kula ya zuba
    abncinshi ya ci.sannan ya dan huta sai ya fita
    zuwa gidan su Ahmad. Cam ya samu wasu daga
    cikin abokanshi suka shiga hira. Ranar dai Abba
    bai je gida ba sai misalin sha daya ko daya shiga
    bai nemi matar gidan ba,ya dibi ruwa ya yi wanka
    sannan ya shiga dakin. Ya lalibo makunnan wuta
    ya kunna,dn Nefa sun kawo wuta. Tana kwance
    irn banzan kwanciyarta da ta iya,dakin sai tashin
    wani irin wari yake kamar na ruma,kamar na
    fitsari ko na datti.Ya kalli ko'ina kullin kaya ne na
    wanki ne,na gaga ne ciki da guri.Ranshi ya
    baci,Ya kuma dubanta ga wata kiba da ta tafka.
    Tun da ta haihu ta zama rusheshiya,gashi bata
    son kama jikinta.Tsaki yaja,sannan ya dauki fiko
    ya fita. kan doguwar kujera ya jefa filo,ya kwanta
    a gajiye.Amma me?sai ya ji dora gadon bayansa
    acikin lema.Da sauri ya mike ya kunna wuta.Duk
    fitsarin yaron ne a kan kujerun dakin,dn haka sai
    ya nufi dakin da takw aje tarkace ya kunna
    wuta,shi ma dai duk shirgi. . Ya share Ya
    shimfida ta barma ya kwanta,a ranar ya dauri
    aniyar maida dakin ya zama nashi din-din-dn.
    Don haka washegari yasa a ka zo a kayi masa
    fenti,ya siyo kati fa ya yar da zanin gado,dk wani
    abu nashi sai da ya kwashe su. Kafin wata guda
    ya maida dakinshi cikakken daki,ya zuba dk wani
    abu da yake bukata. kafin ya fita kullum sai ya
    gyara dakinsa fes. ita kuma sam bata zuwa
    dakin,sai dai in yana da lalura yaje can ya sauke
    ya dawo. kazantarta kam ta kai in da ta kai,tunda
    hr kayan kashi tana zube su a cikin daki. Ya gaji
    yaje ya samu Anty ya fada mata,hr gidan Anty
    tazo ta zazzageta,ta tasata suka gyara gidan,
    amma ko a jikinta.Washegari ta ci gaba da in da
    ta tsaya. Sam babu wanda zai ganta ya ce
    haihuwarta daya. ¤¤¤¤¤¤ ¤¤¤¤¤¤ UMMI yau
    ba wanda ya kaita murna,domin yau dai an basu
    hutu..Sai dai tunaninta zata ko iya kai kanta
    gida? Sunyi ban kwana bata da kudin mota, dan
    duk tayi taba su safiya kudin gurinta, amma ta ce
    yau ko da qafa ne xata gida.sun fito wajan mkrt
    wata maryam tana cema,ki tsaya mota xato da
    xata kaimu cikin kn.ummi tace baxan jira ba.sai
    ga abba kamar daga sama,tsoro ya kamata karya
    ce ta xauna gidan abokin sa da yace.hanka linta
    ya tashi cikin in ina ta gaida shi ya amsa.ya
    shiga mkrtn jim kadan ya dawo.hakan ta sha
    alwashin yau ko da shiya saita je gida.shi kam
    ma ya manta yai mata wannan maganan ma.ya
    sabi akwatinta suka je suka shiga mota. abba
    mamakin natsuwan ummi yake yi, ko da yake
    baxai ce ta natsu ba, qila lafawa tayi.tundaga
    soro ta saki jakanta da bokin tayi ciki da
    gudu,cikin kuka tana kiran ummanta.umma ta
    share do min tsohuwa tana cikin gida,kada tace
    tayi rashin kara,sai tsohuwa ne ta tashi da sauri
    tana fadin oyoyo takwara.suka qungume juna
    tace to menene kuma na kuka?umma ta fito nan
    fa ummi taje ta rungume ta.sai umma ta doje
    tace bubi shirme,sakar ni ni.tsohuwa tace haba
    suwaiba yarinya tana dokin, . Tsohuwa tace haba
    suwaiba yarinya tana dokin ganinki amma ki
    gwasale ta? abba ya ce daman nasan ba
    natsuwan da yarinyan nan tayi,har ina
    yabonta.dubi yanda ta xubarda kayan a soro.to
    xaki debo su.tsohuwa tace bari ni in debo mata
    tunda kai baka da tausayi.laile umma taga
    canji,do min ummi dai tunda ta dawo ko qofar
    gida bata fita ba,sai ko in an aike ta.sannan
    yanxu ba gudu da tsalle tsalle bare tsokana.ga
    aiki har girki ita kema umma komai.alhj yana
    shan shayi da safe,ummi ta yi sallama ta shiga.
    can gefen su umma ta xauna,sannan ta gaida alhj
    ta gaida umma wanda ta saka alhj agaba tana
    masa fira.wannan qa'idan umma ne bata barin
    mijinta shi kadai,in har yana gida.alhj yace
    suwaiba kinga ummina ko?laile abba yayi namijin
    qoqari. yarinya ta natsu.umma tace Allah ya
    amsa addu'an mu ka duba tsayuwan daran da
    muka dunga yi bayan tafiyan ta kan cewa Allah
    ya kintsa mana ita.alhj yace hakane,ummi dai na
    jinsu tana murmushi.can tace alhj anjima xanje
    gidan inna saratu in gaishe ta. qanwan sahura ce
    da ke aure a kabuga.ya ce to ummi, xanba
    umman ki kudin mota ko? ummi ta ce,to na
    gode.ta miqe ta fita ta bar mahaifanta cikin farin
    ciki jin dadin natsuwarta, suna godiya ga Allah
    mai shirya bayinsa.lkcn da ta shirya dan xuwa
    kabuga.sai umma tace ki kwana dan bana san ta
    fiyan yamma,kabuga da nisa.tace to sannan ta
    dauki kayanta kala guda, sannan ta fito.har xata
    wuce sai ta shiga gidan alhj qarami,sahura na
    ganinta ta hade rai,daman daqar take amsa
    gaisuwan ummi tunda ta dawo.ummi ta gaisheta
    a ciki ta amsa,sam ummi bata damu ba,tace
    umma ina fati?ta yatsine baki tace tana gidan
    abba,tace to inta xo ki ce mata naje kabuga sai
    gobe xan dawo.umman bashir tayi tsaki,tare da
    cewa ni yar aiken ki ne?ita dai ta wuce.tun
    dawowan ummi suke shiri da fati kamar me,ko
    yaushe suna tare suna fira.ummi tana mata
    labarin mkrtn su.ita kuma fati tana bata lbrn
    saurayin da tayi fahad,da irin son da take
    masa.ummi tace tab,ni ko xanyi saurayi nafi san
    irin ya abba...... . fati ta dubeta da al'ajabi kina
    nufin ya abba kike so?ummi ta xabura tana fadin
    tir, ko a mafarki Allah ya kyauta.ina nufin mai irin
    hirarsa da tsafta.fati ta qyalqyale da dariya tare
    da cewa ai na xaci shi kike cewa,inko ya ji kici
    duka ummi ta ce,ai ni ba ma da shi nake ba
    tab,shi da yayi auran so?kusan ko yaushe
    yanayin hiran tasu kenan.ummi tana tafe
    wadansu samari suka yi ta binta, sun shawo
    kanta ta tsaya da kyar,kuma har ta masu
    kwatancen gidansu. kwanaki uku bayan haka tana
    ki shingide kan kujeran dakin umma,misalin
    takwas saura ma dare.krtn wani littafi take yi na
    hausa da fati ta ara mata,sam ita bata taba krnt
    irin littafin ba,amma fati ta ce mata ta karanta da
    dadi sunan littafin NAGA TA KAINA na
    (sodangi).kasance wan wannan ne karo na farko
    da ta taba krnt lbrn soyayya,sai abin ya
    birgeta.amma nata ganin gwarxon sojan nan xai fi
    dacewa a ce abba ne, jefi jefi takan kalli abba da
    ke xaune kan kujera kusa da umma suna wani
    xance da bata jiyo su. 'Amma tasan ko me suke
    tattaunawa mai mahimmanci ne a gare
    su.sallamar wani yaro ne ya katse su,umma da
    abba suka amsa mishi a lkc gudu.yace wai ana
    kiran ummi a waje inji wadansu.da sauri abba ya
    kalla yaron,sam ba xai ce me yasa xance yaran
    ya fadar masa da gaba ba.sai ya lumshe ido
    sannan ya kalli ummi wadda kunya ta rufe
    kasancewar yau ce rana ta farko da aka soma yin
    sallama da ita.umma wadda kullum fatanta ummi
    ta samu miji,sai tayi murmushi,sannanta ce da
    yaron kace tana xuwa.abba ya dube ta da sauri,
    umma kin san ko su waye?ta ce, a'a.yace ya
    kamata a san ko su wanene dan kin san bata da
    kan gado,kowa ma sai ta jajibo kuma ma duk
    nawa ummin take da har xata soma tsayawa da
    samari?umma tace,to abba ai gara ta kama
    dahir, tana qare sakan dire ba sai ayi mata aure
    ba?yace gaskiya umma gara ta dan taba krt,dan
    yanxu xamani ne na krt.umma tace,tayi acan a
    dakinta.ta dubi ummi tasgi kije.ummi ta miqe ta
    fita.abba ya miqe shi ma,umma bari dai in gani
    ma su kamun kai ne? umma tace to.., . Sun
    gama gaisawa kenan sai ga abba ya fito.ganinsu
    tsaye da ummi sai ya tsinci kanshi cikin wani
    bacin rai.ya isa gun ya musu sallama, suka
    amsa, sannan suka gaisa.yace daga ina kuke?
    suka dube shi dayan ya ce lfy dai ko? ummi tayi
    karaf ta ce yayana ne.anan suka sake gaida
    abba.bai amsa ba, sai ma cewa yayi na tambeye
    ku kai ma kana tambayana,wai lfy? suka ce,kayi
    haquri,nan suka gabatar da sunansu.mai san
    ummi shine nazir, abokinsa kuma sagir. sun 3a
    masa cewa dukkansu daga kabuga suke.yace krt
    kuke ko kasuwanci? sagir yace,eh krt muke,amma
    muna taba kasuwanci a shagon mahaifinsa da ke
    kwari.abba ya dan yi jim,sannan yace to kai ka
    shirya aure ne?nazir yace eh to, nasan dai kafin a
    tashi yi mata aure na shirya.abba ya ce, to ita
    kam krt xata yi, kuma c ma buqatan ta hada krt
    da soyayya. ya dubi ummi da fatan xaki sallame
    su.ya juya gida.sagir ya ce, wannan wanki ne da
    gaske? ummi tace qwarai kuwa. nazir ya ce to
    yanxu ya kenan? kin ji abin da ya ce.ummi yayi
    shiru tana tunani, ita fa basu kwanta mata rai,
    tun randa ta hadu dasu,sam basu iya saka kaya
    kalar yadda ya abba ke sawa ba.dan haka sai
    tace, ina ganin xai fi mu haqura kada yaxo ni yayi
    ta mun fada.nazir ya ce yanxun haka xaki ce?
    ummi tace, um,sai da safenku.kada ku ja min
    duka.sagir cikin jin haushi ya ce,ki xama
    mangofak qarewan krt.sannan in kin gama wan
    naki ya aure ki. ita dai ta shige gida.kusa da soro
    ta iske umma da ya abba ta yo masa rakiya, tana
    kuma ba shi aaki kan cewa yayi ta haquri,tace ina
    fada maka ko yaushe ba fa fushi ko fada ne xai
    saka matarka a hanya ba.lallashi da nashiha,ka
    dunga koya mata giqki daka nutsu ka koya mata
    ba gashi ka ce ta iya daidai gwargwado ba?abba
    yace,hum lamarin yarinyan nan yayi nisa fa
    umma,wankan jikinta ni xan koya mata? sallah fa
    daga nake da ita.amma abin yaci tura.antynta
    sau nawa tana xuwa tai mata fada duk a
    cnxa,mkrtn ma ta qi xuwa.ni kuma da ce
    ruwanta.umma cikin al'ajabi tace, sallah! sallai
    ma bata san yi abba?abba yace umma baxan
    mata sharri ba... Ta ce Tabdi,to kuwa ba kuwa
    kazantarta ta wuce jiki hr d zcy. wannan ita ce
    kazanta mafi muni. Don haka dole ne ka zage
    damtse don ganin ta kama sallah,to menene
    marabar arne d Muslmi in ba Sallah ba?Abba ya
    ce Umma na mata nasiha na gaji. Ta ce To kasa
    ta a mkrntr Islamiyya,kila ta ji tsoran Allah in
    tana jin Wa'azi. Sannan ka dainga siyo mata
    kasasuwan wa'azi.Abba ya ce Umma kaset nawa
    na kawo mata bata sakawa,Kullum sai indiya da
    Hausa fim,in naki sayan man fetur in tana da kudi
    ta saya. In kuma ba a ta da shi sai ta dauki
    ittafin Hausa ta dukufa.umma ta ce Allah ya
    kyauta,kaje kayi ta hkr tare da addu'a. Ya kalli
    Ummi,sannan ya ce ma umma,kada ta sake fita
    gurin wadanan kananan yaran,sannan ya fita. A
    daki umma take tambayar Ummi daga ina suke?
    Ta ce um,Umma kyale su ni sam ma ba su min
    ba. Umma ta ce to Allah dai ya miki za6i nagari.
    Abba yana kwance a dakinsa ya yi lamo cikin
    bargo,ya kasa amsa ma kanshi tarin tambayoyin
    da ke yawo cikin kanshi. Haka tambayoyi suke
    zuwa masa daya-bayan-daya ,me yasa ya damu
    da lamarin Ummi??me yasa da a ka yi sallama da
    ita ya samu kanshi cikin wani tashin Hankali? Me
    ya sa ranar da zai je mata ziyara ya za6i ya sai
    mata kayan kwalliya? A fili ya ce,don tana
    kanwata.Zuciyarshi ta ki amincewa da haka. Me
    yake shirin faruwa da ni ne? ya fada a fili. Ya yi
    juyi zuwa rigingine,sannan ya dauki filo ya manna
    a kirjinshi, ya ci gaba da magana shi daya. Bana
    zaton cewa Son Ummi nake yi.don lkcn da na yi
    tsananin Son Bishira bn ta6a samun kaina cikin
    wannan yanayin ba. Kai Allah ya tsare ni da Son
    ummi,wannan mahaukaciyar
    yarinyar..........bugun kofarshi da a ke yi ne ya
    katse shi. Murayar Bishira ce ta na cewa Babn
    Walid!Babn Walid!! Ya bude kofar da sauri,ta ce
    Walid ne ke ta amai. Ya fita ya dauki yaron daga
    hannunta yana fadin Me zai hana shi amai,in ba a
    ci sa'a ba har zawo sai ya yi,Saboda
    kazantarki.Sam ba ki lura da me zai wawuro ya
    tura bakinsa. Ta ce Yau fa bai ci komai ba,tun da
    safe yake wannan aman.Ya ce shi ne ba ki sanar
    da ni ba?Ya cire masa kayan jikinsa wadanda ya
    ji suna ta doka karni.. . Ya isa igiyar shanya ya
    ciri wasu yasa masa,sannan ya fita dashi.Wani
    babban kyamis ya tafi da shi,mai kyamis din
    likita ne,sai dai ba na yara ba ne,amma kowa
    yazo sai ya duba shi.Nan dai ya masa bayani ya
    ba su magunguna. Sha biyu dai dai ya dawo,tana
    zaune tana kallo ya ce "A'uzubillahi,wai ke kallon
    nan masifa ya zamarmiki ne?to ki sani na kusan
    fita da kayan kallon nan. Ta ce,Tab,ka kaisu ina?
    dadinta dai dafa gidan ubana a ka kawo su. Ya
    ce ta za su koma gidan uban naki. Ta dafe kirji
    "Zagina ka ke yi?ya dora mata dan a jiki "An
    zage ki,ke din banza,kazama!yazube mata
    maganguna ya fita. Ya jima zaune a kofar
    gidanshi dafe da kai,yana tunanin shin wai shi
    kadai ne bai yi sa'ar mata ba,ko kuwa duk maza
    ne.Ya tuna abokanshi 2 da suka yi aure. Muktar d
    Jamilu,sam ba su da wannan matsalar,duk lkcn
    da yaje gidansu tsaf matansu,ga mutunci da
    mutanta mutane. Shi kuma a cikin abokanshi
    babu mai zuwa gidan sbd bata gainin kowa da
    gashi. 'Yan uwanshi sai wanda ta za6a sannan
    zata yi hulda da su. 'Yan garinsu kuwa can
    ¤ZAMFARA¤In suka zo kiri- kiri take nuna musu
    kyama ga rowa,sam bata hulda da matan
    abokanshi. Ya numfasa zai bi shawarar Umma ya
    gani, amma gaskiya Bishira ba matar zama ba
    ce. Tun da ya dawo sallarAsubahi dakinta ya
    shiga tana ta shirga bacci. Walid kuma ya yi
    faca-faca cikin kashi ya tausasa zuciyarshi ya ce
    "Bishira! . Bishira!!Ya dan duki kafarta,sannan ta
    tashi. Ya ce Ki tashi ki gyara masa jiki kiyi
    sallah.Ta ce,Tab, me ya yi?ya ce, "kashi ya
    yi.kurum sai ya ji ta ce Tab,wannan akwai dan
    iskan yaro.Yanzun dan ubanka kashi ka min?
    Sam bai san lkcn da ya watsa mata mari a baki
    ba,cikin murya mai karfi ya ce "kada ki kuskura ki
    sake ce ma dana dan iska!kar ki sake zagar min
    yaro kada ki yi wa dana baki.Ba zan dauki
    wannan ba. . Ta mike daga kan gadon tana kuka
    Ni ka daka? wlh sai na rama. Kasancewar lebe
    baya raina duka,sai jini.Nan da nan sai kumburi.
    Ta cakumo shi,wlh sai na rama.Ya hankadata kan
    gado ya bar gidan.cikin zcyrshi yana fadin
    ,"Wannan fitina da me tayi kama? Ita kam ruwa
    ta dafa sannan ta wa yaron wanka, cukuikuiye
    zanin gadon ta saka shi cikin baho,sannan tayi
    kwaskwarima ta sabi danta baki suntum ta nufi
    gida tana kuka. Mahaifinta bai nan yana
    Abuja,Hjy Zainu ta kalle ta bayan ta gama kero
    karyarta. Wai don yaro ya yi kashi ta ce yaron
    bai kyauta ba shine ya hau ta da duka da zagi.
    Hjy Zainu ta ce Amma wannan da muciya ya
    dake ki ko?ta ce, Da hannu ne,nushina fa ya
    dinga yi. Hjy Zainu ta ce Ai kin gani ba yadda ba
    a yi ba ki tsaya kiyi karatunki kin ki,kin kafe sai
    kin aure shi,wannan matsiyacin? Dama talaka
    yana da wannan tsiyar.Yanzun za ki zauna mu
    jiraZuwan Alhj,ba za ki koma ba.Ya dai baki
    takardarki in yaso ki koma mkrnt.Su kuma su
    dauki dan nasu. Bishira dai tayi shiru,zcyrta tana
    jinjina rabuwa da Abba d kuma danata. Abba kam
    gidansu ya nufa.Ummi ya soma cin karo da ita
    tana sanye da doguwar rigar bacci,ta dora rigar
    sanyu ta sakar ulu, a kai tana wanke baki da
    busushi. Ta dube shi,mmkn ganinshi tayi a
    wannan lkcn.Sai da ta dauraye baki sannan ta ce
    masa sannu da zuwa,ya amsa a hnkl bai san mai
    yasa ya kasa dauke idanunshi daga kanta ba,hr
    ta gama alwala tayi addu a ta mike. Ta dube shi
    da niyar yin magana,amma sai ta fasa don tana
    tsoron kada ya daka mata tsawa. Ta daga
    labulan dakin Umma zata shiga. Ya ce, "Ke!' ta
    waiwayo cikin hada rai,domin ta tsani kiranta da
    yake da ke!Ya ce Ummana fa?ta kalli dakin Alhj
    Ba ta fito ba,,Ta shige ta zura hijabi ta tada
    Sallah. Ya shiga dakin ya zauna,yana kallonta
    tana Sallah zcyrshi tana nazarin Rayuwar
    Ummarshi. Tun tasowarshi ya ke ganin kulawa da
    kyautatawa da take yiwa Alhj Babba ga biyya,
    sam bata wasa da dk wani abu nashi daga lkcn
    da ya shigo gida ta gama sauraron kowa sai lkcn
    da ya fita. Bai ta6a jin sunyi sa'in-sa ba bare ta
    daga murya sama da tasa.Shin sauran matan ba
    su fahimci irin wannan ladabi ba ne?Ummi tana
    addu'a zcyrta cike da tunanin shi kuma ya Abba
    me ya kawo shi da wannan sassafen? Muryar
    Umma suka ji daga waje tana cewa,"Ummi in kin
    idae ki fito ki share gidannan,ki wanke bayi,Ummi
    ta ce To''. Sam Umma ba ta san Abba ya shigo
    ba,dmn da ta ba Ummi umurni sai ta sake
    komawa dakin mijinta, Ummi ta wanke bayi
    kansu,sannan ta share ko ina na gidan, ta kunna
    risho ta dora ruwan karyawa, sannan ta shiga
    firar doya. Gyangyadi yake daga zaunw, Muryar
    Ummanshi ce ta farkar da shi tana cewa, "A'aha!
    ya bude ido cike da bacci.ZURFIN CIKI book 2 part 4
    ZURFIN CIKI book 2 part 4
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:10
    "A'aha! ya bude ido cike da bacci. Ya kalle ta tare
    da yin mika,ta ce "Lafiya"? Ya ce,Umma lfyr
    kenan.Ta zauna da sauri Me ya faru Kuma? Yayi
    dan tsaki,umma na gaji da auran nan ina ga
    wannan karan xan yar da qwallon mangwaro in
    huta ta quda. umma ta ce abba! abba!! me yasa
    baka da haquri? ban xace ka haka ba abba,ina ce
    jiyannan ka min alqawarin kawo qarshen duk
    wata matsala tsakaninka da matanka?shin ban
    fada maka hanyoyin da xaka bi ka xauna da
    matarka lfy ba?ya kamo hannun ta,umma ba na
    san bata ranki, ban san yadda xanyi da halin
    yarinyan nan ba ne. jiya fa ina kwance taxo tace
    min yarona amai naje kai shi kyamis,ina dawowa
    na samu ta xauna tana kallon,ina mata magana
    ta hayayyaqo min da asuba na tashe ta
    sallah,wai dan yayi kashi shine ta hau xagin
    yaron nan,wai dan iska. ni ko na bige mata baki
    har da cukume ni da dambe fa.umma tace kaine
    harda duka abba? dukan mace?ta xuba tagumi
    tana kallon shi,ya ce umma xaginshi fa tayi,kuma
    kin san dai ba kyau uwa ta dinga xagin danta.dan
    ba haka kikai min tarbiyya ba.kalli rashin ji irin na
    ummi, amma ban taba jin kin ce mata yar iska
    ba.tace to ba sai ka xaunar da ita cikin tsanaki
    ba?? . Yayi shiru a xuciyarshi fadi yake umma ba
    xata fahinta ba.tace, tashi kaje ka bata haquri, ka
    lallasheta.matafa sai haquri,kasan da qashin
    haqarqari aka yi su,dole ka ganta a karka
    ce.saidai nasiha da lallashi,da xaran ka ce kan
    dole xaka miqar da ita,sai ta karye.nan dai ta yi
    ta ma abba fada, har sai da shi kanshi yaga
    cewa eh,yayi saurin fushi.dan haka ya miqe ya
    nufi gida da nufin bata baki.sai dai kuma kash!
    lkcn da yaxo tuni tana gidansu.ya dawo ya sanar
    da umma, tace to dole sai alhj yaji kenan.ta shiga
    gun alhj yana shirin fita. yace yau dai suwaiba
    akwai abin da ya dauke miki hankali daga kaina
    ko? tace, me kagani? yace tunda kika fita ban
    kuma jin duriyarki ba, hatta karin kumallo yau
    uwata ce ta kawo min.ko taya ni shafa mai yau
    ban samu ba, tace uhum, abba ne in gaya maka
    na gani hankalinshi a duk tashe, matsala ce suka
    samu da matarshi,wai ta yi yaji.alhj yace,yaji?
    umma tace eh wai a ce kamar abba bai san
    yadda xai yi haquri da mace ba, alhj yace ina
    abban?ta ce yana daki yana karya wa. Ya ce kira
    min shi.abba ya xauna ya xayyane ma alhj komai
    duk abubuwan da ke faruwa wanda take
    masa,hatta batun sallah da bata san yi duk ya
    fadia.alhj yayi shiru,can ya ce in ko haka ne ba
    qaramin haquri kake yi ba, amma kaje xamu je
    gidan.abba ya ce, ni dama xa a baita can dana
    huta.alhj yace ba xa ayi haka ba haquri dai xa ka
    ci gaba da yi.xuwan su alhj biyu gidan amma ba
    suyi dace ba ance musu mahaifinta baya nan.
    antynta kuwa ta kira shi a waya ya ce yana nan
    xuwa gidanta.da dare suka je da ahmad sun
    same ta ita da mijnta,anty ta tare su cikin fara'a
    aka kawo musu kayan shaye shaye.nan dai abba
    ya fada mata komai.ya qara da cewa ban sani ba
    ko dan ni talaka ne shi yasa bishira bata ji
    maganata? anty tace dame ka gaxa mata?
    iskancintane kawai, wai bishira har da rashin
    sallah,xa ko taci qaniyarta gun alhj.mijin anty
    yace,tabdi lalle kana haquri nan dai suka ci gaba
    da hira har mijin antyn yayi mishi alqawarin cewa
    ya kawo takardunshi.MD din gidan rediyon
    tarayya na jihar kd, amininshi ne. Amininshi ne
    tun da abn da ya karanta kenan za a sama mishi
    aiki.Abba ya yi ta godiya. Bai san da wane baki
    zai gode ma mijin anty ba,tun daga nemna auran
    Bishira yake taimakoshi, darajar su shi da Anty
    da Alhjn su Bishiran yake hkr da halayanta. Ya zo
    ya sanar da su Umman,Sun yi murna hr Alhj ya
    ce dole ne in in masa godiya. Umma ta ce To
    Abba ka gani fa,ta dailin matarka gashi zaka
    samu aiki,ka yi ta hkr fa. Abba ya ce Umma ba fa
    ta dalilinta ba,in Allah ya rubuto zan samu ta
    hanyarshi sai ki gani,ko ban santa ba Allah ya
    kawo sila.Ta ce To yanzun dai ita ce Silar,Allah
    yasa albarka.Sai dai ba zan ji dadin tafiyarka
    garin Kd ka barni nan ba. Ya ce Umma ko ni
    tunda ya ce kd ke kurum ni ke tunan.Umma tayi
    Murmushi,Allah ya maka za6i na alkairi,dk in da
    za ka je.Amin Ummata. Mahaifin Bishira ya dawo
    kuma Alhj ya tasa Abba sun je in da aka kirata
    gata ga shi ga kuma iyayensu. Abba ya jero duk
    laifunkanta bai rage ko daya ba. Sannan ya ce,shi
    ma yana son ta fadi tsakani ga Allah me yake
    mata wanda ba ta So?Nan fa a ka ce ta fadan,
    sai ta shiga Kame-kame, Wai in ya shigo gida sai
    ya yi ta fadace-fadace sannan ba ya zama a gida
    sai tayi bacci,km ga abnci ta dafa amma sai ya
    amso na Ummarshi ya c. Alhjnta ya daka mata
    tsawa."Yi min shiru,yaushe ki ka bar musulunci?
    Ba kya sallah ko?sannan ki bude baki kina zagar
    masa da a gabansa?Ya bige miki baki kin kwaso
    kin taho gida,to a miki uban me?ya dubi Abba
    "Idiris me yasa ma ka mata duka ba?Ai ke babu
    abn da ya dace da ke irin duka. Maza ki kakkabe
    mayafinki ki koma gidanki,bana son in sake
    ganinki da sunan yaji a gidana, . Zan wulakanta
    ki. Kuma game da batun sallah dk lkcn da bata yi
    ba ka dakar min ita ni na saka,batun tsafta kuwa
    kada tayi,ka nemi mata ka aura ka barta da
    tsiyarta. kai dk lkcn da ka samu matar ma zan
    biya maka sadakinta ko 'yar wanene.Sai a lkcn
    Alhjn Su Abba ya yi magana. Hakuri za ka yi
    ranka ya dade,Allah ya saka da Alkairi bisa
    karamcin da a ka yi mana,kuma insha Allah ba za
    su sake ba. Abba ma ya yi godiya,sannan suka
    masa sallama.Ita ko Bishira mayafi ta dauko tana
    kuka suka tafi. Hjy Zainu ranta ya 6aci,taso a
    kashe auran don dama bata son Abba sam,kafin
    zuwan iyayen Abba da shi kansa Abban ta
    fadawa mijinta karairayi,kamu ransa ya 6aci. Ya
    kuma daukar wa kansa alkawari in ya bincika ya
    tarar haka ne dukanta da zaginta yake ba tare da
    ta masa laifin komai ba?sai yasa an raba auran.
    Amma da yaji batun Abba gata a gurin bata musu
    ba,sai ranshi ya baci da ita, har dai batun sallar
    nan.dn haka ya bincike yana da kyau ayi shi,kada
    ka yanke hukunci da maganar gefe daya,wannan
    shi ne adalci. Bayan sun dawo Abba ya rakata
    gida ya zo gurin Alhj da ya ce ya dawo yana
    jiranshi. Alhaji ya masa fada cewa dk in da tara
    tayi to ya kansace a gida. Sannan fadan da ta ce
    yana yi in ya shiga shi ma ya daina,haka ya
    dinga zama yana cin abncin.Abba ya ce to.Umma
    ma da ya shiga suyi Sallama nan dai ta kara
    masa fada tare da nuna mishi hanyoyin da zai bi
    ta ce kuma cikin satin nan yayo mata rijistar
    Islamiya tunda da ita a kusa. Ya shiga ya same
    ta zaune bakin gado tana ta fushi,ya zo ya zauna
    kusa da ita.Yasa hannunshi ya kamo nata,sannan
    ya kira sunanta bata amsa ba bata kalle shi ba
    ya ci gaba da mgn. Kin san dai ina sonki ko??ta
    dube shi Da ba kafin a zuga ka.Ya ce wa zai zuga
    ni? ta ce Wa kuwa in ba Ummar taka ba. Ya yi
    tsam ya ji haushin maganarta sosai,amma sai ya
    danne kada ki zargi Ummata tana sonki kin ki
    fahimta ne kawai.amma mu bar zancan kiyi hkr
    akan abubuwa da nike miki. ki yafe min nima na
    yafe miki. . Ya jawota zuwa jikinshi,hr gobe ina
    sonki sosai.Ranta ya yi sanyi don mata na son
    wannan kalma daga mazajensu. Ya kira sunanta
    ta dube shi cikin ido suke kallon juna,ya ce kin ya
    fe min?ta daga gira,kina sona hr yanzun?Ta kara
    mannewa a jikinshi "Ina sonka sosai ma.Ranar
    dakin shi suka kwana,kuma ranar ce rana ta
    farko da suka soma kwana a dakin nasa. Washe
    gari tunda ya dawo Masallaci ya soma akin share
    gida,lungu-lungu ya gama ya wanke bayi kan su
    sannan ya yako ta da kyar ta tashi ya ce tayi
    sallah ta yiwa yaro wanka. Tayi Sallar,wankan ta
    kuke wai akwai sanyu,sai ranar ta daga. Ya ce,To
    t dafa musu ruwan zafi su karya.Shi kuma ya
    fitar da wankinshi yana yi ya gama ya ce ta fito
    da duk wankinsu ita da yaron.Tsawaya ya yi yana
    kallon tilin kayan,amma gudun kada suyi rigima
    sai ya yi shiru ya ci gaba da wanki. . Ya cire
    kayan yaron da zannuwanta hr ma zanin gado
    wadanda yaron ya yi kashi ta aje su suka
    bushe,,wasu kayan hr da tsutsotsi. Ya kira ta ya
    ce "To kalli kayanki hr da tsutsotsi,wanna n ya
    dac fisabilillah?samo leda ki kwashe su,ba zan
    iya wanke su ba,in kuma za ki wanke to. Nan ta
    samo bako ta kwashe takai gurin bola,ya ce
    Bishira tsafta cikin addini ce,Annabi (S.A.W)ya ce
    Babu mai shiga Aljanna sai mai tsafta. Don Allah
    ki dinga kula,ke kanki za ki ji dadi in har ki ka
    tsaftace ko'ina na gidanki.Ta tura baki ta wuce.
    Ranar haka ya yini wanki kayan yaron dk sun
    dafe kaya masu tsada da kyau irin wadanda a ka
    sai masa daga gidan iyayenta,ranar dai ko shago
    bai je ba. Cikin satin dai babu laifi suna ta
    shiri,kuma tana daurewa tana yin tsaftar
    jikinta,haka nan yasa ta wanke kai tayo kitso. sai
    dai ita gani take dk an takura mata,amma tana
    jin dadin yadda ya sakar mata fuska kamar
    farkonauresu. Mitar da take masa kullum ya
    daina dadewa a waje,ita don Allah ya zauna a
    gida suyi hira. Ranar dai saiya gwada zama tun
    da ya dawo sallar Isha'i ya shigo gida. Tana
    zaune ba riga ya ce,Wai Bishira kayan kwalliyarki
    sun kara ne? ta ce,Me ka gani?ya ce,Rabon da in
    ga kwalli a idonki tun kina amarya bare dan jan
    baki. . Taja dan tsaki "kwalliyar me zan yi sai
    kace wata budurwa?Da dai nayi.Ya ce kin ji wani
    shirme kuma,ban da ke ai matar aure me miji a
    hannu ita ce da yin kwalliya. Ta ce, To ko ma
    nayi ba zama ka ke ba.Ya ce "To yau dai gani na
    zauna,kuma ina son a sheka min kwalliya. Ta
    dube shi Gsky sanyi ba zan iya yin wanka yanzun
    ba.Shiru ya yi yana kallonta,can sai ta zame ta
    kwanta,sai kuma bacci. Ya yi murmushi.Dubi
    matar da ta ce wai ba na zama a gida. to yau na
    zauna amma kalli yadda ta bingire tana shirgar
    bacci. Ya mike ya fice.cikin takaici korafin banza
    kenan take yi tunda ba ta san yadda za ta yi fira
    da mijin ta ba. haka dai abba yayi ta hakuri don
    baxai yiwu ya ce shi kadai zai dauke mata duk
    aikin gidanta ba. sai dai yayi wanda zai iya,amma
    duk wanda ya shigo gidan shi ko ba a fada ba
    yasan matar gidan kazama ce ta bugawa a
    jarida. ummi tana zaune gaban umma,fuska
    shabe- shabe da hawaye.ta rikewa ummar
    hannu."kinji don Allah umma kice wa ya Abba ya
    dawo dani garin nan.wallahi bana son makarantar
    kwana,ni dai bazan koma ba."umma ta ce "haba
    ummi xuwa yanzu ya ci ace kin saba da
    makarantar" ta ce,"umma bazan saba da rashinku
    ba....."karaf a kunnen Abba. ya ce,"to sai ko ki
    shirya sabawa,don wata rana ma aure zaki yi."
    umma ta ce sosai kuwa. tsohuwa dake zaune a
    kofarta,tana jinsu ta sako baki da cewa,"ku dai
    lallasheta,karatun nan fa da ake ta matsanta
    mata bana ganin manzo bane." Abba ya ce
    mata,"in ji wa? kin ji ki,to ana neman aljanna da
    karatun boko kuma ana neman wuta." ta ce,"kai
    ni raba ni da shegiyar karya tunda bata so a
    barta." Abba ya dubi ummi,"kada ma kiyi za ton
    maganar tsohuwa za tayi wani tasiri,gara ma ki
    shirya komai gobe da wuri zamu wuce." ta dube
    shi,"don Allah ya abba." ya mike ki shirya da
    yamma zanzo muje (sahad store). ya dubi umma
    na tafi. . Ta ce,"abba bamu ko gaisa ba,ya mutan
    gidan?" ya ce,"suna lafiya,sauri nake in karasa
    wasu dinkuna,saboda gobe bana nan jibi litinin
    zanje interview da gidan radiyo da talabijin na
    (c.t.v) ta ce,"a'a ka samu anan din ne?" ya
    ce,"eh bana fada miki ba da aka tura takarduna
    can sai suka ce gurin da zasu saka ni akwai wani
    wanda suke jin dadin aikinshi a gurin? don haka
    zasu turo ni kano,suna ganin ana bukatar irina.to
    shine mijin anty ya fada min to yanzu sun kirani
    ranar litinin zasu min (interview).ummi dai na
    jinsu bata ba kukanta ba.abba na ficewa umma
    ta ce tashi kije kiyo kitso ummina,kin ji? dakyar
    taje ta dawo.umma tana yankan kubewa wayarta
    ta shiga ruri,ta dauka Abba ne.ya gaisheta ta
    amsa,ya ce ummana ummi fa ta shirya? umma
    takai duba cikin daki inda ta hango unmi nade
    kan kujera tunda ta fito wanka. Tace can cikin
    kujera,wai sanyi take ji.yace sanyin lfy kuma? ta
    shirya ta sameshi gida,umma tace to gatanan
    xuwa sukayi sallama.umma tace ke ummi fito
    man in kin gama shirin.ummi tace umma nifa
    sanyi nake ji,ina ganin xaxxabi ne xai
    kamani.tace to ku biya ta kyamis kusai
    magani.tsohuwa tace ke yi kwanci yanki, dole ne
    fitan? umma ta miqe tana cewa, yanxu in ban je
    ba da yaxo xai fara min masifan shi ne. ta shirya
    ta fuce rai a bace.a nutse ta ke tafiya har daf da
    qofan gidan ya abba. sallama taji anyi mata.wani
    matashi ne suka gaisa, ya tambaye ta nanne
    gidansu? tace a,a lafiya?ba tare da bata lkc ba ya
    fara xayyane mata manu fanta,santa yake kuma
    da aure,tace kaga mlm sai anjima.ta shige gidan
    abba shiko ya kafe yaqi tafiya.da sallama ta
    shiga gidan,qaran inji baisa aji sallaman ba,dan
    haka ta jingina da rijiya tana kallan tsakar
    gidan.mamakin daya yadda mace daya a gidan ta
    kasa gyara gidan.sai kace gidan namiji, namijin
    ma qaxami. . abba ne ya fita wanka sanye da
    jallabiya fara.ya aje bokitin ya dube ta. yace ki
    siga ciki mana, ai tana falo.tayi
    sallama,bishiratana xaune da baso tana kalan tv,
    ganin umma ta daga labule sai ta hada rai tare
    da cewa lfy? ummi tace ina wuni. bishira tace
    lau, nace lfy? ta fada hadi da xare ido. ummi tace
    ya abba ne ya ce na xauna anan na jira shi. tace
    baxa a xo nan adame ni ba, ehe dan kallo nakeyi.
    ummi ta ja tsaki tare da sakin labulan, ta koma
    ta jin gina da rijiya.bishira ta fito.ke sarkin rashin
    kunya wa kike ma tsaki? ummi ko kallanta batayi
    ba.sannan tace baki isa kixo min har gidana
    ba,kice xakimin rashin kunyan da kika saba.abba
    ya jiyo hargowanta ya fito, yana qoqarin saka t-
    shirt baqa akan faran singiletin shi,wandan jeans
    ne mai laushi blue.yace,menene? tace, wannan
    mara kunyan yarinyan nanne xata sameni har
    dakina tamin tsaki.oa dubi ummi dake kallan
    qasa tamkar bata san me akeyi ba. yace ke
    ummi, ta dube shi da sauri,xan bata maki rai
    kinsan bana san raini ko? tace nifa ya abba
    banfa yi mata komai ba kawai fa.ya daga mata
    hannu,yace banasan ji. yace na fada maki dai
    bana san raini. takaicin duniya ya isheta,ta
    sunkuyad da kai cikin qunan rai.wanna shine
    gaba kura baya damisa.bishiqa kam sai ci gaba
    da mita take, shiko abba tuni ya koma dakinsa da
    qarasa shiri. ya fito fes, sam baxaka ce mijin
    bishira bane.qamshin turaransa ya karade gidan
    ya daga labule.ni na fita. tace sai ina? xan kai
    ummi ta sai duk abinda xata nema dan gobe xata
    koma mkrt. ta tabe baki. ya dubi ummi wadda ke
    cika tana batsewa,sannan ga sanyi alamun
    xaxxabi yana damunta.yace muje ko? ta dube shi
    sannan ta bishi.a qofar gida ya iske wannan
    saurayin,yace lfy, ko kana jiran wanine? saurayin
    ya ce wata yarin....sai ya hango ummi,dan haka
    ya katse batun da cewa yauwa gatanan. . abba
    ya kalleta ke uwar rore rore wannan ke yake jira
    ko? ummi tace oho mashi, bina yake tayi.abba ya
    ce, kayi haquri dan samari,ba aure xa a mata ba,
    krt takeyi. yace nima din bawai ina nufin yanxu
    bane.ya ce na fahince ka.to ka bari sai nan
    gaba,ina nufin in auran yayi sai kaxo ko???? Ya
    dubeta ranshi bace,ke kuma wuce muje.suka bar
    shi nan tsaye yana kallansu.yaga kishi qarara a
    idon abba.yace wannan ba wanta bane shima
    santa yake.ya raya aransa shima yayi gaba abin
    shi.shi kam abba suna tafe yana yi mata fada,wai
    tabi ta sakar ma maxa fuska kowane gaja sai ya
    xo yace yana santa.maimakon ta tsaya tayi
    krtnt,xamani na ilimi,ita dai ta qi kula shi,har
    yanxu takaicinta abin da matarshi ta mata,kuma
    ya nuna ya goyi bayanta.wayarshi tayi ringing,ya
    kalli ummi muje shago na mashin din
    nacan.sannan ya daga wayar,ita tana tafe ne
    amma sam bata jin dadi.da yake tafiyanta yanxu
    tamkar tana jin tausayin qasa take yinta,sabanin
    da da sai dai tayi gudu,shi da ke tafe yana waya
    ya riga ta isa.gefe ta tsaya ya shiga shago bayan
    ya gama amsa wayar.ahmad abokinsa yaxo xai
    shiga shagon ya ganta tsaye.tace ina yini ya
    ahmad? yace lfy lau yar daru.daman haka ya kan
    ce mata.ya shiga shagon yana
    waiwayanta,abbana barma yan shagon sallahu
    wasu kayan da xa a xo dauka,ahmad ya shigo.
    suka tafa,sannan suka gaisa.ahmad yace naxo ne
    in fada maka anjima xamu shiga gidan su hafsa
    dan gaida iyayenta,sai dai kuma ganin ummi ya
    sani jin wani abu.anya ba xan dawo gida da
    neman aurena ba?a rude abba ya ce wace ummi
    kenan? ahmad ya ce qawarka mana.abba ya ce
    dan Allah saki xancen nan kada ma ta jiyo ta
    raina mu,me ka gani naso a gun ummi? dan Allah
    kada ka cta min rai. . ahmad yace, allah in xai
    yiwu, nutsuwan ta birge ni .abba ya ce to ba da
    ni xa aci amanar hafsa ba.ummi kuwa dan Allah
    ka bar xancenta.yaea ahmad yaga abba ya sha
    mur ya tsare gida,dole ya saki batun.suka yi
    sallama ya tafi,abba na cewa sai yaxo da
    dare.yasa yaron shagon ya goge mashi mashin
    din sannan ya tada,ya kalli ummi fuskarshi daure
    xo ki hau.itama tata fuskar a daure take.tahau
    suka tafi,iskar dake kadata tasa xaxxabin dake
    san kamata ta qaru.ya kafe mashin dhn ya
    kalleta,muje mana.ta bishi suka shiga cikin sahad
    store din.tsaye tayi tana kallanshi yana diba
    kaya.da alama na iyalanshi yake diba,dan taga ya
    soma da pampas. Hannuwanta harde a qirjinta
    tana kallan shi,kome nashi yana birgeta.ya
    waiwayo ya dubeta, tsayuwarme kike yi a nan da
    ba xaki dauki abinda ya kawo kiba? ta rasa me
    xata dauka,sai kurun ta dauki makilin ta riqe a
    hannu,ya gama diban abin da yake so,sannan ya
    aje gaban masu amsar kudi.ya dubeta,bakya
    buqatar komai kenan? ta nuna mishi makilin din
    hannunta,tana murxa shi.ya harareta baxa ki
    dauki komai ba,kina da kayan tea dasu complex?
    tace a,a.y2e to ki tsaya kada ki dauka.ya soma
    dibo mata saitin sabulan nan daya taba sai mata
    na aloe vera,dan yaga duk kananan qurajen sun
    mutu.sannan ya hada mata da audugar mata
    guda biyu.ya kai table.lkcn ta dauki madara da
    milo ta kawo.yace wawiya,dalla matsa ki bani
    gu.yaje ya qara tsinto mata ,sanna akayi musu
    total ya biya.suka fita.kafin sukai gida haqoranta
    sun s6a haduwa,gashi tana ta takurewa,yace
    lfy,wani irim xama kika yi haka?tace,sanyinake
    ji.tana magana muryarta na makyarkyata.wani
    dan asibiti ya nufa da ita nan kusa da unguwansu
    aka dubata. Wurin allura,nan fa a ka soma
    daga.Ta ce,ita kam bata san allura.Abba ya daka
    mata tsawa da cewa,Allurar ce abn tsoro?Na
    gane sam ba ki son ki koma mkrnt,a gobe ne
    kuma sai kin koma duk abnki. Ta ce, Naji zan
    koma amma yanzun kam dn Allah Ya Abba kada
    amin allura.Nurse dai sai kallonsu take yi tana
    dariya. kwai Ummi sai ta soma hawaye ita fa har
    ga Allah bata son allura.Nurse ta ce,To ka rike ta
    mana ko ba Amarya ba ce?Naga shagwabar tayi
    yawa. Abba ya ce,Me? cikin tsawa ya yi
    maganar,hr sai da Nurse din ta tsorata,ya ce
    kanwata ce fa,kin ga wannan kucakar tayi kama
    tayi kama da Amare? Nan take Ummi taji ta
    muzanta,sannan km ta tsorata da irin tsawar da
    ya yi,ba ta san lkcn da ta shige a ka yi mata
    allurar ba. Ta fito tana sharar kwalla suka koma
    gida. Sai dai tana hada kayanta a Jaka,Sannan ta
    ga wadannan sabulun da kuma audugar,kenan shi
    ne dama ya sai mata wancan?ko me yasa ya sai
    mata kuma hr da augugar mata? . wata zuciyar
    ta ce,kila dn yaga Umma bata san kan abubuwan
    zamani ba sosai.A fili ta ce,kai umma tasan
    audugar mana. Haka dai ta ci gaba da tufka tana
    warwarewa,hr ta gama shirya kayanta. Yau kuma
    a bayan Tsohuwa ta za6i kwanciya,da dn komai
    ba sai dn suyi hirar yaushe gamo. Sai dai
    Maimakon hira sai ta tsunduma a tunani,ta bar
    Tsohuwa tana ta zance ita daya. Fitarsu da Ya
    Abba ta tsaya mata a rai,ita tayi ta tunowa tana
    murmushi.Sai dai bata Son tuna lkcn da ya yi wa
    Nurse din nan tsawa dn ta ce ko ba amarya ba ce
    kom me yasa zai mata Tsawa? ita kam kalamn
    Nurse din nan sun birgeta,shi kuma daga ganin
    yadda ya yi tsawar nan kalamn ba su masa dadi
    ba.......... wai takwara bacci ki ka yi ne?Muryar
    Tsohuwa ta katseta,ta ce,Idona biyu Tsohuwa.Ta
    ce, Tunanin me ki ke yi ne haka?Ummi ta ce
    "Um" ina tuna gobe yanzun ina can.Tsohuwa taja
    tsaki,Ai mai sunan Malam ya san takan mugunta.
    UMMI dai ta ce "Um.Tsohuwa kuwa sai yi take
    da mai sunan Malam.Tun Ummi naji tana "Um",
    hr zcyrta ta soma tsanar kalaman Tsohuwa. Sai
    dai bata da damar ta katse Tsohuwa tunda dn ita
    take yi,bata da mafita da ta wuce ta bar
    dakin,don haka ta suri butar Tsohuwa,wai zata je
    kewaye(bandaki). Shi ma Abban da ke kwance a
    tsakar dakinshi kan kafet ya tada kai da
    katifarshi,ban da tunanin fitarsu ta dazun ba abn
    da ya keyi. Sai dai damuwarshi daya,me yasa
    samari da dama suke kawowa Ummi hari?Me
    yasa ya ke jin zafin haka?Zuciyarshita amsa da
    cewa,ka so ko ka ki kana Son UMMI."a fili ya
    furta "Haba dai so,Allah ya tsare ni." Tun misalin
    tara Ummi ta gama shirinta tsaf,cikin kayan
    mkrnt mai ruwan hoda,mai gida-gida.Da kuka ta
    bar gidan yau ma. Haka nan kuka take hr suka
    isa mkrnt,ta samu Khadija hr tazo,dn haka tare
    suka kwashe kaya.Kafin Abba ya tafi sai da ya yi
    mata fada kwantankwacn wnda Umma tayi
    mata.Waton ta kula d kanta,kuma tayi abn da ya
    kawo ta,waton krt.Sannan ba ya son tayi
    kawance d yaketa shari'a.irin wanda wasu
    watsatstsun yaran ke yi.(Allah ya shiryesu).
    Sannan ya jadadda mata batun ibada,sannan ya
    kawo kudi ya bata,ta ce Umma fa ta riga ta bani.
    Ya ce,"Ki kara."ZURFIN CIKI book 2 part 5
    ZURFIN CIKI book 2 part 5
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:12
    Umma fa ta riga ta bani. Ya ce,"Ki kara."
    Rayuwarta a mkrnta wannan karon ba laifi,sai dai
    fa hr yanzun ta tunu da gida sai tayi kuka. Su
    Safiyya suna mmkn yadda Habiba take da
    matsanancin nacin gida. ******** Abba ya shigo
    gidanshi dauke da ledajin kayan miya,da sauri ya
    dire su kofar kicin ya nufi Bishira da ke kofar
    bandaki tana shara amai. Ya kama ta,"lafiya?Me
    ki ka ce? Sai da ta gama aman sannan ya karasa
    da ita ta wanke baki da fuska a cikin bayin. Ya
    ce,Ba ki d lfy ne?Ta soma Hawaye, Ka gani ko
    Babn Walid,kila fa ciki ne da ni.Tun wancan Satin
    ya kamata in ga al'aldata amma shiru. Ya ce, To
    menene na kuka? Yi shiru,Allah ya inganta.Ta
    harare shi Dana fa bai shekara ba.Ya ce,To dole
    ne sai danki ya shekara sannan Allah zai baki
    wata kyautar? Ta soma kuka,Ni dai zan je a
    ciremin ne. ya hade fuska,Ban yarda da haka ba.
    Ganin ta tada hnklnta tana cewa "Dama Hjyrsu ta
    ce mata tabi a hankalu ta ki ji gashi nan yanzun
    tana da wani ciki. Ya ce To kada ki damu kin ji?
    Zamu je asibtin dn a tabbatar da cikin kafin a san
    abnyi. Da za suje asibiti shi ne ya dage sai da
    tayi wanka,dn d farko kaca-kaca ta dauko
    mayafi, ya ce sai tayi wanka ta canza tufafi.
    Gwajin farko ya tabbata tana da ciki,nan ta shiga
    kuka. shi kanshi ya damu domin bai so ciki
    yanzun ba.A son ranahi sai an yaye yaron kafin
    wani cikin. Amma ba shi da ra'ayin
    zubarwa,nashi ganin kyautar Allah ce,dn haka ya
    amsa ya kuma gode. Ya lallashe ta da cewa,ta yi
    hkr su amshi kyautar Allah dn haka wani na nema
    da kudi bai samu ba. likita ya ce,Kada ta
    damu,taci gaba da bai wa danta abnci tana hada
    mishi da nonon,a hnkli zata yaye shi bana farat
    daya ba. Bayan ya kaita gida ya kuma
    lallashenta,saiya nufi gurin Umma. Bayan sun
    gaisa,ta tambayi iyalanshi ya ce "Daga asibiti ma
    muke da Bishira." Umma ta dube shi da
    sauri,Waye ba lfy? ya ce, Ita ce.Sai kuka ma take
    yi wai dn an ce tana da ciki. Umma ta ce, Ikon
    Allah, to Allah ya inganta.Sai dai kuma kada
    Walid ya sha ciki. Abba ya ce,likiya ma ya yi
    mata bayanin yadda za ta yi masa,hr ta janye shi
    daga nono cikin hikima.Umma ta ce, Da za ta
    yarda ma an kawo mana shi nan. ya ce,Ai dama
    nan zan kawo shi da zarar an yaye shi Umma.
    Sam bai fada ma Bishira nufinshi na baiwa Umma
    Walid ba,dn yasan ba zata ta6a laminta ba.Sai
    dai itama tasan dole hakan zai yi. Don haka ta
    garzaya gurin Umman Bashir ta shaida mata
    cewa sunje asibiti,dk ta fada mata komai,sannan
    ta ce ita danta take tunani kada ya dauka ya
    kawo wa Ummarshi ita ma a mallake mata yaro.
    Umman Bashir Ta ce Wannan a zaune take,sai
    dai in ko ba a kai shi ba.Amma ki bari daga kin
    kula ya daina damuwa da nonon ki janye shi,zan
    zo in taho da shi wurina. Bishira taji dadi tare da
    cewa, Hakan dai yafi. Sabuwar kazanta ta
    samu,Bishira dk abn bi bangon daki an tofe da
    yawu.Rashin wanka sabo,kai abn nata sai
    addu'a. Ibada kuwa ba a mgn,domin dai tuni ta
    aje Sallah a gefe,Azumi dai tana yi amma in ta
    sha bata ramawa.Allah ya shirye wanda ya 6ata.
    Abba ya dai yanzun tuni ya yafe abincin
    gidansa,matsawar ba shi da kanshi ya girka
    ba,don kuwa dama can shi mutum ne mai
    kyankyani. In zata fita takan wanke kafafunta ta
    dauki kaya ta saka,sai ka rantse tayi
    wanka.Amma da zata matso kusa da kai,nan za
    ka ji kauri na tashu da karni da kuma wari. Dole
    ya hkr da laluranshi ta aure a gurinta,domin in
    yaje shimfidarta ba zata ki ba,amma wari da
    zarni suna hana shi yin komai cikin nutsuwa. In
    kuma dakinshi ya kirata ko bata kwana ciki ba
    har gari ya waye yana jin warin jikinta a
    shimfidarshi don haka lokuta da yawa yake
    hakura da ita. *********** . Ummi tana kwance
    kan gadonta,yayin da Khadija da Safiyya suke
    zaune bakin gadon Safiyyan wadda ke kallon
    Ummi. Hirar masoyinta take basu,Safiyya bata ko
    gajiya da zancensshi. Khadija ta ce,ita ma da
    zata taho har kuka nata Saurayin ya yi. Sai lkcn
    Ummi ta dube su,"kuka Khadija?Khadijata
    ce,"Riris Kuwa. Ummi ta ce, Hu'um ba namijin shi
    yasa nike da za6i a kan irin mijin da zan aura.
    Safiyya ta ce,"ke banza,dk cikin so ne. Ummi ta
    ce Ban damu da sai namiji yaso ni ba,in dai ya
    tara abubuwan da nake so ga namiji to zan yi
    amfani da kasantuwata 'ya mace in koya mishi
    Sona. Khadija ta tashi ta dawo kusa da Ummi,Kin
    san me ki ke fada?Koda yake sanar damu yadda
    ki ke son mijinki ya kasance? Ummi ta ce "Na
    farko mai son Addini,Mai Ilimi duka 2,mai hakuru
    ,sannan yana da saurin fushi,mai kuzari da
    kwarjini. Ma"abocin tsafta da tsantseni,wandadk
    tufafin da yasa sai sun kar6e shi,mai biyayya ga
    iyayensa,sannanmai kula da gidansa,baki mai
    tsare gida,ga yawan Ibada, Safiyya da khadija
    suka kwashe d dry,Khadija ta ce, Ina za ki samu
    dk mai wadannan lissafin da ki ka yi??? Safiyya
    ta ce, Kuma fa bata gama lissafin ba ke ba ki ji
    ana cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba?
    Ummi ta ce,Akwai shi,Ya Abbanmu haka
    Halayansa suke. Yanzu ma da ni ke lissafin shi
    na ke kallo a idona.Khadija ta ce,To ba dan
    uwanki ba ne da shi kenan kin samu a gida.Ummi
    ta ce,Wuu fitina Road,wannan ya mugun tsanata,
    ina son dai me irin halayarshi ds
    dabi'unsa.Khadija ta ce,Har da kamaninsa? Ummi
    ta ce,sosai ma. Saitaga sun sa dry.Safiyya ta ce,
    Malma shi ki ke so,kuma dk yanda a ka yi ba
    shakikin ki ba ne,da aure a tsananinku. Umma
    tayi Shiru tana kallonsu,Khadija ta ce,Habiba
    kenan,wai har saurin fushinshi tana so. Ummi ta
    6ata rai tare da cewa,Tunda kun kasa fahimtata
    shi kenan.Ya zan yi in ce ina son Ya Abba yana
    da matarsa? SAfiyya ta ce,ke dai in da aure
    Tsakaninku kada ki tsaya "ZURFIN CIKI, kizo a
    karshe kina da kin sani. Ummi ta ce,A bar
    zancen. 32... Sai dai kuma a daran ranar ta
    tsinduma duniyar tunani.Tabbas zuciyarta da
    shisshiga take,tunda ta rasa wanda zata so sai
    Ya Abba. Wanda ya yi mata muguwar tsana.Afili
    ta ce,Duk kauce-kauce da kewaye-kewaye ba za
    su kai ni ba,Ya Abba nake so. Hawaye Suka
    soma sintiri daga idanunta. Wannan lkcn ziyarar
    da yazo Abba da Umma d Tsohuwa da Alhj
    Karami dk suka zo. Dadi ya kashe Ummi,ta rasa
    jikin wanda zata fara fadawa don dadi. Alhj
    karami ta soma kamkamewa sannan
    Umma,Tsohuwa kam ai tana manne jikinta hr
    suka zo tafiya.Shi ko Ya Abba yanzun kunyarshi
    take ji,dn haka tunda suka gaisa mgn bata kara
    hada su ba. Sai dai jife-jife suna satar kallon
    juna,in sun hada ido sai ya dan daure
    fuska.Safiyya da khadija sun gaisa da su sannan
    sun yaba da yadda a ke ji da Ummi. Da za su tafi
    kuwa Ummi kuka Tsohuwa kuka,sai da Abba ya
    ce ba za a sake zuwa da su ba,Sannan Ummi tayi
    shiru.Sun tafi sun barta d kewarsu,Kamar yadda
    suma suka tafi suna kewarta. ********** . Bishira
    da kanta ta dauki Walid ta kai ma Umman
    Bashir,domin ta san zai kai ma Ummanshi ne.
    Abba ya rufe ta da fada lkcn d y tambayi dan ta
    ce ta yaye shi ta kai ma Umman Bashir. Ya ce To
    je ki dauko mn yarona,dn ba can nayi niyyar kai
    shi ba,Ta rike kugu,kaje mana da kanka,tunda ba
    ka son zamn danka hannun mahaifiyarka to ni ba
    zan yi saken da Mahaifiyarka tayi ba a ka raba ta
    da danta ina fata ka fahimci karatuna? Kallo
    kurum ya bita da shi,sannan yaja tsaki tare da
    cewa,Dube ki kmr wata Bauna,jiki sai tsami yake.
    Ta ce,Eh dk abn da zaka ce kace. Ya juya ya fita
    rai 6ace. Umma ya Samu ya fada mata, ta ce, To
    menene na bata rai Abba? Can din da nan ba dk
    daya ba ne? ai ba za su cutar da shi ba. Ya ce, ki
    fahimce ni Umma,ba ina nufin zai cutu ba
    ne,amma can da yara kanana,nan kuma babu.
    Sannan......... ...... Sai kuma ya yi shiru tare d
    cewa,Shi kenan. Umma ta ce,Yauwa bana son
    kana daga murya kan abn da bai kai ya kawo ba.
    Allah ya raya mana shi ya kuma sauketa lfy.
    Abba Ya ce Ameen. Gidan (T.V)sun kira Abba sun
    masa (intervier)da kusan wata 2,dmn ya cire ran
    samun akin, ko da yaje suka ce sun dauke shi
    aiki. Abn d yasa suka yi jinkiri daukarshi,suna
    canza tsarukan aikin ne sannan sun sake
    tantance ma'aikatansu. Litinin Abba ya soma
    zuwa aiki kmr yadda a ka bukata,dakin watsa
    labarai a ka kai Abba. Sam bai samu matsala
    ba,dk d shi na mai yawan surutu ba ne,amma a
    cikin sati 1 ya goge da aikin,km an yaba da yadda
    yake watso labarai. Yana yi da Hausa minti sha
    biyar da turanci minti sha biyar,ana sakawa karfe
    7 na yamma. Abba ya kama aiki cikin sa'a nan
    da nam sai farin jini cikin abn d bai fi wata ba ya
    nemi izinin a bashi fili koda mint 15 ne don
    gabatar da wani fili da ya yi masu don matasa.
    filin yana kiran shugabannin matasa na
    unguwanni suna hira da su akan halin da matasa
    suke ciki na shaye- shaye da sace-sace da kuma
    rashin sana'a. Da turanci a ke shirin,sannan a kan
    baiwa sauran matasa na gida su bugo waya su
    fadi nasu ra'ayin,game da abin da ya kawo
    hakan,da kuma hanyoyin da za a bi don magance
    su. Haka nan ya kan samu lkc ya shiga cikin
    matasan musamman ma su shaye-shayen da
    marasa sana'a dn jin ra"ayoyinsu,da dalilan
    fadawarsu cikin harkar. Kafin wani lkc filin ya yi
    suna kuma kullum yakan tallata filin kan cewa ya
    kamata Gwamnati ta dauki nauyi filin don yana
    taimakawa mata wurin inganta rayuwar matasa.
    Cikin ikon Allah sai gashi Gwamnati ta yaba da
    filin,ta dauki nauyin shirin kuma an sa shi hr
    fannin Radiyo. Lallai Abba ya shigo da kafar
    dama,Sannan hukumar gidan Radiyo tayi Matukar
    farin ciki da zuwan Idris Aminu Idris,wannan
    Ma'aikata. Sannan sai Abba ya zama wani sabon
    tauraro wurin Al'umma,dk in da a ka ganshi ya
    zama abn kallo. Matsalar shi daya gidanshi,in ka
    ganshi a waje Sam ba za a kayi tsammanin haka
    zaka samu gidanshi ba,Dattin ya karu,musamman
    da ya kasance yanzun ba shi da lkcn kanshi
    ballatana ya yi sammakon share gidan. Wankinshi
    mai kaiwa yake yi,haka nan nasu ya ce ta dinga
    kaiwa makota gidan wanki. Amma kafin ta hada
    ta kai aiki ne ita dai tayi kallo ko a shiga makota
    hira. Sam Abba ko adreshin Zai bada ya
    gwammace ya bada na gidansu Ummanshi dn ba
    ya so aje gidanshi ************* . Kwanci tashi
    Ummi suna ta fana da jarabawa zuwa (SS2) cikin
    ikon Allah suka gama. ranar da aka yi musu hutu
    kamar ta sani bata tsaya jiran Abba ba,Ta nufo
    gida. Shi kuwa lkcn suna kici-kicin kai Bishira
    asibiti zata haihu,amma yana sane da cewa yay
    Ummi zata dawo kuma hnklinshi na can. Motar
    wani Salis Abokin aikinsa ya aro ya kai su
    asibitin ita d Ummanashi. Bayan ya ba d dk wani
    abu da suke bukata ya ce Umma za shi dauko
    ummi. Umma ta ce,Ka barta tukunna in matarka
    ta sauka lfy gobe sai kaje tunda tana mkrnt ne.
    Ya yi-ya yi Umma ta ki,dole ya hkr. sai bayan
    la'asar sannan ta haihu,Nurse ce ta zo tayi musu
    albishiri an samu 'ya mace. Bayan an kintsa
    uwar,sannan a ka kaita dakin hutu,su kuma a ka
    kawo musu 'yar.Nurse din da ta kawo 'yar ta ce
    d Umma ke ce Mamanta? Umma ta ce,'Eh."Nursr
    din ta ce "kazantar yarinyar tayi yawa,kafin ta
    haihu sai da likita ya korata ta yi wanka,muka yi
    mata aski ko'ina jinkinta datti. Gsky Mama
    mijinta yana kokari,yanzun kuje ku dafa ruwan
    dumi ku kawo mata tayi wanka. Abba ya yi tsaki
    ya ce, kin ji ko Umma,Allah ya kara.Umma ta
    ce,Yanzun kaje gida ka dauki babban filas dina ka
    shiga wurin Umman Bashir ka ce Mata ta dafo
    ruwan Zafi,daga nan ma sa ji haihuwar. Yana
    shiga gidan tun daga zaure ya jiyo Muryar
    Tsohuwa tana cewa,Naji shiru-shiru kin ga dai hr
    yanzu. Yana saka kafa a tsakar gidan muryar
    Ummi ta daki dodon kunnanshi.in da ta ce,Kila
    kuma ta haihu yanzun. jinin jikinshi ya tsinke dn
    jin Muryae. Ya nufi dakin.Tana zaune tana shan
    rake. Ya dubeta, ita ma shi take kallo dn tunda ta
    diro ba wanda take muradin Gani irin shi,cikin
    sanyi murya ya ce,Ummi ke da wa ki ka taho? Ta
    sunkuyar da kai,Ni da wasu 'yan mkrntrmu ne
    muka dawo. Ya ce '"Good,tashi ki dafa ruwan zafi
    ki zuba a babban flask. ya dubi Tsohuwa da take
    ta tambayarshi ko mai dakin nashi ta sauka? Ya
    ce, Eh ta haifi 'ya mace. Tsohuwa cikin takaici ta
    ce,Sai yanzu kaga damar bani amsa?Dan
    walakanci kawai? Kai mai sunan Malam ka gyara
    halinka. Abba ya ce,Yi hkr Tsohuwa dk na gaji
    ne,Nan kuma ina yi wa Ummi mgn. Ta ce kana
    mata fadan ka dai. Ya ce,Tsohuwa wai ni hr
    yanzun ba zan wanku a wurink ba game da
    Ummi? ta ce, Ina fa zaka wanku?Har abada mai
    sunan Malam kai ba me kaunar takwara bane. .
    Yace to naji a bar maganar yanzu dai kishiyarki
    ta haihu.an samu ya mace.tace Allah ya raya
    mana. Yana jingine da bango yana kallon ummi
    tana ta shige da ficen daura ruwan zafi.komai
    cikin tsafta da natsuwa take yi. Sai da tasa
    ruwan zafi ta wanke flask din kasancewar anjima
    ba'ayi amfani dashi ba.ta tafasa ruwan tazo ta
    bashi,ya ciro wayarshi ya mika mata. "sa min a
    caji naga nepa sun kawo wuta" ummi ta jona
    waya sannan ta ci gaba da girkin dare don tasan
    Alhaji bai cika son wani abu da dare ba sabanin
    tuwo. Ta gama wanka sannan tayi sallar
    magariba tana kwance gadon tsohuwa tana
    tunanin abba. Tsohuwa nata lazimi in tayi
    magariba bata tashi sai tayi isha sannan taci
    abinci.ummi ta tuna wayar da yaya abba ya bata
    ajiya. Da sauri ta tashi tare da cewa "ke tsohuwar
    nan anzo tayaki hira kin share mutane" ta mike
    ta nufi daki ta dauko wayar ta kunna HEHE KIN
    MANTA YAYA ABBA KENAN?" Sakwanni ne sukai
    ta go slown shigowa sannan sai kira tashin farko
    data daga wayar muryar mace taji, ta ce "dawa
    nake magana" wadda ta kira ta ce "ina mai
    wayar?" ummi tace "dq matarshi kike magana,ke
    din wacece?" waccac n ta ce "in yazo ki
    tambayeshi? yasan me lambar." nan da nan sai
    ummi ta samu kanta yana juyawa,tayi tsakita
    kashe.ta shiga duba sakonnin da yawansu na
    mata ne masu sonshi,daidaikune na maza masu
    nuna yabawar aikinsa.hankalin ummi ya tashi
    ganin yadda mata suke farautar abinda take
    tsananin so.ta kashe wayar cike da nadamar
    kunnata Hankalin Ummi ta samu kanta yana
    juyawa,tayi tsaki ta kashe.Ta shiga duba
    sakonnin da yawansu na mata ne ma su
    sonshi,dai-daiku ne na maza ma su nuna
    yabawar aikinsu. Hankalin Ummi ya tashi,ganin
    yadda mata suke farauta abnda take tsananin So.
    Ta kashe wayar cike fa nadamar kunnata. Sintiri
    ta dinga yi a tsakar dakin,Sallamarshi ce ta, katse
    ta.Ta amsa ciki,sannan ta zauna ba tare da ta
    kalle shi ba. Ya ce,Bani wayata da abinci 'yan
    asibiti. Ta mike ta dauko masa abncin,sannan ta
    bashi wayar.sai dai tana yin komai ne fuskarta
    daure. Ya ce,Lafiya na ganki wani iri?ta dago ido
    ta kalle shi,ta sake tsuke fuska. lfy lau.Ya ce,shi
    kenan na tafi Sam bata tanka ba. Yana fita ta
    mike a kujera,so takeyi a lkcn ta samu makanta
    mafita,shin ko dai ta tare shi ne ta fada masa?
    wata zuciyar ta ce,In ko ya dinga kwallo da ke
    sai kin rasa mai cetonki. Ta tashi tare da
    cewa,Bari kawai in fada ma Tsohuwa.Zuciyarta ta
    sake rayawa.Tsohuwa fa ba zata yarda ba, domin
    kullum tana bada shaidar tsanar da Ya Abba ya
    mata,ta koma ta zauna. Sai ta samu kanta da
    fashewa d kuka,tana fadin wannan wace irin fitina
    ce ta same ni?me yasa zcyt ke son tozarta ni?
    Me yasa zata so wanda ya tsane ta?Ta mike ta
    shige uwar daka. Gado ta hau tana son ta lallashi
    zcyrta,dn ta daina son Ya Abba. Shi kuma yana
    tafe a mashin zcyrshi na mitar bata gaji da ganin
    Ummi ba,yadda take ta kai kawo ya ke gani a
    idonshi. Lkcn da ya kai musu abnci me jego ta
    gyare,dama ta zubar d jini ne shi yasa suka ki
    sallamarta,sukace sai da Safe. Ya samu kannanta
    sun zo da wata 'yar Babnsu.Sun gaisa an yi 'yar
    hira sannan suka ta fi lkcn ya dauki 'yar ya yi
    mata kallon sosai. Ya dubi Umma kin san
    yarinyar nan da wa take min kama?Ta ce,A'a.
    Bishira ta tsare shi da ido,ya ce lkcn d Ummi na
    karamarta sak wannan. Umma ta ce,Kana nufun
    d Ummi take kama?ya ce,"Eh,Bishira ba kunya ta
    ce,Allah ya kyauta ni 'yata bata kama da wata
    can wai ummi. Umma tayi saurin cewa,Dama
    zolayarki yake ba suyi kama ba.Shi kuma ya
    kalleta.Ko ki so ko kada ki so yarinyar nan sak
    take kama d Ummi. Ya mika ma Umma ita,yana
    ci gaba da fadin Maman Walid kina bani
    mmki,kina zaton zan ki raba 'ya'yanku d Ummi?
    Ya girgiza kai"Sun hadu hr abada ,domin in kin
    tsaga jikin 'ya'yanki dole za ki ga jinin Ummi. to
    ya ya ma ki ke tsammanin zan so wanda ba ya
    son Ummi? Ta ce, "Oho! Ni ba ka sona kenan?To
    in da na gode ma Allah dk dyniya ta san cewa
    Ummi bata kaunarka.dk da kana wanta.Ba ita ba
    ce silar kariyarka?ko an kashe ka ma bata da
    asara. Umma ta ce,'Abba jeka ban son in kuma
    jin bakinka in na isa. / ZURFIN CIKI book 2 part 7
    ZURFIN CIKI book 2 part 7
    Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:16
    Ta samu an saka ranar auren fati da saurayinta
    Fahat,nan fa Alhj ya ce dama ke ni ke jira uwata
    ki dawo. A masu sonki ki fito da daya a hada
    auranku da 'yar uwarki Fati. Hankalin Ummi ya yi
    matukar tashi,ranar kasacin abnci tayi. Da suka
    zauna da Umma a daran ta ce Umma baki fada
    ma Alhj bani da tsayayyen saurayi ba?Umma ta
    kalleta,ba shi yasa na ce Kitsada ba,amma ba kya
    son fita. Duk kin bi kin kori masu sonki Abba na
    daure miki gindi,kin san dai Alhj ba yarda zai yi ki
    wani ci gaba ba,gara ma kin yi kokarin fidda miji
    kafin lkcn da ya dibar miki,in ki ba haka ba ya
    daki da mai rabo. Ummi tasa kuka ranar,kwana
    tayi tunani hr ta yanke shawarar zata fada ma
    Alhj Ya Abba take so. Da safen taje hr dakin Alhjn
    ta gaishe shi,ya ce uwata naga kamar bakinki da
    magana ko?Ta dube shi "Eh,a'a ba komai.Ta
    mike,dakin Tsohuwa ta shiga ta haye gado ta
    soma kuka. Tsohuwa ta dubeta a rude,Takwara
    ke da waye,? Nasan ba zai wuce me sunan
    Malam ba,dn shi ne kadai ke hana ki sukuni. A
    ran Ummi ta ce,shi ne kam,amma ba irin wanda
    ki ka sani ba. Amma a fili sai ta ce,Tsohuwa Alhj
    ne wai in fito da miji,kuma abn da ke damuna ni
    ba wanda na ke so. Tsohuwa ta ce, "Au, shi ne
    abn kuka?To bari kiji bana ba zan goyi bayabki
    ba,dn da ubanki ya ji ta tawa da yanzyn kina da
    diya 2 in da rabo. Amma mai sunan Malam ya ce
    za ki ci gaba da krt,yamzun ko tun da Allah ya
    kawu mu angama wannan kaddararriyar mkrnt ba
    sai aure ba? Ga Bunta nan hr an yi baiko, to rana
    guda za a yi shi in muna cikin masu rai. FUU
    Ummi ta fice,ta shiga dakin Umma tana tunanin
    wa zata fada ma matsalarta?kamar an tsikareta
    ta dauki mayafi zata fice. Umma ta ce, "Zo nan,
    ina za ki? ta ce "Wurin Fati. Tana shiga Bashir
    zai fito . Ya ce Yauwa Ummi ina son magana da
    ke. Ta dawo baya ya fita kofar gida ita ma ta
    fito,suka tsaya ya ce "Ummi gaskiya dama ba
    wani abu ba ne, ni dai na tsinci kaina da sonki.
    Ummi ta dafe kirji da sauri."Sona?" ya ce kwarai
    kuwa, dn haka za ya ki ka gani?ta dube shi,sam
    babu wata alama da ke nuna cewa dan uwan Ya
    Abba ne. Ta girgiza kai "kayi hakuri kawai Ya
    Bashir,wlhy zuciyata ta jima da kamuwa da son
    waninka." ya ce, Me ki ke nufi?Kin fi son bare da
    ni jininku? Ummi ta ce,"Ni dai na fada maka." Ya
    ce, "To kin fada min,ni kuma zan fada wa su
    Alhj." Gabanta ya fadi. Shi kuma ya yi tafiyarsa, .
    Sabon tashin hankali kenan. Sai damuwa ta
    lunku,bata ta6a marmarin zamn mkrntr kwana ba
    sai ranar. Ta rasa me zata yi taji dadi,gida ta
    koma cike da nadamar fitowa,ta zauna a falon
    Umma ta soma kuka. Umman tana dakin mijinta
    ya yi karin kummali. Sai da ya fita sannan Umma
    ta maido hankalnta ga lamuran gidan, kan kujera
    ta samu Ummi ta nata rera kuka. Umma ta ce
    "Ke Ummi lafiyanki? Abun ya soma zama iya
    shege,daga cewa ki fito da miji sai ki tsira kuka?
    To ina ganin kwadantaki zamu yi muci. Ummi ta
    ce, "Ni fa ba kukan da nike yi ba kenan,ni fa Ya
    Bashir ne fa. Umma ta ce Bashir me,? kiranki aka
    yi? Gara daya da ke ki. ta ce ba fa dukana ya yi
    ba wai cewa yai wai fa yana sona. Tab,Allah ya
    tsare ni. Umma dn Allah bana sonshi,gaban
    Umma jikinta a mace ta ce "Tabdi,ai ko in Alhj ya
    ji wannan zancan ta zauna. Ummi ta sake
    firgicewa, cikin kuka ta ce Da na shiga 3 Umma,
    ya ya zan yi ne don Allah?Umma ta ce,"Mafita
    daya ce ki fidda wani kafin zancan yaje wurin
    Alhj. Yinin ranar Ummi ta rasa mafita Addu'arta
    daya,Allah ya turo mata ko ma waye a daran yau
    ta ce ya turo iyayenshi. Wayar Umma tana
    hannunta,ta rubuta text ta goge yafi sau 20 da
    niyyar ta tura ma Ya Abba cewa tana
    sonshi,amma da ta tuno da irin dukan da zai zo
    gidan ya yi mata in ya karanta sai ta share. Ita
    dai ta san shi kadai take so. Tayi Sallar Istihara
    kusan sau 3,amma hr yau zcyrta na nan makale
    da son Ya Abba. Don bayan Isha'i kuwa a ka aiki
    kiranta, ai tare da dan aike suka fita. Wani
    saurayi ne wai shi Sahabi,dan unguwar ne Kuma
    sana'ar aca6a yake yi. Na dai manta. Suka gaisa
    ya gabatar da kanshi sannan ya fada mata dalilin
    zuwanshi ba tare da wani nazari ba,ta ce ta
    amnice. suka yi sallama ta dawo gida,umma ta
    tambaye ta wanene?Ta fada mata,sai dai Umma
    bata gane shi ba. Can jimawa Bashir ya aiko
    Kamal kaninsa wai Ummi tazo,ta ce kaje ka ce
    masa ba zan zo ba,ya sake aiko shi cewa in bata
    zo ba shi zai shigo. Umma ta ce mata tashi kije.
    Ummi hr d kuka ta fita,dn a rayuwarta ta tsani
    Bashir,sbd yanda ya raina Umma. Kuma ba ya
    ganin kowa da gashi sannan tana ganin in hr ta
    auri Bashir zai mata tsakani da auren Abba. Tana
    zuwa ta same shi zaune a dakalin kaofar gida,ta
    isa gurishin. Ya Bashir kiran me ka ke min? Ya
    ce,kin sani kema. Ta ce Ya Bashir dn girmn Allah
    ka bar ni ba,Usaina gidan kurma ce buduwarka
    ba? Ya ce Da ba, ya ci gaba da cewa,Ummi ina
    sonki so na hakika nayi mamakin yadda lkc daya
    zcyta ta kamu da sonki,to wai dn Allah ni me
    yasa ba ki sona? ta ce Ya Bashir ina da wanda
    nake so tun farko..........kamar daga sama suka ji
    muryar Abba yana cewa,Kai Bashir me ka ke
    fada? ya ce sonta nake. Abba sai da wayarshi da
    ke hannunshi ta kwace ta fadi don figici,bai bi
    takan wayar ba ya isa gabn Bashir ya ce, In ka
    kuma furta kalmar so ga Ummi sai na maka
    matsiyacin duka,ke kuma hr da fitowa kin zo tadi
    ko? kafin tayi magana ya ce,Bace min daga nan.
    Bashir ya ce,Amma ai ba laifi ba ne don nace ina
    sonta? Abba ya bige mishi baki tare da cewa In ji
    wa ya ce maka ba laifi ba ne?Bashir ya ce,An
    haramta aure tsakaninmu ne? Abba ya cakumo
    wuyan rigarsa Ni ne nan na haramta haka,kuma
    kar in kara jin wannan mgnr. Bashir ya fige ya
    nufi gida yana fadin cewa Yau zan samu Alhj da
    mgnr. Ina ruwanaka da zaka ce ka haramta min
    sonta? . Abba jikinshi hr 6ari yake dn tashin
    hankali, yasan in mgnr taje teburin Alhj to ta kullu
    yanda yake mishi mgnr hada auran Ummi da Fat.
    Har ya saka kafa a zauran gidan su Umma,sai
    kuma ya fasa ya dawo ya nufi gidan su Bashir
    din,yana saka kafa a zauren gidn Alhj Krm na
    fitowa. Don haka sai yaja baya,Alhj ya fito ya
    ce,A'a Abba ne? Abba ya ce "Eh ni ne. Ya gaida
    Mahaifin nasa,sannan Alhj ya tambaye shi cewa
    Babn naka yana gida? Gaban Abba ya yi
    mummunan faduwa,ko dai Bashir ya fada wa
    mahaifinsu ne? Alhjn ya ce ko ba ka ji ba?Abba
    ya ce "Eh a'a ban riga na shiga gidan ba. Alhjn
    ya ce To bari in ganshi. Nan jikin Abba ya jike da
    zufa. Da azama ya shiga gidan. Mahaifiyarsu tana
    alwala ya ce Umma ina Bashir? ta dube shi
    Lafiya ba ko sallama? ya ce Nayi ba ki ji ba ne?
    ta amsa sannan ta ce lfy ka ke nemanshi? ya ce
    lfy lau. ta ce Yana daki,shima na ganshi ya shigo
    a fusace. Abba ya nufi dakin. Bashir na zaune kan
    katifar idonshi na kasa yana girgiza kafarshi ta
    dama,Abba ya shiga ya ce,Bashir nazo ne in sake
    gargadinka a kan Ummi,sai dai naga hr kayi
    kuskuren fada ma Alhj krm ko,? Bashir ya mike
    ya daga sauti Ban fada mishi ba,amma ina da
    niyya. Ina sonta babu wanda kuma ya isa ya
    hana ni sonta. Abba ya kashe masa fuska da
    mari. Sai suka ji muryar Mahaifiyar tana cewa,
    Kara mishi Abba,ka cika dana. Ta shigo dakin hr
    gabn Bashir ta ce, Ni za ka tozarta? kayi kuskure.
    Ai da in ga ranar aurenka da Ummi gara naga
    gawarka kwance yafi min sauki. Abba da Bashir
    suka dubeta a rude. Ta ci gaba da cewa Bashir
    kai ma kasan ba zai ta6a sa6uwa ba ne in hada
    jini da Suwaiba,kafi kowa sanin kin da nike
    mata,zan iya daukar ranta ba don tsoron hukuma
    ba. Kuma hr dny ta nade ba zan ta6a kaunarta
    ba,kai ko fatan alheri ba zan ta6a mata ba. Ta
    kalli Abba, Baka ta6a faranta min rai ba irin
    yau,dama nasan cewa dole wata rana ka bayyana
    dana in dai kai jinina ne,na gode Allah da yasa ka
    zama mai kishina Kuma ka wanke dukkan
    laifukan da ka min a baya da ka nusar da ni
    Bashir na shirin jefa rayuwata a cikin garari,da ba
    ka mishi mgn ba yaushe zan san yana shirin jefa
    ni cikin bala'i. . Abn da Umma bata sani ba shi
    ne,tuni Abba ya yi mutuwar tsaye,hnklshi ya
    ninka na Bashir tashi,dn haka Bashir ya riga shi
    fita daga dakin. Da kyar Abba ya dago ido ya kalli
    Umma,ta ce Daina damun kanka shi ma din ko
    ba don Allah ba zai dawo hanya,duku-dukayau
    sati guda fa kenan da naje kauye na saida 'yar
    Akuyata guda daya sannan na bada kaji 2 ga
    Bokan kuka sbd a min akin da Ummi ba zata
    samu miji ba. Sai kuma a ce ko satin bai rufe ba
    dana na cikina ya zo ya ce yana sonta? Da sauri
    Abba ya dafa kirji Umma Boka! Boka ki ka ce
    Umma? Inna lillahi wa'inna ilaihin raji'un,Umma
    kin san cewa zuwa gurin Boka shirka ne ga
    Allah? kin san duk wanda ya mutu a shirka Allah
    ya yi alkawarin kona shi a wuta?Umma kina cikin
    hadari............ta kaste shi. Kai Abba!Ni ce nake
    cikin hadari?Ni ce Allah zai kona a wuta? ya ce,
    umma bana nufin haka, ina fada miki ne ki kiyaye
    da zuwa gurin Bokaye makaryata,macuta 6arayin
    Imanin Jama'a. Na ranste miki da girmn Allah
    umma Bokaye 'yan wuta ne,matsawar ba su tuba
    ba. Ta ce, Kai ni rufe min baki,da za ka ce karya
    ne sau nawa suna min asirn kuma yana ci. Ba
    gashi nan da ya min na kada Ummi ta riga Fati
    samun miji baga Fatin ta riga samun ba? ummi
    kuma ba ta d masoya. Abba ya ce, Umma kin ga
    karya ko? wa ya fada miki Ummi bata d masoya?
    ta ce, To me yasa ba wanda ya tsaya? Ya ce, Ni
    dai Umma ki bar zancan nan a wurina, Bashie zai
    bar Ummi ko yana so ko baya so,dn haka na
    hada ki d girmn Allah kada ki koma gidan
    mishieikin Bokan nan. Ta ce, Ba zan koma ba in
    hr zaka raba Bashir da alakakai din yarnyar nan.
    Ya ce Na miki Alkawari. ta ce, Shikenan. Ya fice
    jiki babu karfi.URFIN CIKI book 2 part 8
    ZURFIN CIKI book 2 part 8
    Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:18
    Kasa shiga gidan su Umma ya yi,haka nan ya
    manta sam da batun motar da yazo da ita a
    kofar gidan Umma. Ko Bishira bata san cewa ya
    shigo gidan ba,tana can jarabar kallonta na
    tsiya,ya rufe gidan ya nufi dakinshi. Ranar mu2m
    5 bacci sai dai 6arawo,Umman Bashir kwana tayi
    saka da mugun zare. Umman Abban ma juyi
    kurum take yi hr Alhj ya gaji ya ce,Yau dai sai
    juyi ki ke yi. ta ce Na kasa bacci Alhj. Ya ce,
    Tashi to kiyo alwala kizo ki kama sallah,in kina
    da damuwa ne sai ki fada ma Allah. Umma bata
    tsaya ba,ta tashi. shi ko Abba wani matsanancin
    ciwon kai ne ya hana shi sallah. Ya dai yi
    nasarar yin alwala da ya shiga daki sai jiri. Dole
    ya kwanta rigingine tare da dafe kanshi da
    hannuwa guda 2,sunan Allah yake ta kira dan
    neman dauki. Ita ko Ummi dirshan ta zauna tana
    kuka,hr sai da hawayenta suka kafe,idanunta
    suka shiga zafi,kanta ya soma sarawa gefe daya.
    Ita ma ringingine ta kwanta tare da lumshe
    ido,Istigfari kurum take yi tare da hailala,shi ko
    Bashir mafarkai ne suka hana shi bacci,dk
    mafarkan na Ummi ne. Da safe da matsannancin
    zazzabi ya farka,dn haka bai iya zuwa Masallaci
    ba,da kyar ya yi alwala.yana idar da sallah ya
    kundundune cikin bargo. Matsanancin ciwon kan
    da Ummi ta tashi dashi ya firgita 'yan
    gidan,Musamman Umma wadda ta same ta
    kwance a tsakar daki da safe. Ganin fuskarta a
    kumbure ya tsorata Umma,hr sai da ta kira
    Alhj.Nan fa Alhj ya dauko wayarshi ya shiga kiran
    Abba,kan cewa yazo ya kaita asibiti. Sai dai tayi
    ringing ya kai sau 10 amma ba a daga ba. Alhj ya
    ce Ina yaron nan ya shiga ne?kuma ga motarshu
    a kofar gidan nan,na ganta da asubahi da na fita
    Masallaci. Umma ta ce,Tao Allah yasa dai lfy.
    Har karfe 8 Alhj na neman layin Abba shiru ba a
    dauka ba,ga Ummi rike da kai tana ta salati
    Umma ta ce,Alhj ko Bashir za ka sa ya duba shi?
    Alhj ya koma daki ya dauki hula ya nufi gidan
    Abba. Gidan a kulle ya same shi,dn haka ya dinga
    bugawa.Abba na jiyowa amma ba zai iya tashi
    ba,haka dk ringing din da wayarshi ke yi yana ji
    ya kasa tashi ne. cikin bacci Bishira taji bugun
    gida ya yi yawa,ta tashi ta bude. Da Alhj suka yi
    ido 2,ya ce lfy ba ku tashi ba? Ta ce Mun tashi.
    ya ce Ina maigidan naki? ta ce Ina ga ya fita,bari
    in duba. Ta juya ta nufi ciki. Alhj ya cika da
    mmk,ya za a ce wai mace bata san fitar mijinta
    ba? Anya wannan matar tasan darajan mijin?
    Tunaninshi ya katse lkcn da ta dawo tana cewa
    Alhj yana kwance ba shi da lfy. Alhj ya bita yana
    cewa Ba shi da lfy,amma ke ba ki sani ba?Wanna
    wane irin zama ku ke yi ace kina matarsa amma
    ba ki san cewa ya tashi ba lfy ba? Bishira ta ce
    To ai shi ne bai kira ni ya fada min ba. Alhj ya ce,
    Allah ya kyauta. ya nufi dakin. Abba na kwance
    ya kundundune cikin bargo sai rawar sanyi yake
    yi. Alhj ya yi Sallama ya shiga dakin ya rusuna ya
    daga daidai fuskarshi ya janye bargon ya ce,
    Abbana ba ka ji dadi ba? Abba ya bude
    ido,idanunshi jajir,ya ce Abba kaina ne tamkar zai
    6alle. Sai zazza6i tun daren jiya. Alhj ya ce,Ikon
    Allah Yau kuma abn da na wayi gari da shi
    kenan? Ummi ma na can kwance da ciwon kan,to
    tashi. Shi yasa nake ta kiranka don ka kaita
    asibiti amma da ka daga ba. Yanzu tashi in za ka
    iya ka kira Ahmada abokinka sai ya kai ku
    asibitin. Abba ya ce To Wayar Ahmada din a
    kashe don haka sai Alhj ya ce "Af, na tuno da
    Bashir,kintsa bari in je muzo naga mator can
    kofar gidanmu ko?Abba ya lulubo makullin motar
    yaba Alhj., Zani kawai Umma ta daura ma
    Ummi,sai ta zura mata hijabi,suka shiga bayan
    mota su 3 da Umma da Alhj,sukaje gidan Abba
    suka dauko shi. Bishira taso zuwa amma suka ce
    ba wuri ta bar shi kawai. Asibitin kudi ne kuma
    likita guda ne ya duba su. Ummi dai hawan jini
    ne don ita a ka fara dubawa. Gado likitan ya
    bata,sannan Abba ya shiga shima likitan ya ce
    jininsa ya hau,amma ba kamar nata ba. Nan ya
    roki likitan cewa kada ya fada ma iyayensu abnda
    ke damunsa,ya rubuta mishi magunguna kawai.
    Likitan ya ce Ba komai. Amma me ya ke
    damunku kai da sister dinka ciwonku iri daya
    kuma ya kama ku a lkc daya? Abba ya ce Ba
    komai lalura ce kawai a ka kaddara ta same su
    lkc daya.Da Abba ya fito sai ya ce ma su Alhj
    Zazza6i ne. sai dai shi kanshi ya ji mmkn
    ciwonsu iri daya. Yana jingine da bango a dakin
    da a ka ba Ummi gado,yayin da Bashir ya tsaya a
    gabn gadon Umma tana zaune a kan kujera. Alhj
    krm d Bbba suka shigo tare da Likitan ya kalli
    Abba Yarona kana bukatar bacci ga. Abba ya ce
    To yanzun zan tafi gida. Ya iso kan Ummi wadda
    a ka daura ma ruwa,ya ce ku barta ta huta bata
    bukatar hayaniya,don haka ku rage daga cikin
    dakin. Alhji ya ce, To mun gode. Suka tafi suka
    bar Umma. A mota Alhj ya ce da Abba,ka fada a
    wurin ainkan? ya ce, Eh abokin aikina ya kira ni
    kuma na fada masa. Alhj ya ce,To shi
    kenan,yanzun sai muje can gidanmu zaka fi
    hutawa... .Yanayin aikinku ne ba ka samun bacci
    ko? eh kurum Abba ya ce,amma shi yasan
    tunanin Ummi ne ya ke hana shi bacci da
    matsalolin da yake hangowa. Yinin ranar yasha
    bacci,sai kusan 4 ya tashi ya yi Sallah,ya ji dadin
    jikinshi. Bishira tana gidan Umman Bashir wai ita
    da tazo jinyar miji,tana bata lbrn wai Abba bai
    fada mata ba shi da lfy ba,ya kira Alhj yazo yana
    ta min surutai wai mijina ya fita ban sani
    ba,meye- meye? Umman Bashir ta ce, Da Allah
    kyale su,don wani sabon iskanci ma wai Bashi ne
    ke son Ummi. Bishira ta mike zumbur tare da
    cewa, Bashir fa ki ka ce Umma? Hu'um,lallai da
    wani abu. Bashi da ya tsani Ummi shi ne zai ce
    yana sonta? Umma ta ce, Sannu 'yar albarja,ashe
    kin fahimta,? Tabbas nasan ke za ki fahimta,to in
    gaya miki Bashir ko yau da safe fa sai da muka yi
    ta dashi. Dubi yadda Bashir ke min biyayya amma
    yau ina fada yana fada. wai hr da ce min shi bai
    ga wani mugun halin Suwaiba da nike fada
    ba,tana min alkairi amma ni kullum ina binta da
    sharri. Kai dai jin wannan zancan ka san ba yin
    Bashir ba ne,don haka na ce masa ba komai
    nasan ba yin ka ba ne. Bishira ta ce,Tabdi,Umma
    sai kin tashi tsaye. Ta ce ke dai bari ai ina cikin
    wani hali shi kanshi miji naki sai na nema masa
    taimako. Don wannan ciwon nashi ban yarda shi
    ba, kuma lkcn daya. Fati ta shigo gidan da
    sallama,ta shiga dakinsu ta canza kaya. Umma
    ta ce,sai ina? ta ce Ya Abba ne ya ce in zo in
    canza kaya zamu je asibiti wurin Ummi. Bishira
    ta mike ya farka ne? Ta ce Eh hr ya yi wanka da
    sallah Umma ta ce Bari in same shi bai gama jin
    sauki ba zai tafi wurin wata can kema banza
    mara kishi kin taho jiki Na 6ari,Fati ta ce,Umma
    don Allah ki daina irin wannan abubuwan,wlh
    Umman su Ummi bata yin haka Bishira ta fita
    tana fadin Ai Ummi yanzun ita ce uwar Fati, don
    bata jin mgnr kowa sai ta Ummi,tunda ta dawo
    mkrnt. Sun samu Tsohuwa ma hr ta shiga
    mota,shi kuma Abba yana jingine a jikin Motar
    yana sanye da shadda (Sky blue) Rigar 'yar 3
    Quarter kanshi da hula. Bishira ta ce,Babn Walid
    hr ka tashi? ya dube ta,sannan ya kai idanunshi
    kan fati Shiga muje. Bishira taja baya Ina ba in
    da za ni. Ya kalleta ke Kuma ke da wa? Wa ya
    fada miki da ke nake? yaja tsaki. Ta iso Ummar
    tasu Abba ka hakura mana da wannan tafiyar. Ta
    ce Naji sauki Umma. Tsohuwa ta ce, Mai sunan
    Malam ka shiga don Allah mu tafi. cikin sauri ya
    fada mota suka wuce. Yana yi wa Umman nuni
    da Hannu wai yana zuwa. Tsohuwa ta
    ce,Kinibibin banza ne da wannan matar taka mai
    sunan Malam kana bukata kara aure,me a ke da
    kazamar mace? Abba ya ce, Tsohuwa sha
    kuruminki zan sake aure,ke ce ma za ki bani, Ta
    ce, Ni a wa zan shiga maka ga . Bishira ta fita
    tana fadin Ai Ummi yanzun ita ce uwar Fati, don
    bata jin mgnr kowa sai ta Ummi,tunda ta dawo
    mkrnt. Sun samu Tsohuwa ma hr ta shiga
    mota,shi kuma Abba yana jingine a jikin Motar
    yana sanye da shadda (Sky blue) Rigar 'yar 3
    Quarter kanshi da hula. Bishira ta ce,Babn Walid
    hr ka tashi? ya dube ta,sannan ya kai idanunshi
    kan fati Shiga muje. Bishira taja baya Ina ba in
    da za ni. Ya kalleta ke Kuma ke da wa? Wa ya
    fada miki da ke nake? yaja tsaki. Ta iso Ummar
    tasu Abba ka hakura mana da wannan tafiyar. Ta
    ce Naji sauki Umma. Tsohuwa ta ce, Mai sunan
    Malam ka shiga don Allah mu tafi. cikin sauri ya
    fada mota suka wuce. Yana yi wa Umman nuni
    da Hannu wai yana zuwa. Tsohuwa ta
    ce,Kinibibin banza ne da wannan matar taka mai
    sunan Malam kana bukata kara aure,me a ke da
    kazamar mace? Abba ya ce, Tsohuwa sha
    kuruminki zan sake aure,ke ce ma za ki bani, Ta
    ce, Ni a wa zan shiga maka gaba a baka ku taru
    kai da matarka ku halakata?Duk da Abba yana
    jin jikinshi gim, sai da ya dar dara,sannan ya ce,
    Sai ka ce ma su yankan kai? Tsohuwa kuma da
    za ki ce na cika zcy yanzun ba ga mata nan ina
    da ita ba tana kawo miki karan ina dukanta ne?
    Tsohuwa ta ce Tabdi,ni yaushe ma wannan
    guzumar matar taka zata zo guna da sunan kawo
    min kara? Ban da ma haka ni bani shi da mara
    kunya. Ya ce, sai Ummi ko? koda yake ita ai
    takwararki ce shi yasa lkcn da tayi tata rashin
    kunya ta zama 'yar lelanki. Tsohuwa ta ce ai
    wannan ba kuciya ba ce? Yanzun ko kai ba ka fi
    ta hankali ba.Abba da fati suka sa dry. suna isa
    dakin suka samu Umma suna waya da Alhj,Ummi
    kowa hr lkcn bacci take yi. Abba ya jingina da
    bango yayin da Tsohuwa da Fati suka je suka
    tsaya a gabn gadon. Sunyi Sallama da Alhj shi
    ma ya kira ne ya ji ko Ummi ta farka. Ta ce
    masa ba ta farka ba,kuma Likitan ya ce an fi son
    tayi baccin. Nan suka gaisa tare da tambayar mai
    jiki,Abba kallon Ummi yake,yau daya duk ta fyade
    kmr ta yi sati,sonta da tsananin kaunarta ne
    suka sake mamaye ko'ina na jikinshi. Ya kalli
    Umma wadda ke tambayar nashi jikin, ya ce da
    sauki. Sannan ya kalli Ummi tare da cewa Umma
    wai dame Ummi ta fara? Umma ta ce kamar ya
    ya? Ya ce mmkn ciwon Ummi nake,wai hawan
    jini?Dama can bata da lfy ne? Tsohuwa ta amshe
    da cewa, ko kai ai kasa mata hawan jini,irin
    tsanar da ka mata Mai sunan Malam ai ta isa.
    Abba ya ce Don Allah Tsohuwa ki daina mgnr
    nan. Ya dubi Umma yana me kara maimaita
    tambayarshi. Ta ce ko kusa ai kasan Ummi bata
    cika laulayi ba ma,lalura ce dai yanzun bata ga
    babba ba ta ga yaro,amma mafari daga yi mata
    zancen aure shi kenan take ta kuka. Abba ya ce
    to don Allah Umma ku barta da zancen nan,ina
    krtn take so tayi kayanta,don gudun hawan jinin
    nan kada yakw tashi akai-akai. Tsohuwa ta ce
    Don kawai kada jinita ya hau sai a zura mata ido
    kada tayi aure?ai ko lallai sai dai kada jininta ya
    sauka. in ya hau,aure ya haifeta dole tayi shi,in a
    kasarmu ce ta Zamfara wane ita. . Abba ya ce
    Muje in kai ki gidan Tsohuwa. Ta ce ban tafiya,
    sai naga dama Umma da fati suna ta musu dry.
    Nan dai Abba ya fita yaje wurin likitan ya amshi
    takardn maganin,dn da farko bai rubuta ba
    magaungunan ba. Kwanan Ummi 3 a asibiti a ka
    sallem ta. Abba ya kwashe su zuwa gida.
    Saurayinta Sahabi zuwanshi 2, kuma sun je da
    mahaifiyarshi. sai lkcn ne ma ta mishi kallon
    tsaff,sam ita ba sonshi take yi ba,sai dai gara shi
    da Bashir. Kuma ta lura Bashir din da gaske yake
    yi. Domin kullum zai zo safe da yamma,haka nan
    yakan dan tsaya hr yafi Abba wanda ke zuwa sau
    daya hr tana cewa ina ma yadda Bashir ke nuna
    tausayinshi a gare ta Abba ne. An shuri sati 2 da
    sallamo ta kuma ta warke sarai,sai dai fa hr
    yanzun Alhj yana nan kan bakanshi,ganin Bashir
    na son takura mata sai ta daina fita. Abba ya
    kira Basshir shagonshi wani yammaci,ya sake
    fada masa ya rabu da Ummi sai dai yau da
    lallashi yazo masa,. Ya ce Bashir ka ga
    mahaifiyarmu bata sonka da ummi,dn haka ka
    hkr ka nemi wata,na maka alwashin kashe ko
    nawa ne dn yin hakan zai faranta ran Umma.
    Bashir ya yi 'yar dry,sannan ya mike tsaye Ya
    Abba kenan! kana tsammanin ni wawa ne?nasan
    ba don Umma ka ke fafutukar in bar Ummi ba
    kana yi ne don kana sonta. Gaban Abba ya
    fadi,cikin saurin baki Abba ya ce,In ji wa ya fada
    maka? Allah ya kiyaye. kai ka san Ummi kanwa
    na dauke ta. Bashir ya kakki cikin idon
    Abba,sannan ya ce,"Haba Malam,fadan da ka ke
    da kalaman da ka ke furtawa suna nuna kishinka
    ne karara. Dubi cikin idanunka,kishinUmmi ka ke
    yi. don haka sai ka hkr ka bar min ita,domin ka
    san ba wanda zai fi girgiza Umma tsakanina da
    kai irin ka. Ya nuna Abba da yatsa, Za tafi bakin
    ciki ka zama mijin Ummi fiye da ni. Abba ya daga
    hannu ya falla mishi mari Bashir ya dafe wurin
    sannan ya kalli sau 'yan shagon wadanda marin
    ya janyo hankalinsu. Don farko ba su san abn da
    a ke tattaunawa ba.Bashir ya ce, ka mare ni?
    Abba ya ce, Zan kara maka,ko za ka rama ne?
    Bashir ya ce, Ba zan rama ba,amma zan fada ma
    su Alhj yau dinnan ina son Ummi. ya fita fuu.
    Abba ya zauna ya rike kai yana huci. shi kam
    Bashir ya kudurci niyyar fada wa iyayensu yau
    dinnan. Abba ya kira wayar Umma ta daga suka
    gaisa lkcn karfe 6 na yamma ya ce, Ummi fa? ta
    ce Gata can kwance. Ya ce Ba dai jikin ba? ta ce
    A" aikin karance-karancenta take. Ya ce, Ba ni ita
    Umma. Umma ta kwala ma Ummi kira,ta mika
    mata wayar tare da cewa "Yanyanki ne ke son
    magana da ke. Yau ce rana ta farko da suka yi
    waya a matsayin shi na Abba,ita kuma Ummi, in
    an debe lkcn da suka yi waya a matsayin shi na
    Abba ita kuma Suhailat. Tayi sallama cikin sanyi
    murya can kasan makoshinta ya amsa tare da
    runtse ido sakamakon tsigar jikinshi da ta tashi.
    Ya ce "Ummi ta ce Na'am yaya. Ya ce "Kina son
    Bashir? ta raunana murya. Yaya am sorry to say
    bana son shin gsky. Ya ce To yau kam zai sanar
    da su Alhj cewa yana sonki,in kina san kida
    wanda ki ke so to ki gabatar da shi kafin shi ya
    rigaki. Takaici ya kama ta, kamar ta ce, Ni kai na
    ke so.......ya ce kina jina? ta ce,To Ya ce, kin san
    in su Alhj suka ji ba ki da mafita,Ummi ta ce To
    ni fa bani da wanda nake so shi ne ban san
    yadda zan yi ba. Ya ce, shi kenan matsalarki ce.,
    ya kashe wayar. Ummi tayi shiru tana tunanin
    mafita,ko dai ta hkr ne ta aure Bashir din? kai a'a
    to kuma gashi wanda take so ya ce matsalarta
    ce. Can dai ta yanke yadda zata yi,don haka ta
    kosa Alhj ya dawo. Tun kafin suje wurin cin abnci
    ta same su a dakinshi su da Umma,ya yii wanka
    yana kokarin fita sallar magriba. Ta ce Alhj dama
    wanda ya ke zuwa gurina ne ya ce in fada muku
    iyayenshi za su zo. Dadi ya kashe Alhj ya ce To
    to dan nan unguwar ne? ta ce Eh ya ce To
    madallah dama wannan yaron na sabon titi din
    nan Suwaiba wanda kwanaki nake fada miki
    nasan ubansa a kasuwarmu ya ke? Ta ce Naji
    wanda ya soma zuwa wurin Ummi? ya ce Shifa,
    Uban danai masa zancen naga dansa wurin 'yata
    sai cewa ya yi auran gida za su yi masa,ko ni na
    so hadin nan sai dai Allah bai so ba. Ya kalli
    Ummi Yaushe za su zo? ta ce Ya dai ce in
    tambaya ne. Alhj ya ce To Allah ya kawo su. Da
    dare Sahabi yazo ta ce Sahabi an ce in maka
    mgn ka turo ya ce Alhamdulillah, dama ina son in
    miki mgn sai ina tsoron kada ki ce ya yi wuri don
    haka gabe zan turo. Bashir yazo ya zauna gabn
    Alhj suna cin abnci ya gaishe su. Suka amsa ya
    yi shiru yana tunanin ta ina zai fara? Alhj Babba
    ya ce ya ya Bashir akwai wata matsala ne?Ya ce
    Am dama ina son in ce ni dai ina son Ummi ne.
    Ummi kuma?Alhj karami?Ya ce Eh Alhj Babba ya
    ce Ta amma ya aka yi kayi nauyin baki hr a ka
    ba wani dama? Bashir ya ce Alhj Wanene? Alhj
    karami ya ce Sai ka san shi? koda ba a tambaya
    ba, ba zan ba da goyon baya a baka Ummii ba,
    tashi ka bamu wuri. Abba ya ce, Bashir je ka ci
    gaba da addu'a Allah yasa Ummi ta zam
    rabinka,zan so haka dn na jima ina son zumuncin
    nan. Iyayen Sahabi sun zo kuma an basu hr ma
    an tsaida ranar daya fa ta Fati. Tun daga ranar
    Ummi kullum cikin kuka take wanda iyayenta
    suka kasa gane nufinta. Bashir bai daina cin
    alwashin sai ya auri Ummi ba, dn haka kullum
    cikin aiken kiranta yake. Ban da haka ma ya
    maida hnkl kan sana'arshi tunda ubansa ya mishi
    gorin wa zai ba shi mata ya ki tsayawa sana'a
    nashi ganin in ya rike sana'a r za a ba shi. Abba
    kuwa ya ji ya yi ma gidan wai don ya goge Ummi
    a ranshi. Anya "ZURFIN CIKIN nan zai kai su? .
    Sai mu hadu a littafi na Uku don jin yadda za a
    kare. ZURFIN CIKI book 3 part 1
    ZURFIN CIKI book 3 part 1
    Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:21
    Na Halima Abdullahi K/Mashi 1... Abba ya fito
    cikin suit bakake, yayi kyau matuka hatta
    takalminshi sawu ciki baki ne, tamkar wani black
    America. Igiyar wuyan ta zauna tsam, sai kamshi
    yake. Dakin Bishira ya nufa ya daga labule, ta
    dago ta kalle shi yayi matukar birgeta. Tana
    alfahari da shi matsayin mijinta, ya ce "Kin
    shirya?" ta ce,, "Zuwa ina?' Ya ce, "A'a, jiya fa na
    sanar da ke ki shirya da wuri zamu je asibiti ki
    gaida Ummi". Ta watso mishi wani kallo uku
    saura kwata, tare da cewa "Ko garin nan ba a
    sanyi ba zan fita gaida wata can Ummi ba bare
    da sanyin nan." Ya ce, "Dalili ta mike tsaye "Ciwo
    bai kai mutuwa ba, da mutuwa ya yi tazo ta min
    gaisuwa?" Takaici ya turnu'ke Abba, da yake
    sarkin dankara magana ne, sai ya ce "To ita ta
    kashe shi da zata miki gaisuwa?" Ta kule da
    bakin ciki ta zabga mishi harara "To ai kasan ni
    na dora mata ciwon, don haka dole in je
    gaisheta." Ahankali yake tukin, kira'ar Ahmed
    Suleiman ce ke tashi wadda ya yi murya biyu
    cikin sanyin murya. Wayarshi d ake gefe ta soma
    ruri. Ya kali fuskar wayar, Hajiya Nina ce, don
    haka ya ci gaba da tukinshi, kusan kira na bakwai
    sannan ya daga. Ta ce, "Lokacinka ne za ka iya
    yin duk yanda kaso, amma kafin kazo hannuna
    wacce shawara ka yanke?" ya ce, "Ta me?" Ta
    ce, "Au, ka manta kenan? To ba damuwa za ka
    zo yau ne ko sai an dauko ka?" 2.... 'Yar dariya
    ta kufce masa, "Ki sa a dauko ni sai ka ce wani
    karamin yaro? In kin ci gaba da bibiyata za kiyi
    nadamar hakan." Ta ce, "Ko kuma kai kayi ba, na
    baka awa goma ka kawo kanka in ko ka 'ki, hum!
    Za a kawo ka." Abba yaja tsaki "Yanda ki ke
    zatona na wuce haka". Ta ce, "Idris Aminu Idris
    raina ya biya da kai, kuma dole sai na cimma
    hakan, jarumtarka din nan ta sake bige ni, kasan
    dalilin da yasa na ce nan da awa goma? In ka
    lissafa zai baka bakwai na yamma. Daidai lokacin
    da ake watso mana labarai ina kwadayin ina tare
    da kai, lokaci guda kuma ina kallonka cikin TV
    kana feso turanci, kasan ina son muryarka ga shi
    ka gwanance da iya tsara turanci, sai ka ce
    yarenka. Kada in cika ka da surutu sai mun hadu
    anjiman". Ta kashe wayarta. Abba yayi kokari ya
    tsaida motar shi a gefen titi a hankali ya furta
    "Allahumma ajir ni fi musibati..." ya kifa kansa a
    jikin sitiyarin motar, yana tunanin wai shin ba za
    ta sauya masa a halin da yake ciki ba? Wata
    zuciyar ta ce in tasan kana cikin wani halin ko? A
    haka ya isa gurin aikinsa, tunda suka shiga dakin
    daukar labarai, abokanshi suka gane yana cikin
    wani hali duk da bai kasance mai yawan magana
    ba, amma yau ba kamar kullum ba. Salis ne ya
    kasa hakuri, don haka bayan an gama daukar
    labarai da kyar sun je su yi sallar Azahar suna
    zaune wata Bafulatana da ke kawo musu fura ta
    kawo. 3..... Dama shi Abba bai cika shan fura da
    rana ba, yafi shanta da dare, don haka siyan
    kurum yake yi. Bayan yaje gida sai yasha, amma
    ranar ya ce mata ta bar shi kawai, ta jiya ma
    tana nan bai sha ba. Da ta tafi Salis ya dube shi,
    "Idris ba ka da lafiya ne?" Ya ce, "A'a me ka
    gani?" Ya ce "Ba yanda ka saba ba, duk kwanakin
    nan na lura kana cikin damuwa". Abba ya dube
    shi amma ai kasan nayi rashin lafiya ko? Salis ya
    ce dakata Idris kada kaga kamar na matsa maka
    sai na ji cikinka, ko kusa ba haka ba ne. Ni
    mutum ne mai saurin karantar duk dan Adam din
    dana zauna kusa da shi na awa daya bare kai da
    na zauna da kai tsawon lokaci, muna kuma ci
    gaba da zama. Idris na fahimci kana da matukar
    'ZURFIN CIKI' dalili kenan da yasa ban ta6a
    damuwa da in tambaye ka matsalarka ba.
    Sannan dalilin 'ZURFIN CIKIN' da naga kana da
    shi ne yasa har kwanakin baya na kawo maka
    matsalata da iyalina. Alhamdulillahi ka bani
    shawara kuma nayi amfani da ita, kuma naga ci
    gaba, matsalolina sun ragu". Abba yayi dan
    murmushi. "Wai kana nufin saboda ina da
    'ZURFIN CIKI' ne kaga ya dace ka sanar da ni
    sirrinka?" Salis ya ce "Kusan haka ne, don me
    Zurfin Ciki ya iya hadiye magana, sai dai a ganina
    zurfin ciki wataran zai iya fadawa halaka, ko
    wata gagarumar matsala". Abba ya dube shi,
    "Wace irin halaka? Salis ya ce, "Me zurfin ciki sai
    ciwon zuciya ya kama shi yana muku-muku da
    matsalarshi, wani ma har ya mutu da ita ba
    wanda ya sani. Amma in abu na cinka ka samu
    wanda ka yarda da shi mai amana ka fada masa
    zaka ji dan dadi". Abba ya ce, "To kai tunda baka
    da zurfin ciki, kenan bai dace ka ji matsalar ba?"
    4....Salis ya tuntsire da dariya, "Ta nan ka 6ullo?
    Ai dama ka sani ba ina son yabon kaina ba ne,
    a'a duk surutuna nasan abinda nake fadi". Abba
    ya ce, "Salis na gode da kulawarka, matsalata ko
    ka ji ta nasan shawarar da za ka bani bata wuce
    ka ce in yi hakuri ba, ni kuma ba wannan ni ke
    son ji ba. Salis ba komai nake yiwa 'ZURFIN CIKI'
    ba, yawanci in ina da matsala nakan tunkari
    Ummata ne kuma ta warware min komai. Saboda
    na taso da wannan koyin da ta min, yanda na
    shaku da ita ko su Alhajina ba mu shaku haka
    ba". Salis ya ce, "To me ya hana ka fada mata
    wannan karon?" Abba ya ce, "Ba zan iya ba, sai
    dai in za ka samo min mafita ban da hakuri, to in
    fada maka". Salis ya ce "In sha Allah ba za arasa
    mafita ba". Nan Abba ya bai wa Salis labarinshi
    da Ummi tun farko har zuwa yau. Salis ya
    numfasa, sannan ya ce "Kaga illar 'ZURFIN CIKI'
    ko? Ummin ma taka ce amma kana nema ka
    rasata, ai ba mafitar da ta wuce ka samu
    Ummarka ko Alhajinka ka fada musu muradinka".
    Abba ya ce, "Tabbas haka ce mafita, sai dai idan
    na aikata haka abu biyu za su faru, na farko na
    zubar da mutuncin Alhajina, domin babu girma,
    sun ba da 'ya ba tare da wani dalili ba ya ce ya
    fasa. Sannan haramun ne neman aure cikin aure".
    Salis ya ce, "Haka ne, to hakurin kawai zaka yi".
    Abba ya ce "Ai mun yi ban da bada hakuri ko?"
    Salis ya saki dariya, sannan ya ce "To kayi
    addu'a". Abba ya mike tare da fadin "Ka tayani
    da addu'a". Daga nan ya shiga dakin, Filin Don
    Matasa na Hausa, don likkafar shirin tayi gaba
    yanzu har na Hausa yana gabatarwa. Kullum
    sake kar6uwa shirin yake a gurin Jama'a.
    5......UMMI Tana kwance kan doguwar kujera,
    yau kwana hudu kenan bata saka Abba a idonta
    ba. Tamkar Umma ta san abinda ke ranta, sai ta
    tsinkayi Umma na cewa "Yau kwana uku ne ko
    hudu rabon Abba da gidan nan, sai dai ya kira mu
    a waya. Alhaji dai ya ce, yana zuwa gunsa
    kasuwa". Ummi ta ce, "Nima yanzun nake tunanin
    haka". Ta miko ma Ummi wayarta da ke gefenta.
    "Lalubo min shi in ji". Da ta soma /ringing/ sai ta
    mika mata. Ya dauka suka gaisa ta ce "Abba ko
    dai na maka laifi ne?" Ya ce, "Umma me a ka yi?"
    Ta ce, "Tsaf, ka dauke min kafa, wanda kullum
    komai saurinka sai ka biyo". Ya ce, "Ina nan
    zuwa Ummata, kina raina duk inda nabi, harkoki
    ne suka taru suka sa ni gaba". Ta ce, "Ni kuma
    sai na ke ganin kamar don ba mu dauki
    shawararka ba ne ta game da karatun Ummi shi
    yasa ka". Ya ce, "Umma ba haka ba ne, zan shigo
    da zarar na dawo". Ta ce. "To". Sam shi batun
    shi yayi ba, sai dai baya son yazo ya ga Ummi
    domin da ya ganta yake neman kwanciyar
    hankalinsa ya rasa na tsawon lokaci. Amma
    yanzun kalmar Salis ta karshe daya fafa masa da
    za su rabu a gurin aiki ita yake tunawa. Dafa shi
    ya yi tare da cewa "Miste Man shawara ta
    karshe, ka nunawa kanwarka kana sonta a fili".
    Ya ce "Tab, wannan shi ne me wahalar ai,
    furtawa Ummi kalmar so. Zubar da kai kenan".
    Ga shi ba sonsa take ba, duk yanda mace ke
    girmamaka da zaran ka ce kana sonta shi kenan
    ka zube a idonta. Musamman in kai ke sonta ita
    ba ta sonka, wata ma har da rashin kunya zata
    tsula maka, a fili ya ce, "Ina, ai ba zan ta6a gigin
    bari ta san ina sonta ba". Daga kasan zuciyarshi
    yaji an ce za ko ka sarata. Sai da ya yi sallar
    Isha'i sannan ya yi wanka ya saka kananan kaya,
    ya fito da nufin gidan su Ummarshi. Bishira ta
    bishi da kallo, daga ganin fita zai yi ta fito da
    saurinta tana cewa "Baban Walid! Baban Walid!!."
    Ya tsaya, ta dube shi "Ina za ka?" Ya ce "Gidan
    su Umma". Ta ce, "Ba wani gidansu Umma, kai
    dai kurum tadi za ka je". 6.... Dariya ta su6uce
    masa, sai da ya dara sannan ya ce "To in ma
    tadin zan je ya za ki yi dani?". Ta ce, "Tab!, ai na
    rantse maka kayi kadan. Kullum kuma ina 'kara
    fada maka kai mijin mace daya ne rak!" Ya ce, "In
    ji ki ko?" ta ce, "Eh." Ya ture ta gefe tare da cewa
    "Da sauki tunda ba fadin Allah ba ne". Yayi
    ficewarsa ya barta nan tana ta masifarta. Kan
    dakalin kofar gidan, Ummi ce zaune da Sahabi
    suna hira, duk da cewa Sahabin shi kadai ke ta
    surutanshi Ummi na can duniyar tunanin abinda
    zuciyarta ke so. Tun daga nesa ta shaki kamshin
    turaransa, zaraf ta mike tsaye. So take ta kalli
    fuskarshi amma ya dauke kanshi daga gare su.
    Haka nan ya share sannun da zuwan da ta ke
    mishi tare da shigewa cikin gida abinsa. Sahabi
    ya ce, "Ya Abba na nan kuwa kwana biyu na rabu
    da ganinshi?" Ta dauke kai sannan ta ce "Zan
    tafi gida". Ya ce, "Haba Ummi, zuwana fa
    kenan?" Ta dube shi. Ji take tamkar ta sheka
    mishi mari, ta ce "To kaina ciwo yake yi, sannan
    kuma ga Ya Abba yazo baya son ina dadewa a
    waje". Ya ce, "To shi kenan sai gobe?" Ta ce,
    "Don Allah kada kazo gobe, ka bari sai jibi". Ya
    ce "Za ki azabtar da ni, ba zan iya kwana biyu
    ban gan ki ba." Maimaikon taji dadin kalmar, sai
    taji takaici ya mamayeta. A ranta ta ce,, "Tunda
    ga gyatumarka ba". Ya ce, "In zo goben don
    Allah?" Cikin muryar tausayi yake maganar, ta ce
    "To shi kenan". Ta soma tafiya, ya dan tako ya
    biyo ta tare da cewa "Sahibata mu kwana lafiya"
    A kagare ta ce "Uhum". Ta samu Abba suna hira
    da Umma, ta tura mishi kular birabisko tana
    lallashinshi ya ci, tayi sallama Umma ce ta amsa.
    Ta shiga idanunta kan Abba, ta zauna a kujerar
    da ke fuskantarshi. Umma ta ce "Har Sahabin ya
    tafi?" Ummi ta ce "Eh". Ta tsura ma Abba ido
    tare da cewa, "Ina kwana Ya Abba?" Umma ta ce
    "Wane irin kwana kuma Ummi da wannan daren?"
    Ta ce, "Au, zan ce ina yini?" Ya amsa tare da
    kallonta, "Lafiya". Ya mayar da dubanshi ga
    Umma. "Umma Matar Ahmad fa ta haihu". Ta ce,
    "Eh, ba jiya ka fada min ba a waya? Me ta samu
    ne?" Ya ce, "Mace ta haifa, gashi ta sha wuya".
    Umma ta ce, "Allah Sarki, to Allah ya raya mata,
    zan je in dubota in mata barka gobe". Ya ce,
    "Allah ya kai mu, ai Ahmad yayi dacen mata ba
    kamar ni ba. A da Umma bana tunanin sake aure,
    amma yanzun ina ganin dole sai nayi mata biyu".
    Umma ta ce, "To ba dai yanzun ba duk nawa ka
    ke kuma yaushe kayi wancan?" Ya ce, "Umma ke
    dai ki min addu'a, ban samu irin macen data dace
    da ni ba". Ta ce, "Ina maka addu'a, Allah ya
    shirya maka matarka." Abba ya ce, "Ko ta shiryu
    sai nayi aure insha Allahu". Ta ce, "Abba ni ko
    gani nake ba ka san wadda za ka aure din ba
    itama da nata kalar halin zata zo, sai su taru su
    ruda ka". Ya kalli Ummi wadda ya lura da kallon
    da ta tsare shi da shi kamar tana son jin abin da
    yake fada ne. Ya maida idanunshi kan Umma.
    "Na yarda da tarbiyar wannan yarinyar da nake
    son aure yanzun, duk da yarinyar bata sona tana
    girmamani". Umma ta ce, "Har ka samu kenan,
    'yar gidan waye? Ummi kuwa tuni makoshinta ya
    bushe, ta zaro idanu tana son ji wa kuma Abba
    ke so? 7:....Ya kalli Ummi ganin yadda ta zaro
    ido ya ce "Ke ni ke fadama wa ki ka zaro ido ki
    ka tsare ni da su?" A hankali ta lumshe idanu
    sannan ta maida kanta kan hannun kujera, ya
    fuskanci Umma "Ba 'yar unguwar nan ba ce",
    matsalar da yarinyar bata sona". Umma ta ce,
    "To ka bar ta mana ka samu mai sonka? Yo in
    haka ne ma ka ce gara matar taka ta gida, don
    ita tana sonka". Yayi shiru zuwa can ya ce
    "Umma in dai zan sameta zan aureta a haka".
    Umma ta ce, "Kayi addu'a, ina ko mamakin mene
    ne ta gani na 'ki a tare dakai Abba?" Ya ce cikin
    'yar dariya "Umma ai ba dole ba ne sai ka birgke
    kowa". Ummi ta mike jiri na dan dibanta ta shige
    ciki. Zance ya dada watsewa, ta furta bayan ta
    fada kan gado, ni ina son shi shi kuma ashe yana
    can ya zarme da son wata. Ranar ta raba dare
    tana kuka daga karshe ta soma ba kanta
    shawarar ta samu Abba ta ce a fili dama
    shisshigi ne irin na zuciyata Ya Abba ba irina
    yake so ba. Shi kuwa zuciyarshi ta soma zargin
    wani abu a kan Ummi, irin yanda ya ga tayi
    kamar hankalinta ya tashi da batunsa. In ko haka
    ne zai fi kowa murna, wata zuciyar ta ce ka sani
    ko tsabar jin gulma ne yasa ta kafa maka ido duk
    da haka yasha alwashin bibiyarta. Sun taso daga
    sallar Juma'a shi da su Ahmad gidan budurwar
    Tukur suka dosa, wayar Salis ta katse shi. Wani
    aiki ne ya taso dole ya koma gurin aiki. Ya sauke
    su a unguwar shi kuma ya nufi gurin aikinshi.
    Karfe biyar ya baro gurin aikin da nufin yada
    zango gidan Ummanshi. 8.... Yasan yau juma'a
    duk yanda aka yi zai samu abinci na musamman,
    don al'adarta ce girkinta na juma'a daban ne,
    tana girmama ranar da abincin da ta san mijinta
    zai yi farin ciki da shi. Haka nan ta kan yi
    kwaliyyar musamman, shi yasa yake kara
    kwadayin aura Ummi, ya san zata dauki wannan
    tarbiyyar. Matasa guda uku a tsaye gefen titi cikin
    fara'a da murna suka tsaida shi, ya saba kusan
    kullum sai irin haka ta faru. Matasa kan tsaida
    shi suna ma su nuna jin dadi da ganinshi, a gaisa
    su wuce. Wasu kuma su amshi lambarshi har da
    ma su son adireshinsa, yanzun ma sai ya tsaya
    zai fito, tsum! Yaga sun bude motar sun shigo.
    Biyu baya daya gaba, ya ba su hannu suka gaisa
    su duka. Na gaban ya ce. "Mai matasa ai muna
    jin dadin taimakon da ka ke mana. Ya kamata a
    baka Sardaunan Matasa". Daya daga baya ya ce
    "Sarkin Matasa gaba daya zamu ba shi, don yana
    kokarin gurin binciko matsalolin matasa". Abba
    ya yi murmushi tare da cewa, "Na Gode". Dayan
    da bai yi magana ba sai ya ce "Amma mai
    Matasa ka san da wannan matsalar?" Abba ya
    waiwaya da nufin jin karin bayani, sai ko ya fesa
    mishi wata farar hoda a fuska. Take nan atishawa
    da tari suka tirnike shi. Ya soma mutsuka
    idanunshi bakinshi na furta "Inna lillahi wa'inna
    ilaihir raji'un". Kafin 'yar sakwanni kanshi yayi
    din, kuma ya fita daga hayyacinsa. Suka tuka
    motar suka tashi dashi. * Farkawa ya yi tamkar
    wanda ya tashi daga bacci, a hankali ya bude ido
    tangaran a kan silin, irin na masu hali. Kwan
    lantarki irin na kasaitattun gidaje ya daki
    hancinshi. Nan take ya shiga tunanin me ya kawo
    shi nan? ba 6ata lokaci ya tuna duk abinda ya
    faru, da sauri ya tashi zaune yana fadin "Inna
    lillahi wa'inna ilaihir raji'un". Ya ci gaba da kallon
    dakin, cikin tangameme ne yana dauke da
    tafkeken gado da sauran saitin shi. Sai kafet din
    tsakar daki da kayan kallo, ga kuma kofofi guda
    biyu. Ya tambayi kanshi da cewa me ya kawo ni
    nan? me matasan suke nema a gurina?" Take
    muryar Hajiya Nina ta fado masa, inda take cewa
    "Za ka zo yau din ne ko sai an dauko ka?" ya
    girgiza kai tare da cewa, Lallai wannan makirar
    matar ce tasa aka mi shi haka". 9... Nan take ya
    soma karanta addu'ar neman tsari. Daya daga
    cikin kofofin ta bude, ya kure idonsa gurin da
    kallo, matar ta shigo sanye cikin doguwar riga
    baka mai ma6allai a gaba. Fara ce kyakkyawa,
    shekarunta suna tsakanin Talatin da takwas zuwa
    arba'in da biyar, domin kyawun nata sun 6oye
    shekarunta, ta baza gashi a kafada. Tsura mata
    ido yayi yana son tuna inda ya ta6a ganinta,
    domin tabbas yasan fuskar. Muryarta ce ta katse
    shi,"Dama nasan zuwa yanzun ka farko, kuma ka
    gama nazarin yanda aka yi kazo nan. Kila ma
    tunda kana da kamannin ma su basira ka hararo
    wadda tasa a ka dauko ka". Ya ce, "Kwarai
    kuwa". Lokacin ne ya tuno inda ya santa, wato
    Hajiya Zabba'u ce matar shaharraran Attajirin nan
    Alhaji Uzairu wadda a ke nuno ta a TV da Jaridu
    tana taimakon talakawa da Marayu. Wadda ake
    labarin tsoron Allahnta da gudun duniyarta,
    wadda ta gina Masallatai da Makarantun Addini
    ma su dama. Ya girgiza kai cikin matukar
    mamaki, ta ce "Ka gane ni kenan?" Ya ce (Cikin
    karfin hali) "Lallai mutum mugun ice. Wannan shi
    ne Allah a baki shaidan a zuci". Ta ce "Kai ne na
    biyu da ka furta wannan kalmar, sai dai bana fata
    ka zama na biyu da ya bakunci inda na farkon ya
    tafi. 10.... Ta tako a hankali ta dunfaro shi, ya
    matsa baya cikin zuciyarshi yana korar shaidan,
    'yar dariya tayi. "Nutsu Idris ko ince Abba. Ba
    fyade zan maka ba". Ya dubeta da sauri, "Eh haka
    nace, in na son hakan zan maka, amma ba
    hakanne burina ba". Ta zauna bakin gadon, "Ka
    zo mu daidaita, in kana tsoron ciwo zan baka
    makari, sai dai ina so ka sani bana dauke da
    wata cuta". Ya ce, "Karya ki ke, kina dauke da
    mummunar cuta". Ta ce "In ka tashi daga dan
    jarida ne, ka koma Likita zan baka dama ka
    gwada ni". "Ya ce ba ki bukatar gwaji don ga
    ciwonki nan a fili ciwon zuciya". Ta ce, "Sam ba
    ni da ciwon a zuciyata, to in ma ina da shi me zai
    dameka tunda ba dauka za ka yi ba". Ya sake ja
    da baya ya ce, "Zuciyarki ta kamu da ciwon zina.
    Ta yi duhu dumdum! har bata iya ganin
    gaskiya...". "Ta daga mishi hannu, "Dakata min,
    ban tambayeka labarin wa'azi ba, domin in shi
    nake son ji ina da kaset-kaset kala-kala zan saka
    na ji". Ta mike zuwa wata durowa ta bude, dauri
    uku ta dauko ta aje gaban madubi na 'yan dari
    biyar-biyar sababbi dal! Ta ce, "Wannan za ka
    sha mai ne sannan kasa kati, kuma in ka kwantar
    da hankalinka zan canja maka mota, zaka je
    Makka. 11.... Sannan idan naga kana bin
    umarnina zaka yi suna a aikin jarida fiye da duk
    wani dan jarida da ka sani a kasar nan. Kai zaka
    taka duk wani matsayi da dan jarida ke takawa".
    ta sake nufoshi da tausasa murya. "In kabi yanda
    nace ba kai ba sake kwana a talauci..." Ya
    katseta da fadin, "In naki fa?" Ta hade rai tare da
    zuba mishi ido, "Shima kallonta yake, sai a
    lokacin ya ga tsufanta ya bayyana. Ta juya mishi
    baya tana 'yar tafiya, sannan ta ce "Am sorry to
    say". Ta juya ta dube shi "Za ka mutu". Gabanshi
    ya fadi, amma sai ya yi karfin hali ya ce "In na
    mutu sai me? Dama can mutuwa zan yi ko ba ki
    kashe ni ba. Kuma ni na san ba zan wuce iyakar
    ajalina ba, murnata daya zaki sauke min nauyin
    zunubaina". Ta matso kusa da shi "Ka san
    matasa nawa ke shiga malamai kawai don su yi
    hulda da ni? In ka dade muna hulda shi ne muyi
    wata biyar, sau daya na rike saurayi har tsawon
    shekara daya don yana da hankali". A zuciyar
    Abba ya ce "In fa na daka ta matar nan zan mutu
    ban auri Ummi ba. Sannan ba Allah a ranta bare
    taji nasiha, yanzu bari yabi ta hikima". Ya ce,
    "Saboda me suke shiga malamai don suyi hulda
    da ke? Sannan daman duniya tasan ki kina
    haka?" Ta ce, "Ko kusa, sun sanni a Hajiya Nina
    sai in mutum ya zo ya ganni, in ya sanni to in bai
    sanni ba duk daya. Sudai burinsu kudin". 12......
    Abba ya ce, "Nikam ba zan iya wannan huldar
    ba". Ta ce, "Kada ka bari taurin kai yaja ka
    nadama irin wadda waninka ya ta6a yi. In kana
    da sha'awa in baka labarinsa don ya zamar maka
    Ishara". Shirun da Abba ya yi shi yasa ta ci gaba,
    domin alamar yana son ji kenan. Da a ce zan fadi
    sunanshi zaka sanshi, wani malami daga cikin
    Malaman garin nan, haka nan yanda na ganka a
    TV kana labarai na kwadaita da kai, shima haka
    na ganshi a TV yana wa'azi kuma zuciyata ta
    yaba. Na neme shi ya zo kuma shi na fada masa
    ni ce Zabba'u ban 6oye masa ba. Sai dai nuna
    masa nai aikin rabon zakka zan ba shi, ma'ana
    kudi ne masu yawa ban san yadda zan fidda
    musu zakka ba. Da jin haka sai ya taho, nan
    dakin na kawo shi, sannan na fito mishi da
    maitata fir! ya shiga jawo min ayoyi na numa
    masa cewa ba zan hakura da abinda zuciyata ke
    so ba. Don ban ta6a 'kin cika mata burinta ba,
    shi kuma ya fir ya ki ya nemi ya gudu na bashi
    guri ya dan ci abinci na nuna masa mishi kuskure
    ne ya ce zai gudu. Don gidan nan duk masu tsaro
    ne har da ma layin gaba daya. Da sauri za a
    kama ka a matsayin dan fashi, sannan in ka yi
    kokarin shigo da jami'an tsaro lamarin to, zaka
    kwana ciki. Domin duk a hannunmu suke, amma
    Ustazun ya ki shan ko ruwan gidan nan, gashi ya
    min shame-shame zai mutu don yunwa. Ba arziki
    na saka aka fita da shi kuma aka kai shi gidan
    karuwai a ka ba su na sakar musu kudi suka sa
    shi a daki. Nasa Malamina ya karasa min shi,
    sannan na sa karuwan suka kira 'yan sanda kan
    cewa ga wani ya zo gurinsu amma kwananshi ya
    kare a nan. To dama iyalanshi suna ta nemanshi
    an sace shi nan fa suka dauke shi, na san yanzu
    ka gane kowane Malami ne tunda labarin ya yadu
    a cikin garin nan da ma wajen shi". CIKI book 3 part 3
    ZURFIN CIKI book 3 part 3
    Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:24
    Abba ya ce "Lokacin da muke cin abinci tare,
    Umma ta ce, lokacin da ka ke bata dai, Abba shi
    ne ya fara baki abinci a baki. 20..... Watanki
    hudu, da kin hango shi za ki soma daga hannu,
    Abba ya ce Umma na fa goya Ummi a bayana.
    Lah, goyo? In ji Ummi. Umma ta ce, "Goyo sosai
    kuwa, suka sa dariya, Umma ta ce, "Shi yasa in
    naga yanda ku ke rashin shiri a tsakaninku
    yanzun sai in ta mamaki. Don tun ba ki fita a
    tsumma ba Abba ke rainonki, tun ba ki fi wata
    hudu ba, ki ka tantance muryarshi. Haka nan
    sunan shi ne ki ka fara iya fadi a duniya. Abba
    yana goya ki kin sha yi masa fitsari da kashi da
    tumbudi, wanka da wanki duk Abba ya miki
    Ummi. In ko na aike shi ko zai tafi Makaranta to
    sai da wayo da dabara. Ke har an kai lokacin da
    kin yarda in tafi unguwa in bar ki gurin Abba, in
    ya dawo Makaranta tun daga soro zai soma miki
    wakar da yake miki. Ummin Abba da Alhaji,
    Ummin Umma da Tsohuwa, da kin ji haka za ki
    dibi rarrafe ki nufi gurinshi, kuma duk kudin break
    dinsa zai debo miki tsaraba. Umma na bada tarihi
    Ummi ta zuba ma Abba idanu cikin wani irin
    yanayi da ba zata iya tantance shi ba, shi kuwa
    lokacin ne ya dawo mishi, ido ya yi dan murmushi
    tare da cewa "Allah sarki da na tuna ranar da aka
    yaye Ummi, Umma tayi dariya ta ce, "Ranar tare
    kuka kwana kuna min kuka wai in yi hakuri in
    baki nono". Wata sabuwar kauna da so Ummi taji
    ya rufe ta na Abba, har kwalla ta cika mata ido,
    ta ce "To Ya Abba me yasa ka daina sona?" Ya
    ce, "Ummi ban daina sonki ba, kanwata kiriniyarki
    ce ta hada mu fada dama, yanzun kuma kin
    daina ko?" Ta daga kai alamar eh, Umma ta ce
    "Labarin yanda ku ka kaunaci juna mai tsawo ne,
    kusan kullum sai mun yi labarin da Alhaji". Ummi
    ta kalli Umma shi ne ba ku ta6a bani labari ba?
    Ta ce ba gashi kin ji ba, Tsohuwa tayi sallama,
    suka amsa. Ta ce, "Kai me sunan Malam me ya
    faru da kai? Nan ya warware musu komai, suka
    yi ta al'jabi. Umma ta ce "Ni 'yasu, yanzu haka
    mata suka maida aure ba a bakin komai ba?"
    Kuma ka ce matar aure ce, Abba ya ce dama z
    aki san kowa ce ce za ki ji mamaki fiye da haka,
    don dai kurum na rufa mata asiri ne in taci gaba
    to can gabanta hadu da mai tona ta. Su Alhaji
    suka shigo da sallama, nan suma aka ci gaba da
    jajanta batun, Alhaji Babba ya ce, "Babana ina ga
    dai rahoto za mu kai gurin 'yansanda". Abba ya
    ce, "Alhaji tuni manyan shuwagabannin gurin
    aikinmu suka shigo da hukuma, in Allah ya yarda
    dolenta ta bar ni, Alhaji Karami ya ce, "Addu'a dai
    ita ce z aka kara rikewa, Allah ya ja mana gaba".
    Suka ce Amin. 21... Ranar su Alhaji a tsakar gida
    suka ci abinci anata hira, Ummi dai kallonsu take
    yi amma zuciyarta na can duniyar tunanin labarin
    da aka bata. Ashe har yanzu Ya Abba na sonta,
    Allah ya sa haka har yanzun. Sai kusan sha daya
    Alhaji ya matsa wa Abba ya tafi gida. Abba ya ji
    dadin hirar musamman in ya waiwaya idanunshi
    suna kallon Ummi ta mai 'kuri da ido, Umma ta
    ce, "Ka gaida 'yan gidan". Ya ce "Za su ji, har ya
    kai soro Ummi ta ce Alhaji da an raka shi kada a
    kara sace shi fa, duk suka sa dariya". Abba ya
    dawo yana cewa, "Umma kun rage man fetur
    kuwa? Na san yanzu na gidan ya kare tunda ba
    shi da yawa, bana son kuma sai na sake daukar
    galan na fita". Alhaji ya ce, "Na shigo da mai
    dazu duba nan soro na aje shi, Ummi ta sake
    cewa Ya Abba ka ce Alhaji su rakaka gida, yayi
    'yar dariya kada ki damu Ummi, ina yin addu'a
    Allah zai kare ni. Yau kam Ummi ta dade bata ga
    daren da farin ciki ya hanata bacci ba irin yau.
    Haka nan shima Abba zuciyarshi fes Ummi ta
    fahimci dama can santa yake, da alamu ba zai
    sha wuya gurin shawo kanta kuma cikin
    karammin lokaci. 11 HAJIYA NINA Ta kalli
    matashin, sannan ta kalli jaridar hannunshi ta ce,
    "Me ya'ki kai fa ba jakadan azriki ba ne, a duk
    lokacin da na ganka sai gabana ya fadi,
    musamman in kazo min da jarida". Yayi 'yar
    dariya "Hajjaju makatu sallah Makka Sallah
    Madina, ni dai kin san ba ilimin nan gare ni ba, in
    da z aki tsare ni in karanta ban iya ba, ni dan
    sako ne. Muftahu ne mai siyo duk wata jarida da
    ya ga ta shafe ki, ta amsa ta bude cikin azama,
    hoton Abba ta gani gabanta ya fadi, ta ce dan
    jarida shege ne, yaron nan tallatani zai yi? Ta
    soma karanta labarin zufa tana karyo mata, har
    ta gama. Kafa kurum take karkadawa tana
    tunanin abin yi, murna daya tayi da bai tona ma
    duniya cewa ita ce Hajiya Zabba'u ba. Amma duk
    da haka ba zata bar shi ba, koda yake ta ga
    manyan 'yan jarida na kokarin shigowa ciki, ta
    kai hannu ta dauko daya daga cikin wayoyinta ta
    danna kira. 22.... Jim kadan aka daga ta ce,
    "Karamakallu barka da warhaka, ya amsa da
    Ranki ya dade lafiya dai ko?" Ta ce, "Malam ba
    lau ba, kana ji? Ina yaron da nake baka labari
    dan jarida? Ya ce, Naji. Ta ci gaba, Yaron nan
    kaga yanda ya yayata ni a duniya? Sai na koya
    mishi hankali, da ni zai ja?" Malam ya ce, ya ma
    ki ka ce sunanshi? Ta ce Idris, ya ce To zan kira
    ki anjima, kada ki dauki wani mataki tukunna sai
    na gama bincikena duka. Ta ce an gama. Sintiri
    tayi ta yi tsakanin dargajejen falonta zuwa
    barandar shakatawarta, lokacin da taji rurin
    wayarta tayi tsammanin Malamin ne, sai data
    duba taga Aminiyarta ce Haiya Attine. Ta daga da
    cewa, "Hello Attinen bishasha ya aka yi ne? Ta
    ce, Zabba haka kwallon dan iskan yaron nan zai
    miki? Ta ce, Hum! Ke dai bari Aminiyata, yanzun
    nan na gama karantawa a jarida ban ma san
    hukuncin da zan yanke ma yaron nan ba. Attine
    ta ce, sa su Adda su tura shi Jami'ar mi'kakku
    mana. Hajiya Zabba'u ta ce, "Ai kuma na riga na
    kira Teacher ya ce in saurare shi". Attine ta ce,
    "Eh to kin yi dabara ma, kya iya sa Teacher din
    ma ya tura ba tare da an zargi kowa ba". Hajiya
    Zabba ta ce, "Kin san jami'an tsaro suna cikin
    maganar tsundum! Don haka dole in yi taka tsan-
    tsan, guri daya yaron ya yi min kyan kai, da bai
    fada ma duniya Zabba'u ita ce Nina ba." Attine ta
    ce "Eh yayi wannan adalcin, yanzun bari muji ta
    bakin Teacher". 23.... Shikam Malamin duk
    lamura sun kasa masa daidai, sai kusan karfe uku
    saura, sannan ya kira ta da rawar jiki ta dauka.
    Ya ce, Hajiya? Ta ce, Na'am ya ce ki tattara ta
    batun yaron nan ki watsar domin yanda naga
    al'amuran to fa in mun matsa ba zamu kai labari
    ba. Haka nan allura zata tono garma game da
    damuwar malamin nan, sannan asirinki zai tonu a
    gurin maigidanki. Tsaki taja don maigidana
    Malam nasha fada maka ban 'ki ya ji ba, tunda
    shi ne sanadin komai, tafiya kullum daga waccan
    kasa zuwa waccan, kullum cikin bakin yawon
    neman kudi. Sam baya biya mini bukatata ba
    dole in nema ba? Yarana biyu cal a duniya duk
    sun yi aure su ne kawai zan ji kunyar su sani,
    don haka in zai yiwu ka sa Aljanu su tsotse min
    jinin matsiyaci. Malam ya ce, "Ba zai yiwu ba, ina
    ce tun lokacin da ki ka zo min da batunshi kafin
    ma ki sa a dauko miki shi sai d ana fada miki
    yaron yana da kariyar da take kare shi daga
    Ubangiji. Yaron ma'abocin kyautata Sallah ne,
    tare da yin Azkar, yana da makarin da Aljanu ba
    za su iya tunkararshi ba... Dakata Malam, ta
    katse si duk addu'arshi ya kai Malam ne, kuma
    muka ci nasara a kanshi? Ya ce kila shi Malamin
    kwananshi ya kare dama ke ce sila shi ko
    wannan da sauran shan ruwansa. Ta ce, "Kai ne
    sila dai daina jingina min mutuwarsa, ya ce ko
    kin ki dole ki dauki nauyin zunubin mutuwar
    Malam". Yanzun kuma ta wannan sai ki wamu
    wani don ni ba zan matsa lamba a kan al'amarin
    da Aljanu suka nuna tsoronsu ba, tsaki taja
    sannan ta kashe wayar. Har gari ya waye ba ta
    daina tunani ba, haka nan bata yanke matsaya
    ba. Gidan Aminiyarta Attine bishsha ta nufa, sun
    tattauna sosai sannan suka bukaci sukai koken
    ga wasu Malaman. Sai dai guri uku zancan iri
    daya ne, wato ta bar shi kawai, yayin da guri
    biyu suma zancan su iri daya ne, sun ce zata ci
    sa'ar kashe shi amma asirinta zai tonu zata rasa
    ran 'yarta daya kuma zai yiwu tayi zaman Jarun.
    Ta ce, "Wannan akwai shegen yaro, shi yasa da
    na ce zan sa Aljanu su dauko shi ya ce min yana
    da makaminsu? Daga karshe ta ce na bar shi
    mara rabo". Attine ta ce da dai yafi shi yasa tun
    farko in naga wanda zai ja min aji ni ke watsi da
    shi in nemi wani. Kai jama'a sai kace aikin Allah
    menene amfanin zinar ma da har ake shiga
    Bokaye dominta? Allah ka tsare mana Imaninmu,
    amin. 12 24.... Ummi tana zaune zata wanke 'yan
    kayanta na ciki, ta zubo omon cikin ruwa tana
    faman karkadawa, tana 'yar wakar da ke sata
    nishadi. Sam ba ta ji sallamar Abba ba, yana
    jingine yana kallonta, tana fadin, Akwai wanda na
    ke so, amma kunya naso, ya wanke ni da soso
    dan Yayana. Ta tsoma sikyat dinta da fant da
    'yan bireziyoyinta farare ne ta soma cudawa tana
    maimaita wannan baitin wakar, shi kadai ta iya.
    A jikinta taji cewa ana kallonta, ta waiwaya da
    sauri, idanunta tsaf cikin na Abba, sai ta samu
    kanta da sunne fuskarta cikin cinyoyi. Ya ce,
    "Kunyata ki ke ji ne Ummi?" Ta dago da dan
    murmushi, "Sannu da zuwa Yaya Abba". Ya ce,
    "Yauwa dama kin iya waka?" Tsohuwa daga daki
    ta cafke, tun da ta samu wannan wakar sai ka ce
    me hadda, kullum Abba ya isa kofar Tsohuwa
    suka gaisa. Ya dawo kofar Umma yana tabayarta.
    Ummi ta ce, "Taje Hotoro sunan kanwar Umman
    Bashir da ta haihu, ya manta fa matarshi ma ta
    na can, Tsohuwa ta fito tana cewa, ai Ummanku
    ta juri wulakanci. Waccan haihuwar da Zilai
    kanwar Sahura tayi tas a ka zageta a gidan
    sunan, amma yau ta koma. Abba ya ce, "Ummata
    tayi nisa a zumunci, Allah zai bata lada" Tsohuwa
    ta ce, "Ai sai tayi ta yi, in dai shisshigi ne ba
    kwarjini". Ta dubi Ummi, wai wankin me ki ke yi
    ne har yanzun ina nan ina jira ki yanke min
    farce". Ta hango kayan Ummi na daura ta ce,
    "Kai ni wannan zamani naku yana bani mamaki,
    ace 'yammata suna saka rigar mama? Kunya ta
    cika Ummi saboda Abba da ke gurin. 25.... Abba
    ya ce, "Kin ji tsohuwa, lokacinku da namu daya
    ne? Ku lokacinku kai bai waye ba, ta aje 'yar
    kujerarta ta zauna. Tir da wannan wayewar taku
    ta zamani, yarinya ta fadi a gaban iyayenta har
    ta shiga sa tara mama bata kama dakin kanta
    ba? Mu kuwa da wata ma ba sai tayi haihuwa
    goma ba ma ta sa ran mama ba. Abba dariya ta
    ishe shi yayin da Ummi kunya ta hanata shanya
    kayan ta matse ta aje. Abba ya ce, "Yanzun
    Ummi har wani girma tayi, shekara sha takwas
    kurum ce fa, bata ma cika ba. Ta ce "Mu lokacin
    sha biyu sha daya yarinya ta kama dakinta.
    Ummi ta zanua ta soma yanke ma Tsohuwa
    'kumba, tana cewa To dai nima na kusan tafiya in
    huta gorinki. Abba ya matso, "Ummi don Allah in
    tambaye ki mana? Ta tsaya da yanke 'kunbar
    tana kallonshi, ya maimaita tambayar da gira ta
    bashi amsa ya ce kina ko son wannan Sahabin?
    Ta maida kanta ga yankan 'kunbar duk jikinta da
    hannunta suna dan rawa, a zuciyarta ta ce, "Kai
    ne kadai zuciyata ke so, amma a fili sai ta ce,
    Um, ya ce Yaya hausar um?" Tayi kokarin
    saisaita hawayenta, sannan ta ce Eh, jikinshi yayi
    lakwas, Tsohuwa ta ce, "Zancan banza, in bata
    sonshi zaka daga batun auren ne?" Ai ko tana so
    ko bata so tunda ta kawo shi zance ya kare, ka ji
    mai sunan Malam da zancen wofi. Ya ce,
    "Tsohuwa ni fa ba wani abu na ce ba, kin ga ma
    dai bari in tafi abina. Ummi ina Azimi yau, zan zo
    in yi buda baki anjima. Ta ce, "To." Tsohuwa ta
    ce, "Wai kai ba ka da gidan mata ne kullum kana
    la'ke a nan? Tsoron ta ka ke ji ne da zaka kasa
    lankwasata ta yi maka girki?" Ya ce, "Na nan
    nake son ci Ummi kam tana can duniyar tunani
    tana tambayar kanta shi kenan ta rasa Abbanta?
    Son da da yayi mata da ca dama ba na aure ba
    ne, na 'yan uwantaka ne? Kai ko dai ta fito ta ce
    Abba take so, gaskiya ita fa Sahabi ba sonsa
    take ba. Kusan wata daya kenan rabon da ya
    samu biyan bukata daga matarsa, don gaskiya
    baya iya zuwa dakinta saboda kazanta da kuma
    datti da wari da zarni da 'karni ba za su bar shi
    ya samu cikakkiyar biyan bukata ba. In ta zo
    dakinshi ma jikinta tashi yake, a haka yake
    maneji, amma in iskancinta ya motsa har yanga
    take mishi (Mtsw! Allah rabamu da kazaman
    Mata). Shi kuma yana da wani hali, duk yanda ya
    matsu in har ya nuna mata bukatarshi ta 'ki sai
    ya hakura ya roki Allah ya shiryeta, shi kuma ya
    kare shi da fadawa sharrin zina. 26.... Bai zaginta
    ko ya ce zai nuna mata karfin shi, ko ya ce zai
    tsaya rokonta, shi yasa yake yawan yin Azumi.
    Ummi ta ce, "Umma ki kawo kudi in siyo kwai in
    soya ma Yaya Abba doya, ya ce zai zo shan
    ruwa. Ta ce, "To je ki kasan filo ki dauko, amma
    fa sai kin yi azama don an kusa kiran sallah. Ta
    ce, "Ai na dafa ruwan shayi, sannan na masa
    kunun tsamiya, doyar ce kawai, ta ce "To sai da
    ta gama komai sannan tayi wanka tayi sallah.
    Riga da siket na leshi tasa fari tas, bata damu da
    yin fenti da dare ba amma yau tayi ta feshe
    jikinta da turare wanda shi ne ya sai mata.
    Sallamarshi ta jiyo suna gaisawa da su Umma, ta
    fito ya bita da kallo, kin yi kyau kanwata, Umma
    ta ce yau za ku hoton ne? Ta ce kila, Abba ya ce
    shi yasa ki ka yi kwalliya haka? Ba ta ce komai
    ba sai dai ranta bai so ma maganar da Umman
    tayi ba. Suna hira da Umma ta shirya misi abinci
    ta koma kan kujera ta dauki littafi lokaci-lokaci
    idanunta suna kan Abba. 13 Suna hira da Umma
    ta shirya mishi abinci ta koma kan kujera ta dauki
    littafi, lokaci-lokaci idanunta suna kan Abba. Shi
    ma haka ya ce wai ni littafin nan da ku ke nacin
    karatunshi dame kuke karuwa? Umma ta ce, Ai fa
    gara ka tambaye ta, don ban ga abinda ta ba
    muhimmanci ba irin wannan littafin. Ummi ta cem
    ina karuwa sosai Umma suna koya mana tarbiyya
    yyanda zamu tafi da rayuwarmu cikin tsarin
    Addini da al'adarmu. Abba ya ce amma basa
    koya tsafta da biyayya, Ummi ta ce suna yi sosai
    ma, ya ce Umma ni naga jarabar karatu irin na
    Bishira amma kullum mugayen halayenta bayyana
    suke yi. Ummi ta ce ni ko har addu'o'i zuwa girki
    kala- kala ina koyo, Umma ba rannan nayi
    dafadukan kwakwa ku ka ce ya yi dai ba?" Ta ce,
    "To ki dai dinga daukan na kwarai kina yarda na
    banza, Abba ya ce in haka ne d agaske zan samu
    lokaci in zo ki karanta min in ji, ta ce "To." 27.....
    Umma ta yi 'yar dariya ta ce, "Sai ka ce ba ka da
    aikin yi? Ya ce, "Allah Umma da gaske nake yi
    don in ji wacce irin koyarwa suke yi, marubutan
    ko ko sai shirme?" Kiran sallar Isha'i ne yasa
    Abba mikewa, ita kuma Umma ta tafi kicin don
    shiryawa su Alhaji Abinci. Ummi kam sun bar ta
    cikin takaicin tafiyar Abba don dai bata gundura
    da shi. * Alhaji Ya kalli Umma, wai yau bikin
    yaran nan saura wata nawa? Ta ce, "Wata ko
    kwana dai?" Yau saura kwana talatin da shida,
    ban ga kana motsi ba? Alhaji bikin nan zai
    mamaye mu, ya ce "Yanzun ya za a yi da batun
    kaya?" Ta ce, "Ni da cewa nayi ga Abba sai yaje
    ko kuje ku za6a musu kaya masu kyau a siya,
    kada a ba kafintoci in ba a yi sa'a ba har lokacin
    yayi ba a gama ba". Ya ce, "To zan sa shi ya tafi
    da su kawai su za6a". Ta ce, "Sai kayan girki na
    dai sayi tukwane da risho, sai kuloli". Ya ce, "Duk
    da haka uwata zan sa ta za6i wasu kayan."
    Umma tayi dariya tare da cewa, "Allah ya kara
    budi, nan dai suka yi ta lissafin kudi. Da safe
    Alhaji ya kira Abba a waya ya sanar da shi cewa
    ya dauki su Ummi suje su za6i irin kayan da suke
    so, duk da cewa zancan ya doki zuciyarshi amma
    ya ce "To." insha Allah zamu je, suka yi sallama.
    Sam baya son ya ji batun auran su Ummi, baya
    son rasata, kuma yana ji a jikinshi cewa zai same
    ta. ** ** 28.....Yammacin ranar Asabar La'asar
    lis garin yayi dan sanyi Abba ya nufi gidansu don
    daukan su Ummi zuwa kasuwa. Jikinshi sanye da
    farin yadi mai shara-shara, har ana iya hango
    fara kar din singiletin da ke ciki ta manne a
    jikinshi. Kamshin turarenshi ya cika dakin Umma
    wanda ba shiga yayi ba daga bakin kofa suka
    gaisa. Ya ce, "Ummi su fito don Ummi ce ke
    shiryawa tuni Fati ta fito, ya matsa kofar
    Tsohuwa suka gaisa, sannan ya ce "Umma sai
    mun dawo. Ya nufi waje yana fadin su Ummi su
    mishi sauri. Sun fito za su duru a baya Abba ya
    ce Ummi ta dawo nan gaba, ta zauna ranta
    dagule don ita bata bukatar wani za6i tunda ba
    wanda take so zata aura ba. Haka nan ta
    fuskanci Abba yau yana cikin wani irin yanayi,
    kila daga gida aka 6ato masa rai, nata tunanin
    kenan. Shi kam takaicin zuwa za6on kayan ke
    damunsa, ya kalli wayarsa da ke ruri ya daga,
    Salis ya ce kana ina ne? Ya ce ina nan
    unguwarmu zan kai kannena ne za su za6i kayan
    daki. Ya ce, "Ta ina zaku bi? Abba ya ce kai kana
    ina ne? Ya ce ina nan kusa da asibitin Malam,
    bari in jira ka a jikin gidan man nan, Abba ya ce
    "To." Salis ya kalli yarinyar da Abba ya ce Ummi
    koma baya ya ce, "'Yammata sannunku, suka
    gaishe shi ya yi murmushi ke ce Ummi?" Ta ce,
    "Eh, ya ce ya su Umma?" Ta ce lafiya lau, ya
    maida dubansi ga Abba wanda ke tuki cikin
    nutsuwa ya ce, "Idris akan batun yarinyar nan ne
    don Allah ka daure muje gidansu yau". Gaban
    Ummi ya fadi. Abba ya ce, "Don Allah Salis ka
    bar batun yarinyar nan, kai dai kasan halin da
    nake ciki game da wata". Salis ya ce, "Me yasa
    ka amsa kana sonta, kuma har kana daga waya
    duk lokacin da ta kira ka?" Abba ya ce, "Shike
    nan za mu je da yamma tunda wancan na rasa
    madafa". Salis ya ce kuma fa da hakan zai fi
    maka. Ummi gashin jikinta duk ya mike, suna fitar
    da zufa lumshi ido tayi luf a kan kujera ta kwantar
    da kai, Salis ya waiwaya ya dubeta, yaya dai? Ta
    yi dan yake, "Ba komai." . 29.... Sun je gurin
    kujeru da gadaje, Fati tayi ta ruwan ido yayin da
    Ummi ta koma ta jingina a kujerar da ta zauna.
    Abba ya dube ta. "Ke wanne ki ka za6a? Ita ta ce
    wancan farin". Ummi ta yatsina fuska, "Nifa bani
    da za6i, duk wanda ku ka ga yayi". Salis ya ce, "
    Idris yarinyar nan ina zaton tana sonka, naga
    tunda muka yi maganar zuwa gurin wata ta
    canza yanayi. Abba ya ce, "Kyaleta ba wani ya
    dubeta ba, ke Ummi tashi ki za6a mu ji
    farashinsu, sauri muke. Ta ce, "Ya Abba cikina ke
    ciwo, ka za6ar min don Allah". Ya ce, "Salis ita
    ma a bata farin kawai ko? Salis ya ce, "A daukar
    mata mai ruwan madaran, mai shagon ya ce sun
    fi tsada, Abba ya ce ka daukar mata su. Sun
    koma gefen kujeru nan fa Abba ya ce dole sai ta
    za6a, nan ma wanda ta za6a a ka ce sun fi na
    Fati tsada, suka ji farashinsu su sannan ya ba da
    wani abu suka tafi. Ya sauke su a gida, Fati sai
    ba Umma labari take yayinda Ummi ta shiga
    kuka, Umma ta ce ke kuma lafiya ki ke kuka?
    Ummi ta ce "Umma ni bana son in yi auren nan,
    bana son in bar gida. Fati ta ce, "Shi yasa naga
    tun a gurin shagon kina ta 6acin rai? Umma ta
    ce, "Shirmen banza da wofi, sai ki tayi. Ta fice,
    Fati ta ce Ummi ke kin cika son damuwa. Menene
    na damuwa? Kila ma kina nan unguwar.ovels / ZURFIN CIKI book 3 part 5
    ZURFIN CIKI book 3 part 5
    Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:29
    ummi sannu da zuwanku, nan sukayi masa
    gaisuwa yace ummi kaisu ciki. 36.. Zainab tace a
    ranta wato ma ummi yafara gani, a fallon su
    umma suke don nan ta fara kai su, tace umma
    wanan ce zainab, wannan kuma matar abokinshi
    salis, umma tayi masu sannu da zuwa sanna tace
    ummi ta kaisu dakin bishira, sun shiga sun yi
    mata gaisuwa, bishira tace ke ko gaisuwa baki zo
    min ba koda yake bai dame ki ba, ummi tace
    nima ana ta zuwa min gaisuwan ne a gd, duk yan
    dakin suka kalli ummi, sahura tace ke asuwa?
    Bishira tace ita a mahaifiyar shi, ummi tace
    zainab kuzo muje, tun daga lkcn zainab tasa a
    ranta akwai matsala a wanan familyn din, basu
    jima ba suka yi sallama, inda ummi ta rakasu
    daga can itama ta wice gd, suna shiga soro
    shima ya shigo yace badai tafiya zakuyi ba? Ya
    kalli ummi sun sha ruwa ma kuwa?ummi wadda
    dama idanunta na kanshi ta amsa mishi da
    idanu. Yace yama akayi kuka gane gdn zainab
    tace yaya salis ne yakawo mu, ya kalli matar
    salis yace madam mun gode fa,tace bakomai
    Allah ya jianshi, sam ummi batasan lokacin da
    furucin ya fito mata ba, sai dai taji tace ya abba
    duk ka rame baka cin abinci ko? Shi kanshi yayi
    mamaki don haka ya ya tsura mata ido, sai taji
    kunya ta rufee ta saita kau da kanta daga
    kanshi,don kada su zargeta. Kayi hkr naji wani
    malami yace duk wanda yaranshi kananan uku
    suka rasu to zasu ceceshi ranar gobe. Kaga ynz
    kafara da daya,matar salis tace ai koma dayane
    indai kayi hkr kayi tawakkali,ummi ta kalle shi
    tace to kaji ma,yace ummi nifa tuni na
    dangana,ta sake tausasa murya to meyasa baka
    cin abinci? Ya tausasa murya wadda dama take a
    dusashe yace ummi inaci,tace ya abba baka fa
    yin karya,yace to yau zanzo inci a gabanki, ya
    kalli matar salis wadda ke murmushi, in naci a
    gabanta saita yarda ko? Tace tabbas! 37..Zainab
    wadda takaici ya cikata tace da matar salis anty
    nifa natafi, abba ya dubeta zainabu nagode ki
    gaida su mama sai nazo,batare da ta tsaya ba
    tace to, ummi ta musu sallama itama ta tafi gd.
    Zainab ta dubi matar Salis bayan tafiyar Ummi,
    ta ce, "Duk da son da na ke ma Idris din nan ba
    zan aure shi ba". Matar Salis ta ce dalili? Zainab
    ta ce, "Bana zaton ko matarshi ta gida da ya
    aura ya aje yana sonta irin yanda yake son Umiin
    nan". Abin nasu yayi yawa. Dubi yanda ya manta
    da ni, ta ita kawai yake yi. Matar Salis ta ce, kin
    ji ki da wani shirme, ita da zata yi aure?" Zainab
    ta ce, "Abinda ke tausar zuciyata ke nan in na
    tuna cewa zata yi aure, amma kai naga ji ba zan
    iya ba, haka suka tafi tana ta bai wa yarta
    labarin yanda Abba ke ji da Ummi. Kamar yadda
    Abba ya ce zai zo cin abinci da dare yazo, Ummi
    ta saka shi gaba wai sai ya cinye wake da
    alayyaho da kifin da ta dafa masa. Da kyar ya
    cinye plate din farko ya ce "Ummi na koshi kin ji?
    Ta daure fuska tana kallonshi, shi ma ita yake
    kallo yana dan murmushi. Ya ce, "Ina ma a ce
    tun da da haka muka yi sabo, Ummin cikin
    kwanakin nan kin lura cewa muna shiri". Ta
    harare shi, "Kana zaton na manta da irin dukan
    da ka yi ta min ne? Shi ma ya harare ta tare da
    kwaikwayon muryarta. "Kina tsammanin zan
    manta da irin tsokanar fadanki ne? Ko zan manta
    da Suhailar Kaduna...?" Kafin ya rufe baki tuni ta
    yi uwar daka da gudu, shi kam dariya yayi ta yi
    yana cewa ki zo mana Ummi, kin fitowa tayi har
    sai da ya bar gidan. Duk lokacin da suka kasance
    tare kowannan su yana mantawa yana da wata
    matsala. Saura kwana uku daurin auransu,
    lokacin dangi sun soma zuwa, musamman 'yan
    Zamfara. Ummi da Abba hankalinsu ya kai
    kololuwa gurin tashi. Ranar ya ziyarci Zainab wai
    ko zai samu 'yar nutsuwa. Bayan sun gaisa ta
    sake mishi gaisuwa, shi kuma ya mata bangajiya,
    dama tun da aka yi rasuwar bai zo ba. Ya ce
    "Zainab ina ganin da an gama hayaniyar bikin
    Ummi zan turo". Tayi shiru bata yanke ma kanta
    shawarar matsawar ya cikata da zancan Ummi
    yau kam za su yi ta ta kare. Jin tayi shiru ya ce
    kina jina Ummi... ta katse shi da sauri, "Ba Ummi
    nake ba Sorry Zainabu. Ya ci gaba bakina ne ya
    saba da kiran Ummi, da yake daga ni sai ita ne a
    gidan. Yanzun haka auran nan da zata yi ina cikin
    tsananin kewarta...Zainab ta ce ina Idris? Don
    Allah ni na hakura ka je ka auri Ummi, Abba ya
    dubeta cikin tsananin mamaki. 38.. Me ki ke
    fada? Me Salis ya sanar da ke? Ta ce Idris duk
    wanda ya san so, minti biyar in ya zauna da ku
    zai san kuna tsananin son junanku kuma ni na
    tambayi Salis cikinku daya? Ya ce min A'a tun
    daga nan nasan cewa ku masoya ne, ta nufi
    hanyar gida, da sauri ya sha gabanta. Zainabu
    kada muyi haka da ke, wallahi auranki zan yi. Ta
    ce, "Eh ai na san aurena zaka yi, amma ba sona
    ka ke ba, don Allah ban hanya sonka in zai yi
    ajalina ba zan aure ka ba, ya kauce ta wuce, ya
    bita da kallo har ta shige. Jiki ba karfi yake tuka
    motar har ya iso gida, kukan Muhibba ya jiyo don
    haka ya nufi dakin. 21. Jiki ba karfi yake tuka
    motar har ya iso gida, kukan Muhibba ya jiyo don
    haka ya nufi dakin. Bishira na zaune ta zuba
    tagumi tunanin danta take, ga Abba sam baya
    sakar mata fuska, ya ce "Lafiya Mamina take
    kuka?" Ya shiga ya dauketa Bishira ta ce, "Rigima
    cee kawai, ya nufi kan madubi inda ya hangi
    pampers ya dauki guda daya ya nufi dakinshi da
    ita. Bishira ta biyo shi itama ta zauna a gefen
    katifa kusa da shi, cikin sanyin murya ta ce,
    "Abban Walid don Allah kayi hakuri, ya ce me a
    ka yi? Ta ce, "Gani nayi kana ta fushi, ya ce ni
    bana fushi wannan kadan kenan ki ka gani daga
    cikin sakacinki, na tabbata kin fini jin bakin cikin
    mutuwar yaron nan. Musamman da ki ka zama
    sanadi, amma don batun yawo ni na daina miki
    fada, kiyi tayi illa dai zan nemo wadda zata dinga
    lurar min da gida. Ta ce me ka ke nufi? Ya ce
    aure zan yi". Ta doki kirji tare da fadin, "Aure?" ya
    ce, "Eh". Ta soma kuka haba Baban Walid, wane
    laifi na maka da zaka yanke min irin wannan
    mummunan hukuncin? Ya ce, "Don Allah fita, ta
    ce sai ka fada min dalilin yin auranka, ba za ka
    bar ni in ji da rashin dana ba ko? ta mike an
    zugo ka an ce kayi aure, to bisimilla. Ta fita ta
    zari mayafi tayi gidan Umman Bashir. Abba ya
    rungume 'yarshi ya yi laf a kan katifa shawara ya
    yanke zai tura magabanshi gidan su Zainabu ba
    tare da ya sake bi ta kan Zainabun ba. * Umma
    ta leko dakin Tsohuwa, Ummi kin san na ce miki
    kizo ki kwashe kayanki daga dakina ki adana su
    ko? Kin san dai yau duk na nesa za su iso, ki cire
    wadanda za ki bada. Tsohuwa ta ce, "Suwaiba
    yarinyar nan ina kallonta jiya bata runtsa ba,
    sannan da Asubahi a zaune tayi sallah. Umma ta
    shiga dakin warwas take a kan gado, Umma ta
    tasheta zaune Ummi ciwon kai ta keya ga jiri da
    ta ke gani daga zaune. 39.. Umma ta ce taso ki
    dan watsa ruwa ki karya, mikewar da zata yi sai
    ta sulale a kasa sumammiya, nan suka dau
    salati, Toshuwa kam kuka ta saka. Alhaji ya fito
    wanka kenan ya ji Umma na salati, don haka
    dakki ya shiga ya dauko waya ya kira Abba
    lokacin yana kokarin shiga wanka. Alhaji ya kira
    shi, jin cewa Ummi ba lafiya zari mukullin mota
    ya fito. Sai da suka kai asibiti sannan ya lura da
    silifas ya fito da jallabiyarshi ta wanka, Lkitan ma
    bai zo ba lambarshi suka amsa Abba ya kira shi.
    Ya duba Ummi sosai da kyar suka samu
    numfashinta ya dawo, sun daura mata ruwa
    sannan aka kaita wani daki. Likitan ya ce su zo
    ofishinsa, Ya kalli Alhaji ya ce, "Gaskiyar magana
    yarinyar nan tana bukatar kulawarku, ciwonta
    baya son sakaci. Jininta ya hau ya wuce matakin
    da zata iya samun mutuwar 6arin jiki. Su Alhaji
    suka dauki salati,, ya ci gaba da cewa yanzun dai
    addu'a zamu ci gaba da yi. Allah yasa in ta
    farfado kada wata matsala ta biyo baya. Sannan
    ya basu takardar magunguna". Alhaji ne ya amsa
    don Abba fita yayi ya koma dakin da Ummi ke
    kwance. Idanu ya zub amata, sam bai san cewa
    kuka yake ba, sai da Alhaji ya shigo ya dafa shi
    tare da cewa, "Haba Abba ba girmanka ba ne
    kuka. Addu'a za ka yi Allah ya bata lafiya". Ya
    share hawaye. Alhaji don Allah kada ka sanar da
    Umma abinda Likitan ya ce, Alhajin ya ce ai
    dama ba zan fada mata ba. Bari in je sai tazo ga
    takardar maganin inta zo sai ka siyo, ya ciro kudi
    ya mika ma Abba, Abba ya ce a'a da kudi a
    jikina. Alhaji ya ce ka amsa ka kashe kudi cikin
    kwanakin nan ina sane da duk lokacin da na ce
    kazo ka siyo wani abu sai kawai in gan ka da shi
    ban da kayan dakin da ka siya musu, Abba ya ce
    ai ina da shi ne. Bayan fitar Alhaji Abba yaja
    kujera ya zauna ya zabga tagumi tare da tsura
    ma Ummi ido, a zuciyarshi fadi yake ALLAH ka
    tashi yarinyar nan lafiya, Allah kasa kar ko ina na
    jikinta ya nakasa. Alhaji ya fada wa Umma an ba
    Ummi gado, don haka ta shirya su wuce. Abba ya
    tashi ya nufi ofishin Likitan, bayan ya kwankwasa
    Lokitan ya ba shi izinin shiga, ya same shi yana
    rubuce-rubuce. Ba tare da ya dago kai ba ya ce,
    "Zauna sai da ya kai aya rubutunshi sannan ya
    dago kai ya kalli Abba "Ba dai mai jikin ba ce
    ko?" Abba ya ce, "a'a ina son ne nima agwada
    nawa jinin, Likitan ya ce kana jin jikinka ba dadi
    ne?" Abba ya ce, "Eh da har yasa a dauko fayal
    din Abba kuma ya tasa ya dauki abin gwaji.
    Bayan ya gama ya zaunar, ya tsare Abba da ido
    wai kun yi gadon ciwon nan ne? Abba ya ce,
    "A'a, Likitan ya ce, "Jininka ya hau, sai dai ba
    sosai ba. Kila don kai namiji ne kana kokarin
    kauce ma abubuwa. Zan rubuta maka magani na
    sati daya, kuma ka dinga kokarin yin bacci a kalla
    na wa shida kada ka dinga yawan tunani. Kaga
    kanwar nan taka, sai sa'ar gaske zata tashi
    lafiya. Ku dai cigaba da addu'a, zata yi bacci na
    tsawon awa tara ko goma. Ina son daidai lokacin
    da zata farka ya kasance ta soma dora ido a kan
    wanda suke shiri ko wanda ta fi so a cikin
    mahaifanta ko danginta, Abba ya ce "To."
    Lokacin da ya koma dakin su Umma sun zo har
    da tsohuwa, nan Abba yake fada musu abinda
    Likitan ya ce game da farkawa in tayi. Koda bude
    bakin tsohuwa sai cewa ta yi ai ko dai ba a bar
    mai sunan Malam ba, tunda an ce wanda suke
    shiri, don in taga mai sunan Malam karasawa
    zata yi. * 22. Duk da ana cikin wani hali sai da
    su Alhaji suka murmusa. Abba kam daure fuska
    yayi yana kallon Tsohuwa, Umma ta ce, "Ai da ne
    Tsohuwa. Yanzun shiri suke tunda ta daina rashin
    jinta". Likitan ya shigo ya sake musu bayani
    kamar yadda ya yi ma Abba, sannan ya ce su
    bata guri kada zantukansu ya farkar da ita a
    samu matsala. Suka fito, Umma ta ce da Abba ya
    tafi gurin aikinsa, su Alhaji ma suka fita tare da
    Abba. Fati ta je gidansu Sahabi dan uwansa yana
    kankarar rake a kofar gida, inda yake saidawa ta
    tambayi Sahabi. Yaron ya ce mata ya ffita, ta ce
    To in yazo kaa ce masa Ummi tana asibiti ba
    lafiya, an bata gado. Karfe uku ya iso asibitin
    hankali a tashe, sun gaisa da Umma ta raka shi
    dakin, hankalinshi ya tashi da ganin Amaryarshi
    kwance a gadon. Abba kam yana gurin aikinshi
    amma hankalinshi na Asibiti, su Alhaji ma duk
    nan suka nufo, Abba sai da yayi magriba sannan
    ya shigo asibitin. Jikinshi babu karfi, bai matsa
    sai yaga farkawar Ummi ba ne saboda yasan da
    gaske ba shi ne ya dace idanunta su soma arba
    da shi ba, ya samu su Umma da su Alhaji.
    Sahabi da abokansa duk suna gurin, ya gaida su
    tare da tambayar ko ta farka? Umma ta ce har
    yanzun dai shiru. Ya nufi cikin gurin Likitan suka
    gaisa, ya ce Likita har yanzu ba ta farka ba. Suka
    jera zuwa dakin, Likiran yana cewa cikin wannan
    dan takin zata farka, In sha Allahu. Sun shiga
    takin tana dan motsi suka nufi gadon Abba ya ce
    Ummi. Likitan ya daga mishi hannu alamar yayi
    shiru ita kam daidai lokacin mafarkin Abba take
    wai suna tafiya ya rike mata hannu sai ga
    Sahabi. Yana zuwa ya kama hannunta tana
    tirjrewa, sai janta yake zai fita da ita, Abba yana
    tsaye yana kallonsu. Ita kuma sai kiran "Ya Abba!
    Ya Abba!! Take yi. Likitan ya kara kunne gurin
    bakinta ya dagowa yayi ya dube shi. "Waye Yaya
    Abba?" Abba ya ce ni ne. Liitan ya ce, matsa
    kusa, ya kama hannunta. Ummi. A hankali ta
    bude ido. Ya Abba! Ya abba, zan sha ruwa, ya ce
    to ya kalli likitan za ta sha ruwa, Likitan ya ce,
    "A'a bari ta dan kara warwarewa tukunna. Likitan
    ya kama kafafunta ya dan matsa, sannu ko. Ta
    kalle shi, kin ji zafi? Bata yi magana ba ya dauki
    allira ya 6are ya dan soka mata a tafin kafa ta ja
    kafafunta alamun taji zafi. Ta yunkura zata tashi,
    Ya abba zan tashi, ya tayar da ita zaune. "Likitan
    ya ce Alhamdulillah, Abba ya kalli likitan, ba
    matsala kenan? Ya ce, Ina zaton haka insha
    Allah, Abba ya ce "Alhamdulillahi, ya jinginata da
    jikinshi, sannu Ummina. 41.... Alhaji ya shigo
    yana cewa, "Ina Abba ne?" ya ganta zaune a'a ta
    farka ne? ya kama hannunta sannu uwata. Ta
    kalle shi. "Ina Ummata?" ya ce, "Bari in kira miki
    ita". Yaje ya sanar da su, sun shigo da murna.
    Sahabi ya iso gaban gadon. "Sannu Ummi". Ta
    kalle shi sai ta kwantar da kanta a kafadar Abba,
    "Ya Abba ina son in wanke bakina". Ya ce, "To
    bari in siyo miki Maclean din". Ta ce, "A'a kada
    kaje". Ya gyara zama "To shi kenan." Umma ta
    ce, "Me ta ke so?" Abba ya ce "Baki zata wanke".
    Umma ta ce "Ai nazo mata da maclean da
    burushin nata, don nasan ita gwanar wanke baki
    ce". Nurse ta kawo wani dan kwano na silba
    Ummi ta wanke baki da taimakon Abba. Likitan
    ya ce, a bata tea mara zafi sosai, sannan a bata
    magani. Takaici dan'kam a zuciyar Sahabi, irin
    wannan shigewa da Abba ke matar da zai aura
    tayi yawa. Kai shi fa wannan Yaya Abban bai
    masa ba ma, don yana daure mishi fuska ko
    gaida shi yayi d kyar yake amsawa. Shi fa tun
    ranar da a ka ce mishi Ummi ba cikinsu daya da
    Abba ba ya ji ya tsane shi. Umma ta ce, "Abba
    an kira Isha'i. Sahabi kaje kai ma ka huta yaran
    nan tun tuni ya ke nan". Abba ya kalle shi, "Ya
    kamata ka tafi haka ko?" ya kalli Ummi sannan
    ya dan rusuna "Sannu Ummi". Ta ce, "Yauwa"
    "Innata ta ce in gaida ki da jiki, ni zan tafi sai da
    safe. Me zan kawo miki?" Abba ya dube shi a
    kule., "Don Allah Malam kaje ba za ta iya cin
    wani abu yanzun ba". Umma ta ce, "Abba". Ya
    kale ta, sai ta girgiza mishi kai alamun ya bari.
    Sahabi jiki a sanyaye ya fice tare da cewa "Umma
    sai da safe". Ta ce, "To Sahabi, ka gaida Innar
    taka". Da ya fita ta kalli Abba "Wannan ba
    halinka ba ne kada in kuma gani". Ya ce "To
    Umma". 23. Su Alhaji sun yanke shawarar daga
    auran Ummi a darua na Fati kawai, ita sati biyu
    masu zuwa sannan ta murmure sai a daura nata.
    Gidan su Sahabi sun ji haushi musamman
    Innarshi, sun kashe dan abinda suka tattala don
    bikin amma gashi an daga, su kam da an daura
    auren in ta murmure sai a yi bikin. Sahabi ya
    shigo gidan ranshi a 6ace, ya kalli Mahaifiyarshi,
    "Inna wai sun ki a dauram?" Ta ce, "Sun ki, dama
    ai gaddamar dan yau ce. Ban da shegiyar
    gaddama ga 'ya can da a ka baka a daura ka
    gaddame, to yanzun ina ranar abin da aka mana?
    Gida duk dangi sun cika amma wai a daga biki,
    mu kuma karamin karfi ne da mu, bare mu ce nan
    da sati biyu zamu sake kashe kudi". Sahabi ya
    tuna abinda Abba ya masa a asibiti, shi ne dalilin
    da bai sake zuwa asibitin ba, yaja tsaki. "Kin san
    Allah Inna ni kaina sai yanzun nake jin haushin
    kaina da na ki amincewa da Badariyya. Mu zuba
    musu idanu in za su sake kawo mana cikas sai
    kawai in koma gurin Badariyya." Inna ta ce, "In
    da tun jiya kamin zancan nan da tuni yau ba a
    fasa daura auranka ba an ma da Badariyya". Ya
    ce, "Kiyi hakuri Inna mu ga nufin su". * 42... An
    sha shagalin bikin Fati kuma an kaita gidanta.
    Ummi jiki Alhamdulillah, Abba kullum in zai je aiki
    sai ya biya. Haka nan in ya dawo gida wanka
    kawai zai yi ya tafi, wataran sai goma ko sha
    daya. Abokanshi suna ta zuba duba Ummi, ita
    kanta da lokacin zuwanshi ya karato ta dinga
    kallon agogo ke nan tana kallon kofa. A zaman
    asibitin nan Umma ta gama karantar su tsaf.,
    matukar son juna suke yi, sai dai taji takaicin da
    sai yanzun sonsu ga juna ya bayyana. Lokacin da
    ya kasance an riga an bada Ummi ga wani sai
    dai ta ci gaba da addu'a Allah yayi za6i na
    alkairi. Bashir yayi murna da fasa auran Ummi,
    dama a fasa gaba daya. Yana fitowa dakinshi ya
    ji Ummarsu tana cewa, "Kin san Allah Tasalla,
    uwar yaron nan da zai auri Ummi zata ga bakin
    ciki, don mallake mata da za su yi. Tana ji tana
    gani sai yanda suka yi da shi. Kuma ba yanda
    zata yi sai Allah ya isa". Tasalla ta ce "Ban da
    halin mutanan yanzun ba da sai na fada mata ba.
    Kin san makotanmu ne ta baya, gashi su ba karfi
    ba. Sahabin ne fa ke rike da gidan, kin san shine
    Babban a gidan". Sahura ta ce, "Don Allah Tasalla
    ki taimaka ki fada musu, don ko in har aka yi
    auran nan in suna cin abinci sau uku ne a rana,
    to za su koma dau daya". Tasalla ta ce "Ai ko
    zanje". Tana fita Bashir ya dawo kusa da
    Ummarsu ya ce, "Umma dama da kanki ki ka je,
    saboda za su fi yarda tunda sun ga ke kina da
    danganta da gidan". Ta ce, "To in Babanku ya ji
    fa?" Ya ce "Umma ai in kin fada musu ai kwa6ar
    su za ki yi, sannan kada kije a kan lokaci, kije ana
    gobe daurin auren". Ta ce, "Saboda me?" Ya ce,
    "Saboda su Alhaji Babban suji haushin rashin
    fada musu da wuri". Ta ce, "Haka za a yi, kuma
    in an fasa Malamai zan shiga don a hanata auran
    ma kwata-kwata". Ya ce, "Kada kije wurin
    Malamai yanzun tukun". Ta ce. "Ai dama sai an
    natsa". * Abba ya fito cikin suit bakake, yayi kyau
    matuka hatta takalminshi sawu ciki baki ne,
    tamkar wani black America. Igiyar wuyan ta
    zauna tsam, sai kamshi yake. Dakin Bishira ya
    nufa ya daga labule, ta dago ta kalle shi yayi
    matukar birgeta. Tana alfahari da shi matsayin
    mijinta, ya ce "Kin shirya?" ta ce,, "Zuwa ina?' Ya
    ce, "A'a, jiya fa na sanar da ke ki shirya da wuri
    zamu je asibiti ki gaida Ummi". Ta watso mishi
    wani kallo uku saura kwata, tare da cewa "Ko
    garin nan ba a sanyi ba zan fita gaida wata can
    Ummi ba bare da sanyin nan." Ya ce, "Dalili ta
    mike tsaye "Ciwo bai kai mutuwa ba, da mutuwa
    ya yi tazo ta min gaisuwa?" Takaici ya turnu'ke
    Abba, da yake sarkin dankara magana ne, sai ya
    ce "To ita ta kashe shi da zata miki gaisuwa?"
    Ta kule da bakin ciki ta zabga mishi harara "To ai
    kasan ni na dora mata ciwon, don haka dole in je
    gaisheta." Ya ja tsaki tare da cewa, ballahaza
    wadda bata san mutuncin mijin auranta ba". Ya
    yakice labulen ya wuce yana jiyo ta tana cewa,
    "Ba dai za ni ba ko me za ka ce". Ranshi a 6ace
    ya isa asibitin, Ummi na zaune kan gado ta kosa
    Abbanta yazo, ko karyawa ta kasa yi, yana
    sallama suka hada ido. Nan ta ke ya ji ya manta
    da duk wani bakin ciki da ya taho da shi, ya isa
    bakin gadon fuskarshi dauke da murmushi. Itama
    murmushin take yi, ya ce. "Ummi ya ya jikin?" Ta
    ce "da sauki". Ya Abba kayi kyau sai ka ce
    Manajan Banki". Umma ta saka dariya, shi ma ya
    yi 'yar dariya, "To ko bankin zan koma?" Ta ce,
    "A'a kafi kyau da dan jaridanka Ya Abba, balle in
    kana turancinn nan a labarai". Ya lakuci
    kumatunta "Ko kwanwata?" Ya juya ya gaida
    Umma, Umma ta ce "Ka zo katafi gurin aikinka
    fa". Ya ce, "Umma sai sha daya yau zanje gurin
    aiki". Ta ce, "Ni na ma kosa a sallame mu". Abba
    ya ce "Ai kila a sallame ku yau. Likitan ya shigo
    ne?" Suka ce "A'a. Suna cikin karyawa Likita ya
    shigo ya same su, ya kuma kafa mata dokokin
    daina tunani, daina shiga duk wani abu da zai sa
    ta cikin damuwa. Rage shan gishiri tare da
    samun isassen bacci, ya kuma gargadi su Umma
    su dinga nisantar 6acin
    Home / ZURFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 3 part 6
    ZURFIN CIKI book 3 part 6
    Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:31
    Rage shan gishiri tare da samun isassen bacci, ya
    kuma gargadi su Umma su dinga nisantar 6acin
    ranta. 26. 43... ABBA Ya kwaso su ya maida su
    gida, cikin satin Ummi ta murmure. Sahabi na
    zuwa sai dai da sun gaisa yake tafiya.
    Mahaifiyyarshi ma tazo, amma Bishira da Sahura
    ko le'ke, Bashir ma yana ta sintirin zuwa. Ganin
    haka Alhaji ya ci gaba da shirin biki, mutan kauye
    dai dama an ce kada su dawo, Ummi dai bata
    maida hankali ga komai ba. Ta ce ma Umma zata
    je gidan Fati, Umma ta ce To sai ki je gurin
    Sahura ta kwatanta miki. Abba ya same su suna
    zancen, don haka ya ce ta shirya zai kaita ya
    ajiyeta in ya tashi aiki sai yaje ya daukota. Yanda
    ta samu Fati da Angonta ana ta ji da juna abin
    ya tsokanota, sai dai ta kasa ganin dacewar
    soyayyar da Sahabi. Da mijin Fati ya fita Ummi ta
    ce, "Oh, Fati cikin kwana takwas dubi yanda ki ka
    yi kyau". Fati ta ce, "Amma ban rame ba?" Ummi
    ta ce "Eh to, kin dan rairaye". Fati ta ce, "Kai ai
    dole, gaskiya ina koduwa, wallahi ba ya barina in
    huta". Ummi ta ce, "Da me?" Fati ta ce, "Dallacan
    ki gane mana". Ummi ta ce, "Wai da me? Allah
    ban gane ba". Fati ta ce, "Ai ke sokuwa ce, gurin
    kwanciya mana. Ummarmu ta samu ta dirka min
    kayan sha na mata, gashi nan nazo ina ta shan
    wuya". Ummi ta zaro ido, "Da wahala ne?" Fati ta
    ce, "Tab, ai kin kusa kema za ki ji". Tsoro ya cika
    Ummi. Ta ce, "Zan ce ma Umma ni dai kada ta
    bani wannan kayan matan". Fati ta yi ta dariya
    tare da cewa, "Ke yanzun sai ki iya wa Ummanku
    wannan zance?" Ummi ta ce, "Sosai ma". Fati ta
    ce, "Ko ba ki sha ba yarinya sai kin sha zafi, ana
    kawo ni ko dan kwana daya bai raga min ba".
    Ummi dai ido ya raina fata. Koda Abba ya zo
    daukarta duk ta damu. ** ** 44..... Tasalla ta
    samu uwar Sahabi ta fada mata cewa, in dole ne
    sai danta ya auri Ummi, to ta amso mishi karya
    tambaya. Don kuwa wata rana sai ta taso ta
    ganshi ko da a hanya ne ta rasa samun hakan.
    Inna ta tsure ta ce, sai a fasa babu dole, ita
    dama tuni abin ya sire mata. Ana gobe daurin
    aure gidan su Ummi suna ta shiri Ummi na ta
    kuka, wannan karon ba Umma ba har Alhaji da
    Tsohuwa sun kule da wannan iskancin da Ummi
    ke yi. Alhaji ya ce "Ki sani uwata, wannan karon
    ko kin tsokalo ciwon nan naki auren nan dole ne
    babu fashi. Idan yaso jinin naki ya tashi ya ta6o
    sama ba zan kuma daga auran nan ba". Lokacin
    da Alhaji ke wannan fadan Abba yana gidan yana
    zaune dakin Umma yayin da Ummi ke gefanshi
    tana rusa kuka. Umma ta shigo ya ce "Umma
    don Allah ki lallashi Alhaji a dan daga bikin nan
    mana". Abba bai ta6a ganin ranar da Umma tayi
    mishi irin wannan kallon da ta masa yanzu ba
    tun tasowarshi. Sannan bata ta6a daka masa irin
    wannan tsawar ba ta ce "Kai! Abba shiga
    taitayinka, me yasa yanzun ka canza, ko kai ba
    za ka hukunta Ummi ba da irin wannan yaro da
    hankalin da take mana? Don gidansu kanta a ka
    soma aure? To wannan karon ba za a daga bikin
    ba, in yaso ta mutu, ke ko mutuwa ki ka yi
    gawarki can gidan mijinki za a je a miki sutura".
    Tsohuwa ma daga can tana yo nata fadan tare da
    dauko tarihe-tarihen da tana cewa, "Lokacinsu
    kaza-kaza". Abba ya sake kallon Ummi,
    matsanancin kukan da take yi yana daga mishi
    hankali, ya mike tare da kama hannunta, "Zo
    muje". Ya bude mazaunin direba ya ce ta shiga,
    shi ma ya koma ya shiga motar ya tasheta, tafiya
    kawai suke ba tare da ya san in da suka dosa ba.
    Kukan Ummi na tsikararshi, sun yi tafiya mai nisa
    sannan ya tsaya a hankali cikin wata irin murya,
    ya ce "Ummi ki fada min gaskiya kina son
    Sahabi?" Ta dago ta dube shi, "Ni bana son shi".
    "To me yasa ki ka fito da shi?" cikin dasasshiyar
    murya ta ce, "Ba ni da yanda zan yi ne, saboda in
    ban za6i Sahabi ba za a bani Bashir". Ya ce, "To
    ke yanzun fada min wa ki ke so?" Gabanshi ya
    shiga faduwa don tsoron kada kunnenshi ya ji
    mishi ta ce wani ba shi ba. Ta kuro shi da ido
    tamkar ta ce kai, amma sai take ganin in ta fada
    mishi haka dan shirin da suka soma yanzun zai
    wargaje, kila ma sai ya hada mata da duka. Wasu
    zafafan hawaye suka gangaro kan kumatunta,
    daidai lokacin da yake cewa "Ko dan digo ki ka ji
    son ko waye a ranki kada ki rufe min". 45... Ta
    girgiza kai "Ba na son kowa Ya Abba". Cikin wani
    irin yanayi ya dubeta, "Shi kenan, sai ki je ki
    hakura da Sahabin a sannun kin so shi". Cikin
    kuka ta ce, "Ya Abba Allah ni bana son shi, kai to
    ka hada ni da ko waye mana". Ranshi 6ace ya
    dubeta cikin tsawa ya ce, "Ki rufa min baki tunda
    ba ki ta6a son kowa ba ki zauna da wanda ki ka
    za6i zama da shi. In da kina son wani ne to da
    sai in cije in tunkari su Alhaji, tunda kuwa babu
    sai in ce musu me?" Ya fada mota, ya koma kofar
    gidan. Koda ya tsaya tafi minti uku sannan ta
    fito, yana kallonta maimakon ya wuce gida sai
    kawai ya nufi gidan Maman Iman makociyarsu da
    suke shiri da ita. Shima kanshi na kan sitiyarin
    motar har ttsawon shudewar wasu dakiku,
    sannan ya nufi gida. 27. Misalin karfe tara
    Umman Bashir ta rangada sallama a tsakar gidan,
    Innar su Sahabi ta amsa tare da fadin "Shigo".
    Sahura ta shiga tana tambayar "Ba kowa dai ko?"
    Inna ta ce "Shigo mu kadai ne". Bayan sun gaisa
    ta ce "Ba ki sanni ba ko?" Inna ta ce, "Eh."
    Sahura ta ce, "To ni dai tsakani ga Allah zuwa
    nayi in ba ki shawara bisa ga yarinyar da danki
    zai aura. Tsakani ga Allah yarinyar ba ta da
    mutunci, sannan iyayenta za su mallake miki da,
    don ni kaina ya faru da ni". Sahura don makirci ta
    soma rishin kuka. "Dana maigidana ya ba su riko,
    ina sheda miki wannan zance 'yar uwa yanzun
    tsakanina da shi sai ido, sun makkale shi komai
    shi yake musu, ni ko da nayi wahalar ciki da
    nakuda sai na tashi a banza. To da yake an ce
    ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, shi ne nazo in
    sanar da ke. Amma in kin ji haushi kiyi hakuri".
    Ta yunkura zata mike. 46... Inna ta ce, "Zauna
    'yar uwa, na gode. Nima fa tuni auran nan ya fice
    min a rai, dama da naga shi Sahabin ya dage ne
    sai kuma suka aiko gobe azo za a daura aure sai
    na hakura". Kafiin Sahura tayi magana sai Sahabi
    ya doka sallama, Inna ta ce "Yauwa zo nan". Ya
    nufo ta "Zauna kaji ma kunnenka". Ya rage
    tsawo, Inna ta ce "Baiwar Allah ya ki ka ce?" Nan
    Sahura ta soma zuga sharri, ta kara da cewa
    "Yaro ina ga ma za ka san dan nawa da suke riko
    Abba a ke ce masa". Cikin saurin baki ya ce, "Na
    san shi". Ta ce, "To dana ne da asiri suka amshe
    min shi, sai dai Allah ya isa". Ya tuna irin halayen
    da Abban ke nuna mishi. Yaa jinjina kai, sannan
    ya dubi mahaifiyarshi "Inna to da Kawu yayo
    binciken halayan iyayenta ai ana ta yabon
    halinsu". Inna ta ce, "Kin ji shi ko? To bari kaji,
    kwanaki ma Tasalla da ke bayan layin nan tazo
    ta fadan irin wannan matsalar ban kama ba ne
    don na asanta da shegiyar karya. To kuwa an yi
    biyu ba zan bari ai na uku ba, don haka a daran
    ta tabbatar ma da danta an fasa gobe ya wuce
    gurin Badariyya a daura, su kuma in sun ji shiru
    sa ba wani can". Cike da murna Sahura ta koma
    gida. * Maman Iman tayi lallashin duniya amma
    Ummi ta ki yin shiru, ga zazza6i tamkar wuta a
    jikinta. Sai kusan sha dayan dare sannan Maman
    Iman ta rako ta gida, lokacin Umma tana ta
    neman layin Abba a kashe. Ta ce, "A'a sun dawo
    ne yanzun ni ke neman Abba in ji suna ina ne?"
    Maman Iman ta ce, "Tun dazu tana gidanmu
    zazza6i da ya rufe Ummin, na bata magani ta 'ki
    sha". 47... Umma ta ce "Rabu da ita kar Allah
    yasa tasha, aure dai gobe babu fashim dubi irin
    yanda a ka sa gidan su yaron nan wancan karon
    suka kashe kudi gurin yin girki da sauransu ba a
    yi bikin nan ba. Yanzun a kuma dagawa daga
    lokacin da muka samu?" Maman Iman ta ce, "Ai
    ba zai yiwu ba, sai dai a bi ta da lallashi". Umma
    ta ce, "Mun daina lallashinta tunda ko mun
    lallasheta aikin banza ne". Maman Iman ta ce,
    "To Allah ya kaimu gobem bari in shiga gida sai
    mun shigo aiki da safe". Umma ta ce, "To sai da
    safe". Ummi tana shiga dakin Umma taga baki
    kwakkwance, ta ce a ranta "Mayu, don kalata sai
    da wasu suka dada zuwa". Tana fushi da
    tsohuwa amma duk da haka dakin ta nufa, ta
    kwanta a bayanta don ita tuni tayi bacci. Nishin
    kukanta ya farkar da Tsohuwar, kala bata ce
    mata ba, sai sauka tayi ta shimfida a kasa ta
    kwanta, sannan ta ce "Aniyarki ta biki Takwara".
    Wannan dare gurin Ummi da Abba wani dare ne
    mai cike da bakin ciki da tashin hankali, ko Sarkin
    sata bacci ranar bai samu galaba gare su ba.
    Dukkan su a kan kunnansu aka kira sallar farko,
    Abba ya mike cikin rangaji, jin jikinshi yake yi
    tamkar iska ta dauke shi saboda rashin karfi.
    Ruwa ya diba ya watsa, wanka sannan yayo
    alwala don yin nafila, addu'a yake Allah yasa
    hakan shi ne mafi alkairi a gare shi. Da ya dawo
    Masallaci kwanciya yayi amma baccin ya ki bai
    fita ba sai kusan takwas. Koda yaga Bishira
    zaune a tsakar gida tana karatun littafin sam bai
    ji haushin rashin zuwanta gidan su Umma ba.
    Nashi ganin duk wanda yaje tamkar yana murna
    ne da rasa Umminshi da yayi, ita kuwa da gadara
    ta fito don ya ji haushi, bata je ba yana son sanin
    halin da Ummi take ciki amma ba ya ra'ayin
    zuwa gidan su Umma. Shagonshi ya bude ya
    shiga ya dan zauna har zuwa tara, yana kallon
    lokacin da Jama'a suka yi ta dafifin shiga layinsu
    don halartar daurin auran. Kurum sai ya samu
    kansa da tare dan Aca6a ya hau ba tare da ya
    shaida masa inda za su ba. Koda dan Aca6an ya
    tambaye shi ce masa ya yi mu je. 48.... Ita ko
    Ummi ranar zaune tayi sallah ta koma ta kwanta,
    duk kaikawon ai da 'yan shewe-shewen da jama'a
    dangi da makota tana jin su. Sai dai makoshinta
    ya bushe ga zufa da ta rufeta, duk da yanayin ba
    na zafi ba ne. Karfe goma daidai shi ne lokacin
    daurin auran, layin ya dinke da jama'a, Alhaji
    ranshi a dame don bai ga Abba ba. Ya kalli Alhaji
    Karami, "Ina Abba ne?" Alhaji Karami ya ce,
    "Abokan aikinshi ga su can sun zo ba a ganshi ba
    son daukan daurin auran". Alhaji ya ce, "Su dauka
    mana nasan yana nan tafe". Har sha daya ana ta
    jiran 'yan gidan Ango shiru, su Alhaji suka tashi
    dan aike gidan don a ce ana jiran wakilan ango.
    Amma sai a ka dawo musu da sako wai sun fasa,
    kalmar da ta rikita Alhaji ta tashi hankalinsa. Ga
    jama'a an tara, Alhaji Karami ya ce wadannan
    akwai kananan mutane." Daidai lokacin da muryar
    wani Maroki ta ratso dodon kunnuwansu da
    cewa, "Alhaji ku hanzarta Jama'a sun gaji da
    jira". Alhaji ya dubi Alhaji Karami, "Aminu a daura
    da Bashir". Alhaji Karami yayi shiru, can ya ce "A
    daura da Abba". Alhaji Babba ya ce, "Ina zuwa".
    Ya fito daga dakin Abba na da inda suke yin
    shawarar, ya ratsa mutane ya ce a yi masa
    magana da Suwaiba. Umma ta fito daga kicin ta
    same shi a dakinsa yana tsaye yana kai-kawo ta
    ce lafia? Ya ce Gidan ango ne shiru, an bisu sun
    ce sun fasa. To shi ne na ce me zai hana a daura
    da da Bashir? 49... Umma ta ce a daura da Abba.
    Ya ce, "Haka ma Aminu ya ce. To ni ban ga
    Abban ba ma, amma bari muje Allah yasa hakan
    shi ne mafi alkairi". Take a nan a ka daura auren,
    Habiba da Idris Alhaji Babba ya kirgo sadaki ya
    mika. Alhaji Karami Waliyinta ya amsa, mutane
    na ta al'ajabin yanda lamarin ya sauya. Umman
    Bashir kuwa Bashir din ne ya shiga gidan hankali
    a tashe yana fada mata cewa da Abba a ka
    daura. Nan ko ta hau bala'i da zage- zage. Ummi
    ko tunda ta jiyo guda na alamta mata an daura
    aure, sai ta birkice ta shiga kowa da
    numfashinta. Fati da ke kusa da ita tana
    lallaminta ita ce ta kwala ihu, ba shiri aka yi
    asibiti da Amarya. Fati ta shiga gidansu da kuka,
    nan ta taras Ummansu tana bala'i sai lokacin ta
    ji da Abba a ka daura. Ta ce da Ummar su to
    menen ba shi ke nan ba? Umma ta hau zaginta
    tare da cewa, kar ki ga kin yi aure sai in miki
    shegen duka, Fati dai ta fice ta bar gidan. Sam
    Umma bata ji dar da ciwon Ummi ba, wannan
    karon don haka ma bata bi su Asibiti ba, da
    kanwarta Saratu a ka tafi. Likitan yayi ta fada
    lokacin da yake yi mata allurai, a kuma bata gado
    Umma ci gaba tayi da kula da bakinta. Yayin da
    zuciyarta take fara kar, ta sani kuma tayi Imani
    Allah ba ya tozarta addu'ar bawansa, matsawar
    bawan yayi hakuri tare da dogewa. Haka nan in
    baka samu biyan bukatarka nan duniya ba lallai
    gobe kiyama zaka tarar da abinka. Ta jima tana
    rokon Allah yasa 'ya'yan nata biyu su zam miji
    da mata su haifa mata jikoki masu albarka. Suma
    su Alhaji suna ta sallamar baki sai dai yanzun ba
    wanda ya damu ya gani irin Abba. Fatanshi Allah
    yasa Abban yayi farin ciki da wannan hukunci da
    suka yanke. Salis kuwa burinshi ya zama shi ne
    mutum na farko da zai wa Abba wannan albishir
    sai dai ya kira layin Abba sama da sau hamsim
    bai daga ba. Abinda bai sani ba shi Abba ma gida
    ya bar wayar, haka suka gama dauke-daukensu
    yayi hira da Jama'a da kuma iyayen Ango da
    Amarya don jin ta bakinsu a kan yanda auren ya
    juye zuwa na zumunci. Haka nan suka tafi ya
    samu abin sawa a Taskar labarai, burinshi yanzu
    shi ne ya je ya nemo angon. 28 50.....Abba kam
    kofar dan Agundi ya yada zango gidan su Mansir
    abokinsu, shi ne kurum cikin abokan Abba da bai
    yi aure ba. Yana isa kofar gidan Mansur na
    fitowa za shi daurin auren, wani dan layinsu a
    Gwammaja suka gaisa. Abba ya ce "Bari in dan
    kwanta a dakinka". Mansur cikin mamaki ya ce,
    Lafiya? Abba ya ce lafiya lau. Yana kwance dakin
    Mansur idanunshi suna kallon agogo, zuciyarshi
    tana raya yanzun abar sonshi ta zama matar
    Sahabi. Sai dai bai san dalilin da bugawar
    agogon karfe sha daya daidai tazo gwame da
    bugawar zuciyarshi ba. Zuciyarshi ta fada mishi
    cewa wannan alamu ne na an kammala daurin
    auren. Wasu hawaye ne suka biyo ta gefen
    idanunshi suna sauka a kan filon. Yini zur yana
    dakin in lokacin sallah yayi sai ya fito kofar dakin
    yayi alwala har duhun Magriba ya gabato. Ya fito
    tare da kulle dakin, don Mansur bai dawo ba,
    kuma dama ya ce ba zai dawo da wuri ba. Gidan
    nashi ba kowa lokacin da ya shiga, kai tsaye
    dakinshi ya wuce, ban da idanunshi da suka kai
    kan wayarshi ya manta ma yana mallakinta. Ya
    kai hannu ya dauka, bai ji mamakin yawan
    missed calls din da ya gani ba, kiran Salis ya
    sake shigowa. A kasale ya daga, muryar Salis ta
    ratsa dodon kunnanshi, fadi yake yana
    maimaitawa Ango- Ango. Abba cikin sanyin
    murya ya ce "Salis ya haramta a gare ka ka
    zolaye ni a halin da nake ciki. Sanin kanka kai
    kadai ne kasan yanayin da nake ciki". Salis cikin
    zumudi ya ce, "Kana nufin ba ka sani ba?" Abba
    ya ce, "Me?" Salis ya ce "To bani goron albishir in
    sanar da kai". Abba ya ce, "Don Allah Salis kada
    ka min karya". Salis ya ce, "Ina rantsuwa da
    wanda ya yi mu Ummi matarka ce, da kai a ka
    daura. Ina ka shige lokacin da al'amarin ya canza
    salo?" Abba ya mike zumbur. "Ka fa rantse Salis!"
    cikin dariya Salis ya ce, "Wai har yanzun ba ka
    sani ba? To ka aje min goron albishir dina". Abba
    yasa hannunshi a baki ya gatsa, zafin da ya ji ne
    ya tabbatar da mishi da ba mafarki yake ba. 51...
    Ai sai ya katse wayar ya zube yayi sujjada ya fita
    tsakar gida yana furta "Alhamdulillah." Ruwa yaja
    ya watsa ma jikinshim sannan ya yi alwala.
    Sabuwar shadda ya saka kalar kunkumadi, ya
    fesa turare sama da kala hudu. Hula da takalmin
    bakake, ya nufi Masallaci, daga can za shi gidan
    su Umma don jin karin bayani. Bayan sun idar da
    Sallah, mutane suka yi ta masa murna, nan ya
    hadu da su Alhaji kawai yau sai ya samu kansa
    da kunyar Alhajin. Alhaji ya ce, "Ubana ina ka
    shige duk yau?" Ya rasa me zai ce, sai in-ina
    "Am...na kwanta ne bana jin dadi". Alhaji yayi
    'yar dariya, "Kai dai ka ce kana taya kanwarka
    fushi don mun ce ba zamu daga aure ba, to ba
    mu daga ba amma Allah cikin ikonsa ya sauya
    lamarin". Abba tamkar bai san komai ba, ya ce
    "Alhaji me kuma ya faru?" Alhaji Karami ya
    karaso gurin su yana cewa, "Kai Abba ina ka
    shige ne?" Abba ya dube shi "Nan dan Agundi na
    shiga". Alhaji ya ce, "Oho, shi yasa aka yi ta
    nemanka. To ka ji kuma yadda lamari ya sauya
    ko?" Alhaji Babba ya amsa tare da cewa, "Shi ne
    nake massa bayani, wato Abba iyayen yaron nan
    Sahabi muka yi ta jiransu su zo gurin daurin
    aure, wai ashe su sun fasa. Amma ba su shaida
    mana ba har bin su fa nasa aka yi, gashi mun
    tara jama'a kawai sai Aminu da Ummanka suka
    ce a daura da kai, da ni na ce a daura da Bashir".
    Dadi ya lullu6e Abba irin wanda bai ta6a ji ba,
    Alhaji ya ci gaba da cewa, kayi hakuri mun kara
    maka nauyi ba tare da mun ji ra'ayinka ba". Abba
    cikin matukar murna ya ce, "Haba, ai ko ba 'yar
    uwata ba ku ka daura min aure da ita zan aminta
    bare jinina. Nagode". Sun ji mamakin yanda Abba
    yayi murna, duk da sun san biyayya irin tashi ba
    zai 'ki ba, tare suka rankaya gidan su Umman, so
    kurum yake yaga Ummi. Ba mutane sosai, don
    haka har ciki ya kutsa, sai dai suna hada ido da
    Umma sai ya ji nauyinta, ta fada da fara'a. "Ina
    ka shige Abba?" Yayi dan murmushi, ta ci gaba
    "Sai kuma ka ji yanda abu ya kasance?" Ya ce,
    "Na ji Umma, Allah yasa haka shi ne alkairi". Ta
    ce, "Amin, Insha Allahu". Tamkar ya tambayi ina
    Ummin, amma ya kasa. Umma ta ce "A baka
    abinci ko?" sai lokacin ya tuna da batun abinci,
    amma baya gabanshi, ya ce "Na koshi Umma".
    Ta ce, "To ga na 'yan asibiti can in kayi isha'i".
    Da sauri ya ce "Wa ke asibiti kuma?" Ta ce,
    "Ummi ce, ko 'yan daurin auran ba su watse ba
    don ka ji yarintar nan ta hau farin suma don
    haushi ko leka su ban yi ba. Tana can it da
    Saratu sai Tsohuwa da ta matsa yanzun Alhaji
    Karami ya kai ta". Jikin Abba ya yi sanyi, kenan
    tsabar rashin sonshi ne ya saka Ummi suma? Ya
    ce Umma bani abincin asibitin. Sai da yaje
    gidanshi ya dauko dan mukullin motar, a
    zuciyarshi yana tambayar kanshi ina kuma
    Bishira tayi ne? Zai bude motar kenan muryar
    Bashir ta dakar da shi, "Kaci nasarar samun furen
    zuciyata, amma ka sani ka kulla abota da rashin
    zaman lafiya a novels / ZURFIN CIKI book 3 part 7
    ZURFIN CIKI book 3 part 7
    Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:33
    kulla abota da rashin zaman lafiya a gidanka". *
    52..A fusace abba ya dubeshi"xansa yan sanda
    su rufe min kai inhar zaka cigaba da kiran matata
    da furen zuciyarka,rashin zaman lfy kake cewa?
    An dade ba'ayi yaki abgdn ba kullum,bashir yace
    oho dai ni zanta zuga umma abba yaja tsaki
    tareda shigewa motarshi. Bashir yashiga gdnsu
    inda su ummanshi dasu bishirabke zaune jugum
    jugum tamkar masu zaman makoki,bishira tabi
    bashir da kallo lkcn dayace ga ya abba ya can a
    waje yashiga mota ya kure wanka,kila ma asibiti
    zaije ana fada maku yanaso kuna wani tilasta shi
    akayi,bishira cikin dasahhshiyar murya tace aiko
    da bala'i don ko bazan yarda ba,umman bashir
    tace sha kutuminki bishira,barni dasu zan
    maganinsu, bishira tafita fuu,amma saidai. Kafin
    ta isa gurin motar tuni ya, Cilla yabar mata
    hayaki. Da innna saratu kanwar umma ya soma
    cin karo a asibitun suka gaisa,tace ashe kuma
    haka abu ya zama? Yace eh"nima dana dawo
    dazu nasamu lbrin,tace Allah yasa hakan shine
    mafi alkhairi,abba yace ameen inna,ya mai jikin?
    Tace dasauki,yace bacci take? Tace a'a ta farka
    tun kusan karfe uku,koda fatima ta fada mata
    yanda abubuwa zuka zama,tayita yan koke
    kokenta,gaban abba yafadi****tabbas ummi ba
    son shi take ba inba hka ba meye na kuka? Ya
    kalli inna bari in karasa,tace to kaje tshuwa na
    ciki,a ranshi yace jaraba road,yasan dai ko yane
    sai tshuwa tayi mishi surutu,yana tura kofar
    tareda salama suka hada ido da ummi,sun kure
    juna da kallo,kowanne nason ya fahimci ya dan
    uwansa yadauki abin"tshuwa ta katse su dacewa
    to zakin fama sai ynz kaga daman zuwa? Ya
    dubeta eh" ai eh ace? To me kikeso ince,tace to
    madalla ai na dade da sanin halinka,kuma da ace
    iyayenku sunyi shawara dani lallai da baza suyi
    wanna hadin ba Domin na tabbata kai zaka
    karasa takwara don baka kaunarta, haushi ya
    cika abba abba yana kallon tsohuwa yana tuna
    amsar data dace da ita, ummi kuwa tsura mishi
    ido tayi tana son jin me zaice,yace kamar kin
    sani,tace ahaf shiyasa tausan yar nan kebani
    tausayi, ta soma matsar ido,yace nima yakamata.
    ki tausayamin tnda cusa min ita akayi,ummi
    takoma ta kwanta lakwas tareda hakikancewabl
    kalaman abba sako ne zuwa gareta,matar cushe
    kuma bata daraja,to inaso kasan wani abu
    guda,duk randa naji wani abu daidai da
    wulakanci, toba kaiba har iyayenka saisun san
    naje makura. 52..Dazun nake gaya masu basun
    hada kai sun kulla auren nan ba,duk randa suka
    kuskura sukazo min da batun warwareshi saina
    basu mamaki,abba ya tabe baki tareda kallon
    ummi wadda takasa jurewa tashiga rera kuka,ya
    isa gaban gadon,"jikin ne ummi? Tayi shuru,kinci
    abinci? Nan ma ta share,sai kurum ya nufi wurin
    likitan zuciyarshi na kuna bako shakka kukan kin
    shi ummi keyi,sun zo da likita ya shiga yimata
    fadan kukan da takeyi,a cewar likitan kukan illa
    ne ga lafiyarta,tshuwa ta kalli likita dan nan dole
    ta koka a dauke ka ahadaka da wanda baya
    kaunarka"abba cikin takaici yace subhanallla! Don
    Allah tshuwa kibarni inji da abinda ke
    gabana,tace ina ruwana da abinda ke
    gabanka,likita yayi dariya yace mama yakamata
    ki koma gd haka,abba yace bari inkaita
    indawo,tace ban binka da can dani kazo? Abba
    yace nahuta,likita yayi dariya,da kyar suka lallaba
    tshuwa ta tafi da inna saratu,abba yaja kujera ya
    zauna gaban gadon,bayan fitan likita Idanu ya
    zuba ma ummi,godiya yake ma Allah a zucin shi
    daya amsa addu'ar shi yabashi abar sonshi,itako
    kai ta dukar a ynz takasa tantance kukan farin
    ciki take ko takaicin kalaman ya abbanta? Wani.
    Dan zare dake jikin hijabinta take wasa dashi,a
    zuciyarta kuma tambayoyi ne da fuska data jefa
    masa su,ya katse ta kinci abinci? Ta daga kai
    alamun eh" yace to yakamata ki dangana da
    kukan haka kisani ni kaina da ina nan bazan bari
    su alhji su daura maki aure da wanda bakiso ba.
    53..Da sauri ta kalleshi,yace. amma inkin yi hkr
    zansame su zamu san yadda zamuyi,ta lumshe
    ido a zuciya tace tab! Ai rabamu sai mutuwa,zan
    juri duk wani ki dazan gani daga gareka,ya
    katsxeta kina zance a zuci fadi abnd kikeson
    cewa,tayi tagumi tareda kallonshi,ya abba yakanfi
    dacewa sa dan sanda ne ba dan jarida ba,sbd
    yanada saurin nazartar mutum,to amma meyasa
    yakasa gane tana son shi? Yayi murmushi,zanso
    inji abnda kikeb saqawa azuciyarki ko kinn samo
    mafita ne? 29. Zancan mafitar nan tana bata
    haushi, don haka saita canza zancen da cewa,
    tambaya zan maka guda biyu, ya dan yi shiru.
    Nazari yake, wace irin tambaya zata masa? Kila
    zata tambaye shi ne ko zai amince ya sahale
    mata auranshi, ya dubeta amsa daya zan ba ki in
    kin yarda, ta ce To dama zance ne ya ka ji
    lokacin da labarin sauyawar lamari ya zo gareka?
    Ya kura ta da ido, ya tambayi kansa a zuciya, me
    yasa take son ji@ yayi dan yake, yi tambayarki ta
    gaba, ta tsura mishi ido. Yanzun yaya za ka yi da
    maganar Zainab? Ya yi 'yar dariya, wacce amsa
    ki ke so a ciki? da sauri ta ce ba ni wannan
    amsar. Ya ce, "Kiin manta ni mijin mace hudu ne?
    Ta zaro ido kamar ya ya? Ya yi kokarin danne
    dariyarsa, sakamakon yanda ya ga ta zarana. Ya
    ce, "Ina nufin bayan Zainab har da wata, Ummi ta
    hade rai sannan ta zame ta kwanta cike da dana
    sanin tambayar. Abba ya yi mamakin kishin
    Ummi gare shi, ita da ba sonshi take ba? Ko da
    yake an ce mace ko bata son namiji in dai mijinta
    ne ta tsani ta ganshi da wata. Duk da haka ya ji
    dadin yanda ta nuna kishinta a kanshi, da ya tuna
    da Bishira ya ce tab, wata fitinar tana can tana
    jirana yau. Sam Ummi bata kara magana ba, shi
    kam Abba waya ma yake tayi Inna Saratu ta
    dawo, don haka ya mike ya kalli Ummi. Zan tafi
    ba tare da ta dago ba ta ce, sai anjima. Ya tafi
    yana waiwayonta bayan ya wa Inna Sallama. Kin
    shiga gidanshi ya yi sai kusan sha biyu a nufinshi
    lokacin Bishira tayi bacci, sannan yaje ya sai
    mata wayar da layi don yasan tana son waya.
    Kudinshi kenan ma ya kwashe ya sai mata, bai yi
    wani motsin kirki ba don kada ta farka, ya bude
    dakinshi ya shiga ya fito yana jan ruwan wanka
    kenan ta fito daure da zani a kirji. Jikinta ko dan
    kwali babu, gaban Abba ya fadi ta ce, "Munafukin
    Allah, annamimi dama ashe abinda kuke shiryawa
    kenan? To ka sani dole kasa ke ni don ba zan iya
    zama da Ummi ba, Allah ya kiyaye in hada miji da
    wannan 'yar yarinyar, tunda kai baka ga ai baya
    ba". Ya sassauta murya, "Haba Bishira, wannan
    abin fa Allah ya kaddaro za a yi haka, matar
    murtum kabarinsa. Ta ce, "To wannan ajalinka ce
    tunda wancan ya ki shi ne kai a ka cusa maka.
    Ya bar jan ruwan ya kama hannunta suka nufi
    dakinta, tana ta masifa. Ya ce, kibar maganar
    yanzu dare ne duk makota suna ji za su yi, kuma
    banga bain da zai sa ki daga hankalinki ba. Kin
    san dai ina sonki ko? Ta yi shiru tana kallonshi,
    ya ce ina zuwa. Yaje dakinshi wayar ya dauko
    mata, ga wayarki. Ta ce, "Eh don ka toshe min
    baki k? to bana so, ita wa ya san abinda ka sai
    mata? Ya ce, ya ki ke wannan maganar? Ban sai
    komai ba ko lefe ma tukunna. Ta mike tare da
    jefa mishi kwalin wayar, Ga tsiyarka nan
    matsiyaci, dole ka saka min da haka, tuni a ka
    gaya min tsiyar talaka na tafe. Haushi ya kama
    Abba ya dauki wayarshi ya tafi ya maida yazo ya
    dau ruwanshi yayi wanka, yana jiyo kukanta da
    duk zage-zagen da take yi. Shi kam katifarshi ya
    fada tare da rungume fito yana tunanin ranar da
    Ummi zata maye gurbin filon. 30. Har an tada
    sallah a Masallaci lokacin da ya farka, ya jima
    bai yi irin wannan baccin ba, da hanzari ya fito
    ya nufi ban daki don alwala. Abin mamaki Bishira
    ce zaune kan kujera a kofar dakinta, matar da sai
    ta kai takwas bata farka ba, amma yau bala'in
    kishi ya hanata bacci. Ta ce, "Eh na fito a ba ni
    takardata na gama zama da kai, ko in da take bai
    kalla ba ya ci gaba da abinda ke gabanshi, ya
    nufi Masallaci yana jinta tana ina nan ina jira ba
    zan zauna ba. Haba, gaskiya naji na tsani
    yarinyar ashe mijina zata aura, tsaki ya yi ya
    bude gidan ya fice. Har gari ya soma haske yana
    cikin masallacin, tunanin zuwa gidan yake, daga
    karshe dai ya fita da niyyar zuwa gidan
    Ummarshi. Wata zuciyar ta tambaye shi da cewa,
    tsoron ta ka ke ji ne? Kar ka zama soko dai a
    gidanka. A fili ya furta cewa, tunda na bita ta
    lalama ta ki, bari in koma mata ta zafin, ida din
    me? Sai ya sauya hanya zuwa gida rai 6ace,
    fuska daure ya shiga gidan, tana ta kai-kawo a
    tsakar gida. Ta dumfaroshi sai ka ce sabon
    kamun hauka, daga ganinshi ta dinfaroshi. "Ka
    ban takardata ba ni ba zama da kai, tafiya zan
    yi". Ya harareta "Sai da takarda za ki tafi? Lallai
    ba ki ji tafiyar ba. To ba zan bada takarda ba,
    don ki sani, sai dai in kotu za ki kai can Alkali ya
    baki". Ta nufo shi da zummar shako masa kwala,
    ya ce Kina ta6a ni sai na zane ki, in yaso ki tafi
    da hujja". Ganin yanda Abba ya bude mata wuta
    sai taja baya, Ka isa ka zane ni, ai da ka san ka
    dake ni, don ko sai ka sha dauri. Ya nufi dakinshi,
    wanka ya fito yayi sannan ya yi shirin tafiya aiki,
    amma har lokacin tana nan, ga 'yarta ta tashi
    daga bacci sai kuka take yi. Ta dauke ta ta goya,
    ta shiga dakinta can kuma ta sauke 'yar tasa
    kaya ta fito ta dauraye fuska da kafa ta goya 'yar
    tasa kaya ta fito taja kofar tana fadin." "Tafiya
    zan yi". Ta fito ta same shi yana goge gilashin
    motarsa na gaba. Ta ce, Tafiya zan yi sai an
    kar6ar min hakkina". Murmushi ya saki, sannan
    ya kalleta, ta ina za ki bi in rage miki hanya? Ta
    dawo ta duki motar, Ba zan shiga wannan
    gwanganin motar ba, kai ne bakon mota. Kafi
    kowa sanin daga gidan da na fito, ko motar zuwa
    cefanen gidanmu tafi wannan tsarri. Ya ce.
    "Gurinki ko? Ni ai bani da wadda ta fita tunda
    bata gidan naku nike hawa ba. Sannan kuma
    tunda ba za ki zo in rage miki hanya ba shi
    kenan sai naga sammaci. Ya shiga motar ya
    tasheta yayi gaba, ba tare da ya saurari abinda
    take cewa ba. Ta isa gidansu cikin tashin hankali,
    Hajiya Zainu ta saurare ta tsaf, sannan ta ce "Kin
    dai ga abinda a ke fada miki, kina ganin ba zai
    faru ba ke so ya rufe miki ido, to yanzu an zo
    gurin. Bishira ta ce, "Ai na gane komai yanzun,
    Momy nayi nadama. Ta ce, "To zan tsaya miki
    matsalata Babanku, yana nan a gari na kuma san
    za su zo iyayen Abba. Amma wannan karon shi
    kanshi Babankun zan iya ja da shi, Bishira taji
    dadi sosai, don kuwa duk son da ta ke wa Abba
    yanzun kishi yasa ya koma 'ki. Gidansu Umma
    yaje a gurguje suka gaisa, ya kwashe su da Alhaji
    da Alhaji Karami zuwa asibiti, a motar nema ya
    ke fada musu cewa Bishira ta tafi gidansu Umma
    ta ce a kan me Abba, me ka mata? Ya ce, "Ban
    mata komai ba, ya fada musu duk yanda aka yi.
    Alhaji Karami ya ce, Sahura ke zugata, itama ai
    kwana tayi bala'in. Don haka kada kaje bikonta,
    Alhaji Babba ya ce, "Ba za a yi haka ba, da dare
    kazo muje, Abba ya ce To. Sun isa asibitin tana
    wanka, sun gaisa da Inna Saratu ta fada musu
    tana wanka, sannan likitan ya sallame su amma
    sai sha biyu za su tafi gida, lokacin an karasa
    mata allura. Abba can baya ya tsaya kusa da
    kofar shigowa ya jingina da bango idanunshi suna
    fuskantar kofar bayin, matuka ya kosa yaga
    Ummi. Sanye da hijabi da zani daurin kirji ta fito,
    da Abba suka soma hada ido, bai ta6a kallon
    Ummi da sha'awa ba sai yau. Kamshin turaren
    Abba ya ratsa ko'ina a dakin, ta zare idanunta
    daga nashi, ta kalli Ummanta sannunku Umma.
    Suka ce Yauwa. Ta gaida su sannan ta zauna
    bakin gado tare da sunkuyar da kai, Alhaji Karami
    ya ce, "Uwata jiki kuma ya yi sauki ko? Kanta na
    kasa ta ce, Eh, ta kasa dago kanta, gani take
    Abba ya cika dakin. Abban ya ce, "To ni zan tafi
    don lokacin aikina ya kusa, Alhaji zamu je ne in
    sauke ku? Suka ce To, Umma ta ce In an yi mata
    Allurar anjima ma nemo mai Taxi. Alhaji ya ce, To
    shi ke nan. Umma ta dubi Ummi ba za ki gaida
    Yayan naki ba? Ta saci kallon Abban tare da
    cewa, Au, ban ganshi ba. Ina yini? Ya ce, Umma
    me yasa za ki rokar min gaisuwarta? Inna Saratu
    ta ce, Kai Ummi da iya shege take, ina kallonta
    shi ta fara kare ma kallo sannan ta kalli kowa
    amma wai bata ganshi ba. Su Alhaji dai 'yar
    dariya suka yi sannan suka fita, Abba ya bi su
    tare da yi wa su Umma sallama. * 31. Bayan
    fitarsu, Umma ta dubi Ummi fuska daure, ina
    fatan baki nuna damarar nuna kiyayya ga Abba
    ba ne? Ummi ta sunkuyar da kai, a ranta ta ce,
    "Kin ji Umma da wani zance, ai ina zaton nafi
    Mahaifiyarshi sonshi ma bare ku. "Amma a fili sai
    ta ce, To Umma shi ma fa Ya Abban bai ce yana
    sona ba, Umma ta ce Saratu ji ta da wani shirme.
    Ina ce ita ce zata janyo ra'ayinshi gareta? Inna
    Saratu ta ce, Kwarai kuwa, ta hanyar ladabi,
    biyayya da girmamashi, musamman shi da ke da
    matsalar mata. Ummi ta ce, Kuma ina tsoron
    masifar matarsa ba dai guri daya zamu zauna ba
    ko? Umma ta ce ina ruwanki da matarsa?
    Sannan in ba ku zauna guri daya ba haya zai
    kama? Umma ta ce ina ruwanki da matarsa?
    Sannan in ba ku zauna guri daya ba haya zai
    kama? Kada ma in ji kin kuma zan nan, Ummi dai
    tayi shiru. Da dare Alhaji ya tasa Abba zuwa
    gidan su Bishira, zuwan su ne ma Alhajin yasan
    'yarshi tayo yaji, cikin 6acin rai ya kira wayar
    Hajiya Zainu ya ce su zo ita da Bishira. Ba tare
    da ya jira amsarta ba ya aje wayar, ba tare da
    yasan abinda ya faru ba ya shiga ba su hakuri.
    Hajiya Zainau taje dakin su Bishira ta kira, suka
    nufi sashen Alhajin tana mitar cewa munafukai
    sun zo kenan, ai za'ayi ta bari muje mu ji. Suna
    shiga Alhajin ya kalli Bishira, "Me ki ka zo min ki
    yi a gida? Ta ce, Daddy cin amanata ya yi, aure
    fa ya yi da yarinyar da suka tsane ni. Alhajin ya
    daukin da ke gabanshi na plastik ya jefe ta da
    shi, auren shi ne cin amana don uwaki? Hajiya
    Zainu ta ce, "A'a Alhaji, zan cen gaskiya a duba
    hakkinta itama, ya ya za a dau 'yar da bata
    kaunarta, iyayenta basa kaunarta a ba shi.
    Sannan ta yi magana ya hauta da zagin iyaye?
    Ya ce, "Ke yi min shiru ban tambaye ki ba". Ya
    kalli Abba, Ya abin ya faru? Ban ji ta bakinka ba?
    Nan dai Abba ya fadi komai har ta taho, daidai da
    cewa tazo ya rage mata haya da abin da ta ce
    duka. Alhajin ya yi tsaki ya dubi Alhaji Babba, irin
    wannan ai ba a biyo su, tayi ta tafiya sai dai
    nima in ba zata koma gidanta ba, to ba gidana
    ba. Ya zura hannu cikin aljihu ya ciro rafar 'yan
    dari bibbiyu, Ga shi Abba, dama nayi maka
    alkawarin baka sadaki duk lokacin da ka nemo
    aure. 57..... Abba ya ce, "A'a ka bar su ai an riga
    an yi. Mahaifin Bishira ya ce, "Ni nayi alkawari.
    Suka yi godiya. Ya kalli Bishira, Ko ki bi mijinki,
    ko ki bar gidana. Hajiya Zainu ji take tamkar ta
    shake Abba. Ta ce, "Haba Alhaji, gaskiya ban
    yarda da wannann hukuncin..." Ya katse ta da
    cewa, Ke! Da Allah fita anan. Su Abba suna shiga
    mota Bishira na fitowa da kukanta, dole ta zo ta
    shiga motar. Alhaji Babba ke ta bata baki har
    suka kai gida, shi kam Abba da suke sauke Alhaji
    ya yi nasu gidan, suna shiga ta soma zantuka. Ba
    za ka ta6a samun kwanciyar hankali ba a gidan
    nan har abada, ba dai ka matsa an dawo da ni
    ba? Abba ya yi murmushin mugunta, ai ni
    wannan yajin naki naji dadinsa, gashi har na
    samu gudunmawa, kin ga sai naje kasuwa in
    soma darzo wa Amarya zannuwan lefe. Ya nufi
    dakinshi ya barta nan tsaye tana zage- zage,
    lefen banza, in ma uban lefe ne kai da ita sai na
    koya musu hankali. Kusan goman dare Ummi
    tana kan doguwar kujera, addu'a take yi Allah
    yasa Abba yazo ta ganshi kafin tayi bacci. Can
    kasan zuciyarta kuma kishi ne don tasan sun je
    gidansu Bishira ne biko ganin Alhaji ya shigo shi
    daya sai ta debe tsammani da zuwanshi. A ranta
    take raya cewa yanzun haka suna can suna cin
    soyayyarsu, kamshin turaren shi ne ke mata gizo
    a hanci. Amma sai kunnuwanta suka tsinkayi
    sallamarshi, a hankali tamkar ba ya son a san ya
    shigo. Umma tana ciki? Tambayar da ya yi kenan
    ba tare da ya jira ta amsa sallamar ba, ta tashi
    zaune da sauri a'a tana gurin Alhaji. Ya shigo ya
    zauna ta ce, "Sannu da zuwa". Ya amsa yana
    kalonta, ta sunkuyar da kai, gabanta ke wata irin
    faduwa. Shi kam ji yake tamkar ya manne ta a
    jikinshi, sai dai yana jin nauyin hakan tunda ba
    suyi wannan sabon da ba rin haka zata faru
    tsakaninsu ba. Dakin yayi shiru, ita tana wasa da
    yatsunta shi kuma yana kallonta, can ya ce
    "Ummi". Ta dube shi "Yaushe za ki tare? Ta ce,
    Nima ban sani ba, sai yanda su Umma suka ce.
    Ya dauko kwalin wayar da ya sai ma Bishira ta
    jefe shi da shi ya ciro wayar ya hadata da batir
    din bayan ya 6are sim din ya saka. Ummi dai
    tana ta kallonshi, ya manna chajar a jiki, ya mika
    ma Ummi jona min can, ya nuna mata soke din
    da ke bayanta. Ta amsa cike da sha'awar wayar
    duk da bata nuna hakan ba sannan ba ta ce kala
    ba. Ya ci gaba da cewa, "Karfe nawa a ke kashe
    inji? Ta ce, har yanzu ba a canza daga yanda ka
    ke kashewa ba. Ya ce, "Sha daya zuwa sha biyu?
    Ta ce, "Eh, ya ce in har zuwa wannan lokacin ba
    kiyi bacci ba to ki cire in an kashe, ki kunna ko da
    yake in dai ke ce ba sai na ce ki kunna ba. Ta
    dago ido ta kalle shi, ya ce, Eh kunnawa za ki yi
    ko za ki musa ne? Don kin fi ni ma sanin kan
    waya. Ta ce, Wayar Umma kadai na iya kunnawa,
    sai taka. Ya ce, Oho, cikin dan murmushi, na za
    ci ba za ki fadi tawa ba in tuna miki lokacin da
    kika kunna tawa. Haka nan don tsabar iya sarrafa
    wayarki tun kina 'yar karama ki ka tura ni garin
    Kaduna. * 58....Haka nan don tsabar iya sarrafa
    wayarki tun kina 'yar karama ki ka tura ni garin
    Kaduna. Ta zuba fuskarta cikin tafukan
    hannayenta, sam bata son Ya Abba yana tada
    wannan zancen, Umma ta shigo da sallama tana
    cewa, Yuwa Ummi, ina ki ka sa min 'yar kwalbar
    turaren nan? Ummi ta dago fuska, "Cikin jakarki
    ta rataye. Umma ta dubi Abba, "A'a ha, yaushe
    ka shigo? Ya ce Ban jima sosai ba. Ta zauna ya
    gaisheta, sannan ta ce masa dama Alhaji yanzu
    yake ce min zaman me Ummi ke yi a gidan nan?
    Ya zaci tun daga asibitin zata wuce dakinta,
    Ummi ta turo baki. Umma Alhaji ya gaji da ni
    sosai, suka kalle ta, Umma ta ce, Ji wani shirme,
    me ya yi na gajiya? Ta ce To dubi fa daga cewa
    an fasa aurena sai da ya matsa ya daura min
    aure. Sannann kuma yanzun wai ya zaci daga
    asibiti zan tare? Abba ya ce, Ai yana daki yi
    hanzari ki same shi don shi ya san amsarki ba
    Ummata ba. Umma ta ce, "Wallahi daga nan suka
    share Ummi. Ta kalli Abba ta ce, "To kawai
    yanda za a yi gobe ka kwashe kayanka daga
    dakinka sai a kai na Ummi din kawai. In yaso
    zuwa yamma ko Saratu da sauran makota sai su
    rakota. Abba ya kalli Umma, ni da so nayi a dan
    yi kwaskwarima a gidan kafin sannan na dan
    samu na sai ma Ummin Zannuwa. Umma ta ce,
    "Zancen wofi, yanzun tsirara take yawo? Kawai in
    kana da fenti a hannu a goga a kawo ta haka, in
    babu ma dai goben nan zata tare don ba zan
    amince ran mijina ya 6aci ba. Abba ya yi
    murmushi, to shi kenan Umma da safe kafin na
    fita zan nemo masu aiki ina da fenti da siminti
    sai ayi 'yar kwaskwarima shi ke nan. Dama ga
    kudi nan da Mahaifin Bishira ya bani, wai dama
    ya yi min alkawarin biya min sadaki. . 59...
    Umma ta ce, "Yanzun Alhaji ya gama bani labari,
    Mahaifin yarinyar nan mutumin kwarai ne, don
    Allah Abba ka rike yarinyar nan ko don darajar
    mahaifinta. Ummi ta ta6a baki, kishi ya motsa.
    Abba ya ce "In sha Allahu Umma nima abinda
    nike dubawa kenan, ni ke hakuri da ita. Ta ci
    gaba da cewa, Sannan kada kaga Ummi yar
    uwarka ce ka ce zaka fifitata, sam ba zan yarda
    da haka ba. Kayi adalci a tsakaninsu ka dinga
    addu'a Allah ya hada maka kansu. Ya ce, "In
    Allah ya yarda Umma zan kula. Ta ce, "To maza
    ka tashi ka tafi gurin iyalinka. Sam bai ma dace
    ka fito ba, kamata ya yi a ce ka zauna gida ka
    kara ba matarka baki, ya cee To Umma. Ta mike
    tana cewa, tashi maza. Ya mike yana kallon
    Ummi, yayin da ita kuma ta juya fuskarta cike da
    6acin rai. Ya ce, Ummi ki fa kunna in an kashe
    injin? Sam ba ta tanka ba don haushi, sai da ya
    tafi sannan Umma ta dubi Ummi. Ki tashi ki
    kwanta don gobe ki tashi da wuri, kiyi duk shirin
    da ya dace saboda babu daga kafa a tarewarki
    gobe. Ki ta fasha-fishenki ba zamu kuma yarda
    da kalace-kalacen ciwonki ba, ta tafi abinta. A
    zaton Umma, Ummi tana fushin ba zata tare ba
    ne, ita ko haushinta korar mata miji da Umma
    tayi ya tafi gurin kishiyarta. Koda ta kulle kofar
    ba ta shiga uwar dakin ba, nan kan doguwar
    kujeta ta mike abinta. Jira ta ke a kashe Injin ta
    kunna waya. Abba ko kafin ya isa gida sai da ya
    fita titi ya fanshi kaji guda biyu da madara mai
    tsafta.I novels / ZURFIN CIKI book 3 part 8
    ZURFIN CIKI book 3 part 8
    Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:37
    Jira ta ke a kashe Injin ta kunna waya. Abba ko
    kafin ya isa gida sai da ya fita titi ya fanshi kaji
    guda biyu da madara mai tsafta. 60...Sai dai
    yana shiga gidan ya iske mahaifiyarshi da matar
    tashi suna ta zage- zage. Ya nufi gurinsu, Sahura
    ta ce, Sai yanzun suka barka ka taho? Ya ce,
    "Umma dama ban dade da zuwa ba". Ta ce, "Ina
    ta aiken kazo ina nemanka shi ne ka 'ki zuwa
    saboda ka maida ni 'yar iska ko? Ya ce, A'a
    Umma ba a fada min ba. Sannan aiki ne yasha
    kaina... Ta ce, "Rufe min baki, ai baka daga kafa
    da zuwa gun Suwaiba. To saurare ni da kyau ka
    ji, nazo ne in fada maka cewa ka rubuta saki ka
    ba wannan 'yar iskar yarinyar. Ya ce, Kiyi hakuri
    Umma, ki bari sai a hankali. Bishira ta ce, Umma
    yana sonta fa, jin ku kawai nake. Maganar Bashir
    gaskiya ce da ya ce da shi a ka shirya hakan.
    Umman Bashir ta ce, "Dama Abba kaima son
    Ummi ka ke yi? Ya ce, Umma ba zan ki Ummi ba,
    in kun yi la'akari da kaunar da iyayenta suke
    nuna min. Amman wallahi ban san komai game
    da auranmu ba, ta ce kana nufin kan dole a ka
    daura muku aure ba don kana sonta ba? Abba ya
    yi dan jim, ta ce kai nake sauraro, don ta tafi sai
    ya ce kusan haka dinne, itama kuma ba sona take
    ba. Umma ta ce, Ina ruwana da bata sonka, in
    bata so iyayenta ai suna so. Ni dai bukatata
    yanzun kada ka bari ta tare, sannan ko kusa kada
    taga fuska a gurinka. 33. 61... Umma ta ce, "Ina
    ruwana da bata sonka, in bata so iyayenta ai
    suna so. Ni dai bukatata yanzu kada ka bari ta
    tare, sannan ko kusa kada taga fuska a gurinka".
    Ya dan yi shiru yana tunanin wannan irin lamari a
    zuciyarshi ya ce, bari kawai in lalla6ata, zan yi
    yanda ki ka ce sai dai kuma in su Alhaji suka sa
    kawo ta ni ba zan iya ja da su ba. Sannann ke
    kanki bana so a ce ke ki ka sa ni in ma Ummi
    rashin mutunci, amma ki bar ni da ita in har ta
    yarda ta tare a nan gidan. Bishira ta ce, "Tab, ba
    ko zata tare a nan gidan ba". Umma ta ce "A'a ki
    bari in sun matsa ta tare a nan din ta tare, gara
    suna kusa muna kallon irin zaman da za su yi.
    Can gefe ba sai su rinjaye shi ba". Bishira ta ce,
    "Umma na tsani shegiyar yarinyar nan ne, bana
    son in ganta ko cikin mafarkina, bare a zahiri".
    Sahura ta ce, "Bishira na ce ki nutsu ki bar komai
    a hannuna, in ma zan hada da Bokaye ne ba
    Malamai ba in sha Allahu sai kin dara a gidan
    nan. Ta ce, "To Umma, Sahura ta ce, Yauwa ke
    dai ki zuba ido, Abba dai yana tsaye yana
    kallonsu. Sai lokacin yayi magana, Umma dare fa
    yayi, ta ce to muga ledar hannunka, ya mika
    mata. Ta buda ta gani, "A'a kaza? To ku zuba
    min nawa". Ya mika wa Bishira, Ki dibarwa
    Umma. Ya nufi dakinsa yana jin sallamarta tana
    fadin ta wuce, ya fito ya ce "To Umma sai da
    safe, ya rufe gidan ya koma dakinsa. Da ya shigo
    gidan ne da niyyar lallashin Bishira, amma yanda
    abubuwan suka zama sai ya ji ba ma ya son
    ganin Bishiran. Zantukan Bishiran da na
    Mahaifiyarshi sun saka shi cikin tunani, lamo ya
    kwanta a kan katifa yana ta harsaso irin zaman
    da za a yi a gidan. Anya kuwa ba zai kama wa
    Ummi haya ba? Cak! Hasken wutar dakin ya
    dauke tare da tsayawar Injin. A fili ya futa, Mai
    ya kare kenan, sai da ya yi shirin bacci ya
    kwanta tare da manne filo a kirjinshi, sannan ya
    dauko wayarshi ya kira layin da ya hada cikin
    sabuwar wayar da ya ba Ummi. 62.. Gabanta ne
    ya fadi, lokacin da taga lambar Ya Abba suna
    rawa a fuskar wayar, ta haddace lambobinshi tun
    shekarun baya. A fili ta ce, kenan ma ya hada
    wayar ba yau ya soma hada ta ba, ta sake yin
    lamo a kan gado tare da janyo filo ta manna a
    kirjinta. Ta daga wayar lokacin tana daf da
    tsinkikewa, can cikin makoshinta tayi sallama. Ya
    amsa, tsigar jikinsa a tashe sakamon jin muryarta
    tana ratsa jikinshi, ya ce "Ummi, ta ce Na'am Ya
    Abba. Ya ce, "Kina son ki tare goben? Ta lumshe
    ido, ba ni da za6i Ya Abba, duk yanda ku ka ce.
    Dadi ya cika zuciyarshi. To shi kenan ki tare
    goben, zan yi parking tun Asubahi sai in sa mai
    fenti yayi kafin in tafi aiki. Ta ce, "Ba an ce in
    mutum ya yi aure ana ba shi hutu ba? Ya yi 'yar
    dariya, "To ni ba ki ga yanda auren nawwa yazo
    daga sama ba? Amma duk da haka in na nemi
    hutun za a bani, ta ce kayi aikin kama kawai ba
    sai ka nemi hutu ba.. Ya katseta, "Don ba a sona
    shi yasa ba a damu na amshi hutu ba? Ta ce,
    "Ba nufina kenan ba, naga kana matukar son
    aikinka ne". Ya yi dan murmushi "Kin dai
    wayance kawai, to yanzun haka zaki tare babu ko
    dan kunshi bare gyaran kai irin na Amare? Koda
    yake ba aure so ba ne. Cikin muryar shagwa6a ta
    ce, "Ya Abba ka daina, ya ce me zan daina? Kana
    cewa bana sona, ai kai ma ba ka sona... Ya dan
    yi shiru, yanda ta ke shagwa6ar ne ta tsuma shi.
    Ya ce, ok, to goben sai kije ki gyaranki ko? ta ce,
    "Umma ba za ta bari in fita ba, amma me yin
    fulawa za ta iya ta mini". Ya ce, "To ina ne a ke
    gyaran gashin? Ta ce, "Cikin gari ne, ya ce kin
    san gurin? Ta ce, "Eh, amma ban ta6a yi ba, ya
    ce to ki bari zan shigo gidan kafin na tafi aiki zan
    ce Umma ta bar ki, ta ce "To." Suka dan yi shiru.
    Can ya katse shirun da cewa, "Me ki ke tunani?"
    "Yaushe?" "Yanzun." Ta dan musukuta, "Ina
    tunanin yanda abubuwan za su kasance gobe.
    Yanda har za'a yi fenti, sannan a jire kuma in tare
    duk a gobe". Ya ce "Duk mai sauki ne, ni kuma
    kin san tunanin da nake yi yanzun? Ta ce, "A'a,
    ya ce gobe kamar yanzun muna tare... da sauri ta
    katse wayar, me Ya Abba ke son fada? Ta kashe
    wayar sannan ta kudundune. Ita ma yanzun ya
    jona mata wannan tunanin, a fili ta furta gobe
    kamar yanzun me ya ke faruwa? Shi kuwa sai ya
    ji haushin kansa sakamakon furucin da ya yi har
    ta yanke wayar, wani gefen kuma sai ya ga kila
    don bata sonshi ne shi yasa har ta ji haushin
    furucin nashi. Kila ma yanzun tana can tana kuka
    in ta tuna gobe tana gidansa, dare ya tsala amma
    ya kasa bacci, don haka sai ya mike yayo alwala.
    Sallah ya shiga don kara nuna godiyarsa ga Allah
    da ya bashi Ummi tare da rokon Allah ya kimsa
    mata sonshi, daga karshe ya roki hadin kan
    matansa. 34 63..Yana wanka da safe ya jiyo
    muryar mum dinsa harta zo gdn, a zuciyarshi
    yace innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yana fitowa
    tace wurinka nazo, Bashir yazo ya fada min cewa
    yau za'a kawo fitsararriyar yarinyar nan ko? Abba
    cikin damuwa yace umma nima bansani ba, tace
    munafiki kasani, bari kaji ko an kawota ko
    magana bance ta hadaku da ita ba, kai in ma
    kaje girin munafukan iyayen nan nata su ka ce
    yau zata tare kace saika shirya. Bishira tace
    umma bazan yarda ta tare ba, bai sai min komai
    ba, ya kalli Bishira to itama na sai mata wani
    abun ne? Sahura tace to ina ruwan wani da baka
    sai mata ba? Abba yace toni bani da kudi ma,
    Bishira tace to kudin jiya da babana ya baka fa?
    Umma tace fito dasu, yace umma dama fa kudin
    sadaki ne ya biya min, kuma naba alhji karami
    waliyyinta sai dai ki je gun shi ki amsa, tace don
    kasan bazan tunkareshi bane shi yasa to tana
    binka bashi, zaka chanza mata kayan daki, ka sai
    mata zannuwa sannan ka bata jari, yace umma
    banyi alkawari ba, in dai na samu kudi kuma ta
    kwantar da hankalinta to xan mata, ya nufi daki
    yabar su nan sunata zantukan su. Lkcn daya
    shiga gdn su umman shi, ummi tana linke kaya
    tana sakawa cikin jaka, yana daga bakin kofa ta
    dago ta amsa sallamar shi ta kalle shi, ya kalli
    kayan sam zuciyarshi bata mishi dadi, ya nufi
    wurin umma don yana son neman alfarma abar
    ummi zuwa dan wasu kwanaki don yana so ya
    dan gyara gidan, rashin galihun zai yi yawa, ba
    lefe kuma gida ba gyara? Yayi sallama suka
    amsa, bayan ya gaishe su, ya dukar da kai yace
    alhji dama nazo ne neman alfarma, suka ce
    alfarman me? Yace inaso ne kudan bar ummi
    zuwa nan da sati daya, sannan na gyara gdn,
    kuma nayi mata sabbin dinki, alhji yace ba kana
    da fentin ba? Kaje kasa a goga, sai ka biyo ta
    kasuwarmu ka amshi zannuwa, abba yayi shuru
    umma tace koda wani abu bayan nan? Yace a'a,
    umma tace to an daga maka zuwa gobe, yace to
    umma da alhji nagode, ya mike ya zai fita, yace
    am umma ummi tace zata je gyaran gashi, suka
    yi dariya su kace ai wannan ikon kane, yace to na
    tafi alhji sainazo kasuwar, ummi ta jera masa
    kayan karin kumallo koda ya leka dakin sai tace
    ya abba ka shigo ga break, yace ummi zanyi latti,
    tace to da yunwa zaka tafi? Yace akwai shayi a
    can, tace come on ya abba zoka karya, ya kalli
    agogo minti biyar gareni, ta dau copi ta tsiyayo
    kunu ta mika masa, ya fara kurbar kunun, ta zubo
    kosai a plate tarike a hannunta dauka kaci, ji take
    tamkar ta bashi a baki, tsohuwa ta dago labulen
    dakin, tace zura masa a baki za kiyi? Ummi tace
    kada ya kware tsohuwa, an hana yin magana in
    ana cin abinci, toshuwa tace tafi can da cusa kai
    ba kwarjini, abba ya dire kofi tareda mikewa yace
    ummi saina dawo, ki bari da dare zan kai ki
    gyaran gashi, yasa hannu a aljihu ya zaro yan
    dari binbiyu guda biyar ya bata, tayi godiya ya
    ciro dari yaba tshuwa yace yar sa ido kema kiyi
    kotso da wannan, ta rike baki tana fadin wannan
    yara da munafunci suke, ya fita yana murmushi
    ummi tace a dawo lfy, ya sake waiwayo wa ya
    kalli ummi, suka saki murmushi, 35. 64....
    Tsohuwa da ke bin su da ido ta ce, "Kai ban
    yarda da ku ba Takwara, dama can ke da me
    sunan Malam soyayya ku ke? ---- Umma da ta
    tsinci zancen bayan fitowarta daga dakin Alhaji,
    ta ce "Ya a ka yi?" Ta ce, "Suwaiba ina ga
    yarannan tuni kallonmu kawai suke. Sai wannan
    salo suke wa juna, sannan ga Takwara ciwon
    barin gida shiru, ina ga dama ciwon nan na mai
    sunan Malam ne." Umma ta saki dariya tare da
    cewa "Allah yasa haka ne. Ummi kam cikin daki
    ta kule zuciyarta zallah dadi. Misalin karfe biyu
    Umma ta dan kishingide baya, ta idar da sallah,
    tsuwar wayar da da Abba ya ba Ummi ajiya ce ta
    farkar da ita. Ta ce, Ummi me ke tsuwa a dakin
    nan? Wannan dai ba wayata ba ce. Ummi da ke
    tsakar gida ana mata zanan fulawa ta ce, Lah,
    Umma Ya Abba ne ya bani ajiya. Kila ma shi ne
    ya kirata, ta dubi wadda ta yi mata zanen fulawar
    ta ce Sabira don Allah shiga ki dauko min a kan
    gado. 2missed call ta gani, ta ce kash! Sai gashi
    ya sake kira, kafin ta daga sai da ta leka dakin
    tsohuwa ta hango ta kwance a gadonta. Dama a
    kofar dakin Tsohuwar take ta biyo inuwa ta daga
    wayar tare da sallama, ya amsa cikin dokin jin
    muryarta. Ina ki ka shiga ne? Ta amsa a can
    cikin makoshinta, ana min fulawa a tsakar gida
    wayar kuma tana daki. Ya ce, Ok ana miki zanen
    fulawar ne? Ta ce an ma ganin har ya fara
    bushewa ya saki murmushi tamkar yana gabanta.
    Ana yi miki me kyau? Ta ce, Eh yayi kyau sosai,
    ya ce Good, zan dawo kamar karfe uku saboda
    zan kwashe kaya za a yi fenti a daki, so kin ga
    ba zan samu kai ki gurin gyaran gashin da wuri
    ba. 65... Don haka sai mu bar shi zuwa dare ko?
    Ta ce, "To Ya Abba, ehm za a dafa maka wani
    abu ne? Dadi ya lullu6e shi amma saboda
    burinshi na kimanta Bishira a idonta sai ya a'ah.
    Na hutar da ke zan ci na Antynki Bishira,
    maganar ta soki ran Ummi har ta kasa magana,
    ya fahimci hakan don haka sai ya kawo zancen
    da cewa sai nazo. Ta tura baki tare da cewa
    uhm, tana kashe wayar ta shiga kunkunan cewa
    in yaso kaci abinci gidansu bana ta ba. Tsohuwa
    da ke sauraronta ta sheka dariya tare da cewa,
    ba dai ke kin ce me sunan Malam ba? Sai ma kin
    je gidanshi yarinya ban miki baki ba amma za ki
    raina kanki. Ummi ta cafke cikin jin haushi ta ce,
    wai to Tsohuwa da za ki ce na ce Ya Abba cewa
    nayi ina sonshi? Kuma da su Alhaji suka jona ni
    da shi da naki har da ke za a dinga cewa ban yi
    biyayya ba. Tsohuwa ta ce, Raba ni da gulmarki,
    kina sonshi ai ni ba yarinyar goye ba ce, kina
    waya kina kashe murya, san nan ciwoce-
    ciwancanki duk sun lafa. Sai wannnan rawar kai
    ki ke, to ki sani me sunan Malam dai ya aure ki
    ne don dole, matar cushe kuwa ba daraja take
    ba. Ummi ta ce, "To nima dai ai ba sonshi ni ke
    ba, ni dai tsohuwa don Allah ki daina samin ido.
    Ta mike, Na ma bar miki kofarki. Ta nufi kofar
    dakin Alhaji tana kunkunai. 36. 66... Sai dai duk
    da haka kalaman tsohuwa sun tsaya a ranta,
    matar cushe bata daraja, Ya Abba kan dole ya
    aureta, lallai zancen tsohuwa abin dubawa ne.
    Abba ya shigo gidan uku da doriya, tare yake da
    yara guda biyu, dayan zai mishi dan face-face,
    dayan kuma zai masa fenti. Sune suka taya shi
    kwasar kaya, bai samu Bishira a gidan ba, kila
    tana gidan Ummanshi, ko makota. Sun kama
    aikinsu shi kuma ya shiga kicin don ya dan dafa
    abinda zai ci. Bishira gidan Anty ta tafi kuka take
    wiwi wai ita fa ba za ta iya zaman gidan nan ba,
    ta ce "Aunty Farida tunda kuna shiri da Baban
    Walid ki ce masaya sawake min". Anty Farida ta
    tsura ma kanwarta ido, tausayin Bishiran ya
    cikata. Tabbas kishiya bata da dadi koda
    mahaukaciya ce bare mai hankali. Sai dai ita bata
    da ikon da zata hana ayi kishiyar koda kuwa
    mijinta ne ke son yi, don sunna ce ta mai tsira da
    Aminci. Bishira ta katse mata tunani da cewa,
    dubi fa Anty hatta Dady yanzu yafi son Baban
    Walid fiye da ni. A gabana ya dauki kudi yaba
    baban Walid, a halinni kara na kai a kar6ar min
    'yancina, kuma Momy zata yi magana ya hanata
    cikin tozartawa. Hakan da Daddy yayi ba zubar
    min da kima yayi ba, har da ita Momy? Yaushe
    Baban Walid zai sake ganin darajarta? Anty
    Farida ta sauke ajiyar zuciya, ta ce "Bishira Dady
    bai zubar miki da mutunci ba, illa kara tarairayo
    miki mutunci da yayi daga ke har Momy. Kuma ni
    ba zan ce mijinki ya sake ki ba, haka nan ba zan
    ga laifinshi ba, domin aure sunna ce ta Manzon
    Allah (S.A.W), sam ba zan yi fushi da wanda ya
    raya Sunna ba, koda mijina ne. Kiyi hakuri
    kanwata koda bani da kishiya nasan akwai zafi,
    amma kema kina da laifi, dube ki fa. Yanzu
    Bishira wa zai gan ki ya amince ke kanwata ce ta
    hudu? Zato za a yi ke yayata ce, kin saki kin yi
    ragwaf, nonuwa har ciki haihuwa biyu jal, dubi
    yanda tsabar datti yasa fuskarki da dokin wuyanki
    zuwa bayanki duk kyasbi ya miki riga. Da kin
    zauna kusa da mutum wari ki ke tashi, hakora
    sun miki yalo, kai mijinki fa ya yi kokarin ba
    kowane zai dauki hakan ba. Duk ba ki kalli laifinki
    ba sai don ya kara aure yanzun? Ina ce kwanaki
    garin shegen gantalinki ne ki ka bar danki a gida
    ya fada rijiya ya mutu? To hatta Abban Nasir ce
    min ya yi da shi ne ba zai yarda ba, saboda haka
    ki dawo hankalinki ki zubar da kazantar nan ki
    kama Ibadarki. Bishira ba kya jin kunya a ce ba
    kya sallah? Kuma a tare da haka kina da wannan
    kazantar ki ke kaurace ma shimfidar mijinki.
    Kwanan baya ya kira ni a waya ya sanar da
    nicewa kin ce min ina wari, don haka ni kuma na
    ceya tafi gurin mai tsafta mai kamshi. Shima fa
    Anty magana yake dankara min don ba kisan
    halinshi ba ne. Anty ta ce, "Bishira kina cikin
    hadari, ga kin sallah sannan ga kauracewa miji ki
    kwana Mala'iku suna tsine miki. To daidaita
    sahunki, ga mijinki dan kwallisan dan Jarida mai
    farin jini, ki kalli yanda in yana gabatar da
    shirinsa yanda 'yammata kan kira su ce suna son
    lambarsa. Amma ke kina sakaci da shi, ki dubi
    yanda wata mata ta kawo masa hari kwanaki da
    a ce ya yarda ke ba za ki san kina da kishiyar
    waje ba. Ki shiga taitayinki zan dai miki taimako
    daya in kinamince za ki natsu. 67.... Bishira ta
    ce, Anty taimakon me? Ta ce, "Zan samu Momy
    su taimaka su canza miki kayan daki, sannan
    Dady ya ba mu kujerar Makka ni da ke da Aisha.
    To sai ya ce tunda ke kin ki kwantar da
    hankalinki ki kwantar da na mijinki to ya fasa
    naki, mu harmun yi passport. Bishira ta zaro ido,
    da gaske Anty? Anty ta ce, Allah da gaske. To
    yanzun shi ne ni ke son in ce muje mu ba shi
    hakuri kila ya amince. Bishira ta ce, Tashi muje
    Anty don Allah, Anty ta ce kin tambayo zuwa can
    ne? Bishira ta ta6a baki, nifa ko nan din ban
    wani tambaya ba, wallahi gidan ne bakikkirin
    nake ganinshi. Anty ta ce, "Ki dinga addu'a, kishi
    yayi miki yawa. Sannan ki daina fita ba tare da
    izinin mijinki ba, duk in da ki ka je har ki dawo
    Mala'iku suna tsine miki. Don haka yanzun tashi
    ki tafi gidanki, ni zan samu Hajiya da Dady yau
    din nan kuma in sha Allah za amiki gyaran dakin,
    sannan tafiyar za ta kasance tare da ke. Bishira
    ta ce, Na gode Anty, amma don Allah ki barni na
    dan huta a nan gidan duhunsa nake gani, don ba
    ki ji yanda ni ke ji ba ne Anty ko da dana Walid
    ya rasu ban ji kunci irin wannan ba. Ta sake
    rushewa da sabon kuka wiwi, Anty kallonta kawai
    take ta ma rasa me zata ce. Wayarta ta ciro
    daga chaji ta shiga kiran layin Abba, lokacin ya
    kira kananan kannanshi su Kamal suna ta fito da
    kayan dakin Bishira saboda ayi fenti har an gama
    nashi dakin. Wayarshi da ya ajiye a kan windown
    dakinshi ta shiga ruri, ya duba, Anty ce. Ya daga
    tare da sallama, ta amsa ya gaida ta cikin
    girmamawa da mutuntuwa, ta amsa da fara'a
    sannan ta ce, "Abba ga Bishira nan tazo tana
    kuka, kuma ta ce min ba ka san ta fito ba". Ya
    ce, "Eh haka ne, ta ce don Allah in baka wani abu
    ina son ganinka. Ya ce To zan zo Anty, amma
    yanzu ina aiki ne kayan dakin ta muke fita da shi
    za a yi mata fenti ne, ta ce To ko da dare ne
    haka, ya ce to zan zo. * 68.... Ummi tana ta zuba
    ido ganin Abba amma shiru har a ka yi Magriba
    tayi wanka tayi sallah. Tana zaune har Isha'i tayi
    daga Masallaci shima ya nufo gidan su Ummi,
    lokacin Ummi tana bakin gado tana 'yan shafe-
    shafenta.Ta juyo Abba suna gaisawa da su
    Umma, ta shirya cikin leshi mai ruwan lemun
    tsami, da dan mayafinta fari haka takalminta. Ta
    fito tana zaune kan kujera, ta ce "Sannu da zuwa.
    Za ka ci abinci?" ya ce, "Da sauri haka ba muko
    gaisa ba?" Ta zauna ina yini? Ya ce, lafiya lau. To
    na kawo abinci? Ya ce, daga gida fa nake, ina da
    kuma mata. Ummi ta ta6a baki, oh, haka ne ashe
    kana da mata, gani nayi da matar taka ka ke
    zuwa cin abincin daga nan ta lafe a kujera tare da
    hada rai. Ya mike muje ko? itama ta mike, ya
    kalle ta da wannan mayafin za ki? Ta ce, eh, ya
    ce a'a dauko hijabi ba zan lamunci yafa wannan
    dan mayafin ba. Ta kalle shi kamar ta ce ai
    matarka tana yafa irin shi sai kuma tayi shiru ta
    nufi uwar daki don dauko hijabi. Shi kuma ya nufi
    waje, ta yi wa su Umma sallama sannan ta fito.
    Yana tsaye jikin mota ya ce, ina wayar nan? Ta
    ce, "Gata nan a hannuna ya yi dan murmushi
    yace mayyar waya dama nasan sai kin dauko har
    yanzun cikin haushin maganar shi ta dazun take
    yi. Don haka bata kula shi ba, ya shiga motar ya
    bude mata gefen kusa da direba ta zauna cikin
    fushi. Lura ya yi da hakan, don haka sai ya ce ba
    ni tamata ta ce so nake in loda mata kudi. Ya
    guntse baki don kada yayi dariya, ganin yanda
    tamiko mishi wayar cikin hanzari gata Allah yasa
    bacewa nayi a bani ba. Ta juyar da kai tana
    kallon titi, shima bai sake cewa kala ba har suka
    shiga cikin gari. Ya dube ta, wane shagon zamu?
    Ta ce, duk wanda kaje, ni sanin wani saloon nayi?
    Shagon wata mata ya kaita kusa da inda yake
    aski, sun samu shagon Musulma ce 'yar
    Maiduguri.Shamsy belloRFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 3 part 9
    ZURFIN CIKI book 3 part 9
    Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:40
    nayi? Shagon wata mata ya kaita kusa da inda
    yake aski, sun samu shagon Musulma ce 'yar
    Maiduguri. 69.... Abba ya ce mata ga Amaryata a
    gyara mata kai duk da ba wai gashi ne da ita ba
    ya yi kyau sosai ko nawa ne zan biya. Mai
    shagon tayi 'yar dariya, zan mata yanda ka keso
    ya dubi Ummi wadda ta samu kujera ta zauna
    fuska daure. Ya ce, "Kanwata zan tafi nayi aski
    nima, daga nan sai na dauki matata daga unguwa
    na kaita gida, sannan ta san in har ta bude baki
    to kuka ne zai kwace mata, don haka sai ta yi
    shiru. Ya fita yana 'yar dariya, mai shagon
    Yagana saloon ta ce, "Kai kanwata kun dace fa,
    kuma da alamayana sonki sosai.Ta kalli mai
    shagon hawayen da take makalewasuka zubo, ta
    ce "Anty ina so a nan, dubi fa abinda yake
    min.Komai sai ya ce min matarsa, matarsa, ko
    inaruwana da matarsa? Yagana ta ce, "Yana da
    matane? Sam bai yi kama da mai mata ba.Ummi
    ta ta6a baki ta ce, "Yana da mata da yakeso ni
    bana sonshi, baya sona, iyayenmu ne sukahada
    mu.Yagana ta ce, in ma ke ba kya sonshi shi kam
    yanadauke da tsantsar sonki a idanunshi n
    fuskancihakan. Ummi ta ce, "Anya kuwa? Bana
    zaton yanasona ne, in kin ce yabi iyayenmu ne
    zan fi yardadon shi din mai biyayya ne.Yagana ta
    tura mata kujera, zauna in soma miki,sai da ta
    fara gyara mata kai sannan ta ce, "In mamijinki
    ba ya sonki to kuwa ba za a yi wuyarshawo kai
    ba.Ummi tayi murmushi tare da kallon fuskarta
    tamadubin da suke fuskanta, ki ke gani Anty? Ta
    cesosai kuwa, ki tarairaye shi da kyau, kin san
    shinamiji dai dan shauki ne da son nishadi.
    (((KWARAI KUWWA!!!)))Ga kuma son tarairaya
    kamar jaririn yaro, ummi tace, "To zan yi hakan in
    har yin hakan zai sa ya soni.Yagana ta ce, "Zai
    so ki, zan so kiyi gyaran jiki dafata, Umi ta ce,
    kamar ya ya? Yagana ta ce, kayanmata zuwa
    gyaran fata, wanda za ki sha don 'karinni'ima.
    Ummi tayi shiru, don bata son irin
    wannanzantukan.Ta ce, "Kin yi shiru, Ummi ta ce
    Ummana ta ce bata son in sha komai, tunda ni
    budurwa ce, in je wamijina da ainihin halittata.In
    yaso daga baya sanin saboda 'yan garinmu sunzo
    da shi daga Zamfara. Yagana ta ce, Hakan
    mayana da kyau, domin Amare da yawa suna
    shanwahala sosai kasancewar ba su saba
    ba.Sannan mazajen ba su bambance ainihin
    yandamatan suke. Ummi cikin gundira ta ce, Gara
    ma nagyara fatar.Yagana ta ce, "Wancan ma za
    ki neme shi, ko nangaba Ummi ta ta6a baki, ni
    dai fada min na gayarnfatar.Ta ce, "Ina sai dawa
    in kina so zan baki kije gida kihada kiyi zan hada
    ma angon lissafi da shi Ummita ce, ba ni sai da
    suka gama a ka gyara matagashi fes, sannan ta
    dauko kayan ta shiga lissafamata kamar haka:-1.
    Man Zaitun2. Lalle3. Kurkur4. Madara ta ruwaZa
    ki hada su guri daya ki kwa6a, sannan ki
    shafejikinki da su kafin shiga wanka, in ya bushe
    idan zaki shiga wankan sai ki murje shi tas,
    dukwadannan 'yan kurajen na fuskarki za su
    mutu,jikinki ya yi laushi da sheki.Ga kuma wani.1.
    Sabulun Ghana2. Dettol3. Zogale4. Farar
    AlbasaZa ki hada Sabulun Ghanada da Dettol da
    garinzogale, da farar albasa, ki hada su ki kir6a
    kimurmule shima a jikin za ki ringa shafawa.Da
    fuska kafin ki shiga wanka, zan bar ki da biyunin
    sun amshe ki ma sun ishe ki. Yanzun ko inwanke
    miki kafa? 39. 70.... Ummita ce, "Ina tsoron kada
    yazo kuma kudin shi ba su kai ba, Yagana tayi
    'yar dariya, kina tausayinsa ne? Ki daina tausayin
    mijinki shi ne zai amfana da gyaran da duk za ki
    yi. Ummi ta ce, "To wanke mini".Ta hada kayan
    wankin kafa ta ce yarana ke yi amma zan miki da
    kaina. Sai kuma taga zanen fulawa. Ta ce, "Au,
    an riga an yi zanen fulawa ma ba dama ayi,
    Ummi ta ce, Ohi ni na manta ma, to ki fada min
    yanda zan dinga gyara kafar, ta ce To bari in ba
    ki mai sauki ma. 1. Man kwaka 2. Man shanu 3.
    Man Zaitun Ki samu man kwakwa da man shanu
    da man zaitun ki hada man kwakwa da man
    shanu guri daya, ki shafa da dare da safe. Ki dan
    gasa kafar sannan ki wanke ki shafa man zaitun,
    za ki ga yanda kafafunki za su yi tamkar ta jariri.
    Ko ki yi na ruwan ko kumba, lalle ki hada su guri
    daya ki shafa a kafafunki da dare. Da safe ki
    wanke ki shafa man ridi, wadan nan kurum in kin
    rike su za ki ba wani labari, Ummi tace zan
    kiyaye in sha Allah. Shi kuma Abba yana fitowa
    daga shagon aski kai tsaye gidan Anty ya nufa,
    ya samu Bishira Anty ta matsa mata tayi wanka
    ta bata kaya ta saka. Ta kira mai kitso tazo tayi
    mata ta sata ta shafa turaruka. Tunda Abba ya
    shigo yake kallon Bishira, sun gaisa da Anty,
    sannan ta ce dama dai na ce kazo ne don Bishira
    ta baka hakuri. Sannan in maka tuni da yin adalci
    a tsakanin matanka, kuma na yi wa Bishira fada
    sosai. Ta dubi Bishira, ki ba shi hakuri, Bishira ta
    hada rai tare da turo baki, ta kalle shi cike da
    tsananin jin haushin shi. Kayi hakuri ya ce ba
    komai dama ni ban yi fushi dake ba, a zuciyarta
    ta ce, ba ka isa in baka hakuriba, albarkacin ina
    son zuwa Makka ne da kuma canjin kayan dakin.
    Ya yi wa Anty godiya ta ce ma Bishira gobe da
    wuri kiyi parking din duk kayan ki a waje da mun
    zo sai mu shirya miki. Bishira ta ce, Allah dai
    yasa su yarda, Anty ta ce,"Za mu su yarda in
    Allah ya yarda. Ta dauko wasu kayan sawa da
    sabbin kuloli ta ce ma Bishiran je kisa a motarku.
    Abba ya ce, "Kawo in kai, Anty na gode sai
    anjima, ta ce To Abba ayi ta hakuri". Ya ce, Ba
    komai, Insha Allahu. Suka biyo shi a baya tana
    kara jawa Bishira kunne kan cewa in har ta
    kuskura ta ji wata magana ta 6ullo ta rashin
    mutunci sai ta fasa tsaya mata a kan maganar
    aikin Hajji ko Dady ya amince sai tasa ya janye.
    71.... Sun shigo mata Muhibba tana baya tana
    'yanwutsil-wutsil dinta tamkar kurame, haka suke
    tafiyar. Ta zaci su nufi gida sai taga sun nufi
    cikin gari. Bata tambaye shi ina za su ba, har
    suka isa inda yayi parking ya dubeta, Madam ina
    zuwa, hum kawai ta ce. Ya bude baya ya dauko
    Muhibba ya sa6a a kafada ya nufi shagon saloon
    din. Daidai lokacin sun kammala komai, Ummi ta
    zari hijabinta da niyyar rufe kanta, Yagana ta ce
    a'a kanwata bari ya gani don ya biya ni 'yan
    kudina. Abba bai zaci Ummi tana da gashi ba,
    domin dai acikin Hausawa 'yan Arewa za a iya
    saka Ummi acikin ma su gashi. Yayi laya-laya a
    dokin wuyanta baki sidik. Yayi murmushi, lallai
    kin gyara da kyau. Nawa ne kudinki? Ta fada ya
    ciro ya bata, sannan Ummi tazari hijabinta.
    Mamaki take, Gida ya koma ya dauko Muhibba?
    Yamiko mata ita, Ga 'yarki. Ta amsheta. Yagana
    tace, yarinyar tana kama da ku. Abba ya ce, "Ai
    'yarmu ce, suka yi mata sallama suka fito. Ummi
    da Bishira a tare gabansu ya fadi lokacin da suka
    ga juna. Bishira ta kauda kai yayin da Ummi taja
    baya daga mazaunin kusa da direban da ta nufa,
    ya bude mata baya ta zauna tana rike da
    yarinyar. Ya tada motar suka dauki hanyar tafiya
    kowanne zuciyarshi da abinda take karantowa.
    Ummi tunaninta Abba ya je ya zo da matarshi ne
    don yanuna mata shi fa matarshi yake so. Ita ko
    Bishira nata ganin wulakanci ne na karshe da ya
    dauko ta yazo da ita gurin wannan karamar
    yarinyar. Shi ko Abba addu'a ce a zuciyarshi
    Allah ya hada masa kan matansa, sai kuma ya
    soma tunanin ina zai soma zuwa? Nashi ganin in
    ya kai Bishira gida ya sauke ya tafi kai Ummi bai
    mata adalci ba. Amma ya kula Ummi tana fushi
    kuma yaso ya lallasheta, yana cikin wannan
    tunanin ya tuna dawayar nan. Ya kalli wayar a
    gefanshi. Dan murmushi yayi da ya tuna lokacin
    da ta dangwarar masa da wayar don ya ce ta
    matarsa ce. Yanayin yanda Ummin ke nuna
    kishinta yana birge shi, koda bata sonshi tana
    kishinshi sannan bata masa raini ko rashin
    kunya. Kofar wani gidan saida gasassun kaji da
    ire-iren kayan kwalam ya tsaya. Ya kalli Bishira
    Madam mu shiga ko? Ta ce, "A'a ni fa ba zan fita
    ba, ya ce To bari in dawo, ya nufi ciki. 72.. Ta
    waiwayo ta dubi Ummi, ta ce "Ba ni 'yata
    fitsararriya. Ummi ta mika mata tare da cewa
    nima ai ba cewa nayi a bani ba, ta ce "Kar dai ki
    min rashin kunyaki bar ganin an jona ki da mijina
    ki zata za ki hada sahu da ni. Ummi ta ce, "Sai
    dai kada a kuma in dai batun hada sahu ne, kuma
    ban damu don mijinki ba bai sona ba, tunda ni ina
    sonshi. Bishira cikin daga murya ta ce, oho?
    Dama sonshiki ke yi? Yanzun na gane da nufi aka
    yi. To ki sani kin sai ma kanki masifa da bala'i.
    Ummita ce, "Kin ga bala'inki can, daga nan
    batakara magana ba ta bar Bishira na ta masifa.
    Tundaki ka za6i ki auri mijina zan shayar da ke
    ruwan dana sani. Sai kin gwammace zama a
    kurkuku fiye da gidan mijina, daidai lokacin Abba
    ya dawo da ledoji guda biyu. Bishira bata yi shiru
    ba sai zagin Ummi take yi,"'Yar iska, 'yar daba...
    tsawa Abba ya daka ma Bishira, tare da cewa ba
    ki ji kunya ba da ki ke zaginta amma bata kula ki
    ba? "Ta ce, "To ka ji abin da ta ce min ne? Tsaki
    yaja tare da daukar wayar da ta aje yasa a ledar
    Ummi, sannan ya tada motar. Kofar gidan su
    Umma ya tsaya, Ummi wadda dama ta kosa tazo
    gida, ta bude motar ta fada gida cike da takaici.
    Ya kashe motar sannan ya dauki ledarta ya kalli
    Bishira, Ina zuwa. Kala bata ce ba. Illa baki da ta
    cije, kirjinta na yin wata irin suya. Ban da tana
    tsoron Anty kada ta fasa zuwa gurin Dadynsu da
    tuni ta shago Ummi ta nadi 'yan kayanta. Dakin
    Umma ta shige, Ummar tana shirin fitowa Ummi
    na shiga, ta ce kun dawo? Ummin ta hadiye 6acin
    ranta."Eh, mun dawo Abba a ya shiga gaida
    Umma sannan ya mika ma Ummi ledar, gashi kin
    manta Ummi ta amsa tare da cewa, an gode.
    Umma ta ce, "Me ku ka siyo in ce dai ka sai ma
    Bishira? Ya ce, "Eh na sai mata, kaza ce fa
    Umma ba wani abu ba". Ta ce, "To shi ke nan
    maza ka koma gurin su, yace "To. Tana fita ya
    kalli Ummi akwai waya a cikin zan kira ki, kuma
    bana bukatar ki kashe min waya. Ummi ta ciro
    wayar da sauri, ta dibe shi ba wayar matarka ba
    ce? Ya ce, "Eh tata ce, ta mika mishi cike da
    kunan rai, ga abinku ka kira ni da layin Umma. Ya
    ce, "Ke ce za ki cigaba da rike ma mata
    tawayarta, ba tare da ya jira jin me za ta ce ba
    yana murmushi, Ummi ta kasa gane cewa ita ce
    matarta shi. Ko kallon kazar bata yi ba illa dai
    tayi duk wasu abubuwan da ta saba yi kafin ta
    kwanta, sannan ta kunna wayar tana tsammanin
    kira. 73..... Shi ko Abba koda yazo Bishira tana
    ta mitar don tsohon wulakanci an zo da ita an
    shanya ta, bai ce mata kala ba illa dai motar da
    ya tada suka nufi gida. Gidan duk kaya saboda
    bai maida ba da a ka gama fentin, ya dauki
    tsintsiya ya share dakin, sannan ya shimfida
    katifa ya fito inda take zaune bakin Rijiya.
    Muhibba tayi bacci tana rungume a jikinta, ya ce
    kawo ta, ta mike a fusace ta nufi dakin ba tare
    data bashi 'yar ba. Ya bi bayanta, so kurum yake
    ya lallasheta ba wai don tsoronta ba sai don
    tausayinta, yasan mata kan kishi za su iya yin
    'yar karamar hauka. Wasu ma sai sun yi babbar
    kuma bai dace ana nuna kishinsa ba, shi kuma
    yana nuna ko 'in kula a gare ta, gefen katifar ya
    zauna ya lalubo hannunta ya rike cikin
    nashi."Bishira!" ya ambaci sunanta cikin sanyin
    murya, bata amsa ba kuma bata dube shi ba, ya
    ci gabada cewa, "Bishira ban ga abin damuwa ba.
    Ko damata uku a ka daura min aure da su bare
    daya, inkin yi la'akari da irin son da nake miki ke
    kin san Bishira ba kiyayya ta hada mu ba. Kina
    manta wannan ne? Ta dago ta dube shi ta dan
    soma saukowa, yayi murmushi har yau ban daina
    sonki ba, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta turo
    baki sai kace 'yar yarinya. To ai na sha jin a ana
    cewa so daya ne tak, ya cehaka ne, ta ce "To
    tsakanin ni da Ummi wa ke keyi wa? Da sauri ya
    ce ke, ta ce Allah?Ya sake tausasa murya, haba
    Bishira ya ki ke wannan zancen kema kin sani,
    kuma don Allah na roki ki in muna tare ki daina
    min zancen Ummi, ke kadai ce za6i na. Bishira
    taji dadin wannan kalamai, don haka sukaci
    namansu suka kwanta, ya bukace ta a nan masai
    da ta ce kaje gurin Ummin mana. Ya ce, "Na ce
    in muna tare bana son kina min zancenta. Sai dai
    in kina son ci gaba da horon daki ke min ne.
    Haba Bishira, ko tausayina bakya yi?An fi wata
    uku kina haramta min halas dina. Kullum sai dai
    ina azumi sai ka ce gwauro? Yajawota jikinshi, ya
    rungume da kyar dai ya samu yadan rage
    matsala, sai dai ita ma ya lura tayi missing
    dinsa. Suna kwance har kusan sha daya saura
    tuni ita tayi bacci, shi kam daman so yake tayi
    bacci yakira Ummi. Ya mike yaje yayo wanka
    sannan ya nufi dakinshi. Yaja katifarshi ya kai
    dakin, sannan ya kwanta akai, ya kira Ummi
    lokacin bacci ya soma figarta. Ringing din ne ya
    farkar da ita, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta
    daga, kafin ta amsa sallamarshi sai da tayi wata
    doguwar hamma.Ya ce, "Ke baccin ki ma ki ke
    alhalin na ce zan kira ko? Ta ce, "Amma ka san
    bacci ba ya jira in ya zo,ni kuma ba zan iya yiwa
    bacci gardama ba". Ya ceto sarkin iya zance, yayi
    nufin zolayar ta. Yanzun dai na soma tunanin kin
    soma sona, gabanta ya fafi, sam bata son ya
    gano hakan yanzu. Tafi son sai lokacin da shima
    ya soma sonta. Ya katse mata tunani, hasashe
    na haka ne? Ta ce, ko kusa, mene hujjarka da
    fadin haka? Ya gyara kwanciya. Na farko naga
    ana ta kishina, sannan tun da a kadaura aure da
    ni sai ciwo ya kame kansa, kuma nalura kina ta
    zumdin tarewa a gidana.Ya saki 'yar dariya,
    yasan ya cika mata ciki da takaici, shiru tayi
    nazari take wacce amsa zata bashi, ko dai wayar
    zata kashe? Tamkar ya shiga zuciyarta, sai ya
    ce.... 41 Tamkar ya shiga zuciyarta sai ya ce,
    "Koda wasakada a kashe waya. Ranta ya sake
    6aci, ta ce Ya Abba ka tafka kuskure da kayi
    zaton ina sonka,sam ni bana wani kishinka. In
    don ka ce wayar matarka ce na ce ka rike abinka,
    sanin kanka ne ba ma shiri da matarka, kuma duk
    abinda ka ce nata ne dole na guje shidon ba zan
    dauki wulakanci ba. Batun ciwo kuma daka ce
    tunda aka daura mana aure ka neme shi ka rasa
    dama bani na dora makaina ba, kaima ina naka
    hawan jinin ya tafi? Sannann kuma wane zumudi
    na nuna na tarewa a gidanka, Ya Abba ka sani
    yanda a ka tilasta maka aurena, to ni ma fa dole
    tasa na hakura. Amma ka rike a ranka bana wani
    sonka bani kamarina ina sonka, kalaman nata na
    karshe sun burgeshi har sun sa shi yin da ya
    sanin tsokale zancen. Sai kuma ya canza salo da
    cewa, haka dai ki ka ce amma ina da ja mu dai
    bar zancen, shin dazun kafin ki soma wannan
    tunanin me ki ke yi? Ta danyi shiru tana
    tambayar kanta. Dama mutumin nan haka ya ke?
    Oh yanzun dabara zai min sai ya gano ko ina
    sonshi dole, to kuwa bazai ji ba, ya katse ta da
    cewa ban san ki da karya ba. Ta ce, ina tunanin
    irin ukubar da zan sha a gidanka ne ta
    wulakancin da zaka min, ya yi shiru zuciyarshi
    tana cewa yarinyar nan ba ta san irinson da ka ke
    mata ba ai ta ma dauke ka mugu kenan. A fili sai
    ya ce, "Kuma fa kin yi tunani, Allah yabaki ikon
    daukar ukubar da zaki sha tare kuma dajure
    wulakancin da na tanadar miki goben Ummi. "Ya
    fadi, wai dama da gaske wulakancin zai mata.
    Gyara kwanciya kawai tayi bata kara cewa komai
    ba, kuma bata da nufin cewa wani abu, yasa taji
    haushi sosai, don haka sai ya tausasa muryarshi.
    "Ummi kina ji na?" Uhm" Kurum ta ce, don ya
    gane tana jin shi. Alkawari ta dauka ba zata sake
    cewakala ba, tunda ya hanata kashe wayar. "Ba
    ni da nufin miki..." Sai layin ya yanke daga
    gefanshi, ta ce, "Gara ma haka". Tana kokarin
    kashe wayar gaba daya kiranshi ya sake shigowa.
    Tsaki taja kafin ta daga, kuma a ciki ta amsa
    sallamarshi, sannan cikin murya mai kamar zata
    rushe da kuka ta ce "Ya Abba ni fa bacci nake
    son in yi". Ya ce, "Sam ba wani bacci da za ki iya
    yoa sai tunani". Ta ce "To na ji, ina son yin
    tunanin please".Ya ce, "Tunanin me za ki yi".
    Cikin gundira ta ce,"Dole in yi tunanin yanda zan
    kare kaina daga wulakancinka, don bana
    tsammanin zan dauka" .Ya ce, "Wasa nake miki
    fa." Ta ce, "Uhum, ban amince da cewa wasa ka
    ke min ba, don na tabbata mu ba abokan wasa
    ba ne".Ya ce, "To shi ke nan bari in bar ki kiyi
    tunanin, amma tunanin yanda za ki faranta min
    za ki yi". Muryar Bishira ce ta katse shi. "Oho! Ai
    tun da na farka ban ganka ba na san ana nan
    ana cin amanata". Ya kashe wayar da sauri, duk
    da dai Ummi ta riga ta jiyo muryar Bishiran. Sai
    dai bata fahimci me Bishirar take cewa ba,
    ringingine tayi tare da dora filo a kirjinta, tunani
    take yi wane irin zama za su yi? Koda bata da
    amsa ta kudurce har abada ba za ta dauki
    wulakanci ba, a shi ko a matar shi. Sai dai
    alkawari ta dauka ba za ta musu raini ba,
    matsawar ba su suka 6ullo da hakan ba. *
    ************************************** Shi ko
    Abba rigima suka dinga yi da Bishira cikin tsohon
    daren wai ya cuce ta ya kwanta da ita yazo yana
    hira da wata banza. Kila ma ya saba kwanciya da
    Ummin ne yau bai samu dama ba, Abba ya ce kin
    so kanki in ki ka yimin wannan zaton, don ban
    ta6a nemanki ba, kafinki shigo gidana, ko na
    ta6a?"Ta ce, "Don ka san dai ni ba fuska". Da ya
    gaji da iya korata ya rufe kofar ya koma can
    dakin. 40. 74... Washegarin ranar, ga mamakin
    Ummi tun misalin karfe goma jama'asuka cika
    gidansu, a ka dora abinci. Can kuma saiga yaran
    shagon Abba da dinkunan zannuwan daAlhaji
    Babba ya sai mata.Ranar Abba bai shigo gidan
    ba a waya ya kiraUmma suka yi magana, zuwa
    karfe uku angama yiwa Ummi jeren dakin da yake
    yana da girma yacinye komai tsaf.Fitar 'yan jere
    babu jimawa sai ga Anty Farida dakannasu motar
    tana da kaya tana biye da su, gadoda kujeru a ka
    canzo mata.Suka jera mata sannan suka lodawa
    motar na dasuka dauki hanya suka koma, Abba
    kam yana gurinaiki amma zuciyarshi tana
    gida.Fatanshi Allah yasa yana zuwa ya tarar an
    kaimishi Umminshi, kawayen Bishira da
    makotansu'yan jam'iyyarta duk sun shigo gidan
    sun hadu saizugata suke yi tare da nuna mata
    koda wasa kadata sakar ma Ummi fuska, kuma in
    ta mata takamata ta duki 'yan kayanta.Suna
    gidan a ka kawo Ummi, 'yan kawo Amaeyakam
    suna jiyo habaici da zagin da su Bishira ke yi,don
    haka suka ce kada a kai musu yarinyar.Inna
    Saratu da Inna Harira suka ce ai kuwa sai
    ankaita.Ba ko kunya Bishira ta zabga musu
    harara lokacinda suka fada mata cewa ga
    kanwarta sun kawomata, don Allah su zauna
    lafiya tare da Aminci.In yarinyar tayi ba daidai ba
    ta sata a hanya... takatse su cikin tsawa da
    mikewa tsaye. "Don Allahku fice min daga daki
    amanar kishiya? Har wai muzauna da aminci ku
    ke cewa?Tayi 'yar dariyar yake "Kun yi kuskure,
    ai batacanza daga sunan ta na kishiya ba, kuma
    kowa yasan kishiya abokiyar gaba ce."Inna
    Saratu ta ce, "Baiwar Allah jahilan mata sunesuke
    yin irin wannan tunanin, amma ga masu ilimisuna
    koyi da gidan mai tsira da Aminci
    (S.A.W)ne".Bishira ta ce, "To kawai dai ki ce min
    jahila ki huta,bari ku ji ba za n ba ku a 6oye ba,
    zama ne za muyi shi na rashin mutunci, na kowa
    ya iya allonshi. Don ina kishin mijina, kuma zan
    nuna". Tirkashi! Lallai akwai daru kenan. To
    masu karatu ku biyo ni cikin littafi na 4, kumana
    karshe domin jin yadda za ta kasance atsakanin
    Bishira da Ummi da kuma Oga kwata-kwata wato
    @BABA MONO HAXOR


    No comments:

    Post a Comment


Pages