• ZURFIN CIKI KASHI NA 1 ONE BY BABA MONO
    ZURFIN CIKI KASHI NA 1 ONE BY BABA MONO
  • Download Now ZURFIN CIKI book 1 part 1
    Ummi tana tafe tana yan wakokinta, tareda gudu
    hade da tsalle. cinikin ummi ne gudu, sam bata
    tafiya a hankali.daga can gefe ta hango wata
    yarinya wadda bazata wuce sa'arta ba.
    tace,"yauwa,ga firdausin data tsokane ni" ta nufi
    wurinta ,tasha gabanta ta rike kugu. "fiddausi wa
    kike tsokana? fiddausi tace "ban tsokane ki ba
    fa".cikin tsoro tayi maganar .ummi ta shako mata
    wuya. ina jin lokacin da kika ce ummi tsiga.ban
    ce ba inji fiddausi .ummi ta hankada ta tare da
    cewa "Allah yaso ki." nikan garin da fiddausin tayi
    ya tarwatse a kasa tace "kin gani ko? wallahi sai
    kin biyani"ta soma kuka,ummi ta sheka da
    gudu,sai gida. tana ajiye man gyadan data siyo ta
    nufi ba daki don fitsari ya matse ta .umma dake
    zaune tana fadin. "da mutum!da mutum!!" saida
    ummi ta bude . Ganin yaya Abba tayi,da gudu ta
    juyo ta fada dakin umma,jiki na bari bayan tayi
    bol da dakakken yajin da umma ta daka zata
    soya mai don cin abincin rana. sai kuma ta tuna
    cewa bata tsira ba,don Abba tsaf zai binciko ta.ta
    fito da gudu ta nufi dakin tsohuwa. tsohuwar tana
    sallar azahar.ummi ta tsallake ta ta kutsa kasan
    gado.nan ma tayi ciki da furar da tsohuwar keson
    sha da zarar ta idar da sallah. Alhaji babba tasa
    ya aiko mata da furar daga kasuwa.don tasha da
    rana. Abba ya fito wanka ranshi a bace.dakin
    umma ya nufa yana fadin "ummi ke ummi zonan"
    Ya samu Umma tana tattara yajin da Ummi ta
    zubar, tana fada. Ya ce, "Umma ban san irin
    dukan da zan wa Ummi ba yau. Ta ce,"Abba ka
    mata dukan mutuwa, na gaji da halin Ummi.
    Yarinya sai ka ce 'yar fata? Ka dubata ta tafi
    dakin Tsohuwa, don ta san zata hana a dake ta."
    Ya ce,"Allah sai dai Tsohuwa ta yi ta fadanta,
    amma ba zan barta ba. Ya juya zai tafi, suka ji
    muryar Tsohuwa tana fadin. Ba zan yi fada ba, ka
    kashe ta ka ji mai sunan Malam, ba na son ka
    barta da rai. Ta dubi Umma" ke kuma Suwaiba
    dama kin san ba za ki daraja sunana ba ki ka sa
    a ka sa miki don kiji dadin ci min fuska?" Umma
    ta ce," Ba haka ba ne Tsohuwa, Ummi ba ta yo
    halinki ba. Ita fa rashin hankali ne da ita. Yayanta
    fa ke wanka ta zo ta leka shi, nan kuma tazo ta
    zubar min da barkono. Abba ya ce, "Umma don
    Allah kiyi shiru ki kyale Tsohuwar nan, ai ita ta
    6ata Ummin, duk abn da yarinyar nan tayi sai ta
    hana a yi mata fada. Uhm duk fadanki yau sai na
    dake ta, ba sunan ki ba in ma kece,"Tsohuwa
    tasa kuka gami da salati. "Yanzu mai sunan
    Malam ni ka ke fadawa haka?" ya ce, "An fada
    miki." Umma ta ce, "kai Abba zan sa6a maka
    jeka." Ta juyo wurin Tsohuwa, Don Allah kiyi
    hakuri............... Maman Fiddausi ce tayi sallama
    tare da Fiddausin suka shigo. Ran Maman
    Fiddausin a 6ace, ta tsaya rike da gari a
    hannunta ta dubi Umma. Ta ce, Umman Abba
    dubi abn da Umminki tayi min don Allah, yarinyar
    nan tayo nika da kyar," tun safe sai yanzu na
    samu, amma ta zubar min." Abba ya ce, Kinga
    halinta ko?" Tsohuwa ta ce, "Wannan ba matar
    Bala ba ce?" Maman Fiddausi ta ce, "Ni ce." Ta
    ce," To kije kije ki nemi wanda ya zubar da
    garinki, Ummi ko fita ba tayi ba. Umma ta ce, "
    Ta fita Tsohuwa, na aike ta siyan mai." Tsohuwa
    ta ce," Tsokanarta a ka yi to. Umma ta amshe
    abin garin ta zuba musu, sannan ta ce, "Don
    Allah Tine kiyi hkr." Abba ya nufi daki. Sai da ya
    shirya tsaf, sannan ya dauki belt ya nufi cikin
    gida, dakin Tsohuwa ya shiga kai-tsaye kasan
    gado ya nufa. Ya jawo ta, ta soma kurma ihu.
    Daya ya lafta mata amma ta dane shi tare da
    cukwikuye belt din tana ihu. Tsohuwa ta iso tana
    dukanshi a baya, fadi take "Za ka kasheta ne?
    Jama"a kuyo dauki. Haushin hakan yasa shi
    damko kanta ya shiga zuba mata kola, ya
    sirmiyota ya shiga lafta da takalminshi, tunda ta
    hana belt din. Sai da ya mata tas, sannan ya fita
    ya bar su, Tsohuwa na kuka Ummi na kuka. , Sai
    da komai ya natsa ta leka ta jawo furarta don
    tasha, sai ta ganta a zube. Ta ce, A" a ke ki ka
    zubar min da fura?" Ummi ta ce, To ba shi ne
    janyo ni ba Yaa Abban. Tsohuwa ta ce, "Ai ko sai
    ya siyo min furata. Ta mike ta wuce Umma tana
    rabon abinci, ta nufi soro in da dakin Abba yake
    (Zaure) Ya fito yana rufe kofa, ta ce "Au za ka
    fita ba? To ka sawo min furata da ka zubar. Ko
    kallonta bai yi ba ya rufe kofarshi ya wuce. Ta ce
    mishi "Aikin bana, in ba siyo min ba ubanka ai ya
    dawo ko min dare ya sito min. Abba ya ce, Ku ku
    ka sani. Ra ce, kaima ka sani, dan jakar uba. Ta
    dawo ciki tana mitar ya cika bakin rai. Umma ta
    ce, "Ina Abban? Tsohuwa ta ce, "Ya tafi, in bai
    sai min furata ba ranshi zai 6aci yau a gidannan.
    Umma ta ce "Ni bai ma ci abinci ba ya fita, ke
    Ummi zo ki kira min shi, yunwa fa yake ji.
    Tsohuwa ta ce, "Ba za ta kira shi ba, ya dake ta
    sannan ta kira shi? Tunda bai barta taci da dadin
    rai ba, shi ma ba ya ci ba.,, Umma tayi shiry,sai
    haushin Ummi da take ji kamar ta shake ta ta
    mutu. Ummi tayi wanka ta zura kayan Mkrnt,
    tana saka sandal Umma ta ce, "Ina Ummi? Zo
    nan." Ummi ta tafi tana cewa a ranta. "ALLAH
    YASA DAKIN YAYA ABBA ZA TA AIKE NI, SAI NA
    RAMA DUKAN DA YA YI MIN JIYA, DON YANZUN
    DUK ME YA MIN SAI NA RAMA.........." Umma ta
    katse mata tunani da cewa,"dauki shayin Abba ki
    kai masa kada yayi latti,kai shayin ki dawo ki
    dauki dankalin,yau shi kadai ma nayiwa dankalin."
    Tace,"nifa?"umma tace "ke kina cin dumame
    Abba ko ba ya ci,dan haka dan wanda ya rage
    shi nayi wa." Ummi ta figi kayan tea din ta nufi
    dakin Abba tana tura baki.tare da sallama bata
    jira amsa ba,ta daga labule ta fada. Dabi'ar da
    yake mata fada akai kullum,ya gama saka
    singiletinshi kenan yana kokarin saka riga. Yace,
    "wai ke wace irin majanuniya ce?ban ce miki in
    kinyi sallama sallama sai na amsa za ki shigo
    ba? sai kawai ta saki tiren,ruwan zafin ya zube
    masa a kafa,dankalin ya watse kan rigar da zai
    saka. tayo waje da gudu,sai dakin tsohuwa.ya
    fito da sauri yana cewa,"umma ta kona ni! ta
    kona ni!!" da sauri umma ta fito daga dakin Alhaji
    babba,shima Alhajin na biye da ita yana fadin
    "wacece ta kona ka?" Yace "ummi ce! ummi
    ce!!."nan take Alhaji babba ya rike kafar yana tofa
    mishi addu'a. Umma ta debo kullun kamu ta zuba
    mishi,amma duk da haka sai da yan yatsun
    kafarsa suka kumbura. tsohuwa ta fito daga daki
    tana fadin,"kai ummi bata ji? wai ni meyasa aka
    sa mata sunana?" Abba ya kalli tsohuwa cikin
    takaici yace,"duk ba ke kike daure mata gindi ba?"
    Umma ta shiga dakin tsohuwa ta janye kayan da
    tsohuwa ta jera don kada aga ummi,ta janyota
    tun daga dakin take kwallo da ummi har waje.
    Alhaji ma yau har dashi aka zane ummi,tsohuwa
    dai sai yan mitoci take yi,wai yanxu haka ma
    bata sani bane. Abba dai ranar dai bai je
    makaranta ba,haka nan da yamma sai da ya saka
    ummi a dakinshi ya bata gwale-gwale sannan ya
    zane ta. misalin hudu da rabi na yamma,Ahmad
    abokin Abba yayi sallama a kofar gidan,Abba ya
    amsa ya fito. Suna zaune kan dakalin kofar gidan
    suna hira,sai ga ummi ta yanko da gudu tana
    waiwayen baya. Ya ce,"zo nan."tazo yace,"kinyo
    tsokanar fada ko?" tace,"a'a.yace in har tsokana
    ki kayo zaki sani shegiya mummuna kazama. Ta
    murguda baki,yasa takalmi ya jefeta,ta shige gida
    sai ko ga wani yaro jiki duk kwata yayyanshi na
    biye dashi. ya tambayesu,suka ce "ummi ce ta
    jefa shi kwata"ya taso yaron har cikin gida ya
    kamota dakin tsohuwa ya tsareta ta wanke ma
    yaron jiki,ta kuma wanke kayan. sannan ya
    zuzzuba mata kola a kai.tsohuwa tana ta yiwa
    yaran fada,wai ita ma su daina tsokanarta Umma
    ko lekowa bata yi ba,ya fito ya samu Ahmad yana
    cewa "kayi hakuri na barka kai kadai." Ahmad
    yace,"ba komai" sai Abba ya zauna sannan
    Ahmad ya dube shi. Abba wannan kanwar taka
    kuwa bata da Aljanu? Abba yace,"ba kowa
    akanta,sai iskanci." Ahmad yace."a'a,kai dai ku
    kaita ayi mata rukiyya." Abba yayi dariya,sannan
    yace kasan Allah ba kowa akan ummi,saboda
    Alhaji karami ya taba yin wannan tunanin. ya
    dauke ta yakai ta rukiya bata da komai."Ahmad
    yace tabdi!,gaskiya in ta isa aure duk wanda ya
    aureta akwai aiki babba a tare dashi. Abba ya
    ce,"wane mahaukaci ne ma zaya dibar ma kansa
    ummi?"Ahmad ya ce,"sai ai muku hadin ggida..."
    ya kaima Ahmad naushi a gefen ciki,Ahmad ya
    kauce yana masa dariya. Abba ya ce,"ka cuce
    ni,ace in auri ummi ai sai na hada kayana na bar
    garin nan. nan. Ahmad ya s heke da dariya har
    da rike ciki.sannan ya ce,"don me? Abba ya
    ce,"to wannan yarinyar ba sai ta hada maka
    gobara gida ba?gata kazama ga muni." Ahmad ya
    ce,"kama dai kuke yi." Abba ya bata rai,"Ahmad
    bana so.in har da gaske ina kamada ummi ba sai
    na koma ciki an sake haifana ba. Don Allah ni
    tashi ma ka tafi,don wallahi da don kai bane kake
    fada min haka da sai munyi rigima,na tsani
    ummi,bana sonta sam! Zaune suke a kofar gidan
    Alhaji babba kan katuwar tabarma,sun jere abinci
    suna ci. kullum Alhaji babba da Alhaji karami nan
    suke zama tamkar tagwaye,suna matukar kama.
    mafi yawancin lokuta ma kaya iri daya suke
    sakawa,domin Alhaji babba duk kayan daya saya
    tare yake sai musu. haka nan hula ko
    takalmi,haka nan matansu baya
    bambantawa.shima Alhaji karami duk da bai kai
    samun babba ba yana koyi dashi. Alhaji babba ya
    kalli karami yace,"Aminu ya zancen makarantar
    bashir?" Alhaji karami ya dubi wansa ya ce,"Alhaji
    bashi fa ya fadi jarabawa,jiya na tsare shi da
    maganar sakamakon jarabawarshi yace bai duba
    ba,saida yaji nace zan hada shi da Abba suje
    sannan yace min yaje wai duk ya fadi. Alhaji
    babba yace,"Ash sha! sai ya maimata shekara
    kenan?"Alhaji karami ya ce,"to in ma ba zai
    maimaita ba Alhaji shi ya sani,ba sahura ta bata
    su ba? shi Abba ai ba haka yayi ba,ka dubi fa
    yadda yaki aikin kanikancin nan,uwarshi ta zuga
    shi wai yayi karatu kadai yayi aikin gwamnati.
    kullum haka sahura take kitsa ma yaran."Alhaji
    babba yayi yar dariyar takaici,sannan yace"in
    banda abin sahura yadda kasan nan tamu ta
    zama waye zaici alwashin aikin gwamnati? ina ce
    masu digree ne ke yawo ba aiki?" "har masu
    masters." inji Alhaji karami.ya tashi zaune daga
    kishingidar da yayi,yace dubi misalin dan
    abokinnan naka Alhaji buhari." Alhaji babba ya
    ce,"kwarai kuwa,mas'ud ba.yanxu ma fa kasuwa
    yake zuwa,sai yanxun yake koyon kasuwancin."
    Alhaji karami ya ce,"to daya dora shi a kasuwar
    fa tun farko?shi yasa na fada ma sahura ta bar
    yara su hada da sana'ar hannu. Donni dai yaro
    kamar bashir yanxun ba zan dauki kudina in ba
    shi ba."Alhaji babba yace,"shi yasa kulum nake
    kara son Abba,yaron nan da kanshi yace min in
    kai shi shagon dinki. Har naki suwaiba ta
    ce,"Alhaji ka kai shi in ya iya sana'ar hannu ko
    bai samu aikin gwamnati ba zai rike kanshi da
    sana'ar nan." Alhaji karami ya ce,"to ai kasan ita
    suwaiba tasan abinda take yi.amma sahura sai
    addu'a." Sallamar Abba ce ta katse su,ya zauna
    can gefe sannan ya gaishe su,duk suka amsa tare
    da tara hankulasu gurinshi. Ya mika ma Alhaji
    babba kullin takarda tare da cewa "Alhaji gashi
    maganin (ulser)ne" Alhaji babba ya amsa ya
    ce,"Abba sarkin amsa magani, a gurin wa ka
    samo wannan kuma?" ya ce,"Ahmad abokina na
    raka ya amso ma babanshi,shine nace bari in
    amso muku" yace to Allah ya saka da
    alkairi."Alhajikarami yace"dame ake sha?" Abba
    ya ce,"da madara peak." suka ce"to" daya mike
    zai shiga gida Alhaji babba yace ya shige da
    kwanikan abincin. yau kam Abba bacci yake ji da
    wuri,don haka ya baro shagon dinkinsu wanda ya
    kan kai goman dare a ciki ya nufo gida. Ya bude
    dakinshi ya shiga ya cire riga sai singileti da
    gajeren wando na jeans.ya nufi ciki don ya kama
    ruwa ya kuma yi wa ummanshi sallama. tsakar
    gida ya sameta zaune ta zabga tagumi,inda
    abinda Abba ya tsana shine,yaga ummanshi cikin
    damuwa. da sauri ya isa wurinta,"umma
    lafiya?"ta dube shi "ina fa lafiya,ummi ce tunda
    tayi sallar isha'i ta fice kusan awa guda zance
    jiya ka mata dukan fita wasan dare?" Abba yace
    "to wai me za'a yi wa ummi ne ta zama irin
    sauran yara?" umma tace,"addu'a ce Abba,kuma
    muna yi kullum." ya juya cikin bacin rai,layin su
    Amina kawarta ya nufa,don bata wuce can.duk da
    cewa Amina bata kaita rashin ji ba. can din kuwa
    ya sameta,ta tara zugan yayan layi sai tsokanar
    fada suke yi,ita ce shugaba. wata falwaya Abba
    ya samu ya jingina yana kallonsu,don yana iya
    tunkararta su diba da gudu. shi kam ba za ya iya
    guje-gujen nan ba,duk wanda yazo wucewa sai
    sun tsokane shi,wani su jefe shi,wani kasa zasu
    watsa masa su gudu wani kuma rigarsa zasu ja.
    c can wani shida budurwarsa sun zo wucewa ta
    fizge ledar hannunsu ta watsar,sannan suka ruga
    da gudu. tayo gurin da Abba ke tsaye bata zaci
    da mutum a gurin ba,sai dai taji anyi caraf da
    ita.sai da Abba ya zabga mata koso a tsakiyar
    kai har tayi fitsarin wuya,sannan ya tasata har
    gurin mutumin data yaga ma ledar. suna
    tsugunne suna tsintar lemunsu da ayaba ya
    ce,"malam ga wadda ta yaga muku leda." da
    zafin nama mutumin ya mike,Abba ya
    ce,"gata"mutumin ya shakota yace yau sai naga
    ubanki." Abba ya ce,"ko kara ka kai gidansu nine
    zan hukuntata,don haka gata na kawo maka
    kanwata ce kuma naga lokacin data tsokaneka."
    jikin mutumin yayi sanyi ya ce,"na gode bawan
    Allah,taje taci albarkacinka." Abba yace "daka
    nade ta." mutumin yace,"ba komai,ke kuma ki
    canza hali ke mace ce." Abba yace nagode"
    sannan ya tasa ta zuwa gida. Bokiti ya cika da
    ruwa ya dora mata,,umma rasa bakin magana
    tayi daya sanar da ita tsokanar daya tarar da
    ummi suna yi. Daga karshe ta ce,"Allah ya
    shiryaki,abind ya sameki kada ya sami sauran
    dangi. Alhaji kuwa daya sameta dauke da bokitin
    tana kuka tana fadin "yaya Abba na tuba,bazan
    sake ba." ya ce,"uwata bakya ji ne fatan Allah
    yashirye ki."ya nufi dakinshi.tsohuwa takaicin
    Abba ne ya hanata fitowa tayi magana. nata
    ganin,ummi bata wuce fita tayi wasa da
    kawayenta ba,a cewarta ba laifi ba ne. amma an
    bi an tsangwami yarinya,an hanata walawa.sai da
    Abba ya gaji dan kanshi sannan ya sauke mata
    ruwan. Sannan ya mammaka mata
    takalmi,sannan ta shige dakin
    tsohuwa.tsohuwana daga kwance ta dubeta.
    "yaga dama ya kyaleki?kai mai sunan malam
    akwai mugunta.zo ki kwanta." cikin kuka ummi
    tace,"kayana sun jike,bokitin ruwa fa ya dora
    min."tsohuwa tace,"barshi da halinsa,ace mutum
    ba zai sake ba?" ummi tace,"ai sai na rama,shima
    din sai yayi kuka."tsohuwa ta ce,"a'a,kada ki
    soma zancen ramakon nan.kin san ko kin rama
    ke ce zaki kwan ciki." ummi ta ce,nifa sai na
    rama."tsohuwa ta ce,"baki gaji da shan wahala
    ba kema da shegiyar gaddama,ga zanina nan
    kikin raki ciro ki daura kizo ki kwanta." ummi tayi
    lamo bayan tsohuwa tana tunanin dame zata
    rama abinda Abba yayi mata jiya.har bacci yayi
    gaba da ita waiwaye............. SULAIMAN shine
    asalin sunan Alhaji babba,Aminu kuma shine
    Alhaji karami. tsohuwa itace mahaifiyar su,kuma
    su kadai ne yayan data haifa.Asalinsu yan
    zamfara ne a kauyen daji a karamar hukumar
    kauran-namoda. malam Idris mahaifinsu shine ke
    zuwa yawon fatauci,har Allah ya zaunar dashi a
    garin kano,da matarshi Habiba. sunzo da
    yayansu guda biyu,sulaiman da Aminu.sun yi
    karatun muhammadiyya mai zurfi,amma basuyi
    karatun boko ba. sannan ya dora sukan harkar
    kasuwanci,Allahya albarkaci kasuwancin Sulaiman
    inda harkoki suka bude mishi cikin kankanin
    lokaci. matsalar shi daya rashin boko,malam
    idrisu mahaifinsu yana daya daga cikin wadanda
    basu amshi boko ba lokacin da tazo. Don haka
    sam bai saka yayansa ba.Sulaiman ya auri
    Suwaiba wadda suka dauki watanni suna
    soyayya,ita yar unguwar sheka makaranta ce.
    Amma asalinsu yan Daura ne jihar Katsina.kafin
    aurensu sai da yayi gini a unguwa uku gidaje
    guda biyu iri daya. Ya ce Aminu kaninsa ya zabi
    gida duk da cewa a lokacin baiyi auren
    ba,wannan abu yayi wa mahaifisu dadi. yayi ta
    shiwa Sulaiman albarka,don haka sai aka rufe na
    Aminu,yayin da sulaiman ya tare a nasa da
    matarsa Suwaiba. / ZURFIN CIKI book 1 part 2
    ZURFIN CIKI book 1 part 2
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:40
    Kwanci tashi 5yrs ta miqa suwaiba bata taba ko
    batan wata ba. awannan yr ne mahaifinsu ya
    cimma 1yr da rasuwa. saida aka watse makoki
    danginsu na qauran-namoda suka koma. sannan
    sulaiman yace da aminu, to ni xan dauki tsohuwa
    in maida ta gidana,kai kuma aminu ka fito da
    mata kayi aurenka dan mu xauna kusa da juna.
    tsohuwa ta saka kuka tace wannan yaran nidai
    da ka barni na xauna da gidan xai xama kufai.
    sulaiman yace tsohuwa kiyi haquri, sai a saka
    haya.aminu yace haka xa ayi. daqar tsohuwa ta
    yarda dan tace ita wannan gidan mutuwane xata
    rabata dashi, dan gidane me tsohon tarihi a
    gurinta. ta ce gidan da mijinta ya rasu gidan da
    ya kawo ta tun tanada jajayen sawunta. suka dai
    lallabata. lkcn da aminu ya gabatar da sahura a
    matsayin matan da xai aura, tsohuwa ta tuma ta
    ce ba ta laminta ba, don kuwa kowa yasan
    mahaifiyar sahura gun masifa. sanna sahurace ta
    gajeta. aminu sai ya watsar da mgnn auran
    gabaki daya har tsawan lkc. sulaiman yanata
    roqan tsohuwa ta amince, dan ya lura aminu yayi
    nisa. Ba yadda tsohuwa ta iya, dole ta amince,
    aka sha biki ta tare gidan aminu. mai hali dai
    baya fasawa, dan sahura batasan hulda da
    suwaiba da surukarta, gashi daga kawota ko
    2mth bata yiba ta kama fada da yan unguwa. a
    cikin 3yrs sahura aka samu ciki. lkcn sulaiman ya
    samu xiyarta qasa mai tsarki shida tsohuwa dan
    sauke farali. sunyi addu'a allah ya bashi xuri'a
    shida aminu.suna durowa gida suka samu lbrn
    cikin sahura, murna a gun sulaiman tamkar
    matanshi ne keda cikin.lkcn haihuwa tahaifi da
    namiji murna gun yan uwa biyu ba'a magana,
    anyi shagalin suna inda yaro yaci sunnan mahai
    finsu wato idris shine suke kiranshi abba. Sannan
    Ahaji Sulaiman ya biyama qaninshi kugeran
    makka daga nan ne aka samu ahj Babba da ahj
    qarami tun abba yana jariri ahj babba da
    matanshi suke dawainiya dashi Sahura ba taso
    saidai ba yan da xaitai da ita. domin alj qarami
    na gama shirin fita xai saba shi sai gidan sai yayi
    kukan nono ake maida shi, saidai tayi ta mitar
    cewa anriqe mata yaro gidan,sahura dai in an
    kawoshi bata isa taxoba dan tasan tsohuwa
    tafita danja.duk da gugar xana da haibaici da
    sahura take antayo ma suwaiba ta katanga ko
    inta je gidan, baisa ta daina dawainiya da abba
    ba. cikin hakane sahura wata ran sahura ta tashi
    da xaxxabi mai tsanani da amai, shine taje asibiti
    ganin likita ya tabbatar mata da tana dauke da
    ciki.ko da ta fadama alj qarami ba qaramin murra
    yayi ba ita kuma ta batarai, yace tunda abba
    yana tafiyan shi ko ina ayaye shi. Da yamma
    bayan yadawo kasuwa ya shiga gaida tsohuwa
    shine yake gayamata xa'a yaye abba. tace
    saboda me? ku barshi yayi 2yrs. sai yace ai uwan
    tanada juna biyune, shi yasa, daman sha waran
    da nakesan fada maki shine xanba yaya shi
    kyauta har abada.tsohuwa tace kai amma ka
    kyauta. Washegari da safe shine ma yayi ma
    abba wanka tana kwance ya shirya shi, sannan
    yace mata ta hada kayanshi duka dan xan kaishi
    gidan ahj babba gaba daya. tace kana nufin kayi
    kyauta dashi gaba daya? yace ea. tace tabdi!,ba
    xai yiwu ba. infishari banxane kaxa tayi mana. su
    wa yace kada su dage su samu nasu dan? nima
    wahala nasha na haifi dan, ba shago na bude ya
    fito ba....sam bai kulata ba, ya hada kayan yaran
    ya fita. ya shiga gidan ahj babba da shi. dakin
    tsohuwa ya shiga, nan ya samu ahj babba suna
    gaisawa, yace yauwa, dama gurinka naxo yaya.
    abba ya sauka daga jikin babansa yaje jikin ahj
    babba da gudu, ahj ya dauke shi ya rungume. Ahj
    qarami ya keqa ya kira suwaiba,ta shigo ta xauna
    sai ahj qarami ya soma jawabi da cewa. tsohuwa
    ina san ki xama sheda, yaran nan na ba yaya da
    suwaiba har abada.ahj babba yasake rungume
    yaran a jikinshi wani saban son shi ya ratsa shi.
    idanshi suka kawo qwalla, suwaiba ta sa kuka
    tace mun gode da wanna abu da ka yi mana.
    Allah ya bamu ikon riqeshi da amana. ahj babba
    yace bani da bakin da xan maka godiya, saidai
    ince allah ya qara xumunci. ahj qarami yace haba
    yaya dana nakane, saidai inasan abba ya xama
    xaka kai daya. tsohuwa tace allah ya maku
    albarka daku da yayanku, kaima allah ya baka
    haihuwa. sukace amin. Sahura kuwa mijinta na
    fita da yaro, itama ta xari hijabi ta nufi gidan
    iyayanta, ta shaida ma mamanta cewan aminu
    yayi kyauta da danta, kuma yaba mutanan da
    basa qaunan ta. nan da nan uwar tahau masifar
    cewan ba xai yuyu ba, ai dole ya baki danki.
    shiko uban cewa yayi ai ikon sane, dan haka
    baiga laifinsa ba dan yaba dan uwansa dansa.
    sannan yace ,ta tashi ta koma. uwar tace ba xata
    koma ba, ya ce ta xauna. bai sake bi ta kansu ba,
    ya ci gaba da harkokinsa. shiko ahj qarami cewa
    yayi baxai bita ba, lokacin da ya dawo ya samu
    batanan, sannan bai fadama dan uwansa ba har
    aka kwana. sukuma su suwaiba basu fahinci
    sahura batanan ba dan ba hurda suke ba, saida
    kukaxo cin abinki ahj qarami bai futo da kwanu
    ba. sannan wan yace iyalin naka bata nanne?
    yace yaji tayi, niko baxan bita ba. ahj babba yace
    akan wani dalili ne? ahj qarami yace ban sani ba,
    na dawo gida ban ganta ba. da safe ahj babba ya
    tashi gaba sukaje gidan, sahura ba kunya tace
    danta takesan ya dawo mata dashi, inhar yana
    san xama da ita. Ahj babba yace, indai danta ne
    xai maido shi. ahj qarami yace shi kuma inhar sai
    an dawo da dan to ya haqura da auranta. kuma
    na cikin ta ma inta haife shi xaixo ya ansa ya
    qarama wansa inya so yaga yadda xatayi. duk
    juyin da akayi yaqi yarda daga qarshe ma tafiyan
    shi yayi. ubanta yace da ahj babba kaima jeka
    yadda suka so haka xasu yi. satinta guda taka
    abincin kirki gagaranta yake yi, ita kuma uwan ta
    daina samun wani abu daga gun sahurar ke kawo
    mata. dan haka suka yanke shawaran ta koma,
    duk da haka saida ya shareta na kwana uku
    sannan ya sakar mata. haka ta haqura saidai
    tasha alwashin dun runtsi sai danta ya dawo
    hannunta. sannan ta kulla sabuwan gaba da ahj
    babba da suwaiba kuma tace duk tsohuwa ce
    takitsa abin. abba yana samun kulawa tare da
    tarbiya mai kyau.sahura ta haihu ta sake samun
    da namiji aka samasa bashir, daga nan haihuwa
    akai akai.. Tun abba yana qarami ya koyi wasu
    halaiya na ahj babba. da farko, sallar
    asuba,axahar, laasar, magrib da isha. ahj babba
    kan tasa abba suje masallaci da rana kuma
    umman sane ke turashi. ranan jumaa ahj na
    dawowa gida dan ya tafi dashi. dan haka sallah
    ta xauna ma abba da xaran lkc yayi xai fara shiri
    yi. sannan ya iya sadaka dan dasunje yana bashi
    kudi ya rabama almajirai ko yasa a asusun
    masallaci. sai xumunci aduk lkcn da ahj babba
    xashi xanfara yana tafiya da shi. ya tashi da san
    iyayan shi matuqa bai taba sanin basu suka haife
    shi ba. duk da cewan duk lkc da ya shiga gidansu
    umman bashi takan cemai bafa umman kace ta
    haifeka ba, nice na haifeka. riqonka muka basu. in
    yaji haka sai yace allah kiyaye. sai ya baro gidan
    ita kuma taita xakinsa. inya fadama umman shi
    saitai murmushi ta rungume shi. ya ce aidai kece
    ummata ko? ita kuma tace nice ummanka rabuda
    ita kaji. abba yanada tausayi dan haka ya
    taimaka ma ummanshi aikin gida. shekara sha
    biyu ya sauke kur'ani.a lkcn ne ya gama pry ya
    samu xuwa js1 Abba makarantan masu kudi ya
    ke yi.ita kuma sahura duk yaranta ta batasu,
    musamman bashir. duk lkcn da akace yaje
    makaranta inyace ya gaji, saitace ya xauna kaje
    gobe. ko ahj babba ya korashi sai dai ya labe
    inya tafi shi kuma ya dawo. yafi san xuwa qwallo
    ko shagon game. to hakama qannansa duk sun
    dau irin tarbiyyan uwarsu. cikin haka wata ran
    umman abba ta tashi da matsananciyan mura,
    lkcn ahj babba yaje legos don taho da kaya. ahj
    qarami ne yakaita asibiti bayan gwaje gwaje, an
    gano ciki wata biyu da yan kwanaki. murna gun
    ahj qarami tamkar yayi tsuntsuwa yaaje ikko ya
    fadama ahj babba. suna isowa ya shiga gun
    tsohuwa ya sanar da ita. nan take tasa kukan
    murna.ita kuwa suwaiba tamkar mafarki, sai
    kunya ta isheta. lkcn da ahj qarami ya fadama
    sahura, sai cewa tayi um, bana an tabuka, ni dai
    gani da cikin na shida amma sai yauxu ta samu
    daya. ahj qarami yace kinji matsalanki, ke ba dai
    kiji wani ya samu qaruwa ki taya shi murna ba,
    sai dai baqin ciki. ta ja tsaki bakin cikin me
    xanyi? tunda ni ga nawan. ciki mai laulayi
    suwaiba ta samu, wanda duk abin da taci sai ya
    dawo. wannan lamari ya daga ma ahj babba
    hankali da abba, duk aikin gidan abba ke yi, ga
    makaranta, ko an hanashi sai yayi.dan haka aka
    dauko harira qanwar suwaiba, wanda mijinta ya
    mutu. umman abba dai bata samu kanta ba saida
    cikin yayi wata biyar. sannan ta samu sauki.lkcn
    sahura tanada cikin wata bakwai, lkcn haihuwa ta
    haifa mace, murna gurinta kamarme, dan sai
    yanxu ta samu mace. safiyar talata umma ta
    tashi da naquda, hankalin ahj da abba ya tashi
    matuqa. duk da tsohuwa tana ta kwantar masu
    da hankali, ranan abba ko makaranta bai jeba,
    duk da san makarantansa, har suka dawo sallan
    axahar shuru. ahj babba yace tsohuwa bari na
    samo mota akaita asibiti. tace to. yana fita ba
    jimawa ta haihu. ta santalo yarta mace mai
    matuqan kama da ahj babba. tsohuwa tace da
    abba,mai sunan mlm bi su ahj kace sudawo ta
    haihu. dama harira tasa ruwan wanka lkcn da
    suka xo ta fito daga wanka.nan aka wanke
    yarinya yan barka sai xuwa suke amma sahura
    saida aka. Sahura saida aka kwana sannan ta
    shigo. ta dauki yar ta taba baki tace wannan yar
    baqinqirin haka sai idanu daqwa daqwa. wata
    mata da taxo barka tace ai wannan yar sak
    abba,suna kama sosai. sahura ko kunya ta ce
    basa wani kama da abba. da tasamu kyan abba
    da tayi kyau, umma tayi ma matan alama da
    haunu tai shuru. ranan suna taci sunan tsohuwa,
    wato habiba, dan haka umma ke ce mata ummi.
    abba yana ji da ita, saidai in yanasan tsoka nanta
    sai yace dubeta ta ba ummata wahala, sai na
    xaneki kika girma kika qi mata aiki. umma taita
    masu dariya. tsohuwa ma naji da ita dan guta
    take wuni. tunda ga kan ummi umma bata qara
    haihuwa ba. abba yana aji uku suna qoqarin xana
    (j.s.c.e)ya dage sai ahj ya saka shi shagon dinki.
    ahj yace abba kabar batun dinkinnan ka tsaya a
    karatunka. yace ahj nidai ina so kaga inna iya su
    umma sun huta dakai dinkin su gidan laminde.
    umma tace ka barshi yayi ahj sana an hannu ai
    tanada dadi, kaga in ya gama bokon ba bai samu
    aiki ba xaya riqe kanshi da sana anshi. ahj yace
    to shi ke nan Ahj yace, to shi kenan, wane shago
    ka ke san shiga inkai ka? yace, na can bakin titin
    nan, in da kake saya na lemo. ahj yace shi kenan.
    mafarin shigar abba gurin koyan sanaa kenan.
    ummi ta taso da rigima, tsiwa tare da tsokana,
    wanda yasa suka daina shiri da abba sam. abba
    ne ya kaita makarantan boka da islamiya, kullum
    yaje daukota sai ya raba fada ko ya bada hakuri.
    umma kullum addua take fili da xuciya da lokutan
    sallah, allah ya shirya mata ummi. ita kuma tata
    kalan quruci yan kenan inta girma xata daina.
    tsohuwa takance aini me sunana kingama min
    komai, domin banasan ragon da, da in kai qara
    gara akawo min na bada haquri. duk lkcn da tayi
    wannan kalman sai sunyi fada da abba, dan cewa
    yake ai dama tsohuwan nan tuni na ane kin daure
    mata gindin ta siqa tsokanan yayan mutane. ita
    fa mace ce ba namiji ba, shi kenan bata da aiki
    sai dambe? tsohuwa takance batta tayi. tunda
    ganan abba basa shiri da tsohuwa. ita kuma fati
    yar sahura kamar ummace ta haifeta dan bata da
    hayani. ummi kuma kamar sahura ta haife ta.
    Wata rana abba ya ke cewa, umma da ace lkc
    daya kuka haihu da umman bashir, allah cewa
    xanyi kunyi canjin yaya. umma ta dube shi dan
    me kace haka? yace sbd masifar ummi irinna
    umman bashir ne, fati kuma ba ruwanta kamar
    ke.dariya kawai take yi. kwanci tashi ummi ta
    gama pry, lkcn abba yana shekaranshi ta qarshe
    a jamia. yana karantan (mass comm)ne dan yana
    san xama dan jarida. umma tasoshi da likita
    amma yace baida raayi. tace kaga kai bakada
    hayaniya abba aikin jarida na masu maganane.
    yayi murmushi yace umma kenan. ummi ta samu
    shiga aji daya a qaramar sakandare. maimakon
    hankali abin nata sai gaba yakeyi. aduk lkcn da
    tai laifi abba ya daketa sai tayi wani abun dan
    tabashi haushi, da sunan ta rama. ahj babba ya
    bude mai shago, tare da xuba mishi kekuna.
    tsohuwa tace dakai wanine mai sunan mlm, saika
    tafi da takwarana ta koya. abba yace ko a
    kwafan shago na na ganta ba sai na karya mata
    qafa ba. ummi ta murguda baki, sai daya tafi
    sannan tace allah ya kiyaye inje wannan qaxamin
    shagon nashi. Tsohuwa ta ce,"tafi can kema da
    baki son ci gaba, in banda abinki da zaki kwantar
    dakai ki koya in an tashi auranki basai a saya
    miki keken ba. in kuma shi kika aura kinga
    shikenan inya samo dinkin da yawa saiki taya
    shi, ta ce"Allah ya kiyaye me xanyi da yaya
    Abba,yayi ta cin xalina?ni bana son shi" Umma
    dake gefe tana jinsu ta ce,"ke in kin samu kamar
    Abban ma ai kinji dadi,shine zai ce mai zaiyi
    dake? mara hali irinki." Ummi dai tayi shiru tasan
    inta cika surutu kan Abba yanxun nan umma ta
    doddoketa,umma tafi son Abba fiye da ita. watan
    ramadan ya tsaya,duk daukacin musulmi sun
    dauki azumi ranar da akai na uku Abba ya shigo
    gida karfe daya saura. daga shago yake zaiyi
    wanka yaje makaranta don yanada darasi karfen
    biyun rana. Gidan shiru kowa na bacci,don haka
    bai shiga dakin umman shi ba don baya son ya
    tasheta ya shige bandaki. Da ya gama ya fito ya
    nufi daki kamar ance ya kalli madafi, ummi ce
    tsugunne tana cin abinci. ya tsaya yana kallonta,
    dagowan da xatayi suka hada ido, yace ke! karya
    axumin kika yi? ta toshe bakinta sannan nace
    dan allah yaya kayi haquri. yace fito muje. ya
    kaita dakinshi yasata gwale gwale. da xashi
    masallaci ya kulleta ta baya. ya ce inyaso ki
    tashi kafin na dawo, xan gane. yana fita tahau
    binci ken abinda xata lalata mashi. ta ciro bidiyon
    da yake kallo xata doka da qasa, sai taga kwalin
    wani kaset tana kallon hoton jikin kwali, na
    tsiraici ne. ta xare ido kicin mamaki, tace lalle
    yaya abba, daman shi dan iskane? to kuwa xan
    tona mai asiri. ta turashi cikin xaninta, da taji
    motsin shi yana bude qofa sai ta koma inda take.
    ya shigo ya kalle ta ya ce nasan kin xauna dan
    kinga bananan. ya xauna bakin katifa, sannan ya
    dubeta fuska daure. ummi meyasa kika karya
    axumi? tace ba komai. yace tunda aka fara axumi
    kike karyawa ko? tace yaune kawai yaya abba.
    yace kinsan hukuncin wanda ya kasya axumi da
    gangan. Tace eh an fada mana a islamiya, amma
    mlm yace sai wadanda axumi ya wajaba akan su.
    ya kalle ta cike da mama ki, a xuciyanshi yana
    cewa, yanxu har yarinyan nan tasan akwai
    wadanda axumi ya wajaba akansu? afili kuma
    yace lalle ummi kina buqatan sa ido. dama
    saboda bai wajaba akanki ba shiyasa kika karya?
    to daga yau xansa maki ido, kuma xan fadama
    umma ta sa maki ido. hakanan duk wani abu da
    akeyi lkcn axumi an daina qyale ki, xaki ringa
    sallar tarawi, ke har tahajjud sai kinyi shi. sannan
    bayan axumi saikin rama wannan axumin. ya
    xuba mata ranqwashi a tsakiyan kanta ,tare da
    cewa tashi ki fita munafuka. daga dakinshi bayi
    ta shige ta qara kallon kwalin, sannan ta maida
    ta soke shi, tace sai na tona maka asiri. da dare
    bayan angama bude baki, abba xai tafi tarawi ya
    shigo dakin umma yace ina ummi? umma tace
    gatanan kan kujera tayi sharkaf, wai yau taji
    axumi. abba ya shiga ciki yana kallanta. yace
    umma xaki yaudara ko yar rainin wayau, tafa
    karya axumi daxu da rana na ganta tana cin
    shinkafa. Yace shine kika xube wai ke kin sha
    wuyan axumi ko? umma ta dube ta tana mamaki,
    tace abincin da kike kinba almajirai da ma qarya
    ne? ya dubeta yace biyu kenan ga larya axumi ga
    qarya, xaki sani. tashi muje salla ko in ballaki.
    umma tace allah ya shiryi halinki. abba yayi
    dariya tare da cewa, kema dai umma yaxaki
    amince da batun wai tac almajirai abinci, su basa
    axumi ne, umma tace tunanin haka sam bai xo
    min ba. saida ya sakata sahun salla, sannan ya
    nufi gun maxa. bayan ya gargadeta da cewa in an
    idar ta jira shi, inyaxo batanan sai ta sani. koda
    aka idar da yaxo bata nan gurin ya kaure da
    dambe da wata yarinya wai da suna sallah tana
    bigeta. shine daga idarwa ta cakume yarinyan da
    fada. bai tsaya sauraranta ba ya cire ta kalmi ya
    shiga dukanta, sannan ya tasata xuwa gida. sai
    da ta shige dakin tsohuwa sanna ya koma nashi
    dakin. hakanan suka ta xuwa masallaci har
    axumi yakai ashirin. Ahj ya kawo masu shadda
    da leshi da atamfa na sallah ita da umman su
    bashir da fati. ya suya masu takalma da mayafai,
    abbane xai masu dinki, ran ummi baya son dinkin
    abba, domin wanda take so bashi yake mata ba.
    ta ce umma dan allah nidai a bani dinkina na
    kaima laminde, yaya abba baya min ne kyau.
    umma tace kije ki karbo da kanki. tace ai baxai
    bani ba ne, xai dakeni. umma tace ai nafi san ya
    dake kin, lamindan finshi dinki mai kyau tayi ne?
    ummi tace nidai gara ita. tsohuwa tace ai banga
    lkcn da mai sunan mlm xai faranta ma takwara
    ba, kullun burinshi ya quntata mata. umma tace
    tsohuwa ummi fa ba a mata gwaninta, inace dinki
    in yayi mata har aro ake xuwa yi? ta dube ta
    tace keda shine inya jiki kyayi biyu babu, yaqi
    maki dinkin luma ya hana kayan bare kiba
    laminde inga ta tsiya. qarfe dayan dare ya tura
    dakin tsohuwa tana xaune a kan sallaya tana
    addua, abba yayi murmushi. tsohuwannan kina
    birgeni dama kina ibadan dare? ya kalla kan
    gadonta, ummi taya dai dai tana ta bacci./ ZURFIN CIKI book 1 part 3 ZURFIN CIKI book 1 part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:42 Ya kalla kan gadonta, ummi taya dai dai tana ta bacci. Yace, ummi ke! ummi!! tashi. tsohuwa tana yi masa alama da hannu gami da gyaran murya, wai ya bar ummi maimakon haka ma sai ya dauki wani kofi nan gefansa da guntun ruwa a ciki ya watsa mata a fuska. ta farka firgigit, yace taso, da sauri ta tashi yace dauko hija binki maxa. ta dauka suna fita tsohuwa tana sallamewa. tace kai mai sunan mlm ka lafama yarinyan nan haka, wai axumi wajaba akanta yayi da xaka tasheta da tsohon darannan xuwa masallaci? yace kema in xaki, xo muje. ya tasata suna tafiya tana hada hanya suka tafi tahajjud. sai qarfe hudu na asuba aka tashi. ummi har kuka tayi saboda tsananinjin bacci, amma tana tsoran kar ta kama bacci yaxo ya same ta. tun tana layin bacci har ta gyagije. sakamakon tashinta da matan kusa da ita keyi. kafin kwana uku ta saba da sallan dare, lkc nayi xata farka. abba yana xaune ga dinki gabanshi amma yana can tunanin bushira, yarinyan da yake matuqan so ce. amma yana shakkan fada mata,dan iyayanta sunada kudu matuqa. kuma shine yakema duk yan gidansu dinki. Ahmad abokinshi da ke gefe kuma sai yayi murmushi, yasan tunanin bushiqa ne ke damun sa, dan haka sai ya ce, abba kasan allah, abari ya huce shi ke kawo raban wani. haka kuma ZURFIN KICI, ba xai kai ka gaci ba. ka fada mata kawai. abba ya ce hum ,ina tsoron kada ta ce bata sona, dan bansan ina xansa raina ba. ahmad yace daga ganin yadda take jin kunyanka tana sanka. abba ya kalli ledan da ke dauke da dunkunan su bushiran, yace ina xatan yau xasuxo amsan kayansu, dan tun jiya nace suxo.ahmad yace to in sunxo kayi qoqari ka fada mata mana, indai ba ragon namiji kake ba. abba ya tsurama qasa ido yana tunanin in sunxo mai ce mata? kusan awa biyu sukaje sukai sallan axahar, tungan motan ta tsaya yasan tasu bushurane. shi kadaine a shagon sauran basu dawo ba. bushura ta shigo da qannansu da yarsu aisha. ya taresu da faraa, suka gaisa kan bushura na qasa, sam bata iya kallan abba tela kamar yadda suke kiranshi. Ya tura masu kayansu suka duba sunata murna dan ya masu wadda sukeso. aisha ta aje masa cikon kudinsa kan table. har sun fita yagadai baxai iya hakuri ba, yace bushura xo gashi. ta juyo tana dariya taxo. yace bushura inasan na fada maki wata magana gashi kuna sauri ko? ta kalli motan tace fada min. yace kina sona? ta xare ido sannan ta ruga da gudu. gabanshi na faduwa, bata tsaya ba sai mota. ya kwantan da kanshi akan keken yace menene maanan gudun da yarinyannan tayi? ya tambayi kansa, qarfe uku sunada lecture, amma baya xatan xashi makarantan. ahmad ya dubi abba wanda daga ka dube shi xakasan yana kin damuwa. yace wai banaga sunxo ba? ko ba motan su bane? shiya bandawo ba nakuma hana yaran dawowa dan ku sasanta. abba yace um, inaga yarinyannan gara na haqura, dan bana san insa kaina cikin tunani. ahmad yace ban gane ba, abba yace, to naga daga tambaya tana sona, saita kwasa da gudu ta shige mota. ahmad yayi yar dariya sannan yace ,amsan ta baka. tana nufin tana sonka. abba ya harare shi kada ka maidani dan iska, ina ta magana ta xabga da gudune shine tana sona? yace jeka tambayi manya .yaci gaba da cewa kaine baka mata magana da hikimaba, ka fito mata kai tsaye baka sakaya ba. abba yace, kai nifa ka sanni ba ruwana da wata kwana kwana, idan abu yayi min bana kwana, inko bai min bama haka, ni ba ruwana. Ahmad yace sai xurfin kici ko? da ya aka shawo kanka ka fada mata,abba ya mike tare da kallan agogo, yace inada lecture. gida ya nufa dan shirin xuwa makaranta, har yayi kamar ya tambayi ummanshi cewa in ka ce ma mace kana sonta taji kunya ta gudu wai alamun so ne? sai kuma ya kasa, yana jin nauyi amma in bai samu wata manufa ba dole yaxo ya tanbaye ta dan baya boye mata komai.bushura yar ahj sale ce kwamishinan gona na wannan xamani, gidansu yana karkasara. danqareran gida ne ginin xamani, sun san abba ne sanadin dinki da yayi wa wata qawansu jamila.dinkin yayi matuqan birge su dan haka suka fara kawo masa dinki, tun ranan da ya fara ganin su bushura ta kwanta mashi a rai. to ashe ita ma yamata.shiyasa yau daya furta mata take ganin kamar anmata gafara da aljanna.wata xuciyar tace ,to yanxu da kika gudu in ya xaci baki sansane fa, nan take hankalinta ya tashi har tana rayawa ga abba can da wata.dan haka taga dolene ta koma gun sa inhar tana sansa. dan tasha ganin mata na masa tayin kansu in sunxo kawo dinki.nan ta soma tunanin wace dabara ce xatayi ta fita?saiko ta warware daya siket din kayanta cikin dare.da safe ta nunama momynsu tace mata telan ya manta bai hada wannanba,dama yace xai gwada nine kafin ya hada.momy tace direba ne xai kai mashi.bushura tace momx xaifa gwadani ne muje dai xa kaini.tace to kuje, bushura ta danyi gayunta suka tafi.saidai kash! bata samu abba ba ance mata yana gida. tace gidan da nisane, aka ce mata babu nisa,dan haka ta sa aka rakata.tacema direbansu tana xuwa telan na gida.gidan ba nisa. A qofar gidan su abba ta tsaya, sai ga ummi ta sheqo da gudu tana dawowa daga aike.ta tsaya tana kallan bushura, sannan tace lafiya?bushura ta dubeta. yauwa abba yana nan?budan bakin ummi sai tace yaje kashi ya fada a masai.bushura ta dafe qirji, yaushe? ummi tace oho.sai ga abba ya futo sanye cikin shadda bulu mai duhu yana ta qamshin turare.shawara ya yanke lkcn da yake xaune a shago kan cewa yaje gidan su bushura,tunda gidan kwamishina ba boyayye bane,suka hada ido da bushura,ta saki faraa sannan ta dubi ummi,kince ya fada ina? ummi tayi ciki da gudu.ya bita da kallo sannan ya kalla bishira,me tace maki?bishira tace, ba komai.saidai dariya da maganan ummin tabata.yace tunda baxaki fada min ba xomuje ki gaida ummana.cikin muryan jan hankali tace ina jin kunya.ta bude jakanta tace kamanta baka dinke wannan siket dinba.yace mugani,yaga yadda aka warware shi aka cire xaran da kyau. murmushi yayi dan yasan ya dinka siket din,kusan shinema na farkon dinki.ya gane yaran nata qila san ganinshi take san yi. Ya dinke siket din yana cewa"to amma sai dai ayi min izini inzo gida in kawo da kaina in na gama." tace haba dai,ya za ayi in taso ka?"ya ce,"ba komai,in dai anyi min izini sai inzo," ta ce,"to in maka kwatance?" ya ce,"a'a huta kada ki bata bakinki,nasan gidanku zanzo anjima bayan tarawih." ta ce,"to." sai mun zo" tace"ku dawa? ya ce,"abokina mana,kinga zo muje gurin ummana ku gaisa." Bishira ta bishi cikin jin kunya.tun kafin su shigo daman ummi ta shiga gurin umman da gudu tace mata"umma ga budurwar yaya Abba." Umma tace budurwa kuma? tace eh ai zama su shigo.daga nan ta kara kyallawa dakin tsohuwa tana fada mata. Umma dai jim tayi dan bata da wani burin da ya wuce ta baiwa Abba ummi,kuma da tasan har zai ga wata can da wuri haka data fada masa kudurinta,sa tay 'ZURFIN CIKI' gami da nauyin baki....... sallamar Abba ce ta katse ta ta ce,"shigo Abba." ya ce Umma bakuwa ce taxo gaisheki.Umma ta fadada fara'arta tace to shigo,ba dai surukar tawa bace?" ya ce,"ai ita ce kam" Bishira ta shigo tana sunne kai,ta gaida umma Umma ta ce,"masha Allah,Allah yasa rabon muce."Abba yana dariya ya ce,amin ummana."ya dubeta,"tashi ki gaida kakata." suka nufi dakin tsohuwa,umma ta jinjina kai .tabbas Abba nason yarinyar,in ta dubi yanda yake fara'a da zumudi. a fili ta ce,"Allah yayi mana zabin alkairi."ummi na kwance kanta na cinyar tsohuwa,sai ta kalli bishira ta tuntsure da dariya,lokacin da suke gaisawa da tsohuwa. Abba ya ce,"dariyar uban me kike yi?" sai ko ummi ta sake shekewa da dariya. ya nufota ya suri kafafunta,tsohuwa ta ce haba mai sunan malam yanxu in bata yi dariya ba kuka zatayi?" ya ce,Bishira tashi muje" Tsohuwa tace to yanmata mun gode ki gaida magabatan naki,sannan kiyi ta hakuri da halin wannan miskilin." Umma ta ce,"tsohuwa kodai kishi ne?suka yi sallama,ummi wadda tunda ya shureta ta rigasu fita sai ta dauki takalmi Bishiran guda daya takai soro (zaure). don haka da suka fito suka shiga nema ummi ta kule uwar dakin umma tana ta dariya tana lekensu. Abba ya ce,"ummi! ummi!!" taki amsawa ya nufi waje da niyar dubota don yasan ita ce zata dauki takalmin,sai ga takalmi a kofar shi. Don haka ya dauko kawai ya dawo ya bata umma ta ce,"ka kaita su gaisa da umman Bashir." Abba ya ce,"a'a ba yau ba."ya rakata wurin direbansu,kusa da shagonshi sukayi sallama da alkawarin zai zo washegari. yaje kuma bishira ta fada masa lallai tana sonsa sai dai tana tunanin iyayenta ko zasu amince? ya ce,to shi dai zai turo magabatansa su nemar masa izinin zuwa zance kamar yanda yake a shari'a Bishira tace a'a ya bari tunda yanxu shekarar farko take a babbar sakandare(s.s.1)ba za a bari ya dinga zuwa ba,amma zasu dinga haduwa gidan yarta dake na'ibawa. Abba baida zabin da ya wuce ya yarda da hakan tunda tace baza a barta yin tadin ba.sai dai fargabar shi kada nan gaba sunyi zurfi cikin soyayya ace ba za'a bashi ba. ta ce,"Babana bashi da matsala,amma momy dinmu ce abin tunani."Abba ya ce,"shikenan Allah ya shige mana gaba." soyayya ce mai karfi ta kullu tsakanin Abba da bishira,wanda har ummanshi da kanta tasan cewa Abba yana son yarinyar. Domin duk lokacin da zaije gurinta tana lura da zumudin da yakeyi,kazalikain tace ka gaida surukar tawa, bakinsa baya rufuwa. Don haka sai ta tattara batun ummi ta aje a gefe addu'a ce kadai bata daina ba.ana sauran kwana uku sallah.Abba ya siyo fenti yazo da mai fentin nana ak fente gidansu ciki da bai. Da yamma kuma ya kawo dinkunan su ummi da fati,ummi tasa ihu,sam irin dinkin da ta aro gurin kawarta Amina ba shi yayi mata ba,ya zai mata dink iri daya da fati? ya ce,"kin isa ki sani in miki dinkin da kike so?ta ce to ni dai bazan sa ba umma ta rafka salati tana kallon ummi ta ce,"ummi kina da hankali kuwa? kudi kika biya ko ko Abban sa'anki ne?" tace cikin kuka to ni umma ya zai min iri daya da fati? ya dubeta a fusace,"in kin bari na dauki kayannan wallahi bazaki sasu ba." Umma ta ce,"ni da zaka daukesu ma da naso"tsohuwa ta fito ta ce,"saboda me? akan wane dalili zaka amsar mata kaya?tunda baka mata wanda take so ba sai ka kyaleta." Da hannu Umma tayi mishi alamar yayi shiru,sannan ya fita waje.Abba ya kada kai ya fita. washe gari kuma ya shiga da me fenti har cikin gidan Alhaji karami,sahura tana daki lokacin da yake nuna ma mai fenti guraren da zaya fara. Ta fito daga daki ganin Abba sai ta hade rai sannan ta ce,"mune kashin baya? ai dama ka bar shi tunda baka mai da mu wani abu ba,mu ne dai baka so din mahaifanka. Ta dalilinmu zaka shiga aljanna,ba dalilin wasu banzaye ba da sauri ya nufi hanyar fita waje don baya son yaji zagin da zata yiwa Alhaji da Ummanshi. wannan na cikin dalilin dayasa baya son zuwa gidan Alhaji Babba da Umma,sune suka ci kashi da fitsarinsa. suka bashi tarbiya da ilmi,suka ci da shi suka shayar dashi.amma sam basa yi masa abinda umman Bashir ke masa. haihuwarsa ce kadai su Alhaji babba basu yi ba,sahura tana zuwa har shago tayi masa rashin mutunci,sannan ta ce ya bata kudi,ta ce ya ba bashir kudi ko ta aiko fati. Bai taba kin bata ba,amma duk da haka bai tsira daga zagin rashin mutunci ba.ta ce ya tare a gidan ummanshi komai nashike mata,wai da kuma sam ba haka bane. Umma bata taba tambayar shi sisi ba,haka nana duk lokacin da ya bata wani abu ko ya sai mata,sai tace ina na umman Bashir? kaje itama ka bata,in ko bashi da yawa ni naci girma ka bata. Ranar sallar idi kuwa ummi koda tayi wanka kin saka sabon kayanta tayi sai na bara. Lokacin da zasuje sallar idi,Abba ya fito daga wanka ya kalleta ina kayanki sabo? ta tura baki"ni baxan sa ba." Yace,"to zanga wanda zaki bi masallacin,kuma ki kara magana saina fasa bakinki."sai ta wuce kofar dakin tsohuwa,sannan ta ce,"to ai dai nima nasan hanya,kuma sai naje."ta fada dakin da gudu. ya bita bata san yaga tsohuwa lokacin da ta shiga wanka ba,bayan fitowarsa.don haka ya ritsa ta ya kwakkwada mata mari,sannan ya rike mata kunne. zan kara fada ki fada? ta ce,"a'a kayi hakuri." ya saketa ya wuce,ta zauna tana kuka. misalin karfe hudu na rana ,bishira ta iso shagon dinkin ita da direba,shagon a rufe.don haka ta ce su karasa gidan. Can dinma baya nan,amma sai ta fito ta shigj gidan dauke da tire babba cike da kuloli. cikin kunya ta gaida umma,ta kuma bada a aje masa.umma ta ce,"to ko ina Abba yayi? kila gidan su Ahmad yaje."umma ta ce,"ke uwar gudu ina yayanki?" ta ce,"nima na ganshi?" karar bude kofarshi suka ji,ta ce,"leka in shine kice yayi bakuwa.shine kuwa,jin cewa ga bishira ya shigo da zumudi. Umma tace ka kaita ta gaida umman bashir. yace to, ta fito ta tafi kicin ta bar masu dakin,ashe ummi tana uwar daki tana jinsu.ya ce,yanxun fa daga na'ibawa na ke,ina ta xumudi in ganki. tace,na xaci ba xa kaxo ba ne,nace bari inxo ni,dan baxan iya kai dare batare da idanuna sunganka ba.ummi ta toshe bakinta saboda dariyan da yakesan kufce mata,yace sai inga kamar bakya sona.bishira tace haba abba, in kace haka bakamin adalci ba.yace to wadannan kulolinfa me kika kawo min?ta ce bude ka gani.ya bude ya gani yace kai, lalle ashe ni dan gatankine? tace sosai ma.ya marairece murya yace to bani abincin a baki.ummi daga cikin dakin tace, la'ilaha illallahu.abba ya miqe da sauri.kafin ya ankara ummi tayi fitan bindiga tsakar gida tana fadin la'ilaha illallahu,dama yaya abba dan is....umma ta gwabe mata baki,bayan ta fito daga dakin ahj babba.ummi wadda inta s6a magana ko ana hanata sai ta kai aya.ta dafe baki,tace maci gaba da fadin,umma to kinji abinda yake ce mata ne? umma ta jefeta da takalmi tare da cewa,wai baxa kiyi min shuru ba? ummi tace,to fa cemata yayi xai bata abinci a baki,kuma daman xan nuna maki wani kaset da yake kallo. Abba ya riqe kai tare da cewa ummi in na kamaki xaki sani, kaset din wa kikaga ina kallo? tace na yan is....da gudu ya bita ,yayin da umma ta jefa mata murfin kwano,amma duk haka ko da ta fita waje saida tace masa sai na nuna ma ahj kwalin kaset din.take ya tuna da kwalin kaset din daya boye,wanda ya qwace a hannun bashir,kaset din tsiraici ne wanda laanannu sukayi.abba cikin takaici yace,kai ummi! kai ummi!! kinsan allah in kina wasa dani xa karyaki a banxa.ta ce to ba a dakinka na gani ba?yayi qwafa,allah ya sani ya tsani ummi kamar ya shaqeta ta mutu.sai ya samu kanshi da qin komawa gidan,kunya da nauyin umma yake ji,yasan dai ba xata kama xancan ummi ba,amma yasan xuciya da xargi,qila xuciyanta ta xargi wani abu.bashir ya fito daga cikin gidan su abba yace,yauwa bashir shiga gidanmu kace bishira taxo. Bashir rai bace ya shiga,dan yana jin haushi ya amsar me kaset.ya shiga umma na qofar kicin xugun tana tunanin halin ummi.bashir yayi sallama umma ta amsa.yace,abba ne yace in kira bira ne ni yace ne?umma tace gatanan ciki,taxo bakin qofa ta kalli bishira kanta na qasa tana mamakin ummi.yarinyan sam bata ji.umma tace kixo yana kira awaje.cikin kunya ta fita, yace da bashir rakata gun ummanka su gaisa.bashir yayi fara,a antynace ke nan?abba yayi murmushi. bishira ta xauna gaban ummansu bashir suka gaisa. bashir yace,budurwan abba ce. sahura tace,yau kika taba xuwa nan unguwan? kanta na qasa tace, xuwana biyu kenan.ta kalli bashir tace kaji ko? amma shine ko a turo ta nan gidan.nina haifi abba amma an gaje min shi.tace yarinya duba nan.bishira ta dubeta,ta dafe qirjinta ni na haifi abba nine uwansa.matan gidan can mai gidana ya bada shi a gunta,da ubansa da maigidan dan wa da qani ne amma sun gaje shi.bani da ikon sashi ko hanashi amma sun mallakemin shi. da muryan tausayi take maganar. Bashir yace, umma indai ya aurota xamu samu sauqi.bishira tace kada ki damu, insha allah komai xai warware. tace, to yan nan na gode.fati ta shigo ta gaidata cikin nutsuwa, bishira tace wannan qanwansa ce? umma tace eh, ai su ga sakamakon mugunta nan sun haifi yar muguwa mara jin magan. bishira tace, kai yarinyar bata ji. fati ta ce abba ya ce kixo.sahura tace kinji ko? shifa ko nan gidan baya qaunan shigo wa.bishira ta miqe ta balle jaka ta ciro sabbim kudi yan ashirin ko irgawa bata yiba ta bata, tace kinsaya goro.sahura tace harda abin arxiki?to an gode.bashir yace antyna inane gidanku?tace karkasana gidan kwamishinan gona.bashir ya raxo ido, nako san gidan,lalle antyna ina qara gaisuwa.bishiratayi dariya.abba na tsaye suka fito,yace mata to ki tafi xanxo amjima. tace baka kaini dakinka ba.ya girgixa kai, bai dace ba wannan ba mutunci bane,sam bai kamace yar mutunci suna xuwa dakin samari ba. bishira tace danme? yace sharia bata amince ba, damin duk lkcn da mutum biyu suka kebe,musamman mace da namuji. Abba yace na ukun su shedan ne. irin wannan yana haifar da xinace xinace a bayan qasa.tace hakane ta tafi.abba ya rakata har mota, bashir kuma tamkar maroqi, sai fadi yake allah ya tsare antina ki sauka lfy.bayan tafiyanta abba bai iya shiga gidan ba tunaninshi daya kada umma ta xargeshi.dan haka ya nufa gidansu ahmad.ya ba ahmad lbrn abinda ya faru.dariya ahmad yayi tayi.yace kai amma wannan ummin taku yar dirama ce. abba yace cikin takaici yanxu kai har kaga abin dariya?yaja tsaki yace allah na tsana ummi, namata muguwan tsana. dubi wannan yarfin da tai mani. ahmad yace xata bari, wata ranama ko ance tayi watace sam batayi ba.abba yace taf wannan yarinyan dawuya in xata taba yin hankali, duk wanda ya aureta ya auran ma kanshi fitina.ahmad sai dry yakeyi. da magariba ya shiga gidan,cikin saa ya samu ummi tana cin abinci.nan take ya kama hannun ta har saida tayi yar qara, yace muje ki dauko min kwalin kaset din da kika dauka, Umma tace, Abba na soma tunanin yarinyar nan tan da aljanu da gaske. abba yace hakama alhaji qarami yace, amma fa anje babu kowa akanta. ya saki ummi bayan ya ranqwasheta. sannan ya ce, in kika sake yarda ki kaga wani abu a dakina kika dauka sai na balla ki. washegari abba ya tasa ummi ya nufi gurin masu ruqiyya, amma da aka mata babu kowa a kanta kamar yadda ya xata. ya dawo ya sanar da umma,umma tace na gode allah.halinta ne ita kuma irinta kenan? yace irinta kenan umma,baxata canxaba saidai muyi ta mata addua, soyayyan abba da bishira ta bunqara,har dangin abba sun san da batun,sahura duk tabaxa ma dangi.sanadiyyan maganan da tayi ma bushiran na cewa an rabata da daxta. wata rana bishiran tace masa xata xo gaida ummanshi,yace to cikin xumudi sai tace, umman su bashir fa nake nufi, ba ance ita ce mamanka ba? abba ya ce inji wa? inji ummanka. abba yace sam, ummana ba xata fada miki ba sai dai ko ita umman bashir din. tabbas itace ta haifeni, amma ba itace ummana ba.tace dan me? nan take ya hada rai. Abba yace mata ba matsalanki bane, so ban so ki saka kanki ciki. nan take ta yarda da batun umman bashir.ta a mince qwarai umman da abba ke kira umman shine muguwa ce.kuma itace ta raba abba da umman shi.dan haka saita tsiri xuwa gun umman bashir, tare da yi mata kyauta.shiyasa suka saba sosai.duk xuwan da bishira xatayi sahura saita kukkushe umman abba, tare da yi mata sheri. dan kawai bishira ta tsaneta,kuma bata xuwa gunta koda taxo anguwan. abba bai taba sanin haka ba,ita kuma umma bata taba fadan mai ba, dan ummi ta taba fada mata cewan budurwan abba tana xuwa gun umman bashir kuma bata xuwa gunki. umma tace nida umman bashir duk daya ne intaxo gunta tamkan taxo guna ne. sai kuma habaicin da take jiyowa ta katanga sahura nayi.har ya kai umman abba na ganewa in bishira taxo, domin inxata tafi xakaji umman bashir tana cewa,to na gode yar albarka bakya gajiya da abin arxiki,ai ko baki kawo min komai ba yancina da kika fara qwato min kin biya ni. kuma ina tabba tan maki inkinga abba bai aureki ba baya ry/ ZURFIN CIKI book 1 part 4
    ZURFIN CIKI book 1 part 4
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:45
    Wannan furucin ke sa bishira na qara shige ma
    sahura, duk wannan sha'anin da sukeyi abba bai
    sani ba. wanci tashi abba ya samu digree,
    sannan yaje kamp din shi a damaturu jihar
    yobe.sati biyu yayi sannan ya dawo. cikin sati
    biyun nan da baya nan ummi ta baxa iya
    shegenta son ran ta, umma ta qosa abba ya
    dawo saboda yanxune ta gane tsoran abba yake
    sa ummi tayi mata aiki da aike.dan tasan in ya
    sani baruwan shi da pushin tsohuwa,xai
    nakadetane, amma ahj da umma duk abinda
    ummi tayi daxaran xasu hukunta ta xata sa masu
    kuka tace dan de aci mata xarafine.shi yasa suka
    sakama ummi sunanta,sannan kuma suke
    dukanta a gabanta,imba hakaba maisa basuyima
    mai sunnan malan ba?dan dole suke qyaleta ,duk
    da ummi ta soma tasawa amma sam bata yi
    hankali ba. shekarun ummi sha uku tana js2
    amma ko yaushe qara tirewa ummi keyi. addua
    kurun sukasa agaba,kuma sunsan allah xai amsa
    masu. Ranan da abba xai dawo ummi ta kama
    yima umma aiki da aike, dan kar a fadama abba.
    a ranan ne ummi taga wata alama da ta
    tsoratata cikin fitsarinta. a rudenta da hauka ta
    nufi gun umma tana cewa, umma na shiga uku
    na, fitsarin jini nake yi. umma tace, wane irin
    kuma fitsarin jini? ummi sai tsalle take tana fadin
    ta bani ta lalace. umma tace ke xonan. ta jawo
    ta xuwa cikin daki, tace ke yimin bayanin yadda
    kika ga abin. ummi ta cire xani xata cire siket.
    umma tace, ke dakata min bance ki nuna min ba,
    yaya kalanshi yace? ko da tayima umma bayani
    sai ta fahince girmane ya kama ta. dan haka sai
    ta kamo ta ta xaunar kusa da ita, tayi mata
    bayani game da abin data gani, sannan ta nuna
    mata hadarukan da take ciki a halin yanxu. tace
    ummi ki natsu kiyi hankali, kisani yanxu kinkai
    wani matsayi wanda xakiyi taka tsantsa da
    rayuwanki. hadari na farko shine wasan banxa da
    maxa, kece mara hankali indai kin sama abokin
    wasa ba ruwanki da maxane ko mata ke dai kiyi
    wasa, Umma tace kisani yanxu xaki iya daukan
    ciki, indai har kika bari wani namiji ya shiga
    harkanki. ummi tayi xullo tace umma ciki irin na
    bara'atun baito? umma tace, eh ummi tace
    wanda har suka yar da yaran aka xo aka kama
    su yan sanda? umma tace tabbas. ummi cikin
    fargaba tace to ni umma baxan yi ba. ta soma
    kuka, to a kaini asibiti a bani magani mana.
    umma tace duk bayanin dana maki baki fahinta
    ba? ai wannan kin dunga yinsa kenan har
    qarshan rayuwanki, ko kuma in kinkai wani
    mataki na tsufa. ummi tace, to shi kenan, yanxu
    kuma inna yi wasa da maxa sai in xama irin na
    bara'atu? umma tace qwarai kuwa. ummi tayi
    tagumi tana tuna yadda suke tsokanan bara'atu
    inta fito. suna cewa tayi cikin shege tayi cikin
    shege! ta dubi umma tace xan daina ma yan
    maxa magana. umma tace ki dinga maganarki da
    kowa, kidai kula da kanki, sannan duk sokanan da
    kikayi da xunubin da ki ka kwasa to fa ki sani an
    bude maki fayel. Umma tace xunubinki xaki
    samu,gashi bakya san sallar kan lkc, sannan ga
    karya axumi.ummi ta sake tsurewa ,tare da fadin,
    to ba tsohuwa tace min inna mutu baxa ayi min
    hisabi ba,wai ni yarinya ce wai makarantan
    annabi ibrahim xa a kaini.umma tace da kenan
    kafin ki soma kalar wannan fitsarin, yanxun kam
    in kin mutn xa a tambaye ki a cikin kabari,
    tambayoyi uku masu sauqi, masu wuya agun
    mara rabo.sannan xa a maki hisabi inkinyi mai
    kyau kiga mai kyau. tayi tagumi, umma ta manna
    mata tsumma a jikin pant. tace tashi kisa in
    kuma kinje gun haukan guje guje ya fado mutane
    sun gani shi kenan asirin ki ya tonu, kowa yasan
    kin girma. ummi dai ranan lafewa tayi kan kujera
    tanata tunani. tana kwance lkcn da ake hayaniyan
    dawowan abba kannanshi ne suka shigo mai da
    kayansa. qasa ya xauna a dakin umma, ya miqe
    qafa domin duk a gajiye yake. umma tayi ta dire
    mai abubuwan ci wanda tasan yanaso a gaban
    shi. sannan ta ba fati kudi ta sayo mai lemun
    kwalba, dariya yayi ya ce,ni dan gatane, shiyasa
    ina can ina tunaninki ummana, har nace inama
    ana tafiya da uwa da na tafi da ke.umma cikin jin
    dadi tace allah sarki abba, niko ina nan ina maka
    addua allaih ya baka abin da kaje nema,yace
    ummana kenan. ummi dai tana jinsu sam baima
    gantaba, sai can ya lura yace a,a kekuma lfy?
    umma tace bata dan jin dadine. yace tabdi,lallai
    kuwa ciwan nan yayi tsanani, ummi da ko a
    gadan asibiti take bata daina halinta? umma tace
    ai yanxuma nasan lafawa yayi ko ummi na?
    ummi dai kallansu take yi. abba yace allah ya
    yaye. suka ci gaba da firan su yana bata lbrn
    camp tare da nuna mata hotunan da suka dauka.
    yace dan ba kusa bane da kunje min kunyi kallo.
    ummi da xata bayi sai tafiya take wani iri tare da
    ware qafa. saboda rashin sabo. tsohuwa tace a,a
    takwara lfy? ummi tace, fitsarin jinin nake yi.
    umma ta fito da sauri tace ke ummi xo. tsohuwa
    ta saka salati, tare da cewa yarinnan nan badai
    faduwa kikayi ba. ummi tace nifa ban fadi ba
    hakanan ya xo min. umma tayi mata daquwa
    tace bayin kenan? tsohuwa tace ke suwaiba
    yarinyan nan faduwa tayi? da yake umma ta
    fahinci hausanta sai tace um,lkcn tane yaxo.
    tsohuwa ta saka salati tace, ni habiba yau naga
    abinda ya isheni? yarinyan yar shekaru nawane
    kwata kwata. lalle xamani, to sai ayi axaman
    aurad da ita. umma tace waxai kula ummi da
    sunan aure ni suwaiba? ki kalla haukan data keyi
    a gari. abba cikin daki yace umma wa tsohuwa
    take cema ayima aure? umma tace ummi itama
    cikin dariya. yace tabdi jam to wannan takwaran
    taki waxai kwasa, ga muni ga rashin hankali.daga
    bayi ummi tanata murguda mai baki tana cewa
    eh din. Tsohuwa kuwa masifa ta hau yi,"gaka nan
    mara mutunci a gabana kake zagin takwara?kai
    mai sunan malam ka kiyaye ni" shi dai ya fita ya
    nufi dakinsa don kintsawa,yana mamakin ummi
    ta zama babba. Koda umma bata fada mishi ba
    ya gane haka ne ta yadda tsohuwa tayi maganar.
    tsohuwa ta dubi umma ta ce,"ki na daure ma mai
    sunan malam gindi yana ci ma takwara kashi a
    hannu,alhalin yana zaune a inuwarta.nan fa gidan
    ubanta ne." umma ta bata rai matuka,ta ce
    "tsohuwa ni da Abba da ummi duk daya suke a
    gurina,don Allah kada ki kuma furta haka har
    Abba yaji. kai ni da za a ce in zaba tsakanin
    ummi da Abba,na rantse Abba zan dauka."bata
    jira abinda tsohuwa zata ce ba,tayi ciki abinta.
    tsohuwa ta gama yan mitocinta ta shiga daki.
    Kwana biu kamar gaske,ummi an nutsu, amma
    abinda ya takura mata na daukewa sai umminku
    ta ci gaba da gashi, sai ma abinda ya karu. Abba
    ya daga ido sama yana kallon wasu tsuntsaye
    suna ta shawagi a sama, zuciyar shi tana cikin
    matukar damuwa sakamakon sheshshekan kukan
    da bishira keyi, bata san cewa ya fita damuwa da
    tafiyarshi kaduna ba? in ma da don ta ita ne da
    sauki tunda gidansu da waya zai iya zuwa
    (telephone) na bakin titi ya kirata. damuwar shi
    umman shi. ta katse shi "yanxu Abba haka zan
    daina ganinka?" ya sake tausasa murya."haba
    bishira, ina kano ina garin kaduna?" ta ce, "tabdi,
    nifa dalilin kukana taron matan kaduna nake ji, an
    ce kwarjini garesu. kawai kaje ka sa samu wata
    ka manta da batuna." Yayi murmushi "bishira
    kenan, kada ki dauka son da nake miki mai rauni
    ne da har zan canza wata dake, ni dai ki min
    addu'a." ta ce,"sam ban yarda da wannan zancen
    ba, ni dai bari in kira antina mijinta zai iya
    taimaka maka a barka kano." kafin ya ce komai
    tayi ciki da gudu. yayi yar dariya. bishira tunda
    ya ce kaduna aka tura shi duk ta damu. Anti ta
    fito daga kicin, bishira ta ce, anti kizo inji Abba.
    anti ta dubeta, "in zo?" bishira ta kama hannunta
    "don Allah aunty taimako zaki mana, zo ki ji." 49-
    suka xauna sannan abba ya gaidaa anti cikin
    girmamawa.bishira ta dube shi ka fada
    mata.abba yace me?tace anti kinga fa kaduna
    aka tura shi,ni kuma wlh ba xan so yaje garin nan
    ba.anty ta sa dariya.to yanxu so kike yaqi xuwa
    ko so kike ya tafi dake? tace,ni so nake ki yima
    abban nasir bayani,nasan ba xai rasa sanin wani
    da ya sani ba.abba da anty suka sa dariya,yace
    kamar yaya?tace yayi magana a barshi anan
    suka sake tuntsira dariya.tayi fushi ta miqe fuuu
    ta nufi cikin falon gidan.anty tace bishira tana
    matuqan sanka,dan allah ka kula da ita.ya kalleta
    ya sunkuyad dakai,yace nima anti ina santa,kuma
    tuni nasa manya susan xancan,saboda in samu
    natsuwa,amma tace tana jin tsoron
    mamanta.anty tace eh to,dole taji tsoro dan ba
    dole bane hjynmu ta yarda,amma shi babanmu
    bashi da matsala.abba yace to ni dai xan tura a
    kowane lkc,dan ahjna yayi min magana tun kafin
    tafi ta camp. Din nan yake ta min zancan." Aunty
    ta ce,"to in kun tashi fa ba gurinshi za'a tura
    ba,gurin kaninshi ne dake jakara.amma kafin
    hakan sai an nemi izinin Alhajinmu din." Abba ya
    ce,"to ni ko wa zai shige min gaba gurin neman
    izinin?"aunty ta ce,"Abban nasir zan sanar
    dashi,insha Allahu har wannan din ma batun
    (service)din naka zan mishi bayani." cikin murna
    abba ya ce,"to na gode,Allah ya saka da
    alkairi"anty ta ce,"ba komai" ta mike "bari in turo
    ta don nasan tana can tana cika sai ka bata
    baki." yayi yar dariya tare da cewa"to". ta zauna
    tana kumbure-kumbureya ce"haba tawan har
    yanxu baki huce ba?" ta sake kauda kai gefe,ya
    ce"to shi kenan,yanzun dai na fasa barin
    kaduna." ta dube shi da sauri,"ka fasa barin
    kaduna fa ka ce?" yayi yar dariya"au na
    manta.kece duk kin ruda ni,cewa zanyi na fasa
    barin kano." ta share yar kwallarta,"to shikenan"
    ya ce,"naji dadin kiran anty da ki ka yi.ina ganin
    nan da yan kwanaki su Alhajinku zasu sanni,Allah
    yasa ace an bani ke." Wayyo dadi,ta tuntsure da
    dariya.abbana nawa,bana zaton cewa zaka kai ni
    murna a ranar."ya mike zan tafi "ta ce tun
    yanzun? to ka ce ina gaishe dasu umma." Ya
    ce,"umma bata cin mike,kullum sai ta ci in gaishe
    ki da kyau.amma ke kin ki zuwa gaida ta." ta
    ce,"kasan fa ni bana iya sakewa da ita,nafi
    sakewa gurin umman bashir." ya ce,"kunyarta ki
    ke ji?" ta dan tabe baki tare da daga kafada kila.
    ya ce,"ina mamakin yanda kika saba da umman
    bashir,alhalin ummana tafi saukin kai." ta ce,"ga
    wannan kanwar taka mara kunya." ya yi yar
    dariya sabida tuno abind ummi ta musu. ya ce a
    hankali,"zaki saba da halin ummi."ta dube
    shi,"tun ranar dana soma ganin ummi din nan fa
    ban taba jin cewa ina sonta ba." ranshi yadan
    sosu,har ma ya gimtse fuska,amma baice kala
    ba.lura tayi da canzawarsa.don haka sai ta ce"ka
    min afuwa in na bata maka." nan ma bai amsata
    ba.illa sai da safe. Tamkar Alhaji yasan yadda
    abba suka yi da antin bishira,da safe Abba yaje
    gaida shi ya ce,"babana zuwa yanzun ya kamata
    a ce mun shiga maganarku da yarinyar nan."
    Abba ya sunkuyar da kai tare da ce wa,"um,dama
    gidan antinta da naje dazu munyi zancen,yanzun
    dai su ce sai an nemi izinin shi baban nasu. ta
    ce,mijinta zai masa magana,in yaso sai kuji ranar
    da zaku je din." Alhaji ya ce,"to shikenan.Allah ya
    kai mu.yanzu yaushe zaka tafi kaduna?" kafin
    abba ya bashi amsa,ya ci gaba da cewa,ban so
    ba sam da wannan yin nisan da zaka yi damu
    Abba." Abba ya ce,"ina hasashen cewa za a barni
    nan kano da yardar Allah,bisa ga taimakon mijin
    yayar yarinyar da nake zuwa gurinta." Alhaji ya
    ce,"to Allah ya yarda,sannan in an fada maka
    lokacin da zamu gana da waliyyan nata sai ka
    sanar dani." Abba ya ce,"to." Alhaji ya ce,"ina son
    mu danyi bincike kan yarinyar amma mahaifinta
    sannanne ne,anata yabonshi." Abba ya ce,"to."
    Ranar juma'a da misalin karfe biyu da rabi Alhaji
    ibrahim (wato abban nasir,mijin anty farida),ya
    samu sirikinsa a gida. bayan sun gaisa ya
    tambayi yan jikokinshi sai Alhaji ibrahim ya
    ce,"suna lafiya.dama makasudin zuwan shi
    ne,akwai wani yaro da ke zuwa gurin
    bishira,yawancinan gidanmu suke zance. to
    gaskiya na yaba da hankalin yaron,sannan ya
    damu yana son ya turo iyayensa.to shi ne nace
    bari in nemar musu izini tukun." mahaifin bishira
    ya kalli surukinsa ya ce,"aisha ko bishira?" Abban
    nasir ya ce,bishira ce." ya gyara zama. "bishira
    ta gama sakandare ne?" Abban nasir ya ce,"ai
    Alhaji ba yana nufin ayi auren yanzun bane,a san
    dashi ne." Alhaji ya ce,"bana haka,ka sani sai dai
    tayi abu daya,in karatun karatun,in auren to
    auran. Ibrahim kasan wani abu daya? duk lokacin
    da kasa yarinya ta soma tsayawa da saurayi
    bayan tana karatu,musammanirin bishira irin
    wadda tasan tsarina amma ta danne ta turo min
    saurayi to gara ayi mata auren. Domin doguwan
    soyaryannan bata da ma'ana,qarshe sai wata
    shedana ta biyo baya,balantana bishira tana da
    rawan kai.ya matsa kusa da wayan tangaraho
    wadda aka jona ta ke amfani a daukacin gidan,ya
    dannan nanbobin sannan ya kira hjy.ta amsa
    daga sashanta,yace bishira na ciki? tace tananan,
    yace ki turo mani ita,tace to.gaban bishira ya
    badi,ganin mijin yarta a gidan dan tasan abinda
    ya kawo shi.ta xauna can gefe tace,gani dady,ta
    gaisa da abban nasir.mahaifinta yace nasan
    kinsan dalilin xuwan ibrahim ko? kanta a qasa
    tace,a'a. yace.yace to saurayin da ce xuwa gunki
    ne yake san ya turo magabatansa,kuma nasan
    kinsan da batun?sai dai inasan kisan abu daya
    bana san doguwan soyayya,da xara nagama
    buncike akan yaran wanda shari'a tace.inna
    gamsu,to fa aurad dake xanyi kije can ki qarasa
    karatun in kina so.ahj ibrahin yace yaran yace shi
    ba dole sai anyi yanxu ba.nufin shi a amince
    mashi.shi kuma xai jira har ta gama
    makarantanta. ahj ya katseshi ta hanyan daga
    mai hannu,ibrahin kaidai sheda ne bewan bana
    haka, kuma ba a haka dani ko?yace auran yata fa
    kakeyi,ka san tsarina.ibrahinyace na sani ahj.
    yace yauwa,ina nan ban canxa ba.yace yanxu
    abinda nake san ka dashi kafin na amince da
    xuwan iyayan shi.ya dubu bishira yace kinasan
    shi kin amince dashi? tace eh yace tashi ki tafi
    angama.kai kuma inasan kashiga unguwa uku ka
    binci komin labarin yaran da usilin shi.ahj ibrahin
    yace angama.yace naso ace sai ta gana
    karatu,dan sai anyi sa'a xata qarasa,anma hakan
    xaifimin akan doguwan soyayya kafin inxo inajin
    haushi.ibrahin ya miqe to ni xan tafi.ahj shima ya
    yunqura xai tashi sai waya ta kama ruri dan haka
    sukayi sallama anan. ummi ta shiga gida daga
    makaranta take,akuyan umman bashir tagani ta
    gani a gidansu tana masu barna a kicin da sauri
    ta koma ta saka sakatan gidan,sannan ta
    dawo.ta kama akuyan ta kaita bakin fanfo ta tara
    kanta sai kuka akuyan take tayi. Umman bashir
    ta jiyo daga gidanta,da sauri ta fita taxo tana
    buga gidan tana mashifa.yan baqin
    ciki,mahassada,yanka min akuyan xaku yi?san
    ummi bata ji ba, dan gidan ba kowa. umma taje
    sheka can gidansu,hta kuma tsohuwa taje
    gaisuwa n mutuwa nan kusa dasu.saida taga
    akuyan ta galabaita sannan ta janyo wata leda ta
    daura mata a bindi,sannan ta saketa.akuyan ta
    tashi da gudu tayi hanyan fita,tace shegiya gobe
    kixo ki bude mana abinci kici.taje ta bude qofar
    ta jiyo muryan umman bashir,dan haka sai ta cire
    sakatar sannan ta dan sanmata qofan akuya tayi
    waje da gudu.saboda ledar da ummi ta qulla
    mata,sai take ganin kamar binta ake,dan haka ta
    nausa cikin unguwa da gudu.umman bashir na
    ganin akuyarta tayi fitan bindiga,sai tabi tana
    cewa,ku taremin.ummi ta koma ciki tana
    dariya.ita kuma umman bashir daqar ta samu aka
    ruqo mata akuyan ta.aka kwance ledan taruqo ta
    xuwa gida.sai masifa take, tana isowa qofar
    gidan umma na RFIN CIKI book 1 part 5
    ZURFIN CIKI book 1 part 5
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:54
    Ita kuma umman bashir daqar ta samu aka ruqo
    mata akuyan ta.aka kwance ledan taruqo ta xuwa
    gida.sai masifa take, tana isowa qofar gidan
    umma na isa. tace yar baqin ciki kun kama min
    akuya kun jiqata xaku kashe min,ta ta allah ba
    takuba.umma tace akuya kuma wani iri?ni bana
    gidan dawowa ta kenan.ta ce kina nan muna
    fuka.umma sai ta shige gida,amma duk da haka
    sai da umman bashir ta bita har ciki tace sai ta
    doke mace akan akuyan ta.umma ta shige daki
    can qurya tasamu ummi a kwance,tace ke uwar
    yan daukan magana, ke ce kika jiqa mata akuya?
    umma tace cinye min abinci tayi.nan abba ya
    riske ta tana ta tsine tsine.yace meya faru?tace
    kai ja can ka bani guri,dan baka san darajata
    ba,banda an raina ni yaya xa'a kama min dabba
    a jiqa?in nai magana sai a maidani mahaukaciya
    ko haquri baxa a ban ba.abba yace to kiyi haquri
    in sha allah baxa a qara ba.tace baxan haqura
    ba,tunda inta mutu nike da asara.umma tafito
    tace to yanxu ya kike san ayi?ni dai bananan
    ummi ce da wannan tsiyan wai ta sameta ta
    cinye mata abinci. umma tace kinsan halin ummi
    kuma nima haquri nake da ita.tace to ni baxan
    iya haqurin ba.umma ta finciko ummi ta hanka da
    mata.ta gata na ki rama mata.ta juya cikin daki
    ta kama harko kinta.ba kunya ta kama ummi
    tana ta jibga.abba takaicin mahaifiyan shi ya cika
    mai xuciya,amma bashi da daman cewa ta
    bari.shin baxa tai tunani ba takama yar matan da
    tariqe mata danta riqon adalci da amana,tana
    duka haka? sai data gaji dan kan ta sannan ta
    fito.abba ma fita yayi cikin takaici,ummi kuwa
    kuwa tayi tayi har tsohuwa ta dawo,ta sameta
    xaune tana dirxan kuka. Dama taci karo da abba
    a waje tace mai sunan mlm har ka dawo xaka
    kuma fita?yace um.tace miskilin banxa saikace
    mai ciwon hakori,ta riska ummi tana kuka,tace
    umhum daman tunda naga ya fita yana ta
    maxurai nasan yaci xalinci.kai na gaji da halin
    mai sunan mlm.umma tace,ba ruwanshi.ummi
    taqara satin kuka ba umman bashir bace taxo
    tayi min duka.meki ka mata?wai din akuyan ta
    taxo ta cinyemin abinci,shine na jiqata da
    ruwa,shine taxo tamin duka kuma gashi banci
    komai ba, ko qala bata ceba,ta juya sai gidan
    umman bashir.ta sameta tana sinke kayan
    miya.tace ke sahura saboda bakida mutunci shine
    xakixo har gaban uwarta ki daka?sahura tace na
    daketa,kamme xata jiqa min akuya?tace wane
    shegen ne yace ki saki akuyan ki har taje taci
    mata abinci?to kashedin ki mara mutunci da baki
    san girman nagaba ba.bashir ya fito yace a'a
    tsohuwa kidaina xagan mana uwa har cikin
    gidanmu.tace iye!kaxone ka nuna min rashin
    tarbinyan ka?nan har wata uwa gareka?nanfa sa
    in sa ya tsarke a tsakaninsu.ummata juyo su
    tarasa yadda xatayi,sai ga abba ya shigo.yauwa
    abba shiga gidan can ka lallaso min tsohuwa taje
    kasgedi ataba yar gwal dinta.ta dubi ummi tace
    duk aka yar marajin can ni naji dadin dukan da
    tayi mata,dan dukan algaki tayi.banda xalunci ya
    xata kama dabba ta jiqa? abba ya fita ba tare da
    yace qala ba. abba na shiga gidan bashir yana
    tsigale tsohuwa tankar xai kai mata duka,abba ya
    daga hannu ya wanka ma bashir mari,sannan
    yace tsohuwa saankace da xaka dunga mata
    wannan fadan.ya dubi umman bashir dan allah
    kiyi haquri.sannan yaja hannu tsohuwa,shi kuma
    bashir yana ta xagin abba yana cewa allah ya
    isa. umman bashir ta ce abba tir da hauhuwan ka
    tir!tir! kuma gab nake da in dagama ka nono.cak!
    abba ya tsaya kalaman mahaifiyan shi sun shi
    jeshi,a hankali ya saki hannun tsohuwa batare da
    tasan ya tsaya ba.dan sababin da takeyi yaja
    hankalinta.ya juyo har gabanta yace dan allah ki
    yafemin ki ya femin.ba tareda ya jira amsan ta ba
    ya fita. baiji muryan taba amma koda bata ya fe
    maiba jikinta yayi sanyi.da yamma bayan su ahj
    babba sun dawo kasuwa sai suka shiga dan
    gaida tsohuwa.nan ta saka masu kuka suka rude
    tare da fadin me aka mata?cikin kuka tace ni
    sahura xatai ma rashin mutun ci tare da danta
    bashir nan ta koro masu bayanin komai. Ahaji dai
    sukai ta bata haquri,ahj qarami yace shi kam dole
    ya cimata mutunci daga ita har bashir din.da
    suka fito ahji babba ya ce kada gaje ka mata da
    tsin hankali,nashihaxaka yi mata shi kuma bashir
    ya girmama yayansa.abba kuwa yana fita sai ya
    bar layin dan bacinrai,dakin ahmad yaje ya
    kwanta duk da cewan ahmad din bayanan.tunani
    yake tayi akan mahaifiyanshi,yadda ta runtse ido
    da alkairin da umma da ahj suke mata.ahj qarami
    cikin damuwa da takaici ya shiga gidansa,da
    bashir ya soma yin karo,nan take ya rufeshi da
    fada.sahura na ji ta taso cikin mashifa kada ya
    xagan mata da,dan ya nemi tare mata
    mutunci.ahj yace har wani mutunci ne dake
    wanda xai kare maki?to da kinada mutuncin kin
    tunkari mahaifiyata ki mata cin xarafi?tace har
    gidannan ta shigo saboda na daki yar gwal
    dinta,takan wannan wara mutuncin yarinyan xata
    xo ta xage ni?umma tace ma ahj babba ka fito
    gashi can fa ahj qarami rigima ta kaure
    tsakaninshi da umman bashir.da qyar ahj babba
    ya kashe wutan,abba da ya dawo yaji hayani ma
    mahaifanshi sai ya qara barin layin sai can sha
    daya na dare ya dawo ya kwanta,ranan ko abinci
    bai ci ba.da safe yana gaban umman shi yana
    fada mata kalaman da umman bashir ta masa
    jiya,una ta ce ashsha,kai banji dadin wannan
    kalaman na sahusa gare ka ba.saidai na gode
    daka nemi yafiyanta,sannan ka kiyaye duk abinda
    xaisa tayi maka munmunan furuci.dan bakinta
    dafine a gareka.kada kaga cewan baka yimata
    komai ba,to intayi ma mugun furuci sai
    kamaka.yace xan kula,tace yauwa abba.saka
    makon binci ke da mahaifin bishira yasa amishi
    iri daya da wanda sirikinshi ibrahim yayi
    mishi,ma'ana halayan kirki da mutuncin iyayanshi
    da shi kanshi yaran.duk dadai ance masa ba
    wasu masu hali bane?sai rufin asiri da suke da
    shi.wannan bai dameshi ba tunda dai ance mashi
    yaran yana neman na kanshi,sannan yana karatu.
    to tunda tana sanshi ba ruwan shi. ya kira wayan
    cikin gida ya kira hjy sai yaji sallamanta ta turo
    qofa.yace yauwa dama ke xan kira.ta dire tire
    mai dauke da kayan shayi akai,sannan ta xauna
    tana gaishe shi. Ya amsa sannan yace ina jin
    gobe masu neman auran bishira zasu je wajen
    yaya a jakara. Hajiya zainu ta gyara zama,"ka ce,
    bishira ko Aisha? ya ce bishira dai tayi yar dariya
    yaushe bishira tayi saurayin da har zai turo? ya
    ce,"a'a ba ki sani ba? ta ce,"na dai ji yanzun" ya
    ce to na basu izinin turawa tun jiya tunda tana
    sonshi babu ruwana da doguwar soyayyar nan
    kin sani Hajiya zainu ta hade rai,"amma kana
    sane da cewa ss2 zata je ko? ina laifin ta gama
    sakandare? Tace ,"gaskiya ranka ya dade ka bar
    batun auran bishira." ya dubeta,"kada ki damu
    kanki fa.don kin san ba zan canza ba" ta bata
    rai,to dan wanene? shima ya daure fuska dan
    babanshine.ta mike a fusace ta fita sai dakin su
    bishira. Lokacin suka farka daga baccin da suka
    koma bayan sallar asubahi.ta ce,"ke bishira,ke ce
    kika turo saurayinki gurin dadynku? wai yaushe
    ma kika yi saurayin? Aisha tayi zaraf tace, momy
    kin ma san wanene? hajiya zainu ta ce,"wanene?"
    Aisha ta ce telanmu Abba din nan." Hajiya zainu
    ta saka salati Abba tela? tela fa? Aisha ta
    ce,"tela kuwa" hajiya zainu ta isa gurin bishira ta
    rike mata kunne. "kece kika zabi auran tela? me
    ya ci shi kansa bare ya baki? zai iya da
    karatunki? wallahi tun wuri kije ki fada ma
    dadynku bakya sonshi." Bishira ta ce,"nifa shi
    nake so momy."hajiya zainu ta rufeta da duka.
    washe gari su Alhaji babba da abokinsa Alhaji
    sani,sai makocinsu malam ma'aru suka je
    nemawa Abba auran bishira a jakara gidan Alhaji
    musa wan mahaifin bishira. an amshesu hannu
    biyu,sunyi magana ta fahimta an basu,kuma sun
    karba.an yanka sadaki da dukiyar aure,sannan
    sunce suna so za'a hada da yarta. Su Alhaji suna
    ta godiya nan dai gemu da gemu suka rabu cikin
    mutumta juna. Hajiya zainu ta dauki karan tsana
    ta dora ma bishira,tunda tayi-tayi cewa ta janye
    batun auran Abba taki,ta ce to bazan miki komai
    ba.sannan in babu ta sameki kada ki ce kin
    sanni,in ki ka zo nan gidan da sunan neman
    taimako saina wulakanta ki. Duk bishira dai ta
    yarda,nan aka sa rana kusan wata shida. Abba
    ya iso kofar shagonsu da sauri don hangen da
    yayi gurin ya cika da jama'a,yana zuwa sai yaga
    ashe ummi ce tazo wucewa ta taba wani shagon
    fale-fale ta taba sai yayi mata shocking. shikenan
    ta tsaya tana jiran wa zai zo tasa shima ya
    taba,can sai ga wani yaro,tace kai ka iya karatu?
    yaron ya ce,"eh" ta ce karya kake in da gaske ne
    nuna mun acan.da gudu yaro yaje ya dangwala
    dan yatsa a kan A sai ko shocking ya debe shi ya
    jefa kwata. Ashe yayan yaron na kallonta sai ko
    ya biyota shine ta fallo da gudu ta fada
    shagon,shi kuma y ce sai ya duketa. Abba ya
    kalleta kallon tsana ya ce,"fito shegiya ya
    hankado ma yaron ita ya ce ka mata dukan tsiya
    yaron ya ce na hakura ta ci darajarka Abba ya ce
    don Allah ka duketa,don wannan bata da wani
    amfani daya wuce duka. yaron ya ce,ku dai ku ja
    mata kunne don kar taje tasa dan wani a
    matsala,ko ma ya rasa ransa,domin shocking zai
    yi kisa nan da nan. Abba ya ce dama zai kasheta
    ai da munyi murna.ummi ta kalleshi a ranta ta ce
    sai kazo ka kashe ni. Bayan kowa ya watse na
    nan yasata tsalle kwado. Ahmad abokin shi ya
    shigo shagon ya ganta tana ta tsallen kwado ya
    ce a'a Abba meye naka nasa mace irin wannan
    horon? Abba ya ce kasan Allah da ace yarinyar
    nan namiji ce da tuni na zuga an kaita gidan
    horon yara,kaini da in kayi kisan kai babu laifi da
    sai na ba yarinyar nan gamalan 20 tasha ta
    mutu. Ummi cikin kasa-kasa da murya ta ce
    nima da zaka mutu a dadina. Ahmad ya ce haba
    Abba ya kake irin wannan maganar? ya dubi
    ummi tashi ki tafi abinki.ummi taki tashi don
    tasan in don Abba ne sai ta tashi ya ce ta sake
    sabon lale don haka sai ta ci gaba da tsallan
    kwadonta. kuma bata nuna kasalarta domin ya ce
    sai taji jiki tukunna zai barta. wannan ya shigo ya
    ce Allah sarki ai mata hakuri wannan ya shigo ya
    ce don Allah a kyaleta.sai kurum ta saka kuka. da
    kyar Ahmad ya shawo kansa har ya ce ta tashi
    ta tafi.ya ce kuma inta yarda yazo gida ya samu
    tayi wani laifim shi da ita ne.daf da magrib yana
    sauri za shi masallaci sai ya ganta da dan tasi
    tana kasa shi kuma yana tuko motar a hankali
    yana ce mata an kusa gidan tana cewa eh. bata
    lura da Abba ba saida ya ce ke ina zaki? da sauri
    ta fice da gudu dan tasi yace ke yarinya zo nan.
    Abba ya matsa gurin shi ya ce malam lafiya? dan
    tasi ya ce yarinyar can ce ta taro ni tun daga
    bakin titi.wai an aikota ta kira dan tasi za'a dauki
    kaya zuwa wambai. nan na dibo fasinjan cikin
    gari ne ma sauke su tare da basu hakuri,to da
    mukazo hanya sai tace mun jaki ne za'a dauka
    nace jakin lafiya? ya ya za'a iya saka jaki a tasi?
    ta ce mun ita dai tashi aka ce mata ta taro,kuma
    nayi-nayi ta shigo motar taki. Abba ya ce,kayi
    hakuri karya takeyi,kanwata ce.wallahi bata ji.
    dan tasi cikin takaici gashi ya sauke fasinjanshi
    yajuya ya tafI. Abba ya nufi masallaci yana
    kyalkyata dariya.don shi lamarin ummi tsoro ma
    ya soma bashi jaki a tasi.kai shima dan tasin
    mashiririce ne.banda haka tunda ta furta jaki ai
    sai ya kama gabansa. yau bai ma bi ta kanta
    ba.don yana sauri yaje gurin masoyiyar sa
    bishira. Ummi ta shiga ajinsu na makaranta.kai
    tsaye ta nufi kujerarta wadda babu wata yarinyar
    data isa ta zauna duk ajin don suna matukar
    tsoron ummi. Tun daga lokacin data bigi kirji ta
    ce kujerarta ce,kowa ya sallama mata.malamai
    ma da suka gaji da rabon fada cewa suka yi a
    bar mata kujerar. duk makarantar babu wanda
    bai san ummi ba,malamai da dalibai saboda
    yawan fadanta da tsokana,har malamai bata bari
    ba a tsokana. sun fita fitsari ita da kawarta
    Amina,kafin su dawo malamin (social studies)ya
    shigo. Amina ta ce ummi dubi har malamin(social
    studies)din ya shigo. ummi ta ce,"ina ruwana,ko
    wanene ma ni shiga zanyi abuna."Amina ta ce,"in
    dai tica hassan ne gara mun juya don sai ya zane
    mu." ummi ta ce,"tab ai gara dukanshi da in tafi
    gida yanxun wannan mugun yaya Abban ya ci
    zalina." sam ummi bata kalli malamin ba,sanda
    take takai kujerarta,yayinda Amina ta labe ta
    kasa shigowa,kamar cikin mafarki taji muryarshi y
    ce,"ke daga ina ki ke?" ta dubi gurin da
    sauri,"yaya Abba ne ya hade rai,fuskar nan tashi
    babu annuri sai kace mai bada mugun labari. ta
    tsorata matuka,ya ce" zo nan kiyi 'kneel down'."
    jiki na bari ummi taje ta zube gaban allon.nan
    take yayi mata bulala guda goma masu kyau.
    take yan ajin suka shiga taitayinsu,don sunga
    ummi tsiga tana kuka irin wanda bata taba yinsa
    ba.don ko an duketa daurewa takeyi ta kuma
    shanye dukan. sannan sabon malami dan bautar
    kasa kamar yadda ya gabatar musu da Kansa
    daga zuwa yayi wannan duka.lalle dole su
    tsorata. ya ce,wuce ki zauna dakikiya mai idon
    jaki.wannan kalma ta daga hankalin ummi,domin
    taga yan ajin sun guntse dariya. ummi ta koma
    kamar ruwa ya cinyeta a cikin ajin duk tsokanarta
    ta tsiya,tsunguli wancan,shuri wancan,duk an
    samu saukinta. taimako daya Allah yayi mata,duk
    da halinta ta da kan daukar karatu.a zaton Abba
    bata iya komai ba,tun da basa shiri. don haka
    baya ko duba takardunta,islamiya ne yafi tsarata
    don tashi hikimar fannin addininta ne dole a
    matsa mata ta sani,boko kuma in bata yi ba ta
    yiwa kanta. duk rubutun da Abba yayi ummi yake
    ta dawowa ya ce ta karanta shi in ko ta mike sai
    ta karanta shi tsaf.in da ta dan samu saukin shi
    kenan. tun daga wannan ranar ummi alkadarinta
    ya soma karyewa gurin yan ajin,domin in suna
    fada shh da yazo ba bin ba'asi ita yake horawa.
    sannan in ta duki wani kafin ya shigo.daya shigo
    za'a fada mishi,don shine ya basu damar cewa
    duk wanda ta taba in yazo a fada mishi. duk da
    sun gano kanwar shi ce,gashi kuma wani lokaci
    tsokanarta suke tunda ya ce mata ummi mai idon
    jaki. sam bataji dadin zuwan Abba ba amma
    tasha alwashin itama sai ta mishi abinda zaiji
    bakin ciki kwatankwacin yadda taji. wata rana
    Abba ya siyo wayar sadarwa, lokacin tana farkon
    fitowa,yazo da ita gidan yana nuna ma su umma.
    nan akayi ta mishi murna umma ta ce,"kai
    Abba,kai da zancen aurenka ke karatowa ina kai
    ina siyan wannan abar har kusan dubu ashirin ka
    ce?" Yace umma amfani kai,kema xan sai miki ai
    tunda nan gaba kadan xata sakko.ahj babba dai
    yace xaya bani kudi in sayo musu shida ahj
    qarami.ummi na wanke wanke tana kallan
    su,wayar ta birgeta,irin wanda suke gani a cikin
    fina finan indiya, ta xata yan sanda ne kawai
    suke riqe irin wannan wayoyin.kai ko na bakin
    titin nan da take ganin mutane na bugawa birgeta
    yake yi,har ta tuna ranan da sukayi doguwan
    tafiya sukaje phone book.suna xuwa suka tarad
    ana layi,haka suka koma gyefe saida kowa ya
    gama sannan suka shiga sunata latsa latsan
    nanbobi suna karawa a kunne.saida wani mutun
    yaxo ya kore su,bayan ya dundungure masu kai.
    tayi murmushi, sannantace a ranta, allah yasa ya
    sai ma umman su,ita ko ta samu abin latsawa.
    daya nunama tsohuwa wayan tace shirman
    banxa,inba qarya ba da wannan xaka kira wani
    daga nesa?yace kn da a saudiyya kike xan kira
    ki.ta ja tsaki tayi daki shiko ya fice nana
    dariya.cikin satin ahj babba ya ba abba ya hada
    masu waya da layi,ahj babba yafi kowa murna da
    wayan, saboda shi mata fiyine. Wata safiya abba
    ya shiga wanka, umma na kicin tana soya masu
    dankalin hausa. zirif ta shige dakin abba tanata
    danna danne,da taji motsin bayi sai ta aje ta yi
    waje da gudu.saida ta tabbata ya shiga daki sai
    tayi xirif da shige gida.lkc da taxo kawo mai abin
    kari tasame shi yanata danna wayan,ya dubeta
    kinxo kin tabamin waya ko?da sauri tace a,a.yace
    munafuka,kece gashi kinyi min delete din duk
    numbers din dake cikin wayan, muguwa. tace to
    ni na shigone?ya harare ta yace fita, da ace ban
    rubuta lambobin na aje ba da yanxun kin min
    asara, muguwa kawai. ummi ta fita tana dariyan
    mugunta,domin in da abin da tafi so bai wuce
    taga bacin ran abba ba,kamar yadda tayi imani
    shima burinsa kenan. umma ta lakato man xafi
    tana shafama ahj a qafa tana murxawa.yace
    yauwa suwaiba kamar kinsan tun daxu yakemin
    kwankwatsa.daxidariya tace in dan tamu ne
    kariqa ware ranaku biyu a sati kana hutawa.yayi
    yar dariya,ina wani hutu da xanyi a gidan
    nan,matsalar ummina kadai ta ishe ni.umma tayi
    dariya,sannan tace ai ummi sai addu;a Ta canya
    xancan da cewa,af na manta niko yanxu auran
    abba yayi wata hudu nangaba?ya ce hudu ne da
    yan kwanaki.tace tofa!gashi ni uwarsa banida ko
    kobo,bari naxo na kama sana'a. ya tuntsure da
    dariya,sannan yace sai yanxu kika san da
    sana'a?itama dariyan tayi tace, in ba haka ba ahj
    ranar biki ko an kirani bana amsa ba.yace gashi
    kuma ke xaki mishi lefe.tace,to na shiga
    aljihunka,in yaso in an soma sana'a sai in biya
    ka.yasa hannu ya dago fuskanta yace sannu
    sarkin wayau.suka sa dariya.yace in san muje
    yaga gidajen nan na layin gabanmu,sai ya xaba
    guda daya a baiwa masu hayar notice sai a gyara
    shi.tace ya xabi na farkon layin dan yafi
    kxau.yace amma bashida girma.tace ya ishe shi
    daga shi sai matarsa fa?wanda ke cikin gidan ba
    mata bixu ne dashi ba?yace to xamuje dai ya
    xaba.sannan akoma kan lefe,tace allah ya saka
    da alkairi,allah ya kaimu.yace amin.wayanshi
    dake caji ta soma ruri,yace dauko min wayar
    can.ta miqe tana cewa har naji tsoro,na kasa
    sabawa da wayan nan.yace kuma gashi na kusa
    bar maki ita. tayi dariyan jin dadi,tana
    kallanshi.to ni wama xai dinga kirana?yace ni
    mana,bana iya yi miki wata magana in na kira
    abba na ce ya kawo maki,sai inga kamar yana
    tsaye,inko taki ce dana kira sai ki kebe daga
    jama'a muyi hiranmu. tayi dariya, daidai lkcn da
    kiran ya sake shigowa,ya daga. ahj buhari ne
    wanda ke sarin kaya gun shi daga kaduna.suka
    gaisa yace ahj ka kira kan in dauka ta katse.ahj
    buhari yace,dama ina san ince maka ne dan allah
    gobe xan shigo,kasa ahada min kayan nan da
    wuri.yace ba komai xa a hada.bayan sunyi
    sallama umma tace ni abin da yake bani al'ajabi
    da wayan nan, har kullum yanda xaka kira wani
    daga nisan duniya,kuma kuyi xance radau.ahj
    yace ci gaba kenan,wata rana ma sai kinga
    fasahan data ninka wannan.tace haka ne.abba
    yana xaune gaban ahj da safe bayan sun
    gaisai,sai ahj yace abba ina ganin da yamma ko
    xuwa dare kaje ka duba gidajen nan ka xabi
    guda,saboda a ba su notice dan a gyara
    didan.yace ahj ba sai naje ba duk wanda aka bani
    yayi.ahj yace ummanka tace ka xabi na farkon
    layin. cikin murmushi abba yace,ta shi
    kenan,nima shina xaba domin duk abinda umma
    ta xaba min shine xabina. tuni sahura ta fito da
    anko,xaqewanta da nuna isarta akan bikin sai
    kace ba dan fari ba. duk dangi sai surutunta ake
    yi,har danginta.umma kan cewa tayi anko ba
    shine damuwanta ba,dan haka sam bata bi ta
    kansu ba.abba a cikin ajin da yake koyarwa,ummi
    tana 2n gefe in da yayi mata maxauni a qasa,can
    in da ba knwa sakamakon ganowa da yayi in tana
    ajin ba a xaman lafiya,sannan babu me ikon xama
    a kujeranta.yace,in ma ya sake ganinta ko a wace
    kujera ce bas,xai ballata.rubutunda yayi take yi
    ranta bace.ya kalli gun datake yace ke!ta dago ta
    dube shi,yace xo nan.taje yace,amso min bulala
    acan ajin.kafin ta dawo sai da ta duke wata
    yarinya ta rugo.nan kuwa yarinyan ta biyo ta har
    aji,abba kam daya amshi bulalar saida ya xaneta
    tas.sam abba ya sama uni ido ko ta ina,ba
    makaranta ba, ba gida ba.dan haka ta matsu yayi
    aure ya bar gidan sannan ya gama service dan
    shi ya qara gaba. tabbas lkcn auran sa xata yi
    party.RFIN CIKI book 1 part 6
    ZURFIN CIKI book 1 part 6
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:56
    Tabbas lkcn auran sa xata yi party. Ummi party
    xatayi na murnan barin gidan shi.ahj ya ba umma
    wayarshi kamar yadda ya fada mata,ya ba abba
    ya suya mata layin mtn kamar yadda ya fada
    mata.ummi tafi kowa murna da wannan
    wayan,domin in umma ta aje takan dauka tayi ta
    latse latse,har dai ta iya abubuwa a wayan
    saboda ta iya karatu.kwanci tashi bikin abba ya
    rage saura yan kwanaki.duk gida biyun sai shirya
    shirye suke,mu samman gidan amare saboda yan
    mata biyu xasu auran.gidansu abba tuni ahj yasa
    an masu fantin gidan biyun,gidan ango kuwa ya
    sha gyara da fenti.ahj ya sabunta mishi qofofi da
    wundunan gidan, batun lefe kam dama tuni ya ke
    sayen xannuwanshi da kadan da kadan yana
    kawo ma umma tana adanawa.dan haka ahj
    karami yana kawo akwatuna umma ta fito da
    kayan dan tasan me xa a qaro.sannan ya yaba
    da hankalin abba.wannan ya nuna mishi cewa
    abba xai iya riqe gidanshi.lalle sana'an hannu
    tana da amfanh ga yayanmu a wannan xamanin
    namu.umma tai mashi lissafin sauran abubuwan
    da xannuwa da leshi xuwa shadda,tace ahj dan
    allah adubo mana masu tsada, Ahj yace suwaiba
    xan yi daidai qarfina,ba xan yi qarya ba dan sun
    san cewa dana talaka ne,kuma suka ba shi.umma
    tace,sai batun abin da xa a ci.yace suwaiba
    kenan,saunawa xakimin lissafin kayan abincin?na
    xata ma xakice kayan sawanku?umma tace suma
    a kawo mana da wuri dan mu dhnka da wuri,ba
    abba xan ba c saboda harkokin sun masa
    yawa.saura sati uku biki aka kai lefe.hjy xainu dai
    unguwa ma ta tafi a ranar,danginta na maigidan
    su ne suka amsa.sai yatsina suke tare da raina
    kayan da suka duba ma sai um da um suke
    cewa,wata tace to an gode fa,tunda taji ta gani
    mu menene namu?suka ba da tukuici, nan dai
    yan kai lefe suka dawo jiki babu qarfi.koda suka
    dawo suka sanar da umma sai tace ku qyale
    su.mu dai mun yi daidai qarfinmu.umman bashir
    kuwa da qannanta suka kai mata labari cewa,tayi
    ina ko xa suyi maraba da kaya?suwaiba ta karbe
    mishi kudi bada xuba kayan kirki ba,banga
    laifinsu ba.ummi kam sai dibar ma umma kayan
    abinci take a boye tana kaiwa gidan maman iman
    maqotansu ne,matan suna shiri da ummi, don ita
    rayuwar ummi dariya take bata,ta gwado shinkafa
    ta kawo,taliya,ta tsiyayo mai,ta ce sauran kayan
    miya da magi,har nama debowa zanyi. maman
    imam ta ce lallai kawayenki zasu sha party.
    ummi ta ce tab ai dole inyi party zan rabu da
    alakakai sarkin mugancin duniya. maman imam
    ta saka dariya,ummi ta kuma fita da gudu tana
    fadina na tuna inda gishiri da maggi suke. daga
    gidan amare anzo anga gidan amarya,nan ma sun
    tafi suna mita,fadi suke "bishira batayi sa'ar miji
    ba,wata ta ce ya aureta ne don kudin ubanta.
    koda suka je suka fada ma hajiya zainu fasalin
    gidan,daki uku ne duka falle dai dai sai kicin da
    bayi a tsakar gida. kanwar zainu ta ce,"kai
    gaskiya bishira bata yi dabara ba.hashimu dan
    gidan Alhaji mansur ya jima da sanar dani ya
    kamun bishira." hajiya zainu ta ce,"shi kadai?ko
    yayan abokan babansu nawa ke sonta?tunda taki
    tsayawa tayi karatu ta zabi ta auri tela,ba shi
    kenan ba?dubi gidan ubanta amma ta zabi zama
    a wani gida dakuna jere sai ka ce ajin
    primary."lol. suka ce,"kwarai kuwa kamar ajin
    makarantar gwamnati."ta ce,"shi kenan ai kaya
    dai asai mata daidai tsarin gidanta ba iri daya za
    a sai musu da Aisha ba." sun siyo sunje sun jera
    komai ras,yanzun kam sai daura aure ya
    rage,Abba da abokanansa walima kadai ya shirya.
    can gidan ne suke ta bukukuwansu irin ma masu
    hali.shi kam dai yasan yan'uwanta ba sonshi
    suke ba. sam be je gurin shagalinsu ba. ranar
    lahadi aka daura aure,misalin karfe goma na
    safe,unguwar kam ta cika da mutane da motoci.
    Abba da zugar abokananshi salisu yayan amare
    yayi musu jagora cikin gidan. sun gaisa da
    mutane sannan suka fito kowa fadi yake."kai
    amma angon bishira zankadede dashi
    tubarkalla."gashi Abba da iya daukar
    wanka,tsafta ce dashi ga son kamshi. KAI MATA
    IYAYEN GULMA. Can gidan ango ma anata
    shagalin cin abinci, jama'a dangi da makota sa
    gudunmawa suke ba umma tana a'a amma sai
    ace ta rike sabida ita mutum ce mai kyauta.
    umman bashir kam sai takaici take ji,kowa ya
    shigo sai dai ya ce mata."Allah ya sanya
    alkairi"kawai musamman ta shigo gidan don taga
    ko ana ba umman Abba ne. Nan fa na fita ta
    koma gida babu ko kunya tana ta masifa, fadi
    take "lallai suwaiba,gudunmawar auran dana duk
    ita ce ke karbewa? gaskiya naga sai dai amin
    Allah sanya alheri a wuce,to da sake,ni na haifi
    abuna ta bari sai ta tashi auran wannan
    figaggyar yar tata sannan ta amshi bikin." ta
    gama fadanta ta matsa,danginta suka soma yi da
    ita,suka ce wa zai baki wani abu ke da ko dan
    uwanki baki san ki bashi gudunmawa ba bare
    kyauta.tsinanni yar rowarki ce taja miki."
    kanwarta ta ce,"sahura sai dai ta ci na wani ba
    dai aci nata ba,dama irinsu sun cika son banza."
    ummi kam anci kwalliya an gayyato kawaye
    anata party a gidan maman iman,an kunna rediyo
    sai rawa suke yi,kafin a gama partyn an bige da
    fada da dambe,da kyar aka rabasu,nan taro ya
    watse. da misalin karfe takwas na dare,ango da
    abokanshi sun taso sallar isha'i Ahmad ya ce don
    Allah ango muje mu rakaka. ya ce,"Allah sai nayi
    wanka."mukhtara ya ce,"gidan cunkus da jama'a
    zakayi wanka?" Aminu ya ce,"don Allah malam
    kazo mu tafi,in ma kifi zaka zama a gidanka."
    Abba ya ce,"bari dai ku gani." a zaure suka ci
    karo da ummi,ya ce,"ke jeki ki wanke bayi ki kai
    mun ruwan wanka." ta sobare baki ta koma ciki
    tana fadin. na dai kusan hutawa, masifaff. ta
    wanke bayin sannan takai ruwan,yana shiga gidan
    dangi sukayo kanshi,ga ango! ga ango!! abokan
    wasa suka za na can zamfara suna tayi masa
    tsiya. dan gidan ummanshi yau dai za a kwana
    wani gidan ba na umman tashi ba.ya dai samu
    ya shige wanka. bayan ya fito ya bude
    dakinshi,ya shirya cikin wata shadda
    mirror,lokacin su ake yayi.ruwan kasa mai duhu.
    yasha hula mu hadu a banki ita ma kalar
    shaddar,ya feshe jikinshi da kalolin turaruka.ya
    shigo cikin gidan yaje kofar dakin umma. ya ce
    umman tana nan.aka ce mishi tana dakin
    Alhaji,yayi sallama a kofar falon Alhajin basu ji
    ba,suna ta hira tsit ya yi lokacin da yaji umman
    tana cewa Allah dai ya basu zaman lafiya da
    zuri'a tagari. Amma har ga Allah naso Abba ya
    auri..... ringing din wayar shi ce ta hana jin kowa
    ummanshi ta ce,sai dai muryar Alhajin ya ce
    wallahi suwaiba nima tsarina kenan. ahj yace ta
    allah ya riga ya shirya ba ita ce matarshi ba.ya
    daga wayar,ahmad ina xuwa mana. ba tare da
    yaji abinda ahmad din xai fada ba ya katse
    kiran,dan yaji haushi.yaso jin wacece iyayansa
    suka so ya aura?ya sake doka sallama,suka
    amsa.ya shiga ya xauna ya gaishesu,sannanya
    dubi umma.dama naxo miki sai da safe ne.ahj da
    umma suka yi yar dariya,umma tace to
    abba,yanxu dai ka girma,dan allah kyawawan
    halayenka dinnan kaci gaba da su.yace na
    gode.ahj ma yayi masa nasiha,daga nan ya fita
    jikinshi a sanyaye.da muwarsa me yasa umma
    bata sanar da shi yarinyar da taso mishi ba
    tuntuni?haka dai suka rankaya da abokanansa
    dan xuwa dakin amarya. gidan kam tun daga
    tsakar gida qamshi ke tashi.sun taradda
    qawayenta biyu,ita kam tana lullube kan
    gado.nan dai suka sayi baki akayi yan shaqiyanci
    tare da barkwanci,sannan qawaye suka yi mata
    sallama suka tafi,shima ya raka abokansa. ya
    dawo ya xauna bakin gadan yana dubanta, itama
    kallonshi take cike da so. sukayi ma juna
    murmushi,ya janyo ledan kaxan da suka shigo da
    ita. Ya warware takardar,y yago cinya ya mika
    mata a baki,"ci,nasan yau kin wuni da yunwa
    ko?" ta ce,"na koshi bana jin yunwa ma,ni kam
    duk yau banji yunwa ba." ya ce,"ni ma haka,dama
    yau bai da ce muci abinci ba."ta dube shi da
    alamar tambaya a kwayar idanunta.ya ware
    idanunshi. "taron da muka tara ko ina cike da
    jama'a." yayi yar dariya sannnan ta bude baki ya
    saka mata kazar.ta dan figa.haka yayi ta bata
    tare da zuba mata juice a kofi shima yana bata.
    ta ce,"to kaima ka ci." ya ce,nima ke zaki
    bani."ta sunkuyar da kai don kunya sannan ta
    dauka ita ma ta soma bashi. sai da suka yi
    dam.sannan ya ce mata kije kiyi alwala kizo muyi
    sallah. ta ce ai tun dazun nayi sallah.ya ce
    wannan ta ma'aurata ce,zamu gode wa Allah
    taare da rokonshi zuri'a tagari,da kuma fatan ya
    tsare mu daga sharrin shaidan dama duk abin ki.
    Ta fita ta dauro alwala,shi kuma ya kuskure
    baki.shine yaja su sallar,raka'a biu sannan sukayi
    ta addu'a,shi ne ma yake addu'ar ita kuma tana
    cewa amin. bayan sun idar da sallah idar da
    sallar,ya yi mata tambayoyi game da addini ta
    sanar da shi,yayi mata yan gyare-gyare sannan
    suka kwanta. sam Abba be daga kafa ba,a ranar
    ya angwance abin shi.don haka yayi kwanan farin
    ciki. da asubahi ya dawo masallaci,har lokacin
    amarya tana ta shirga bacci ya zauna bakin
    gadon yana kallonta.yasa hannunshi a gefen
    kumatunta. "sleeping beauty" tayi mika sannan ta
    bude ido,ya ce"a tashi ayi sallah ko?gashi sai
    kinyi wanka ko?" ta ce,"eh." ya ce, "to tashi ki
    gani gari ya soma haske." zani taja ta daura
    daura ta nufi waje. da kallo tabi tsakar
    gidan,sannan ta dawo dakin Abba.bazan iya jan
    ruwa daga cikin rijiya ba. ya fito da sauri yaja
    mata sannan yakai mata bandakin,ya dawo yayi
    taja yana cika robobin ruwanta.sai da ya cika
    mata komai,sannan ya koma dakin. lokacin ta
    idar da sallah.ya dauko Alqur'ani mai girma ya
    zauna gabanta,ya ce "madam zamuyi karatu." ta
    dube shi tareda yatsina fuska,"wallahi bacci
    nakeji."ya ce,"daure muyi ko aya biyar ce," ta ce
    cikin shagwaba,"ni biyu." ya ce,"to bismillah,mu
    fara ta sama ko ta kasa?" ta ce,"ni kam ko ta
    ina, don haka sai ya soma mata daga bakara
    yana yi tana maimaitawa,aya biyu kusan minti
    ashirin ta ce, "zan kwanta." Ya aje kur'ani ya
    kmama hannunta,zo muje kicin mu gani me zamu
    nema.dan dole ta bishi zuwa kicin din.suka tsaya
    suna kallm kayan, tukwane ne zuwa kuloli da
    sauran tarkace,sai risho.ta dube shi cikin yanayin
    tsausaya ma kanta. tace, sun qi sai min gas
    cooker wai gidana ba flate ba ne bai dace da gas
    cooker ba. ita ko anti aisha an sai mata, kayan
    girkita ma duk yan chaina. tausayinta ya tsirga
    ma abba, ya jawo ta jikinshi ya rungume, kada ki
    damu bishira, duk abin da a ke sai ma yar gata
    xan sai miki, matsawar Allah ya hore min. ya
    janyo kwalin risho din ya ciro shi, ya hada yace
    xan siyo lagwani da kalanxir kenan ko? tace eh.
    ya miqe bari na dawo. tace to. ta nufi daki ta
    fada kan gadanta taci gaba da baccinta, shi kam
    gidansu ya nufa. tun daga nesa ya hango ahj
    babba xai shiga dakin waje, in da aka sauki baqi
    maxa, da alama ahjn ya hango shine shi yasa ya
    tsaya a bakin qofar. abba yana cike da fara'a ya
    rusuna xai gaida ahj shi kuma ya miqa masa
    hannu, dan haka sai abban ya kama suka yi
    musabaha. ahj yace Alhamdulillahi abbana, ka
    xama mutun, sai ayi ta hakuri da rayuwa. abba
    ya sunkuyar da kai yana tambayar kanshi ko
    manya suna ganewa ne in kayi auratayya da
    matanka? ahj ya katse shi da cewa, ya kwanan
    iyalin taka? tare suka shiga gun baqin, yana
    gaida su ya fito xuwa cikin gidan. yana leqawa
    dakin umma bata ciki, sai baqi. wata uwani dake
    matsayin abokiyan wasansu tace ango amarya ta
    koro ka ne? yace, keni karki dame ni, ina umma
    na? umma daga kicin tace, gani nan dana, xo
    qyale su uwani. gurinta ya nufa yana cewa,kina
    kicin ashe? tace, eh ina hada ma baqi abin kari
    ne. yace kalli yanda duk suka yi mana kaca kaca
    da gidan,wannan in sun tafi sai kin sha aikin
    tsaftace gidan.tace to yana iya?dole in gyara in
    sun tafi,ai arxiki ne ma xuwan nasu.abba yayi
    dan murmushi,sannanya canxa maganan da
    cewa,umma galan din kananxir muke so.tace,ga
    ma kananxir din can da ahj ya siyo jarka babba
    wai saboda biki.nace yaushe girkin biki xai yiwu
    da kananxir?shine na aje shi.sai kadau galan ka
    cika.yayi murmushi. Yace kai ahj akwai qoqari,
    musamman lkcn bikin nan.umma tayi yar dariya
    tare da cewa ko abinci fa baya iya tsayawa
    yaci,in na masa magana sai yace bijin da guda
    ina yaga ta cin abinci?abba ya girgixa kai,Allah
    ya rama muku da mafificin alkairin da kuke
    min,yasa ni ma in goya ku kamar yadda kuka
    goya ni.tace amin abba ai muma kana yi mana
    biyayya Allah yasa albarka a cikin auran, ya baka
    yaya masu binka kaima.yace amin. ya isa gida da
    kalanxir da lakwani ya samu ta koma bacci,dan
    haka ya hada ya dora ruwan xafi ya juye cikin
    plaks yaje ya ce ta shi mu karya. tayi juyi tare da
    cewa sai an jima,dama tun jiya sun shigo da
    biredi da kayan tea,shima sai ya sake
    kwanciya.ya mannata jikinshi suka koma
    bacci,goma da ishirin wayarsa ta tashe shi da
    ruri. ya daga ahj ne ke san ganinsa qarfe sha
    biyu.yace,ya sanme shi can kasuwa,ita ma ta
    tashi.nan suka karya sannan yayo wanka ya tafi
    kiran abba.kaya ne ya ba shi da kudin mota, yace
    ya kawo ma baqi yan xamfara da xasu koma gida
    yace ka tabbata ka dauki shatar mota har
    Zamfara abba ya ce to.sai da ya samu motar
    sannan yaje ya loda su suka daga,suna ta
    godiya.yau satinsu daya cir umman shi ke kai
    masu abinci,sannan ita kuma ya shigo da kayan
    marmari,sai kaji ko tsire da balango.abba ya
    shirya tsaf cikin qananan kaya xai tafi shago,yace
    madam yau fa abinci xaki yi mana,kin san
    abokaina su ahmad xasu xo muci abinci,in yaso
    daga nan sai mu wuce gaisuwan surukai gidanku
    a matsayin kina amarya wanda xaki soma girki
    yau, me xaki dafa mana? ta tashi xaune duk abin
    da ka ke so.dadi ya rufe shi,kowanne dai ki mana
    fatana shine ki birge abokaina.tace an gama.
    yace to bari inje xan turo yaran shago da abinci
    da cefane tace to, har ya tafi kuma ya dawo
    yace, xan biya in turo miki ummi,tace saidai in
    fati.yace,ummi tafi fati hanxarin aiki fa.tace eh
    nafi son fatin.kamar kullum sai da ya soma shiga
    gun ummarshi suka gaisa ta tambaye bishira,
    yace lafiyi lau.yaci gaba da cewa, yau nema xata
    soma girki,nace na turo mata ummi tace wai
    fati.umma tayi murmushi, sannantace kai ko
    yaushe xata so a tura mata ummi umma tace ina
    xata so a tura mata ummi? ita fa ba natsuwa
    gareta ba.abba yace, duk da haka tafi fati
    hanxarin aiki. umma tace,yanxu dai tura mata
    fatin.ka ko sai kayan abinci?yace ina fa,yanxu dai
    xan je bin wasu yan kudadena.tace ina xuwa
    baqar leda ta ciro a cikin adakan suturunta,taxo
    ta xauna sannan ta umurce shi da ya xauna.ta
    miqa mashi ledan tace,kwance ka gani.abba ya
    kwance ledan yana cewa menene a ciki ummana?
    kudin da yayi arba da su su suka bashi amsa
    yace,umma kudin nan fa?tace gudunmawa ce da
    jama'a sukayi ta bani,ka gansu nan.yanxu ka je
    ka siyi kayan abinci da su.abba yayi dariya,
    sannan ya kullesu ya miqa mata tare da cewa.
    Allah ya kyauta in amsan makh kudi, ki boye
    abinki. tace bana son muyi ta jan magana
    abba,kawai ka riqe kudin nan.muryan tsohuwa ne
    ta katse su,inda take cewa yanxu ke suwaiba
    hakan da ki ka yi adalci ne? yar gudunmuwar da
    ki ka samu kiba mai sunan malam duka, ummin
    fa? umma tace,to tsohuwa ummi me xatayi da
    kudi yanxun?abba yace kai wannan matan sa
    idan ki ya gota misali. Tace kai tafi can,ni rufemin
    baki,ke kuma suwaiba da kike cewan haka ba kya
    siyan mata yan tukwane da kwanonin nan na yayi
    maigida cika duba ne ku ke ce musu ko ci bari
    kallo? umma da abba suka sa dariya,tsohuwa ta
    sake jin haushi ta ce eh dole ku min dariya tunda
    kema kin xama shi,ai sai kiyi ta bashi naki ne ba
    nawa ba.umma tace yi haquri tsohuwa, gani nayi
    nan gaba muna sa ran abba shi ne xai ma ummi
    kayan dakin ma gaba daya tace,me kika ce?tab
    mai sunan mlm ne xai yi wa takwara wani abin
    axo a gani?shi da ya tsaneta.abba yace,in lkcn
    yaxo ke kya yi ma.ta tafa hannu cikin jin
    matuqan takaici ta ce,a gayawa mai xuciya ba
    mai dukiya ba,dan ko xan mata.ta nufi dakinta
    tana fada.umma tace,tashi abba,dauki kudin nan
    kaje. yace,wallah umma bari dai in dauka tunda
    kin matsa,amma ba xan amsa duka ba.ya qirga
    dubu uku,tace ka qara dan kusan dubu tara ne
    kudin,yace haka ma ya isa ki adana sauran.tace
    shi kenan. daga nan kasuwa ya wuce,ya sai
    kayan abinci.bayan ya amso wadansu kudaden
    shi ya hada ya kai mata. Sannan ya yi cefanen
    kayan miyan rigijif da nama ya aika yaran
    shago.dama kafin ya bar layin ya shiga gun
    umman bashir ya gaisheta.da tana ta bace bacen
    rai,sannan da yace umma ina fati? taje xata taya
    bishira aiki ne.sai ta washe baki,tan bandaki.
    yace to in ta fito ki tura mata ita.ya fice
    abinshi.biyu saura ya iyo gidan,tun a tsakar gidan
    yake jin qamshin shinkafa.ya isa kicin din tuni ta
    sauke shinkafa sai miya.yace ki xubama yaran
    shagona.ya dubi fati da ke yanka latas yace,in
    kin gama jamin ruwan wanka a rijiya.tace to.yana
    daki yana sa kaya yaji sallamar abokanshi.da
    sauri ya fito, suna ta yi masa tsiya ango kasha
    gyara, munxo dibar girki. abba ya bude musu
    falo,falan yaji jeran samiru abin yayi na xamanin,
    ga kujeru suka xauna suna yaba dukiyar da aka
    xuba cikin falon.ya fito yace bishira ta saka hijabi
    taje su gaisa.ya dauki abinci ya kai musu,sannan
    yasa fati takai filet da ruwan sha,shi kuma ya
    koma daki dan qarasa saka kaya.a xatam shi xai
    samu sunyi nisa da cin abincin amma sai me?
    dukkansu su shida kowanne filet din gabansa
    shaqe da abinci da nama,ga cokali a
    hannunsu,amma kowannansu juya abincin
    yake,yace a,a kuci mana kai muke jira ka bude da
    addua.tsaki yayi, yasan halin ahmad gun
    xolaya,dan haka sai yace muktar kuci abincinku,in
    kun bi ta ahmad xai ta bata mana lkc.cokali ya
    dauka shima ya xauna kusa da sunusi ya ce mu
    ci tare.take ya yatsina fuska tare da dawo da
    abincin ya xube shi kan ledar yana tande
    harshansa.dan danan gishirin da ya kama masa
    harshe ya ragu,cike da kunya ya dubi abokanan
    nasa suna ta dariyar da suke gimtse.da farko ya
    dubi sunusi,wai gishiri ka qara ne?sunusi ya
    ce,qila dai gishirin nan da bakin buhu ta
    xufa.muktar yace dubi gaban rigata ni da shegen
    kwandayi na tura nama a baki na tauna ya qwace
    saboda tsananin qarfi ya dawo ya fado min
    jiki.abba ya miqe cikin damuwa ya ce bari in
    maku wata miyar. ahmad yace a,a duk yunwa
    muka debo, inda yaji da mai a bamu muyi maneji.
    abba ya fito xuwa kicin.fati ce xaune da nata
    abincin tana ta juya cokalin. Abba yace ina
    bishiran?taje daki.ya daga murya ya kirata,ta
    amsa sannan taxo.ya dubeta fuska a daure ke
    dama ba ki iya abinci ba shi ne ki ka toxarta ni
    cikin abokaina?maimakon ki fada min? tace, to ai
    fati ce nace tayi miyar, danni bansan yadda a ke
    yi ba. haushi ya kama shi.ya dubi fati, ke dama
    baki iya komai ba kema?shashasha, gara ki koyi
    girki, dan duk macen da bata iya girki ba ba mace
    ba ce.ya daka mata tsawa, tashi kije gidan
    ummana ki ce ta baki abinci inji ni,ni da abokaina
    ne.sallamar yaron shagon shi ne ta katse shi,ya
    gaishe su sannan ya ce,naxo daukan abincin.ya
    dubi bishira,kina da yaji?tace,eh gashi can cikin
    kwalba da ummanka ta aiko min.ya ce,xuba ma
    yaran nan yaji da mai.ta ce ai akwai miyar.yace
    miyar ai ta xama guba.fati ta dauko abinci cikin
    kula xata fita,yace wannan fa?ba aikenki nayi ba?
    tace na ummanmu ne xan tafi mata da shi,ita ce
    ta ce duk abin da a ka dafa inxo mata da shi, shi
    ne yaya bishira ta xuba mata.abba baice qala ba,
    sai al-ajabin halin uwarshi ya ke yi. Bishira ta ce,
    kawo ita ma a kwashe miyar a xuba mata mai da
    yaji. ya daka ma fati tsawa,kai mata haka ni ki
    dauko min abinci gun ummana, minti uku na baki
    in kin wuce biyar xa ki sani.da gudu ta fita tana
    shiga gidansu ta aje bata tsaya yin surutu ba, ta
    fita da gudu.dan wake umma tayi,Allah yasa tayi
    da yawa,dan haka ta xuba musu ta dora ma fati
    ba tare da ta tambeyeta dalilin aikowarshi ba. sai
    dai a ranta tana ta saqe saqe tace,qila sun fasa
    girkin ne,ko kuma bai kai kayan abincin ba.koda
    fati ta kai musu dan waken nan suka baje suka
    kwashi dan wake suna santi.bishira tana jiyo
    shewarsu.abba na cewa ummana ta iya girki, bari
    in xo in sa muku waigi.muktar yace, ka kai
    amaryarka ta koyo girki.garzali yace,saboda irin
    wannan matsalan kafin in auri yarinya sai na
    tabbata ta iya girki.ahmad ya ce daya daga cikin
    illar auran yaqan masu kudin nan kenan,
    sangartattu ne basu iya komai ba tun da a
    gidajensu ba sasu a ke yi ba.ado yace wasu ba
    amma wasu suna saka yaransu.
    vels / ZURFIN CIKI book 1 part 7
    ZURFIN CIKI book 1 part 7
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:59
    Ado yace wasu ba, amma wasu suna saka
    yaransu,dan wani abokin wasanmu a kaduna ya
    auri yar wani attajiri, ba kaga girki ba kala
    kala.abba dai yana ta binsu da ido,har aka yi
    kiran sallar la'asar suka fita xuwa masallaci,daga
    can xasu wuce gaida surukai.bishirata dinga jin
    haushi,wai abokan abba sunxo har gidanta sunci
    mata xarafi.ummi ta fito dan xuwa gidan su
    amina,domin akwai wata xainab da wai ta musu
    gulma xasuje su.kirata har gida su dake ta.suna
    xuwa kuwa suka tsaya a waje suna tunanin
    yadda xa suyi ta fito,amina ta ce muje mu ce
    mun xo gunta ne, inta xo rakiyan mu mu duke ta
    mu gudu.haka kuwa suka yi,har ummarta tana ba
    su quli quli,ita ga me qawayen yan tana rako su
    tun daga soron gidan suka soma dukanta.sai da
    ummanta ta fito sannan suka gudu.ta ce yar tata
    kin san gidansu?xainab tace,na sani.ummar tata
    ta taso ta.su kuwa su ummi suna fitowa sai suka
    canxa hanya.amina tace dan allah muje gidan
    amaryan abbanku,naji ana ta labarin jeranta an
    ce kaya ne na uban gari. . Ummi ta ce,"duk da
    son kirgan samirana ban taba zuwa ba,saboda na
    kula ita ma yar rainin wayau ce kamar mijinta."
    Amina ta ce,"ke dai muje inga samirun da aka ce
    jajaye wai masu shida-shida" ummi ta ce,"mu
    fara bi ta shagonsa in yana nan to sai muje,in ko
    bayanan ba zani ba ya dake ni a banza." duk da
    cewa shagon da gidan tsakaninsu da nisa sai da
    sukaje suka duba sukaga yana nan,sannan suka
    je. gidan shiru sunata sallama,ummi ta nufi wata
    kofa ta tura,ta yafito Amina,"zoki gani nan ne
    falon."suka kirge samiru tsaf,sannan suka fito. ta
    window ummi ta leka nan ta hango bishira kan
    gado tana ta bacci,suka je kicin suka leka suka
    tura dayan dakin da ba kowa. nan ma sukaga ba
    komai ciki,an dai shimfida ledar kasa an sa
    manyan robobin ruwa. suka fito,ummi ta
    ce,"gaskiya matar nan banza ce,dubi yadda
    mukaje tana ta bacci." daga can suka sake zuwa
    gidan wata amaryar don kirga samira,sai kusan
    magariba sannan ta shiga.umma tana alwala ta
    ce,"to tunkiya uwar tumbele,tun yaushe ki ka bar
    gidannan sai yanzun kika waiwayo? sai kararki
    da jama'a keta kawo min?to na gaji da
    halinki,bari Alhaji ya dawo,wato tunda yanzu
    babu Abba a gida shi yasa iskancinki ke son yafi
    da." tsohuwa ta fito,"suwaiba da a ce ba a
    gabana kika haifi takwara ba,to da zance ba yarki
    ba ce,ba dama yarinya ta fita wasa?" umma ta
    ce,"ban hanata yin wasa ba,amma tayi shi a gida
    yawo ne bashi da dadi." tsohuwa ta ce,"a'a karki
    wani fada ma Alhaji,ta daina ko takwara?" ummi
    ta ce, eh.umma dan haushi ta shige daki ta barsu
    anan. lokacin da su Abba suka je gidan
    surukanshi an amshe su ba yabo ba fallasa,har
    ma da zasu tafi aka basu (uniforms)din bishira na
    boko wai ranar monday lallai ta tafi makaranta.
    sun zaga gidajan danginta dake kusa,sannan
    suka dawo gida.ya sameta tana fushi,shima
    shareta yayi don yaji haushi barnar abincin da
    tayi masa. dadin dadawa gidan nan yanda ya bar
    shi haka ya tadda shi.ita kanta batayi wanka ba
    ta kwanta tana ta uban bacci.fita yayi daga
    gidan,sai goman dare sannan ya shigo ya rufe
    gidan yaja ruwa yaje yayi wanka. sannan ya
    shiga dakin,tsayawa yayi yana kallon gadon
    mutsu-mutsu,sannan ga kaya nan duk a kai.ita
    kuma tana kwance rike da wani littafi tana
    karantawa. . Ya ce,"bishira wai me yasa bakya
    son kakkabe gadonki? ta dube shi nifa duk na
    gajine.tsaki yaja tare da cewa me kikayi da har
    kika gaji? bani guri ni in gyara shimfidar zan
    kwanta. shine ya kakkabe shimfidar sannan ya
    kwanta.duk da ya cike da bukata amma haushi
    ya hanashi kulata,sai ma baya da ya juya mata.
    Abba yanada tsafta sosai,haka nan ma'abocin
    son kamshi ne,duk da gyara gami da tsafta irin
    na ummanshi wata ran har cin gyaranta yake
    yi.sam baya so yaga ko ina rakwacan,yafi son
    komai ya ganshi a muhallinsa. dole kullum shi ke
    share gidan ya wanke ban daki,sannan da rana in
    ya dawo ya dora abinci. litinin duk makaranta
    suka koma daga dogon hutun kirismeti da suka
    samu.Abba ya koma kan aikinsa na bautar
    kasa.dan haka kusan tare suka fita da bishira ta
    wuce makaranta shima ya wuce wurin koyar war
    shi. . Ya rigata dawowa gidan,dan haka gajeren
    wando ya samu ya shiga tsabtace gidan.sannan
    ya dora dafa dukan taliya. uku da minti sha biyar
    ta shigo ya dubeta ina kika tsaya? ta ce,ba ko
    ina mufa makarantar mu biyu da rabi ake tashin
    mu.dan ma na samu direban gidanmu da yazo
    daukan kannena shine ya kawo ni. Abba y sake
    had'e rai,motar gidanku? Bn baki kud'in mota
    ba?Ta ce ka bani, ya ce to bn amnce ki sake
    shiga motar gidanku ba. Ta ce,"kan me ? ya
    harare ta ba tare d ya bata amsa ba,y nufi kicin
    tabi bayanshi d harara,sannan ta shige d'aki. A
    ganin Abba sam babu wani sauki da ya samu a
    auranshi,nashi ganin wahala ya d'ebo ma
    kanshi,kwanciyada ita ne kurum zai ce ya k'aru d
    shi acikin auren. Ya shiga gidansu d
    sallama,Umma ta amsa tana zaune kan sallaya
    bayan ta idar d sallar Isha'i. Ta ce,Abba ba a je
    an kwanta ba?ya zauna tare d d'an jan tsaki ta
    ce,A'a ha,jikin ko garin? Ya ce,Umma gaskiya ni
    abubuwa sun cud'e min,yarinyar nan tunda a
    kawo ta sam ban huta ba. Umma ta saki dariya
    "ka ji Abba d wani zance,dama ce maka a ka yi
    ana bauta d hutu? Aure shi bautane. Ya ce,Tsaya
    kiji fa ummata,kinga tun Asubahi in nayo Sallah
    zan hau sharar gidan,in shirya in je gurin d nike
    koyarwa. In dawo in dafa abnci,sannan in tafi
    shago kuma don takaici in na zo kwanciya ni zan
    kakka6e shimfid'a,ita bata iya komai ba ashe
    daga gidan nasu.Ni fa har ta soma sure min......
    "Kai Abba! Umma ta katse shi d sauri, kada in
    kuma jin wannan furucin, kana hauka ne?yanzu d
    fada min menene matsalarka?in dai abnci ne ka
    bari zan diga aiko muku da shi. Ya ce umma ya
    ya ma za a yi haka?Tab ai ba zai yi wu ba,Ta dai
    zo ta koya sati d lahadi. Umma ta ce,To shi
    kenan,tazo din.kayi ta hkr Abba,nasan ka kai ma
    d zuciya,don Allah kada ka sake in ji wata
    fitina,ka lalla6a matarka kuyi zamnku lfy. Abba
    ya ce, To ko da ya sanar d Bishira cewa yana son
    taje gurin ummansa ta koyo girki,sai ko ta tuma
    ta ce ita ba zata je ba,dama dai gurin umman
    Bashir ce, Ya ce,shi kuma gurin ummansa ya
    turata,koda Asabar din tazo kin zuwa tayi,shi
    kuma sai ya shareta ta ya daina girkinki. Sai dai
    yaje gidn ummanshi yaci,hatta ranar litinin d suke
    d makaranta bai dafa abncin ba da ya dawo a
    galabaice da yunwa ta iso. Bashir ya ce, Ni har
    fata nake wata rana 'yar sa' in'sa ta hadu ku
    umma,wlh in mata shegen duka. Bishira ta ce,Ni
    dai bata isa ba, in ma ita ce ta turo shi dn in
    dinga zuwa gidnta to ba zanje ba. Haka suka yi
    ta zagin umma,daga bisani Bishira ta mike ta tafi
    dn kada ya dawo bata nan. Rashin iya girki ya
    kawowa masoyan 2 rashin jutuwa,wanda ko
    magana Abba bai cika yi mata ba. In ta zauna
    tayi ta kuka tana mmk,me ta mishi ya juya mata
    baya dan da nan? Yau kam abn ya yi kamar
    kaurace mata ya yi daga dakin baccinta, ya dauki
    filo ya tafi falo ya kwanta. Tayi ta kuka. Kasa
    jurewa tayi ta mike ta bishi,kwankwasakofar tayi
    kusan sau 3 ya ce "Waye?" cikin muryar kuka ta
    ce, Ni ce, Abba don Allah ka bude. Ya kunna
    wutar falon,sannan ya bude ta shigo ta zauna
    kusa d shi, ta ce, Abba wai mi na maka ne ka
    tsane ni? ka duba fa ko wata daya ban rufa
    ba,kasan dai yadda a ka yi auranmu yanzun in
    Mahaifana suka ji dariya za su Min. Amma ba
    komai sai biredi ta samu ta k'asuma,d ya tafi
    shago sai ta yafa mayafinta ta nufin gidn umman
    bashir. koda tai sallama umman tana kan turmi
    zaune suna ta ganzar rake ita d su bishir. umman
    Abba ce ta aiko musu da shi don rashin Adalci
    suna sha suna yi da ita. Suka shiga lale d zuwan
    Bishira, ta kalli bashir 'Ina fushi da kai, shine
    wato har yanzun ba ka zo ba ko? ya ce, Tab, sau
    2 ina zuwa zan shiga gidan sai yaya Abba ya fito
    ya ce min kina bacci, na gane nufinshi baya son
    ina shiga masa gida,shi yasa na share.Bishira ta
    ce Um, wannan Yayan naka halinshi sai shi,
    yanzun ma fa fushi yake dani. Umma ta ce," A
    kan Me kuma? wai shi dole sai nazo gurin
    ummarshi na koyi girki, ai ko nace wlh ba ni
    zuwa. Umman bishir ta rafka salati. sannan tace
    'Naga ta kaina ni Sahura,kai Allah ya isa
    tsakanina d Suwaiba. yanzun kuma ta gama d ni
    ke ta sako a gaba, so take ta shiga tsakaninku?'
    Abba ya kura mata ido, yasan abn d ta fada
    gaskiya ne ya ce "Me na miki to?" ta kalle shi,"Ba
    ka ma san abn d kayi min ba?Ta ga daya yanzun
    fa kaurace min kayi. Ya ce ba kya gyara
    gadonki,ni kuma na gaji d gyarawa. Ta saka tafin
    hannunta cikin nashi zo muje in gyara.
    Tausayinta ya ji,ya tashi ya bita yana kallonta
    duk kakarin d ta yi dn t gyara ta kasa. Sai dai shi
    ne ya gyara, Sannan ya janyo ta suka
    kwanta.Sam bata d gardama ko nuna gajiyawa a
    gurin ba shi hakkinshi na kwanciya. In zai zo sau
    nawa ba ya damunta,gurin da ta ke birge shi
    kenan. Amma ba wannan ba ne kadai namiji ke
    bukata,Musammanirin Abba dan kwalisa. Wata
    ranar Jumma'a bayan sun tashi daga mkrntr da
    ya ke koyarwa,ya ce da Ummi ta jira shi zaya
    aike ta gida. Kudin cefane ya bata ya ce taje ta
    sai kayan miya d nama ta kai gidanshi, Sannan
    ta tsaya tayi masa miyar tare d yi masa sakwara.
    . Shi kuma zai je ya fada ma umma, dn yana son
    d dunkunan wata amarya d yake son karasawa
    ummi ta zun6uri baki bayan ta amshi kudin ta
    wuce tana yankun-kunai, ya ce "Ke!" ta waigo "Zo
    nan . ta dawo, Ya kama mata kunne, Kin san
    kwana 2 bn ta6a lafiyarki ba ko?to kiyi abn d yau
    zaki gwammace ba ki zo duniya ba. ya
    rankwashe mata kai, Sannan ta wuce tayi ce
    fanan ta nufi gidn Matar gidn tana zaune d kayan
    mkrnt a jikinta,,Ummi ta mata Sannu harara ta
    zuba ma Ummi, Ummi ko ta rama,sannan ta ce
    "Mijinki ya ce in zo in yi mashi sakwara d miya.
    "Bishira ta ce, To sai ki koma gidn ubnki ki dauko
    tukunya d murhu b dai nawa ba, Ummi ta ce, To
    ni dai gaskiya d ubana ba. Bishira ta taso tana
    cewa Sai na wa? Ummi ta ce, Oho,amma ba
    nawa ba. Za ta kai mata duka ta goce ta ajiye
    mata kayan miyan ta ce " Gashi sai kiyi, kila ma
    baki iya girki ba ne. Taje ta fadawa umma, Umma
    ta ce "Ke ummi karya ki ke daga zuwa zata hauki
    d zagi sai ka ce Mahaukacciya? To kije ki fada
    wa Abban in ya so sai kuje tare ya fada mata
    amma fa kada ki ce masa ta zage ki, ki ce masa
    dai yazo ya fada mata zaki tayata. Ummi ko kyn
    mkrnt ba ta cire ba ta nufi gurinshi,yana tsaka
    dinki taje,Ummi sai ce masa tayi ta ce ba zam
    mata girki d tukunya ba. Ya ce Muje gidn ganin
    nan. "a kofar gida ta zauna tana jiranshi, sai d y
    shiga sannan ta bishi. Tana tsaye tsakar gida
    tana jin rigimar d suke yi.Bishira ta dage ita fa
    babu mai yi mata girki d kayan aiki, shi kuma ya
    ce tunda ba a koya miki girki ba a gidnku dole ne
    in sa kanwata ta mini. Ta ce ya turo Fati
    mana,wannan maran kunyar yarinyar mata
    tarbiyya ba za ta zo mata gida ta zage ta ba.
    Ran Abba ya 6aci, ya ce Ga ki nan mara
    tarbiya,ina fada kina fada ina matsayin
    mijinki.,Ummi tafi ki tarbiyya domin uwar d ta
    bata tarbiyya ita ta bani har ki ka amince ki ka
    aure Ni. Ta ce, Ta baka tarbiyya ko ta asirceka?
    Ta mallake ka har baka ganin Mahaifiyarka d
    gashi sai ita. Zancen ya soki Abba sosai Har ya
    daga hannu zai mareta sai kuma ya fasa,ya juya
    ya fita. Fatanshi Allah ya sa ummi bata ji ba,dn
    yasan tsaf sai ta fada ma Umma. Tana zaune
    gefen rijiya ya nufo ta,Ummi ina kayan Miyan?
    tana nuna masa su tare d cewa 'Gasu ya
    ce,Dauki ki kai ma ummana. Har ta kai bakin kofa
    ya sake cewa "Ummi!"ta tsaya ya zo ya kalleta
    Ummi kin ji me Bishira ta ce? Ummi ta dube shi
    cikin ido,,sannan ta kalli hanyar fita. Naji duk
    abnda ku ka ce,Ya lumshe ido "Ummi dn Allah ka
    da ki fad ma Umma. Ta tsura mashi ido,bata
    ta6a jin Abba ya yi mata magana cikin tattausar
    murya ba sai yau tunda ta taso. Ta ce, "To." Ta
    juya, yasa ke cewa Ummi. a waiwayo Don Allah
    kin ji? kai kurum ta daga sannan ta fita Tafe take
    tana Mmkn me yasa Abba baya son Umma taji
    zagin da Matarshi tayi Mata? Hakika d taso
    Sanar da Umma amma yanda ya yi 'yar Murya
    yana rokonta sai t jure,koda taje gida bata sanar
    d Umma ba. Cewa tayi kawai ya ce a ma barshi
    sai dai cikin ranta ta tsani Matar Yaya Abba fiye
    d tsanar d ta yi wa Abba. Shi kuwa Abba duk
    wata hulda tsakaninnshi d matarshi ya dakatar d
    ita,saboda yana son nuna mata matsayin umma a
    gurinshi. In ya fita tn Asubahi bacce ke kawo shi
    gidan,wanka ma cn gdn Umma yake yi sai ya ce
    mata Bishira tana mkrnt. A cikin rana t 3 hnklnta
    y gama tashi,taje t fadawa umman Bashir,ta aiko
    yaje tayi ta fadan gami d zazzagnshi,ya bata hkr
    y fita. Amma sam Bishira, bai canza mata ba. Sai
    ma sabon salon d ya dauko na yn kaura daga
    falon zuwa dayan dakin d babu kowa,dk kayn
    sawanshi y tattara y koma can. Abba yana d zcy
    g taurin kai,Umman Bashir ta ce,"Yanzun in kin
    samu saukinshi to uwar goyonshi ki ka fada
    mawa, km gwada ki gani za ki gane ta fini a
    gurinsa. Sannan ki g aikin asiri. . Shi kuma zai je
    ya fada ma umma, dn yana son d dunkunan wata
    amarya d yake son karasawa ummi ta zun6uri
    baki bayan ta amshi kudin ta wuce tana yankun-
    kunai, ya ce "Ke!" ta waigo "Zo nan . ta dawo, Ya
    kama mata kunne, Kin san kwana 2 bn ta6a
    lafiyarki ba ko?to kiyi abn d yau zaki gwammace
    ba ki zo duniya ba. ya rankwashe mata kai,
    Sannan ta wuce tayi ce fanan ta nufi gidn Matar
    gidn tana zaune d kayan mkrnt a jikinta,,Ummi ta
    mata Sannu harara ta zuba ma Ummi, Ummi ko
    ta rama,sannan ta ce "Mijinki ya ce in zo in yi
    mashi sakwara d miya. "Bishira ta ce, To sai ki
    koma gidn ubnki ki dauko tukunya d murhu b dai
    nawa ba, Ummi ta ce, To ni dai gaskiya d ubana
    ba. Bishira ta taso tana cewa Sai na wa? Ummi
    ta ce, Oho,amma ba nawa ba. Za ta kai mata
    duka ta goce ta ajiye mata kayan miyan ta ce "
    Gashi sai kiyi, kila ma baki iya girki ba ne. Taje
    ta fadawa umma, Umma ta ce "Ke ummi karya ki
    ke daga zuwa zata hauki d zagi sai ka ce
    Mahaukacciya? To kije ki fada wa Abban in ya so
    sai kuje tare ya fada mata amma fa kada ki ce
    masa ta zage ki, ki ce masa dai yazo ya fada
    mata zaki tayata. Ummi ko kyn mkrnt ba ta cire
    ba ta nufi gurinshi,yana tsaka dinki taje,Ummi sai
    ce masa tayi ta ce ba zam mata girki d tukunya
    ba. Ya ce Muje gidn ganin nan. "a kofar gida ta
    zauna tana jiranshi, sai d y shiga sannan ta bishi.
    Tana tsaye tsakar gida tana jin rigimar d suke
    yi.Bishira ta dage ita fa babu mai yi mata girki d
    kayan aiki, shi kuma ya ce tunda ba a koya miki
    girki ba a gidnku dole ne in sa kanwata ta mini.
    Ta ce ya turo Fati mana,wannan maran kunyar
    yarinyar mata tarbiyya ba za ta zo mata gida ta
    zage ta ba. Ran Abba ya 6aci, ya ce Ga ki nan
    mara tarbiya,ina fada kina fada ina matsayin
    mijinki.,Ummi tafi ki tarbiyya domin uwar d ta
    bata tarbiyya ita ta bani har ki ka amince ki ka
    aure Ni. Ta ce, Ta baka tarbiyya ko ta asirceka?
    Ta mallake ka har baka ganin Mahaifiyarka d
    gashi sai ita. Zancen ya soki Abba sosai Har ya
    daga hannu zai mareta sai kuma ya fasa,ya juya
    ya fita. Fatanshi Allah ya sa ummi bata ji ba,dn
    yasan tsaf sai ta fada ma Umma. Tana zaune
    gefen rijiya ya nufo ta,Ummi ina kayan Miyan?
    tana nuna masa su tare d cewa 'Gasu ya
    ce,Dauki ki kai ma ummana. Har ta kai bakin kofa
    ya sake cewa "Ummi!"ta tsaya ya zo ya kalleta
    Ummi kin ji me Bishira ta ce? Ummi ta dube shi
    cikin ido,,sannan ta kalli hanyar fita. Naji duk
    abnda ku ka ce,Ya lumshe ido "Ummi dn Allah ka
    da ki fad ma Umma. Ta tsura mashi ido,bata
    ta6a jin Abba ya yi mata magana cikin tattausar
    murya ba sai yau tunda ta taso. Ta ce, "To." Ta
    juya, yasa ke cewa Ummi. a waiwayo Don Allah
    kin ji? kai kurum ta daga sannan ta fita Tafe take
    tana Mmkn me yasa Abba baya son Umma taji
    zagin da Matarshi tayi Mata? Hakika d taso
    Sanar da Umma amma yanda ya yi 'yar Murya
    yana rokonta sai t jure,koda taje gida bata sanar
    d Umma ba. Cewa tayi kawai ya ce a ma barshi
    sai dai cikin ranta ta tsani Matar Yaya Abba fiye
    d tsanar d ta yi wa Abba. Shi kuwa Abba duk
    wata hulda tsakaninnshi d matarshi ya dakatar d
    ita,saboda yana son nuna mata matsayin umma a
    gurinshi. In ya fita tn Asubahi bacce ke kawo shi
    gidan,wanka ma cn gdn Umma yake yi sai ya ce
    mata Bishira tana mkrnt. A cikin rana t 3 hnklnta
    y gama tashi,taje t fadawa umman Bashir,ta aiko
    yaje tayi ta fadan gami d zazzagnshi,ya bata hkr
    y fita. Amma sam Bishira, bai canza mata ba. Sai
    ma sabon salon d ya dauko na yn kaura daga
    falon zuwa dayan dakin d babu kowa,dk kayn
    sawanshi y tattara y koma can. Abba yana d zcy
    g taurin kai,Umman Bashir ta ce,"Yanzun in kin
    samu saukinshi to uwar goyonshi ki ka fada
    mawa, km gwada ki gani za ki gane ta fini a
    gurinsa. Sannan ki g aikin asiri. . Bishira t nufi
    gurin umma t same t zaune tana yankan ku6ewar
    miya. tun d a ka kawo ta yau ne rana ta farko d
    ta zo. Umma ta ce, "A'a Maraba d Bshra. shigo
    koda yake je ki gaida tsohuwa. Taje suks
    gaisa,Tsohuwa ta ce Ke dai wannan yarinyar
    kirkinki d sauki,a ce tunda ki ka zo unguwar nan
    baki ta6a zuwa kin gaida iyayensa ba? Umma t
    jiyo 6aram6aramar d Tsohuwa ke yi,d sauri tazo
    ta ce Tsohuwa b laifinta ba ne, laifin Abba ne. Ba
    sai ya kawo ta ba za tazo? Jin haka Bishira ta
    samu bakin magana,wlh Tsohuwa laifinsa ne nayi
    in zo ya ki,yanzun hk kararsa na kawo. in y fita
    tn Asubahi sai dare bana sanin shigowarshi.
    Yanzun ni tn jiya ma bn sa shi a idona ba,Umma
    ta ce Shi Abban ne ke hk? Ta ce IIlahi kuwa, ni
    bana son in je gidanmu in kai karanshi ne amma
    shi baya gani,yanzun fa ya tattare y koma dakin
    nan d ba kowa. Ran Umma ya 6aci, a irin
    tarbiyyar da ta yi wa Abba bata zaci zai
    wulaqanta mace ba, . Ummi tana shigowa daga
    Islamiyya ta ce,maza d sauri shagon yayanki kira
    mn shi. kan keke ta same shi yana t dinki, t shiga
    d sallama,sauran yaran shagon ma suna t
    dinki,ta ce yaya Abba Umma ta ce kazo yanzu.
    Ya dube ta me ya faru?Ta girgiza kai,bn sani ba,
    ta dai ce kazo. Take ya mike,ita km t fice d gudu.
    A ranshi ya ce ko yaushi Ummi zata yi hnkl t
    dinga tafiya irin t mata? Yana shiga gidn umma t
    rufe shi d fada,ba tare d tambaye shi dalilin shi
    na yi wa matarshi abn d yake mata ba. Ta
    ce,"Maza gata nan dakin Tsohuwa kaje ku koma
    gida ka bata hkr. kanshi na kasa bai ce kala ba
    ya nufi dakin Tsohuwa. Ya dube ta Tashi muje.
    Har daki suka shiga ya dube ta kiyi hkr. Ta ce, To
    nima kayi hkr. Ya ce kin ga matar d ki ke zagi ta
    baki gaskiya alhalin danta nake fushi. Ya ce ki
    kula kici albarkacinta karki sake ki km fadin wata
    mummunar magana a kanta,km hucewar da nayi
    da hkrn d na baki kada ki zata dn kin isa
    ne,umurninta na cika,ta ce to na daina. . Da dare
    gidn Umma ya je ya bata hkrn dn yaga ta dau
    zafi, ya ce, "Umma yarinyar nan bata kyautawa,
    abn d take min ni d har zan kai wa yarta kara na
    gaji. Umma ta ce, kada ka soma,kayi t hkr in
    girkin ne matsalarku tunda bata son tazo ta koya
    kai ai ka iya,sai ka ware lkc ka zauna ka dinga
    koya mata kasa tayi kana kallo har ta iya. Ya ce
    To, amma kin huce kin daina haushina,? Umma
    ta ce , sam ban jin haushinka Abba raina yana
    6aci ne in ji an ce ga laifinka, ya ce to na gode
    ummata. Shawarar Ummanshi ya dauka,ranar
    farko ya ce ta dora farar shinka fa sai da ya koya
    mata yadda zata dafata kashi-kashi,harkala 4.
    Sannan ya ce,tayi jajjage tayi tana wai-wai ita
    duk ta gaji. Yana gefe zaune d wayarshi yana ta
    Game sai d yasa ta tayi miyar komai yana nuna
    mata yadda zata yi. Sai gashi kafin wani lkc
    Bishira ta iya girki, gurin tuwo ne a ka danfi
    samun matsala,sukai kwana 4 suna yi yana
    gudaji. . Yanzu sun samu jituwa dk d dai abncin
    ma ba ya samunshi kn lkc sai dai kuma fannin
    tsafta.Duk da yakan zage ya gyara gidn d shara
    kullum in ya dawo Masallaci ya wanke bayi
    fes,cikin dakunan a nan matsalar take, sannan
    jikinta ma bata son gyara shi. Cikin haka ta kamu
    d laulayin ciki sun je asibti sun samu magunguna
    dk d hk amai ko ruwa tasha sai y dawo, dk hnkln
    Abba ya tashi y kira wayar Anti ya sanar d ita.
    Da dare tazo dubata ita d mijinta suka zo,sun
    same su Abba yana bata tea,ganin Anty,Bishira ta
    soma kuka wai ita zata bi Anty. Anty ta ce A"a ki
    zauna ga mijinki na kula d ke, ni dai bana zama
    in kin je gidana ba zai miki dadi ba. Sunyi Murna
    d Abba ya fada musu ciki ne, take Anty ta kira
    Mahaifiyarsu ta fada mata. "Tabdi!" in ji hjy. tun
    yanzun? To Allah ya raba lfy. Anty ta ce to sai
    anjima,dn jin yadda hjyr bata yi murna d cikin ba,
    km bata so Abba ya gane. Ta dubi Bishira, Momy
    ta ce a gaisheki d jiki, Bishira ta ce ba za ta zo
    ba?Rannan d muka yi waya d Anty Aisha ta ce
    min ita ko Momy taje / ZURFIN CIKI book 1 part 8
    ZURFIN CIKI book 1 part 8
    Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:01
    Ni kuma sai naga ta min qanqanta. Ummi ta ce,
    ahj kaima ka sai mota ne mu dinga shiga? ya ce,
    to xan siya mamana, ki dunga min addu'a kinji?
    umma ta ce, nayi murna abbana, ya yi abin
    hawa. bari in je masa albishir. tsohuwa ta taba
    baki, sannan ta ce, kullum burinku da tattalinku
    na ne sunan mlm ne, ita takwara kun maida ta
    baya. umma ta ce, sai na dawo. ta fice, dan
    tasan tsohuwa da mita. abba yayi murna samun
    abin hawa, domin da dan nisa in da ya ke xuwa,
    waton makarantarsu ummi, in ya shirya ya kanxo
    gidansu ummanshi ya dauki ummi su tafi. jwanci
    tashi su ummi an shiga aji uku, lkcn abba ya
    gama service din shi, ya amshi certificate. bayan
    sun je sun yi faretinsu. dakin umma ya dire, ummi
    tunda ya shigo take kallonshi da kayan yan
    bautar qasa. ita kam kayan suna birgeta, ya dube
    ta kallan fa? ta dauke kanta, sannan ta murguda
    baki, umma ta nufi kicin tana dariyar halin ummi
    da abba. dama ummin tana kwance kan kujera ne
    tana wasa da wayar umma, yace ta ga me kyau
    tana ta kallona, ba xa dai ki samu miji mai kyau
    kamar ni ba. . Ba ta san lkcn da ta ce, tir, da me
    kama da kai gara in mutu banyi aure ba. ya
    dubeta da sauri sannan ya dauki hijab din umma
    ya jefeta, tare da cewa, mummuna, qaxama gaki
    mahaukaciya. wama xai aure ki? sai kn
    mahaukaci dan umanki. ta hade rai tana
    kallanshi, ya ce daina kallona me kama da
    goggon biri, in kuma kika min wata magana in
    xane ki. fuu ta tashi ta shige uwar daki. tana jiyo
    hiransu da umma, in da yake cewa, naso a ce
    ummi tana aji uku ne lkcn da xan bar
    makarantantan mu bari tare, saboda sam bata ji.
    gashi akwai mlmn da aka samu a makarantan ma
    su bata yara, sannan tana da wata qawa da aka
    kama da wani malami a bayin makaranta. sai da
    taci duka sannan ta rabu da yarinyar. umma ta
    daff qirji tare da cewa, na siige su ni suwaiba, to
    ko amina ce qawan tata? abba ya ce, ba ita ba
    ce. umma ta ce, hu-um, to makarantar boko dai
    ba tilas, da yaro ya fada cikin irin wannan
    rayuwar gara a bar bokm. abba ya ce, ina ganin
    xan nemi koyarwa a makarantan, in naci sa'a an
    daukeni to sai ta qarasa har lkcn. . Abba ya ce
    Ina ganin zan nemi koyarwa a mkrntr in na ci sa'
    an daukeni to sai ta ci gaba hr zuwa lkcn d zata
    gama,sai in bar koyarwar. Umma ta ce,To hkn za
    a yi. Ummi km daga cikn dk take mgn ita 1,ta ce
    Da na shiga 3,ka ci gaba d koyarwa a mkrntrm ko
    dai ka ci gaba d hn ni sakewa? In yana aji
    numfashi mai karfi ma bana iya yin shi,Allah yasa
    kada a dauke ka. Murna kmr me gurin Ummi d
    taga an yi bakwai 2 Abba bai zo ba,hk na nufin
    ba a dauke shi a mkrntr ba. . Don hk ta ci gaba d
    tsula tsiyarta. Kwatam! a sati na 3 sai gashi ya
    zo daukarta suje mkrnt,hr kuka sai d ummi tayi
    don takaici. Daga dawowarshi km y dora mata
    daga in d ya tsaya,d rashin mutunci,hr t soma yi
    mishi fatan mutuwa,dn tana ganin matsawar
    Abba yana raye baza ta ta6a jin dadin rayuwar
    dny ba. Tunda cikin bishira ya samu t daina zuwa
    mkrnt, Abba bai matsa mata ba,amma d yaga t
    soma dan jin dadi,sai ya ce ta fara zuwa. . Haka
    ta ke zuwan yau taje gobe ta ki zuwa ta ce ba a
    komai hr lkcn biyn kudi yayi. Duk d tsadar mkrntr
    hk Abba ya fige ya biya,daga bisani ma sai ta
    daina zuwa, Abba ya kira Anty a waya ya fada
    mata Bishira ta ki zuwa mkrnt. Yaya-yayi ta
    ki,shi km gsky ta zo tayi mata fada,dn ba ya so
    su momy suga laifinshi., Don ko d suka je
    gaisuwar surukai sai d ta ce "Kada a katsewa
    'yarta krt"Anti ta ce za ta zo. . Ai kuwa ranar d
    Anty tazo taga ta kaici gidn Bishira,ko ina
    datti,Falon d ta leka dk kura d yanar gizo-gzo.
    Cikin dakin baccinsu kuwa ko ina yamutse d
    kaya,bngo dk t tofe shi d miyau,sannan g wani
    gwangwani madara gefenta ta kusan cika shi d
    miyau. Gashin kanta rabi an tsefe shi rabi ba a
    tsefe ba.jikinta fari sol tamkar bai ta6a ganin
    ruwa ba. Anty t doka salati tare d cewa Bishira
    me zan gani hk?Dan ubnki hk ki k dawo? Dubi
    gdnk?dubu kanki? A kanki a ka soma ciki?nan t
    zauna ta zageta tas, sannan ta taya t suka gyara
    gidn suna yi tana fada. Ta ce Hk ki ka ga ina yi a
    gidana?Ko sauran jama'a hk suke yi? Za ki sa a
    zagi uwarmu a ce an sangarta ki alhalin aikin
    gida dk a na sa ku.Sannan kin ki mkrnt,to ki sani
    kanki zaki cuta dn kuwa dk ranar d mijinki y
    zama wani abu 'yar boko zaya nema ya tafi d ita
    cikin lamuranshi. . Zan km hada ki d momy.byn
    sun gyara gidn t sata tayi wanka t dauki kaya
    masu kyau t saka. Gwangwanin miyau tasa t tayi
    jifa dashi,ta ce ki dinga saka sweet ko goro a
    bakinki zanje nan d sati 1 zan dauko momy muzo
    tare. kin san dai me zai biyo baya. Abba da ya
    shigo gdn byn Isha'i dk d cewa dare ne sai d y
    gane an tsaftace gdn,Domin kamshi tare d iskar
    da ke kadawa a gdn sun bayyana hk. Dakin ta da
    ya yi wa kaura yau kam hr bakin gado,ganin t
    cikin kwalliya yasa shi cikin wani yanayi wanda
    ya kwana 2 bai shiga ba. Ko abncin bai nema
    ba,ya shiga caftar Syy,wnd ita ma dk d tana
    laulayi tana ra'ayin hkn,don hk sai suka rankaya.
    Kwana 2 ya dan samu sauki kazantar dn tana
    tsoron momynsu tazo ta gani,sannan tana zuwa
    mkrnt. Amma d momyn tazo tayi mata fada t
    tafi,shi kenan sai ta koma gdn jiya,dama
    Hausawa sun ce mai hali ba ya fasa Halinsa.
    Haka dai hr cikin ya tsufa Umma tasa shi ya sayi
    dk wani abu da mai jego da jaririnta za su
    bukata. . Ita km ta daka yajin mai jego ta tanadi
    sabulun salo zuwa Kwallin da za a sa ma jariri.
    Wani dare Abba y kira Umma,Alhj ne y daga nan
    y sanr d su bishira bata d lfy,yana ganin haiuwa
    ce. Alhj d kns y raka umma hr gidn suka buga
    Abba ya bude,suka shiga.Ranar Alhj y yi burin
    mota,dmn d yana d mota yanzun sai su tafi
    assibiti. Bishira bata d juriya,dn hk sai raki take
    yi,tana fadin a kaita assibiti. A daddafe suka kai 4
    dare Ahlj ya je ya taso abokinshi suka kaita
    assibiti tare d su umma,karfe 8 na safe ta haifi
    danta namiji. . Umman Bashir d taji sai ta hau
    fadan me ya sa ba a sanr d ita ba?Alhj karami ya
    rufeta d fadan cewa,ita wace irin mutum ce? Sam
    ita bata son Alkairi ba,sannan ya fita ya yi wa
    Alhj babba barka,dg assibti gdnsu iyayenta suka
    wuce d ita ba tare d sun nemi shawarar mijinta
    ba ko ta iyayenshi. Hjy ce ta bada wannan
    umurnin,rai 6ace Abba ya zo gurin umma dn ita
    ta baro gurin ne d iyayenta suka iso. Ya
    ce,"dama umma umma haka akeyi sai a daukar
    wa mu2m mata a tafi da ita ba tare da neman
    izini ba?to gaskiya bazan yarda ba." umma ta
    ce,"ka kyalesu, Allah ya raya.shi kenan, tafiya da
    ita ba laifi bane tunda ita kadai ce a gidan ba mai
    kula da ita matsalar dai da basu nemi izininka
    ba." ya ce,"sai ka ce ba zamana take ba?
    wankan gidan addini ne?dama fa niyyata in kawo
    ta nan gidan ki lura da ita." umma ta ce,"to
    yanxu dai hakuri kawai zan baka,ka bar
    maganar." tayi ta lallashinsa har dai ya
    hakura,amma shifa ya dau alwashin sai ya nuna
    musu nasa ikon. umma ta hada abubuwan data
    tanada suka tafi da makota.bayan sun shiga
    gidan aka kai su gefen da maijego take. sun sami
    dakin tamkam da jama'a nan dai suka zauna aka
    gaisa,sa wani gani-gani ake musu ga talakawa.
    umma ta ce,bishira ina ummar taku mu gaisa?sai
    da ta yatsin fuska sannan ta kalli
    kanwarta"sumayy a kije ki cewa momy ga
    baki,koda yake kice mata yan gidan su Abba ne."
    Hajiya zainu tana zaune da kawayenta da suka zo
    barka, tana labarta musu rashin mutuncin dangin
    mijin bishira dashi kanshi mijin. ta ce,"yau
    kwananta uku tunda tazo gidan nan bashi ba
    danginshi,kuma yanda bishiran take fada mana
    laifin masu rikonshi wato wan ubansa da
    matarsa. sun mallake yaron sai abinda suka
    ce,hajiya nafi ta ce,"ku nuna musu kuskurensu ne
    yanzu haka tunda kika ga sun mallake shi kila
    shine mai dan samun gunshi suke ci." Hajiya
    sabuwa ta ce"shi yasa auran talaka ko tsiya,yar
    wajena Amina da tazo min da wani wai sun hadu
    a ummara,koda na bincika sai na tarar likita
    ne.karamin likita ubanshi dashi ya dogara na ce
    ba dani ba." Hajiya zainu ta ce"ai gara shi
    wannan fa tela ne." "TELA?" kawayen suka hada
    baki, ta ce"au dama ku duk fadan da nayi lokacin
    biki baku ji ba? tabi ta nace sai shi gashi nan
    yanzun ya wulakanta mu." Ta dube su d
    wulanqacin da ya fi Ki haihu kwana 3 tun dg
    asibiti miji bai kuma bi ta kanki ba? Hjy Nafi ta
    ce in bai zo don kowa ba ma yazo dn dansa.
    Zainu ta ce Ina nan ina jira ko shi ko danginshi
    domin........ Sumayya ce ta katse su da sallama.
    Sannan tace momy wai kizo ga yan gidan su
    Abba sun zo. su duka suka mike ita d kawaynta
    suka nufi gurin su Umma. Hjy Zainu ta kalli gurin
    d su umma suke,sannan ta kalli Bishira,
    wadannan sune 'yan gdn Su Abban? Bishira ta ce
    Eh ummar tasa ce gata nan. ta nuna umma Hjy
    zainu suka kalli juna d kawayenta sannan suka yi
    'yar dry wanda hkn ya kashe jikin umman. Tasan
    cewa akwai wani tanadi d a ka yi mata. Hjy
    Zainu ta ce d kawayenta ku mu zauna,aikin
    zaune yafi na tsaye. Suka zauna. Ta kalli umma
    Dama ko ina son ganinki,ke ce uwar goyon tasa
    ko? ta ci gaba To gsky ba ki yi wa dnki tarbiyya
    ba,sbd rashin mutunci a yi maka haihuwa amma
    kwana 3 ba zuwa ba aike? Kuma sai yau za ku
    kwaso kafa kuzo in 'yarki ce zaki so hk?umma
    tayi shirun tana tunani, ta kuma rasa me zata ce
    dn tund take ba a ta6a ci mata mutunci ba irin
    wannan ba. Amma ita bata iya fada ba,dn hk sai
    ta ce, To Hjy a yi hkr, bn san cewa Abba bai zo
    ba,Amma zan tsawata mishi,dn kuwa bai kyauta
    ba. Sai dai km shi ma bai so yadda a ka dauko
    masa mata ba izininshi ba,dn ya same ni d
    fushinsa ya ce min shi ba ya son wankan gidan
    nan,sannan ba a yi shawara da shi ba a ka taho
    d ita nan. kin ga km hkn bai dace ba..........
    "Dakata min Hjy zainu ta katse ta Shi ne ya
    haifar min 'yar d hr zan tsaya neman izininsa?
    shi kuma a wa? Ramatu mokociyarsu ta ce "Miji
    km hjy ai ba abn wasa ba ne. hjy nafi ta ce ko?to
    ke kinji hjy Zainu tabdi!Tun farko kuskuran naki
    ne da ki ka bar 'yarki tayi irin wannan auran na
    rainin d tsiya. Umma ta ce d abokan tafiyarta
    wadanda ko dan (ba) ba su ce ba, ta ce kuzo
    muje"Ta dubi hjyr "Allah ya baku hkr.Hjy zainu ta
    ce Ai ban ga gama maganata ba. umma ta ce,To
    fadi ina jinki. Hjy zainu ta ce Sako ne zuwa ga
    danki ki fada masa ba komai muke nema dg gare
    shi ba,abn d ya siya ma na yaron dk mun canza
    wasu sdb dk 'yan gida ne. Bukatarmu ya zo ya yi
    wa yaronsa huduba,in km ya kai gobe za mu yi
    masa d kanmu. umma ta ce Abba ya yi wa dansa
    huduba,tn lkcn d a ka haife shi. Hjy Zainu ta
    ce,To ai bai yi shawara d uwar yaron ba,ko d ya
    ke ga ki dawa zaiyi shawara? Uwar d ta haife shi
    ma bata zama komai ba, a dai ji tsoron Allah.
    umma jiki ba karfi ta fito. Su Ramatu suka biyo
    ta hr kuka sai d umma tayi dn takaici. koda taje
    gida sam bata fada ma kowa komai ba,illa dai dk
    wanda ke gidn yasan yau umma tana cikin 6acin
    rai. Hatta ummi da bata d kn gado sai d tayi ta
    tambayrta,umma baki d lfy ne?ta ce Eh,kaine ke
    ciwo. Da ta zauna sai ta shiga tunani so take
    lallai sai ta gane aibnta,ko kasawarta akn Abba.
    Ta kasa fahimtar mallakr d a ke fadin tayi wa
    Abba. Tana ganin nuna tsanarta ga Abba shi ne
    mafitarta. Abba ne ya katse mata tunani d cewa
    Ummana ina t zuwa ba kya nan. Ta dube shi g
    mmknta ba ta iya bayya tsanarta g Abban,
    maimakon hk ma sai ta samu kanta da cewa
    Naje ganin jariri ne. Ya shiga ya zauna kusa d ita
    t dube shi Yanzu Abba dm bn isa in fada maka
    mgn ka ji ba?Dama kin zuwa kayi ka duba
    matarka da danka? Ya shafa kai,Umma anjima d
    dare zamu da su Ahmad ni haushi sukai bani. Ta
    ce to ka tabbata yau din kaje,Sannan ko sun
    nuna ma fushinsu naka kawai ka ba su hkr,Ya ce
    to umma ta ce Na sanka d zcy ne. Ya ce to zan
    kiyaye Umma. Ya kuma dabn ta ummata yau na
    ganki a yanayi mara dadin gani. ta dube shi kaina
    ke ciwo Abba na kuma sha magani. Da gaske
    ciwo kanta ya dinga yi dn damuwa. Yace Allah y
    kara sauki. Ya fita. Da Ahmad d Muktar suka
    je,sun ci sa'a Alhjn yana gari. suka shiga suka
    gaishe shi suka kuma yi wa juna barka. Sam ba
    ruwanshi da matsala,Suka shiga ciki tare d
    Sumyya,sn samu Aisha ta zo ita d mijinta.
    Bishira km hade rai tayi lkcn d taga su Abba? Su
    Muktar suka dauki jariri,sannan suka gaida mai
    jego. ta amsa tana musu wani kallon daga ina?
    Aisha ce taje ta sanar d uwar tasu. Nan ko ta
    shigo ta samu su Abba d abokanshi. Ta shiga
    zazzaga mishi masi fa,wai sai yau yaga damar
    zuwa?Ai ta samu lbrn yadda yake wulaqanta
    mata yarinya. ta ce km a bakin mahaifiyarka naji
    kaji tsoron Allah ka talike a gurin uwar goyonka
    sai yadda ta ce. to 'yata tafi karfinta. Abba sam
    ba zai juri ji ba,dn hk ya mike ya fita. tana ta
    cewa saurare ni ko waiwayowa bai yi ba. Su
    Muktar dai suna ciki suna bata hkr ya kira wayar
    Ahamad ya ce zan tafi in ba za ku fito ba. Ya
    kashe ba tare d jiran asmar Ahmad din ba, hk
    suka fito. Muktar ya ce Tabdi! lallai matar
    gidannan bata d mutunci.Ahamd ya ce ka fada
    ma mai gidan Mana. Abba ya ce Ni sai ma in
    sakar Musu 'yarsu "Kul in ji Muktar, Kada kayi hk
    Ahmad ya ce, Ashe hr umma suka yi wa rashin
    mutunci dazu? Abba ya ce Ummata?Muktar ya ce
    Eh, bayn fitarka take fada,Abba ya yi shiru dn
    takaici. Gidanshi ya wuce,gado ya hau ya
    kwanta. . Tabbas sun ci zarafin ummarshi,dn ya
    ganta cikin yanayin da bai ta6a ganinta aciki ba.
    Ko me dame suka fada mata?Umma bata
    cancanci cin zarafi ba.Ranshi ya kai makura
    gurin 6aci,ya rufe gidn ya nufi gdn su Umma.
    Lkcn d ya shiga umma ta nufi dakin
    Alhj,Sallamarshi ce ta tsaida ita,ya shiga dakinta
    ta dawo ta shiga. Tana cewa Abba hr ka dawo
    daga gurin ma su jegon?bai amsa ba,kanshi na
    kasa,dmn sai ya samu kansa da jin kunyarta
    sakamakon abn d aka mata sbd shi. Ta ce lfy
    Abbana?Ya dube ta,maimakon amsa sai ya ce
    umma me suka ce miki dazun d ki ka je gidn?
    Tayi dn yaki ita a dole Murmushi , Na me Abba?
    ya ce mamn bishira ta ce taci miki mutunci ko?
    Umma tayi 'yar dry,sannan ta ce ko daya ta dai
    fada maka hk ne dn kaji haushi. Ta ciga ba d
    cewa,Abba dn Allah ka bi sannu hr t dawo...... Ya
    ce umma na san sunci miki zarafi sosai "ZURFIN
    CIKI' ne da ke umma shi yasa ki ka shanye,
    amma yanayinki dazn y nuna.Umma b zan zauna
    d matar d baya san darajarki, dk kuwa yadda na
    kai sonta,ina ga zamanmu ba zai yiwa d bishira
    ba. Umma ta ce "Kai! Kai!! kul na sake ji zanyi
    fushi d kai me tsanani Abba,dk hakkinsu d ke
    kanka matarka d danka ta ka sauke su,kuma
    koyaushe kaje ka gansu, ba km na son su Alhj
    suji wannan zancan. Ya ce yanzun hk zan zauna
    umma cikin 6acin rai? Tunda na auri matar nan
    bn huta ba,kema baki daina shan zagi ba? umma
    ta matso kusa da shi ta dafa kafadarshi. Abbana
    ka sani cewa ba a toru ka dny dn k huta ba,nawa
    ganin duk wanda a ka haifa daga ran d ya diro
    dny y gama hutu komai jin dadinsa,komai
    kudinsa,ko mulki. Hutu daya ne in ka mutu ka
    sadu d rahamar Allah,ita kuwa Rahama bata
    samuwa g wanda bai bi Allah d manzo ba. Bn
    Allah kuwa shine kada ka bata masa,kabi dukkan
    abn d Manzonsa ya yi umurni,Sannan ka hanu
    daga abn d ya yi hani. Aure bautar Allah ne Kum
    sai kayi hkr sannan za ka yi bauta d kyau. hk dai
    umma tayi ta wa Abba nasiha hr zcyrsa t sauka,
    sannan sukayi Sallama. Washe gari misalin karfe
    2,Abba ya dawo gida dg mkrnt d yake koyarwa,
    dn suna ta shirye-shiryn jarabawa (J.S.C.E.) Su
    ummi ne za su zana,wnk y fito sai ga wayr Alhj
    ta shigo.Y daga cikin girmamawa. Bayn sun gaisa
    Alhj ya ce Abbana kana ina ne? Ya ce ina nan
    gida.Alhj ya ce kaje gidanmu ka amshi mukallin
    dakina ka shiga kasa mukallika bude dirowar nan
    tawa,zaka g wadansu ta kardu irin littafin nan na
    rubutu. kabi a hnkl za ka g wani a samnshi an
    rubuta Alhj Sale Jigawa,d ajami ne rubutun,maza
    ka kawo min. Abba ya ce to.,Yana cikin duba
    littattafan sai ya ga wani an rubuta wasiyya,dk
    littattafan d ajami Alhj yake rubutu, Abba ya dauki
    littafi ya bude shafin farko an rubuta........ Babi
    Na Daya "Ni Alhj Sulaiman, nayi kudirin ko bayan
    raina 'yata Habiba (ummi) zan aurar d ita ga dan
    Idrisu(Abba). Da sauri Abba ya rufe littafin
    gabnshi yana wata muguwar faduwa,ya sake
    budewa ya kalli kwanan wata. Alhj yayi rubutun
    ne ranar d a ka haifi ummi,Ya yi sauri ya maida
    komai ya dauki wnd aka aiko shu yana zufa ya
    kalle dakin ya maida wa umma makullin ya fita
    da sauri Ya buga mashin can ya hango ummi
    suna dambe da wani yaro an raba su ta tirje
    kafafunta ba ko takalmi, mayafinta taci damara
    da shi. Ya ce "Ke! tn dg nesa ta jiyo muryar
    Abba,ya yi mata dakuwa ta kwashi takalmanta a
    hannu ta yanka d gudu. Yabi ta da kallo hr ta
    shige gida ya lumshe ido tare d fadin "Innalillahi
    wa'inna ilaihin raji'un."Me ma ya kai shi bude
    littafin wasiyyar Alhj Babba, Duk garin kano akwai
    mutumin d ya tsana irin Ummi??
    @BABA MONO HAXOR


    No comments:

    Post a Comment


Pages