BAKIN CIKI (TRUE LIFE STORY) 2 to 1
Ta wuce inda aka aiketa kamar zata tashi sama sbda saurin ta dawo gida.Ta zubewa inna cefane,ko zama bata yi ba ta fara fadin "inna mama na cikin hankalinta kuwa? Tace,me tayi? "Kin san danliti ya dawo....""Danliti?" Waye shi? Dan gidan buzu mai shayi fa inna."Oho ,ina jin ki me yayi? Lokacin da aka yi bikin yaya Abdulrahman danliti yaga mama ya nuna yana son ta wlh a lokacin ko kallonsa bata yi amma ban san yadda aka yi ya shawo kanta ba,ynzun nan na gamu da ita Ta fito shagonsa leda cike da kayan sweet." Inna ta dafe kirji ido waje,mama fa kika ce? Wlh inna ni kaina mamaki ya kusa kashe ni.Danliti dan iska!"Inna tace,mun shiga uku ni saude wai! Ban ga ta zama ba dole in bincika na tabbata gidansu ba'a sa ni ba! Kai mama kamar mai hankali,me zai tsone mata ido a wajen yaron nan?Kai Allah ka shirya mana yara.Bari babanki ya shigo Insha Allahu yau din nan za ni gidan gara a yiwa tufkar hanci,kar ya kai mu ya baro!" Ya kamata inna,ni ina ganin ma kamar fada suka yi da Al-ameen don tun dawowar ta bata so ayi maganar sa."To ba sai ta fadi ba,ko yayyinta sun isa su kira shi su sasanta su balle ga iyayensa a gari."Ni ma dai hakan na gaya mata. Tace min babu ruwa na" "ita mama din ta fadi hakan? "Ko yanzu ta maimaita min kiris ya rage mu yi fada a titi,inna ta kuta,ta numfasa,kai jama'a yara halin su sai su,Ita fa ta kawo shi ba dole aka yi mata ba?Ta zabga tagumi bakin tana maimaita salatin Manzo,Da azahar mahaifin baraka ya shigo gida,inna saude ta maida masa halin da ake ciki.Nan da nan ya bata umarnin taje ta bincika,ai bata bata lokaci ba,cikin tsakar ranar nan ta kama hanya ta nufi gidan uban dawaki.Umma na daki tare da abban shi ma shigowarsa kenan gidan aka gabatar masa da abincin sa yana ci.-Inna ta shiga suka gaisa sannan suka koma dakin umman.Bayan sun gaisa da en hirarrakin zumunci kafin tace.magana ce tafe dani yaya amma ki duba ko alhaji ya gama cin abincinsa zan so in fade ta a gabansa."Nan take jikinta ya mutu,tace me ya faru saude?"To magana ce data shafi mama na rashin jindadi shiayasa nace ba zan bari ta kwana ba dole in zo in bincika,sai dai alhaji shi yafi dacewa ya sani,tunda nayi sa'a yana nan.Tayi dan tagumi......Subhanalillahi!Bari in yi masa magana.Ta mike jiki a salube ta shiga dakin abba ta iske ya kammala tace,wai magana ce tafe da saude idan ka gama ka taso muje,To muje gani nan".Ta gyara zama ta maida musu abinda baraka ta gaya mata umma ta shiga tafa hannu,abba kuwa sai daya mike."Kar dai ace shi ne yazo jiya da daddare?Lallai biri yayi kama da mutum,ina maman take? Umma ta dube shi ido taf da kwalla,tana daki. Kira min ita!Ta mike ta fita,har suka dawo tare babu wanda ya tanka sbda tsabar mutuwar jinin jikinta,a darare ta karaso dakin tana fadin,inna sannu da zuwa."Ta zuba mata ido,ke ma sannu."Ta gaishe da abba da umma na mata kallon mamaki,ta dube shi suka hada ido,tace abba ga-ni" yace,wanene yazo gun ki jiya? Ta sunkuyar da kai,tayi shiru,ya daka mata tsawa,ko baki ji ne?Nace waya zo gun ki jiya? Tana rawar lebe tace dan-liti?"Kin kuwa san ko waye danliti a garin nan? Tayi shiru,mama ni kike so ki mayar tsohon bnza,ki tozarta?jiya me na gaya miki? To ni ba hayaniya na kira ki mu yi ba domin a iya sani na ke mai hankali ce,kin san abinda ya dace,kin fi kowa sanin cewa saura 'yan watanni suka rage bikin ki.Sannan idan kika nutsu kika yi tunani ba mutuncin mu bane daga ke har mu ace an gan ki,kina karakaina a shagon wani ma,balle danliti sbda haka nake umurtar ki daga rana mai kamar ta yau,bana son in sake jin wani labari makamancin wannan!Ina fatan kin fahimce ni? Ta kara sunkuyar da kai yayin da idanuwanta suka fara tsiyayar ruwan hawaye,umma ta muskuta ta karbe "kin bani mamaki ba kadan ba mama,wai ma in tambaye ki,me kike nufi da bin sa har shagonsa? Shiru babu amasa,umma ta cigaba,wannan katon sakarci da me yayi kama?A zaton ki abin birgewa ne yadda 'yan mata ke tsayuwa kofar shagon samari suna amsar abin hannun su?Ban taba zaton hakan zai fito daga gareki ba mama kuma mun saurara miki ne kawai sbda wannan shine karo na farko da irin haka ta faru!" Inna tace,kin ga gidan nan da dukkan jama'ar gidan dake cikin sa ana ganin girma da mutuncin su musamman mahaifnki,don girman Allah kar ki bari wani ya rusa wannan ginin,ya hure miki
kunne ya kai ki ya baro,kin ji mam? Ta goge
kwalla bata ce uffan ba,abba yace,to mun ci mun
rufe anan bana son ki sake aikata wani
abinda zai sa ayi miki zama irin wannan,kin ji ni? Ta
amsa da kai tana goge kwalla.umma tace
tashi maza muje ki dauko min ledar kayan da
aka ce ya baki,a iya sani na dai baki da yunwar su,maza
tashi muje!Ta mike da kyar umma ta tasa
ta suka je dakin ta dauko ledar.Umma ta
fizge cikin zafi tace,Allah yasa in sake gani ko ji sai kin sha
mamaki!" Ta fice ta bar dakin,ta bar
mama cikin tashin hankalin da bata taba jin irinsa
ba,har inna ta gama zamanta ta bar gidan mama na aikin
kuka a daki domin dai tamkar sun kara
debo soyayyar danliti ne sun kara antayawa
cikin zuciyarta.Ita wannan ranar da suke kwakwazon
an sanya mata ta jima da manta saurayin
ma balle ranar,ba shi a idon ta ko birnin
zuciyarta.Al'amarin ya daurewa iyayenta
kai,shin wai me mama take nufi da kukan ta?
Tambayar
zukatan su kawai suke yi amma basu da
tabbacin amsa.Karfe takwas da rabi cif!
Lokaci ne
da motar danliti ke fakin a kofar gidan uban
dawaki,kai tsaya ya aiko yaro a kira masa
mama,abba na nan a falo yana gadin
zuwansa
don haka yace da yaron yaje yace tana
zuwa. Umma ta fito masa da kullin ledar kayan
kwalamar da ya ba mama Abba ya karba
ya bi
bayan yaro kamar jiya,yau ma yana
harde jikin
motarsa yana kada mukullai sai dai yau kananan
kaya ke jikinsa,gaba daya ya firgita kofar
gidan
da kamshin turare.Yana hango uban
dawaki
tilasa ya gyara tsayuwa yana 'yan kame kamen
gulma ko kafin ya karaso ya tsugunna
yana
fadin,sannu alhaji,yace yauwa sannu,ya
sake
fadin ina wuni? Lafiya kalau,mike abin ka,magana
zamu yi,ya mike a hankali yana sunkuyar
da kai
kamar muminin gaske.Abba yace
magana guda
daya ce nake so zan gaya maka danliti,'ya ta
sakeena na riga nayi mata miji,tuni aka
sa musu
rana har ma lokacin ya kusan zuwa da
yardar
Allah sbda haka ina rokon ka da girman Allah
kayi hakuri ka nemi wata,daga yau kar ka
sake
zuwa gun mama don tana da miji,ina
fatan ka ji
ni? Ya dan yi shiru jim kafin yace naji alhaji
amma nima ina roqon arziki ka bar ni in
rinka
zuwa muna gaisawa,tnda ba'a daura
ba.Wlh..."Abba ya katse shi,ba zai yiwu
ba danliti domin koda babu alkawarin wani akan
mama kai
kanka ka sani zai yi wuya ka sami
auranta,sanin
kanka ne kaf garin nan babu wanda ya
san tushenka,kaje kayi tunani mana.Ya saki
baki
yana kallon abba ran sa a bace,abba ya
mika
masa keda yace ungo nan,yasa hannu ya
karba kafin ya cigaba da fadin,abubuwan daka
bata ne
dazu tunda ba auranka zata yi ba bai
kamata ta
amshi kayan ka ba.Don Allah kayi hakuri
ka nemi daidai kai,sai da safe.Ya juya ya shige
gida
abinsa ya bar danliti a tsaye.
)Ya kara harde kafafuwansa yana irin
murmushin mugunta,sannan yace ko
banzo ba ita zata zo wajena,koda kuwa kasheta
zaku
yi ta
dawo.Dama ai zuwan nawa na hure
kunne ne ba
wai neman nake da gaske ba."Yayi er
budurwar dariya ya bude motar sa ya shiga ya sake
fadin,sai ni dan gidan buzu mai shayi
taba ni
kaga tsiya da bala'I!Ya ba mota wuta
yaja ya bar
harabar gidan hankalinsa kwance.Sabanin mama
da take ji kamar ta saci jiki cikin daren
nan taje
wajen danliti shiyasa tayi ta leken
falo,amma
kash!Abba da umma sun ki tashi har dare yayi
sosai suna tattauna zancenta.Daren nan
bata yi
barcin kirki ba sbda bakin cikin an hana
ta fita
ganin danliti.Gari ya waye ko alama umma ta ki
sakar mata fuska,sam abin bai dameta
ba Allah-
Allah take yi kowa ya kama
gabansa,itama ta
samu ta sulale,ai kuwa abba na fita karfe goma
umma ta gama abnda take yi,ta dare
gado kamar
yadda ta saba barcin safe,mama ta gama
caba
kwalliyarta ta sadada ta bar gidan.Ta kwarara
sallama kofar shagon danliti,ya taso cike
da
fara'a yana amsawa kafin yace,a zatona
ke ma
zaki juya min baya ne,har na fara shiga damuwa,jiya
sam ban yi barci ba.Ta dube
shi
cike da tausayi tace nima haka danliti ko
gyangyadi ban runtsa ba,me zai sa na
juya maka
baya alhalin na san cewa nima zan cutu? Ya zura
mata ido a marairece yace,abbanki ya
nuna baya
so na ban san yadda zanyi da rayuwata
ba
sakeena,kar ki bari ciwon zuciya ya kama ni.Kwalla
suka taru cikin idanuwanta tace
ka
daina fadar wannan maganar don
Allah,in ka ga
na rabu da kai to sai dai su kashe ni in
daina numfashi,zuciya ta kai take so kuma
bana
ra'ayin auran kowa face kai." Kwalla suka
zubo bisa kuncinta.Da sauri ya
tauko sabuwar tìshu kware ta ya yago ya
miko mata,"share hawayenki, ki daina kuka.Na
yarda
dake sakeena,amma mece ce mafitar
mu? Ta
dan kada kai tace, "zanyi tunani,ka ban
dan lokaci kadan,zan samo mana mafita.'ya
daga
kanta ya fito ya gyara zaman benci.Yace
zauna
kiji
Ta zauna gefe shi ma ya zauna ya fuskanceta
sosai yace,me zai hana ba zaki gaya
musu ni
kike so ynzu ba?Ta daga ido ta dube
shi,jim,amma ba tace komai ba,yace "kar
kiji tsoron komai kai tsaye ki gaya musu ke
kin
sauya ra'ayi ni kike so,za'a yi miki tilas
ne?Dole
a baki wanda kike so,don babu wanda zai
zauna miki da shi,idan kuma kina son in rasa
raina ne
shikke nan........Ta kada kai tace,"nace ka
daina
fadar rasa rai danliti idan ka mutu nima
mutuwar zan yi.Ka kwantar da hankalinka insha
Allahu a
yau zan gaya musu na sami sauyi wanda
hankalina yafi kwanciya."Ya dafe kirji,ya
lumshe
ido yace,kin sa naji sanyi cikin raina sakeena.Ya
bude ido ya bi ta da kallo ya cigaba,idan
kika yi
min haka kin gama min komai sarauniya
ta,ba
zan cika baki ba sai mun yi aure zaki ga tsantsar
son da nake miki,bana jin akwai wata 'ya
mace a
fadin duniyar nana da zata sami irin
gatan da zan
nuna miki." Tayi dan murmushi tace,Allah ya
nuna mana,yace amin.Ya dan gyara
zama ya
sake gadin,"wai sakeena kin san cewa
kin fi
kowa kyau a duniyar nan?Ta saki baki,ido waje
tace,duk duniya? Wlh duk duniya babu
mace mai
kyau irin naki,ta kada kai tana murmushi
tace,"ka
daina fasa min kai danliti,ni na san ban kai ka
ba,ya washe baki ya nuna kansa ya9e "ni
kuma?
A'a ni dai kike son ki fasawa kan,ina ni
ina ke?
kin gan ki kuwa?kin ga wannan dan bakin naki
dagwas ba karamin kashe min jiki yake
ba."Ta
sunkuyar da kai tana 'yar dariya ya bita
da kallo
yana shafo habarsa."Mama!" Muryar kawai taji
anyi mata wani gigitaccen kira,gaba
dayan su
suka kalli mai magana,ta bi shi da kallo
babu
tsoro ko wata fargaba tace,ah!yaya ali! saukar
yaushe?"Ya kara tsuke fusk,yace me kike
yi
anan?"Tace me kuwa?Ba komai,taso
muje
gida,kaje ina zuwa,"ina wasa dake ne? nace ki
taso mu wuce." "Ta dubi danliti suka
hada ido
yace,tashi ku tafi sai wani lokaci ko?Ta
dan
numfasa ta mike ta wuce,yaya alin dake tsaye,ya
bi ta da sauri ya sameta,"mama,wai
mafarki nake
yi ko kuwa gaske ne?Ta yamutsa fuska
"da aka
yi me?" Zaune na gan ki kofar shago kina hira da
wani...." 'Wani? Ba ka ma san danliti
ba?"Shut up
don Allah!waye danliti kike gaya min
magana ba
dadin ji?Hauka kika yi?Ina mutunci ga'ya mace
tana hira da maza a kofar shago gaban
jama'a?
Ban san ki da wannan ba,yaushe kika
canza
mama? Ta ballo masa harara ta ja dogon tsaki ta
kwahsi sauri ta wuce shi,shi ma ya biyo ta
yana
fadin,ban gane nufin ki ba?"Ta juyo ta
dube shi
tace,wai menene yaya ali?"Shi kike so?" 'Ai
kaji,menene na sake tambaya?
ya kara cika da mamaki,'Ban fa gane shi
ki
ke so ba mama.Ina Al-Ameen din?" Ido
jajur! Ta dube shi,"kai ka san wannan sunan,don
girman
Allah ka kyale ni da tambayoyin nan." "Ba
zan
kyale ki ba Mama,hasali ma sai na gaya
wasu Abba.Wannan ai zubar da mutunci ne da
cin
amana!Me ya tsone miki ido a wajen
Dan-Liti?Ke
ma kin shiga sahun 'yan matan da yake
ruda da kyan sa ne?Kai na ya daure Mama.Allah
yasa
abinda na ke gani da ji ba gaskiya bane."
Da
gaske ne yaya Ali! Kuma ko baka gayawa
su Abba ba,ni da kaina zan gaya musu."Ta
zura da
gudu ta bar shi tsaye, shakare da
mamakinta.Kafin ya iso gida kansa,ya
kusa
fashewa sbd tunani da al'ajabi.Rokon Allah kawai
yake yi Allah yasa mafarki yake yi. Kai
tsaye
sasan su Mama ya zarce.Suna tsakar falo
umma
ta tirke ta da tambaya,"Idan biki gaya min inda
kika je ba sai na sumar dake yau a gidan
nan!"Yayi sallama.Umma bata iya
amsawa ba,sbd
bacin ran da take tare dashi.Ya-ce,'yanzu
na koro ta daga shagon Dan-Lati suna
zaune bisa
benci suna hira Umma.Yaushe Mama ta
sauya
haka? Tuni Umma ke sallallami,ta dafe
kirji ta-ce "shagon Dan-Lati ki ka koma Mama?Mu
kike so
ki zubarwa mutunci a garin nan? Ai kuwa
baki
isa ba,ba ki isa ba Mama!'Ji ka ke tim! Ta
rufe ta da duka ta ko'ina.kafin yaya Ali ya kawo
mata
dauki,ta sha dan banzan duka.Kukan ta
ya watsu
cikin sassa,matan gidan da kananan yara
suka sheko don ganin meke faruwa?Al'amarin
ya
daure masu kai,ganin Mama na birgima
tsakar
falo tana ture hannayen Yaya Ali dake
kokarin rarrashinta
[11/01 19:21] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***2(TRUE LIFE STORY)
Wa ya mutu Ali? "suka tambaya,yayin da
umma
ta fito daga daki dauke da wayar rediyo
kafin su
yi aune,ta fara tsula mata.Haba gaba daya
matan suka cafke hannun Umma, 'Hajiya
Halima!
Lafiya wannan abu haka?Me ta yi da zafi
irin
wannan duka?" Umma na haki tace wai yarinyar
nan ita ce zata siyar mana da mutunci?
Ta rasa
wanda zata tsaya da shi, sai Dan-Liti?
"Dan-Liti?
Waye Dan- Liti?"Dan gidan Buzu mai shayi mana!
Yau kwana uku kenan muna fama da ita
ta rabu
da yaron nan,ta ki! Jiya yazo kofar gidan
nan.Alhaji da kansa ya same shi ya gaya
masa tana da rana a kanta.shine don dibar
albarka ta
bi shi shagon sa,yanzu Ali ya ganta ya
koro ta!
Wace irin tijara ce wannan sbd Allah!
Tuni suke kallon juna suna tafa hannu,hajiya
hajo tace "danliti kuma?Waye bai san
tarihin su
ba a garin nan?Yaron da tun tasowar sa
garin
nan basu da aiki sai bata 'ya'yan mutane koda
baki da wayau sosai ai kin yi dan
hankalin da
zaki gane buzu mai shayi kasurgumin
kwarto
ne,shi kuwa danliti kananan yara sau nawa ana
kama shi dasu?Ko kin mance ranar da
dubu ta
cika suka ci shegen duka.Danliti ya sha
da kyar
shi kuwa buzu ya shura barzahi?Me ya dawo da
shi kike kwadayi da har idon ki ya rufe
kika kasa
duban kazantar dake tare dashi?Hajiya
Gaje tace
"duk ba ma wannan ba kina nufin zaki fasa auran
Al-ameen ne?Umma tace,karya take yi
sai dai
bayan ran mu,bari kuma alhajin ya
dawo,yau din
nan zai maida ta minna tnda zaman naki anan
abinda ya haifar kenan!Ta tashi da gudu
ta fada
dakinta har da danna sakata ta bar su
nan suna
maida yadda aka yi. Shi dai yaya ali tunda ya
sunkuci jakar sa
ya
fada dakin mahaifiyarsa bai sake
kyakkyawan
motsi ba sai tsabar tunani.Muryar
mahaifiyarsa yaji a kansa tana fadin,"kai kuma
yaushe
ka
shigo garin?"Firgigi ya dube ta na'am!"Ta
zura
masa ido,nace yaushe kazo?Ya sauke
gwauron numfashi yace,"zuwa na kenan
inna".ciwon daya
sami mama,ai ya same ni domin jinin mu
daya......"Gafara can sakarai kai ka san
wannan,da su ma sun san cewa jinin ku
daya ba'a hana ka auranta ba ai sbda haka
ban ga
dalilin dogon tunanin da kake yi ba,don
daga ita
har iyayenta basu san ka na yi ba!Gara
tun wuri ka halkantu ka gane cewar alhakinku ne
ya
kamasu!Idan ba haka ba,ina mama,ina
danliti?
Marasa asali da tushe ga tarin abin gori
da na kunya a jikin sa?"Ya dafe goshi
idanuwansa suka
kara kadawa,yayi hucin zafi ya
dubeta,"duk
wannan maganar bata taso ba inna
abinda nake so ki gane shine muddin mutuncin
mama
ya
zube,to martabar gidan nan gaba daya ta
fadi,ashe kuwa dole in damu tnda nima
dan gidan
nan ne,ga shi kuma mama ta dauko hanyar bada
mana kasa a ido.
Tace can dai zata badawa iyayenta masu
kwadayi,ban sa aka ba balle ya dameni
wahalar
banza kake yi dama ruwa da abinci ka samu ka
ci,daya fiye maka wannan sakarcin!Ya
sake dafe
goshi yana kada kai,me yasa innar sa
baza ta
gane ba?Takaici ya kara kama shi ya sunkuci
jakarsa ya koma dakinsu.Haj Gaje ta
shigo
saboda gulma ta cigaba,sharri kala kala
suka yi
ta jifar uban dawaki da su.La'asar sakaliya abba
ya dawo gida ya iske idanuwan umma
sun jirkita
jajur!Ga kumburi sun yi,ko bai tambaya
ba ya
tabbatar akwai abinda ke damun ta,don haka ya
kasa cin abincin data kawo masa,ya zura
mata
ido yace kamar akwai abinda ke damunki
sadiya?
Tace akwai matsala alhaji amma ka ci abincin
sai mu san abin yi."Fuska ki ta bayyana
tashin
hankali dake tare da ke ban jin abincin
nan zai
iya wuce min ba tare da naji damuwae ki ba.Gaya
min uwargida,ni kadai gareki
wanda zai
saurari kukan ki."Ta dan yi murmushi
karfin hali
tace mama zata siyar da mutuncin mu a
garin nan gara ka dauketa ka maida minna ko
abj ta
zauna can har zuwa lokacin
bikinta."Gaban sa ya
fadi yace,me tayi?Bata daina zuwa
shagon yaron nan ba,yau ali da kan sa ya koro ta
tana
zaune
bisa benci suna hira,benci fa a kofar
shagon
bakin titi?Kamar mama yadda muke a
garin nan take zama tare da danliti?Ta goge
kwalla,ina zan
sa BAKIN CIKI Alh,anya kuwa mama ce
ke aikata
wannan abu?Hankalin alh yayi
mummunan tashi ya fuskanci umma da kyau ya
sanyaya
murya
yace,ki daina zubda mata hawaye halima
ke
mahaifyarta ce,sai abin ya kara wargaje
mata......" "Ba yin kai na bane alhaji,hawayen ke
tilasta
wa kansa zubowa."Yace duk da haka ki
rinka
daurewa kina mata addu'a,insha Allahu
gobe zan maidata minna ko ta ki ko ta so dole ta
zauna.Ni
abinda ban gane ba shine,tana nufin ta
fasa
auran Al-ameen ne?Idan wani abu yayi
mata ai sai tayi bayani,ba wai ta nemi ta maida
mutane
sakarkaru ba!Ina take ne?"Tace tana
daki a kulle
tun safe daya koro ta,haushi yasa nayi
mata duka har ynzu bata fito ba."Ya mike cikin
fushi
ya nufi dakin ya buga da karfi yana
fadin,"tashi ki
bude kofar nan!"Tana budewa ya cafko
hannunta ya jawo ta zuwa falonsa,hakan ya sanya
mama
cigaba da tsiyayar hawaye,ya cillata
tsakar dakin
ta zube gefen ummanta.Ya zura mata ido
yace,"ashe wani lokaci zai zo da zamu ce ki bar
abu ki ki bari mama?Kin dai san
maganara auren
ki da al-ameen ko?To ynzu nake so ki
gaya min
manufarki ta bin danliti shagonsa.Gaya min inji
tun kafin mu tara 'yan kallo!Tayi kasa da
kai
kukan ta ya karu.Abba ya daka mata
tsawa,"kuka
na tambaye ki? Ki gaya min dalilin bin sakaran
yaron nan nace?Ta cigaba da share
kwalla tana
mutsu mutsun rashin gaskia,leben ta na
makyarkyata tace,"shi....shi na
ke......na..na...ke so ab...."Umma ce ra doke ta da
bayan
hannu
tace rufe mana baki mara kunya!"Ta dubi
abba
dake tsaye sake da baki tace,"ka ji ko?Ni
na san take-taken ta kenan!"Ya matso ya cafki
kunnenta
cikin tsawa yake magana."Idan barci kike
yi to ki
farka ki bude kunnuwanki da kyau ki
saurare ni! Ni ba tsohon banza bane,in har kin ga ki
auri
yaron nan,tabbaci hakika ni uwaisu na
mutu an
binne ni cikin kabari na!
Ya girgiza kunnen kamar zai tuge shi,kin ji ni!
Wannan itace magana ta karshe da zanyi
akan
danliti kuma gobe ki shirya kayanki zan
maida ki
minna!"Ya shirga mata dundu tare da fadin,"tashi
ki bani wuri!Ai bata iya tashi ba nan ta
baje ruf
da ciki sbda tsananin zafin dundun da
yayi mata
abnda bata saba ba,sai ta ji shi har cikin kayan
cikinta sun dau zafi ba kadan ba,Ta fasa
kara
mai shiga zuciya tace wayyo Allah na
shiga uku!
Na shiga uku!Yaya ali ya mike a firgice,gabansa
ya yanke ya fadi ya fito da sauri yana
tsinkayar
kukan mama,ya nufi sasa.Umman ke
fadin,'ba ki
shiga uku ba mama sai nan gaba muddin baki
dauki nashihar da muke yi miki
ba!"Hannu biyu
yaya ali yasa ya ciccibe ta ya mikar da
ita,zafin
duka da tsananin BAKIN CIKI dake dankare cikin
ran ta yasa ta kwakume.Yaya ali bakin
gado ya
zaunar da ita ya dago fuskar ta hannu
biyu yake
share hawayenta,yayin da nasa kwallan ke
neman sauka,yace "haba mama ki yiwa
kan ki
fada mana!"Murya na rawa tace,me nayi
masu
yaya ali!Sbda Allah me nayi?"Me kika yi? ynzu a
wajen ki wannan ba laifi bane?Haba
mama!Ba
haka kike ba,kin sauya da yawa kar dadin
bakin
danliti yasa hankalin ki ya gushe,laifin me al-
ameen yayi miki kike so ki yi masa
wannan
sakayyar?A zato na koda babu Al-ameen
nine
mutum na farko daya kamata ki fara kawowa ran
ki don na dade ina yawo da ciwon son ki
mama.Ki tausaya mana me zai sa ki
canza
kyawawan halayen ki?
Ya Girgiza kunnen kamar zai tuge shi. Kin ji ni!
Wannan itace maagana ta karshe
da xanyi
akan Dan-liti, kuma gobe ki shirya kayan
ki, zan
maida ki bani wuri. Ai bata iya tashi ba,
nan ta baje ruf da ciki, saboda tsanannin xafin
dundun
da yayi mata. Abinda bata saba ba, sai
taji shi
cikin kayan cikinta sun dau xafi ba kadan
ba. Ta fasa kara mai shiga xuciya. Tace wayyo
Allah na
shiga uku! Na shiga Uku! Yaya Ali ya
mike a
afirgice, gabansa ya yanke ya fadi, ya fito
da sauri yana tsinkayar kukan mama, ya nufi
sasan.
Umma ke fadin baki shiga uku ba Mama,
sai nan
gaba muddin baki dauki nasihar da
mukeyi ba miki ba! Hannu biyu Ya Ali ya sa ya
ciccibeta ya
mikar da ita, xafin duka da tsananin
BAKIN CIKI
da ke dankare cikin ranta ya sa ta
kwakume Ya Ali. Bakin gado ya xaunar da ita ya
dago
fuskar
ta hannu biyu yake share hawayen ta,
yayin da
nasa kwallan ke neman sauka. Yace,
haba mama kiyi wa kanki fada mna! Murya na rawa
tace, me
nayi musu Ya Ali? Saboda Allah me na
yi? Me
kikayi? Yanxu a wajenki wannan ba laifi
bane? Haba mama! Ba haka kike ba, kin sauya
da yawa
kar dadin bakin Danliti ysa hankalinki ya
gushe.
Laifin me Al-ameen yayi miki, kike son ki
masa wannan sakayyar? A xato na koda babu
a
alameen, ni ne mutum na farko daya
kamata ki
fara dawowa ranki, don na dade ina yawo
da ciwon sonki Mama, ki tausaya mana, zai
sa ki
canja halayenki? Ta xuba masa kwala-
kwalan
idanuwanta da suka kara fitowa waje
jajur! Tace, Yaya Ali ina ganin girman ka, ka kyale ni
da
wadannan surutan, don ba xa suyi tasiri
ba. Ni
nace ina so Al-ameen, yanxun kuma
bana son shi Danlilti nake so. Ra'aryi nane, ba sai a
kyale ni
ba, ko akwai wanda zai zauna min da
shi? Ya
bita da kallo, ta sa aya kafin yace, ki
daina tunanin wannan ra'ayin na ki mai yuwuwa
ne, kin
dauko katon aikin da xai rushe martabar
gidan
nan a idon jama'a. Idan baki son Al-
ameen, ki musanya da ni Mama, zai fi miki kyau a
bisa
shirmen da kie sonyi. Ta runtse ido tace,
yaya Ali
je ka kawai! Ba ki son gaskiyya? Ta
kauda kai kwalla na tsiyaya. Ya sanya murya yace,
xan bar
ki ki kwanta kiyi tunani sosai, cikin kan ki.
Ina
rokon ki girma da Allah, ki manta da
kudirin da kika dauko. Bata tanka ba, haka bata
dube shi ba
yace, A bakin tofa ya tsaya ya kare mata
kallo
kafin ya sake fadin, bana so ana taba
jikin ki mama, tamkar ni ake tabawa nakeji. Pls
ki sauya
tunaninki. Haushi ya kara kuma ta, ta
juya masa
baya. Ya fice yana kara waigen ta. A
daren nan daga ita har Yaya Ali babu wanda ya iya
cin
abincin balle barci. Tunanin Mama shine
xata ga
yadda za'ayi a raba ta da garin nan. Cikn
xuciyar ta tasha alwashin ko sun maida ta, zata
dawo,
dole su gaji su kyale ta da wanda take
so. Dalilin
da yasa ke nan, yau kwata-kwata taki
bude kofar ta, kowa yayi bugu, iyayinsa har
kawunninta, sai
dai kalaman bakin su suka kare. Amma
mama
taki bude kofarta. Duk wanda ka duba
ransa bace yake, musamman Abba, fuska
kamar gobara
ya dubi Umma yace, dauko min tabarya!
Ta mike
a salube ta shiga kicin ta dauko masa
tabarya, ta mika masa. Alh basiru yayi caraf! Ya
karba. Yace
karka balle kofar nan yaya, asara biyu
xa'ayi.....
Yace yarinyar nan dole ta bar garin nan,
ba xata xauna tana jawo min xagi ba, ana kallo
na tsahon
banza, bansan abinda nake yi ba! Buge
min kofar
nan, ko ka ba ni da kaina, in sauketa!
Kowa yayi cirko-cirko. Alh. Basiru ya kai wa kofa
duka da
tabarya, sai ga sallamar Yaya abdul-
kareem.
Basu gama amswa ba, yaci gaba da
tambaya, lfya? Me ya faru da kofar? Abba yace,
nayi farin
cikin xuwanka, don ni ma a yau nayi
niyyar tafiya
gunka. Me ya faru abba? Umma ya naga
kamar kina kuka? Yace, mama ce.... Me ya
sameta? Ya
kwashe kaf halin da suke ciki ya gaya
masa. Kai!
Bai gaskanta kunnuwansa ba, shi yasa
yace, abba ban yarda da wannan maganar ba,
ya
kamata asake bincikawa. Abba ya xuba
masa ido
jajur! Yace, wannan maganar ni Uwaisu
nake gaya maka ita. Abdul kareem kasan kuwa
ba za
ayiwa mama kage ba, domin ni na
haifeta.
Saboda haka gidan ka xata xauna can
har xuwa lokacin bikinta! Yace, ya xama wajibi, don
ganin
nan da kuka yi min xuwa nayi in tafi da ita
dama.
Al'ameen ya damu kwarai har yana ganin
kamar wani abu ne ya faru da ita ake boye
masa. Wlh
jiya ya turo mahaifiyarsa da yamma wai
ta zo ta
bincika masa lfiyar mama, shine nace shi
kwantar da hankalinsu Insha Allah da kaina xanje
in dawo da ita. Wannan al'amari ya daure
min
kai. Yaushe mama ta canza haka? Kawu
Basiru
yave xancan banza takeyi, tunda ita ta kawo
Al'ameen har aka sanya musu rana, bata
isa tace
ta canza shi ba! Wannan karya take yi.
Haushi ya
kara kure yayanta, ya mike ya suer tabarya ya
kaiwwa kofar duka sau biyu kofar ta
balle, bata a
dakin. Ya nufi kofar bayi ya murda can
ma
garkamen yake, bai tsaya wata-wata ba, ya maka
mata tabarya. Bugu daya kofar ta
wangem, sai
ga mama jikin bango ta fita hayyacinta
saboda
tsabar kuka. Al'amarin tamakar mafarki yayana
yake gani. Ya xura mata ido, yace hauka
kikayi
mama! Me Al-ameem yayi miki? Iye? Yayi
miki
laifi ne da ba zaki fada ba! Sannan ki rasa wanda
zaki bi, sai dan liti!
Kinji abinda nace? Kin yi karya ki xuabar
mana
da mutunci a garin nan! Zo mu wuce, ban
son jin
komai daga gareki! Ta sulale kasa hannaye biyu
bisa kanta, ta kara fasa kuka mai
tsananin
gaske. Matan gidan suka kutso kai cikin
bayain
suka tarairayo ta, suka fito da ita dakin. Yaya
yana fadin ko mutuwa zakiyi yau, sai na
tafi dake
mu je can idan Al-ameen ya kira waya, in
tambayehsi a gabanki, muji abinda ya
hadaku! Amma yaro na sonki yana tattalinki.
Iyayeynsa
na ririta ki, tashi guda kice ba kiyi da shi,
aikin
san wannan karya kikeyi. Ina kayan ta
suke umma? Hada mata si don baxan bata
lokaci ba!
Gaba daya suka yanyame ta da fada
kowa na
fadin albarkacin bakinsa, su Umma na
hada mata kaya. Su Hajiya Hajjo na rarrashi ta suna
bata
baki tare da gyara mata jiki da fuska.
Yaya Ali
kuwa yana xaune gefe rayuwa tayi masa
bakikkirin! Ana janta, tana togewa suka saka ta
gabn motar yayanta. Ya jefa jakar ta
gidan baya,
daga nan yayi sallama ransa bace, ya ja
motar
yayi gaba da mama. Dole ne ya saurar daidai
shagon Danliti, domin akan mahada
shagon yake.
Tsayuwar su wajen, ya jawo hankalin
Danliti
xuwa garesu. Ya xuba wa Mama idanuwan sa
suka sha kwalli rangadau! Haka ita take
kallonsa
kwalla fal! Suna neman sauka. Ya daga
kanka ta
fito kofar shagon, irin duban da yake mata ya
bayyanar da damuwarsa karara bisa
fuskarsa.
Tausayinsa ya lullubeta, nan da nan
hawayen
suka fara bulbula. Yayanta bai kula ba, kokarin
sa, duk motocin da suka kawo, suka wuce
shima
ya samu ya haura. Yawanci duk manyan
motoci
ne, kamar yadda akansan babban titi ne, wanda
ya mike ya tafi har lagos. Suna
tsagaitawa ya
cilla tasa motar ba tare da ya fahimci
Danliti da
mama sun ruga sun gama magana da idanuwansu
ba. Kawai ji yayi ta kara
gocewa da
kuka mai karfi. Ya dan dubeta, ya kada
kai. Yace,
Al'amarin ki na bani mamaki, look kina
jina? Saurare ni muyi magana ta fahimta. In
tambayeki
xaki bani amsa? Hankalinta sam ba
awajen sa
yake ba, balle ta saurare shi. Fuskar
Danliti take gani, irin yadda ya shifa damuwa yana
neman
xubar da hawayensa, shi ya kara dagula
mata
lissafinta. Yace, saboda Allah zaki gaya
min Al- ameen yayi miki da zaki juya masa baya?
Tayi
shiru, danliti na cigaba da yawo a idonta.
Yace,
kin kuwa san tun ranar da kika dawo
garin nan. Al-ameen ya rasa nutsuwarsa? Ban iya
kirga
yawon wayoyinsa ba, tunaninsa kina
cikin wani
matsanancin hali ne aka boye masa. Kar
ki saki reshe ki kama ganye Mama, domin kowa
yasan
Danliti lalata rayuwar ki kawai zai yi, ya
kai ki ya
baro ki tashar danasani. Ki ga ya min
idan Al- ameen yayi miki laifi ne, ni da kaina xan
masa
magana in ja masa kunne. Kinji? Bai yi
aune ba
yaga ta balle murfin motar ta dire waje.
Ta mulmula cikin ciyayi. Cikn tashin hankali
ya take
birki.... Allah yasa ba babu mota a
bayansa, yayi
fakin gefen titi, ya fito. Can ya hange ta
tana kokarin tashi, amma ta kasa, kafin ya
gangara
wajen 'yan tsirarrun jama'ar wajen sunyi
caa!
Kanta. Suka ciccibota, suna sallalami
tare da mamakin yadda aka yi abin ya faru. Gaba
daya
gwiwowin ta sunyi mugun kurjewa ta
xura da
gudu amma bata je ko'ina ba mutane
suka cafke masa ita. BAKIN CIKI yasa ya dauke da
wani
mahaukacin mari daya tilasta mata
xubewa kasa.
Wani dan dattijo cikinsu ya kama shi.
Yace, haba malam yaya haka kuma? Baka ganin
kaddarar da
ta sameta? Da ta mutu fa? Ku rinka
kulawa da
murafen mota mana don gudun irin
hakan! Idanuwan sa ajuye yake magana, kyaleni
da
yarinyar nan baba! Da kanta ta bude
murfin ta
fito! Iskanci ne kawai, dama kin mutu, mu
huta da wannan BAKIN CIKIN da kike son jefa
mu!
Saboda haka xan koma in gayawa abba
kin bude
mota ki diro, ni kuma ba xan tafi dake ba,
ki xauna kiyi duk abinda kika ga dama
agarin nan,
tunda lalacewa kika xaba. Allah ya shirye
ki! Ya
shura takalmansa ya koma mota ya tayar
yayi kwana ya koma gida ya bar Mama anan
tana
faman kuka, jama'ar dake wajen suna
mamakin
wannan abu har sun kasa fassara shi.
Dan dattijon nan shi ya riko ta hankali suna
tafe tana
bashi labarin wai auran dole ake son yi
mata.
Kwarai kansa ya daure jin cewar ita 'yar
gidan Uban dawaki ce, don haka ya tasa ta har
gidan.
Amma me? Suna xuwa kofar shagon
Danliti ta
xarce can tayi xamanta bisa benci. Dan
liti ya fito aguje da ayuba, mamaki ya rufe
ayuba, shi
kuwa dan gogan munafuncin ne yasa
gaba, sai
yazo ya narke a gabanta. Yace, saboda
me sakina, kinaso ki rasa ranki ne? Tace
gara in
mutu da su raba ni da kai, ya dubi Ayuba
a
gigice. Yace, kawo min mukullin mota
ayuba! Ya shige shagon da surinsa, shi kuma ya
juyo gunta
ya marairaice yake fadin, aure na Allah
ne
sakeena, ina so ki yarda da wannan. Duk
iya son da muke juna idan Allah bai nufi auran
mu ba,
babu yadda xamuyi. Don me xaki nemi
halaka
kanki? Bata bashi amsa ba. Ayuba ya
mika masa mukulan. Bai jira tace wani abu ba, ya
kamo
hanninta taso muje asibiti asa miki
magani.
Dattijon nan ya bisu da kallo, duk tausayi
ya rufeshi. Rashin sani kenan, ya fi dare
duhu,
domin shi gani yake irin haka ke jefa yara
yawon
banza..
[11/01 19:24] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***3 (TRUE LIFE STORY)
Wasu iyayeyn na da ra'ayin rikau, idan kuma
ka bibibya kwadayi ne, wata kila wancan yafi
wannan kudi ne? Sai dai kuma ai uban dawaki
mutumin kwarai ne, me xai sa ya aikata haka
akan yarsa? Duk da cewar dan dattijon nan
talaka ne, ya doshi gidan uban dawaki, don ya
bashi shawara. Fuskar Umma a sharkaf da
hawaye take muryar ta har rawa takeyi, bai
kamata ka baro ta can ba abdul... Yaya xanyi
umma? Kona cusata cikin, sake fitowa xatayi.
Mama ba zata mutu a hannu na ba, umma ta tafi
inda take son xuwa, kanta tayi mawa. Fatana
kwai Allah ya yaye mata abinda ke damunta.
Kuyi hkr ku kyaleta anan domin ina mai tabbatar
muku xata xauna can ba dawowa xatayi ba.
BAKIN CIKI ya hana abba magana, sai A. Adamu
ya iya fadin, gaskiya, gara ta xauna a cigaba da
yi mata nasiha watakila a dace. Kuyi hkr Yaya
mu dauki wannan a matsayi kaddara. Kai abdul
idan ka koma Al-ameen ya kira ka kwantar masa
da hankali ka... In ce masa me kawu? Gaskiyya
xan gaya masa shi ma ya hkr da ita tunda ba ita
kadai bace 'ya mace. Allah xai bashi wata. Ko
kuwa? Abba ya dube shi, sai yanxun ya iya cewa,
karka gaya masa haka abdul, da yardar Allah sai
inda karfina ya kare akan mama. Indai ni na
haifeta kuma ni ne xan daura mata aure Insha
Allahu shine xai aureta. Kawai ka bashi hkr kayi
masa wannan bayanin da naga ya maka yanxun.
Ya dafe goshi yayi huci zafi kafin ya dubi Umma.
Yace ki share hawayenki, umma ki yi mata
addu'a Allah ya shiryata. Ni xan koma sai yadda
ta kama. Basu amsa ba, ya mike kawu Basir da
Adamu suka yo masa rakiya kuma suna gaya
masa kalaman da suka dace ya gayawa Al-
ameen. Da dan dattijon nan sukayi kicibis yana
sallam cikin xaure suka amsa nan take. Yace
baka shaida ni ba ko yaro? Nine wanda yaga
lokacin da yarinyar gidan nan ta bude murfin
mota ta fito, tayi min bayani ita 'yar mai girma
Uban dawaki ce, shine nace ai mai martaba yana
da saukin kai xan xo in bashi shawara game da
auran dole, yayan ya dube shi da kyau. Yace
hakan ta gaya maka? Yace, kwarai hakan ta
fada. Yace to tayi maka karya, kawu ka na iya yi
masa bayani, don na tabbata abba baxai iya
fitowa ba ahalin da yake ciki. Alh. Basiru yace
yanxun ina take? Yace tana can ta tsaya wani
shago har sun tafi, zai kaita asibiti. Suka dubi
juna, yaya yace, kunji ko? Mama ta tafi, bata jin
kira saidai addu'ar Allah ya shiryata. Ni na tafi.
Ya fice ya barsu nan tsaye. Alh. Basiru ya dubi
tsoho yace mun gode baba, amma kayi hkr,
bazaka ji komai daga gareni ba, saboda ban sami
izinin yin hakan ba. Maganata gaskiyya da nake
so ka gane shine karya yarinyar ke maka, tare da
shegantaka irin ta yaran yanxun. Mun gode da
kulawarka. Tsoho yace, shikenan nima na gode,
amma don girman Allah abi a hankali asamu a
sulhunta. A. Basiru yace ba komi baba mun
gode. Sukayi sallama ya shige gida. Tsho ya
kama gabansa cike da wasi-wasi cikin ransa.
Falon Uban dawaki A. Basiru ya koma ya
xayyane masa labarin da tsho yaxo da shi, da
kuma shawarwarin da ya bayar. Abba bai iya
cewa komai ba saboda tsabar bacin rai. Sun jima
suna tausar xuciyar Abba sannan suka koma
sasan su, inda matan suke xaune dirshan suna
xuba gulmace gulmace. Suna zagin mama da
iyayenta. Basu hanasu ba, hasalima zama sukayi
suka dora xancan babu dadin ji, ita kuwa baiwar
Allah mama, tana tare da Danliti cikin mota,
bayan fitowarsu asibiti, yana ta faman
rarrashinta, don ta daina kuka ta kwantar da
hankalinta, da kyar ya samu ta nutsu ta daina
xubda hawayen. Yayi fakin kofar shagon sa ya
juyo ya fuskance ta. Yanxun ya xamuyi mu
fuskanci juna abba ya gane cewar idan ba mu
auri juna ba, komai zai iya faruwa da mu? Tace,
ai ga misali nan na fara nuna masu kuma ba xan
fasa ba, ina nan akan baka na. Ya marairaice
yace wannan misalin bana son irinsa sakeena,
don bana son na rasaki. Gaba ki daya kin fita
kamanninki kin kuwa ci abinci yau? Ta kada kai,
abinci ba xai iya wuce min ba Dan liti ina cikin
wannan masifar meye illar ka? Da abba xai ce
samm baka dace dani ba?
Ya lumshe ido, ya bude kafin yace,
saboda suna ganin ni bako ne, bani da kowa
agarin nan..... Ta katse shi, hakan shine xai nuna
daga sama ka fado? Wannan ba hujja bace
Danliti, son rai ne kawai irin na iyaye ni kuwa ba
xan yarda ba, sai dai muyi ta ba juna wahala. Ya
ja gwauron numfashi ya sauke, ya lalubo yatsun
ta ya runtse su cikin nasa, ya xuba mata ido
yace, nasan ki na sona sakeena, amma ki daina
damuwa ko sun hana ki xuwa wajena, sannan ki
daina wasa da rayuwarki, don tana da
muhimmanci aguna. Abu da gaba, ki daina zama
da yunwa, ita ma zata iya illata minke. Yaunxu
abinda nake so dake, ki zo muje shago in hada
miki tea ki sha, sannan kije gida ko sun zage ki,
kar ki ce dasu komai, don kar su sami damar
dukanki. Kinji bebi na? Ta amsa da ka. Tace,
yauwa mai kyau, to dan kalle ni mana, ta dube
shi suka yiwa juna xuru, jim kafin ta kauda kai,
tana dan murmushi, shima murmushin yayi yana
mata kllon kwadayi, ya ja yatsunta xuwa bakinsa
ya sumbata. (kuji dan iska). Ta kwace da sauri
ta kara sadda kai. Yace, bebi na kenan, sarkin
kunya. To muje ko? Zaki iya sauka ko in zo in
fito dake? Ta balle murfin batare da tace wani
abu ba ta fito, shima yayo waje yana kallon
yadda take dingisawa har cikon shagon sa. Ya ba
za mata tabarma ta zauna. Ayuba na mata
sannu. Akwai wani labule jikin wata kwana a
shagon, sai alokacin ta gane daki ne. Cikinsa Dan
liti ya shiga ya fito da filas da kofi da cokali ya
aje gabanta. Yace ga ruwan zafi, ki daga idonki,
ki duba duk irin madarar da kike so, ki zaba na
dauko miki. Tana murmushi tace, kai wacce iri
kake sha? Yace ai bana shan madara a tea,
ganye kawai nake sha. Kinsan buzaye ai? Tayi
dariya tace, ba'a raba su da jiko. Yace shayi dai.
Ta ciga da dariya tana fadin, to shayi, wai
menene sirrin shayin nan ne? Yace xan gaya miki
amma da farko wacce madara kika zaba, in
dauko miki? Na kowa ki sawa cikinki abinci.
Tace, bani peak ta ruwa. Ya mike ya dauko hade
da katon bread ya hada mata tea mai kauri,
domin duka ya juye peak din. Tana sha, suna hira
ya gaya mata ire-iren shayin su. Bayan ta
kammala, ya matsa gareta yace, yanxun ya
kamata ki koma gida kiyi barci, ki huta kinji?
Karki damu ko an hana ki xuwa nan, wane tym
zamu hadu. Ke dai kiyi addu'ar fatan samun
nasara. Tace, Insha Allahu zanyi. Yana murmushi
ya mika baki ya sumbaci kuncinta. Ta sunkuyar
da kai tana murza yatsunta. Ya zura mata ido,
gaba daya jikinsa yai la'asar, sannan ya dago
habarta, suka dubi juna, yace I love U! Tace me
too, yace, to ki tashi kije gidan, zaki iya ko? Tace
xan iya. Ta yunkura ya taimaka mata mikewa
suka fito tare ta sallami Ayuba, ya dan taka mata
kadan ya dawo, yana zuwa ya kwashe da dariya,
ya mikawa Ayuba hannu suka tafa. Ayuba yace,
baka da kyau dan iska. Yace raina kama gayya!
Gaskiyya ta gurzu, na tausaya mata wlh. Shegiya
akwai taushin fata, baka ji ba kamar auduga, duk
ta susuta ni. Ya zura masa ido yace, tunda kuka
shiga, na karance ka, shi ya gaba na yayi ta
faduwa, kar ka sata labulan nan. Yace, ko na
sata ba zata hani ba, nake gaya maka kuma babu
abinda zai faru dani. Kawai dai ban yi niyya bane
yanxu, ni nasan abinda nake hari. Yace a dai rika
tuna Allah Danliti, shagalinka yayi yawa kuma ina
ma kwadayin cin ubanta nakeyi, ai har uanxun
duniya bata fara zaginta ba. Kaga da sauran
mutuncinta. Ya bishi da kallo, bai ce komai ba,
yayi tsaki ya tashi ya koma shago abinsa. Tana
tafe tana dingishi, ta iso gida, kanta tsaye bata
fargabar komai ta fada zaure, kicibus suka yi da
Ya Ali sabe da jakar sa zai bar garin. Ko kallon
sa batayi ba ta wuce, ya biyota yana kiranta bata
waigo ba, balle ta amsa, ta shiga sasan su har
falo yana binta. Su abba na kallon ikon Allah,
domin dai Mama bata saurara ba, cikin dakinta ta
shige. Ya Ali na shigowa ya gansu, ya ja birki
amma ransa na son ya shiga wajen mama, yayi
magana da ita, abba ya dube shi. Yace, Ali ka
daina wahalar da kanka abanza, mama bata
bukatar komai sai addu'a. Saboda haka ka kama
hanyarka ka koma bakin aikinka. To amma, kayi
hkr Abba, don girman Allah karku daketa, kamar
yadda kace nayi mata addu'a kuma kuyi mata
addu'ar. Yace, na yarda da kai Ali, amma ban
yarda auran kowa ba, sai wanda na aminta da
shi. Zan gani idan ita zata daura wa kanta aure
ko mune? Yace, haka ne Abba don Allah ina
rokon 2mins in ishiga in dayi mata nasiha, koda
bazata saurere ni. Ya suke numfashi yace, shiga
Ali, Allah ya sa taji abinda zaka gaya mata. Ya
aje jaka ya wuce cikin dakin. Tana kwance niyyar
barci ma takeyi, kamar yadda Danliti ya
umarceta. Yana shigowa ta runtse ido ta juya
baya, ya tsya kanta yace, komai zakiyi, dole in
gaya miki gaskiyya, tunda kunnuwanki naji.....
Fadan hakan yasa tai sauri ta toshe kunnuwan
nata da yatsunta. Yace aikin banza kike yi Mama,
kuma rayuwar ki na cikin hatsari, muddin baki
daina jefa su abba cikin BAKIN CIKI ba. Menene
anfani abinda kika aikata yanxu? Ki kashe kanki
a banza da wofi, ba asarar Danliti bane, don na
tabbata duk tsananin son da yake mi, ba zai
hallaka kansa ya biki ba. Ki nutsu kiyi tunani.
Akwai abinda magabatan mu ke hangowa
kan wannan ra'ayin naki. Ni zan koma kuma ina
fatan zanji canji daga gareki? Ya juya ya fice
bata re da ta daga kai ta dube shi ba. Wani
dogon tsaki ta raka shi da shi, wanda ya tilasta
masa juyowa ya dubeta ji, sannan ya karasa
ficewa. Ya dauki jakarsa ya kara yiwa su Abba
sallama, ya bar gidan ciki da Al'ajabin maras
misaltuwa a zuciyarsa. Bayan tafiyarsa, su
Umma suka shigo gunta ta tana kudundune ta
dunkule wuri daya, ko 'ina jikinta ciwo. Umma ta
zauna gefen gadon shi kuma Abba n atsaye
kanta, yace Mama barazanar kashe kanki ba zai
sauya abinda ke cikin raina ba, idan ma baki sani
ba, ki sani gara ki mutu da mutunci na ya xube a
idon duniya. Saboda haka fadowar ki a mota bata
girgiza ni ba balle ta cire daidai da kwayar zarra
na alkawarin da na daukarwa Al-ameen da
iyayensa. Mu zuba ni dake, duk wani matakin
rashin kunyar da kika hau, ni na fi ki hawa
matakin karshe! Ya juya ya bar dakin. Umma ta
kura mata ido, hawaye suka cika idanuwanta,
tace Mama zaki iya tashi ki saurare ni? Ta shiru
bata motsa ba, ta sake fadin, idan har ni na
haifeki kuma na isa dake, to ki tashi zaune ki
fuskance ni. Ta jima kafin ta yunkura ta tashi
fuskar ta sharkaf da hawaye, kamanninta sun
sauya, saboda fitinar da ta daukarwa kanta a
tunanin iyayenta. Umma ta zura mata ido, kafin
tace, nasiha xan miki, idan kiji ki dauka wahala ta
kare miki, idan kuma kince ba haka ba to rayuwa
zata cigaba da yi miki kunci, domin Allah ne ya
wajabta miki yi mana biyayya, muddin ba mu sa
ba masa. Ban jin akwai wani dalili ko hujja da
xaki gayawa ubangiji da ace kin mutu sakamon
bude murfin motar da kikayi, ki fado lasa.
Wannan ya nuna muraran kin kashe kanki ne da
gan-gan. Ma'ana kin mutu kafira. Me zai jawo
miki wannan masifar da hankalinki da komai? Ko
kuwa kina so ki nuna mana kin fi karfin mu cikin
dan kankanin lokcine ne? Kina nufin mu sanya
miki ido ki zubar da mutuncin ki da mu a garin
nan? Ban taba tunanin Mama, ke din nan zaki
zama kaza kici share baki a game da irin so da
Kaunar da Al-ameen da iyayensa syka nuna miki.
Haka kuma ban taba mafarkin ke din nan zaki iya
hango wani da namiji ya rufe miki ido har kice
kin fo sonsa akan Al-ameen. Kina nufin daman
can yaudara sa kike yi ba tsakani da Allah kike
sonsa ba? Har yanxun mafarki nakeyi Mama, don
ba gaskanya abinda yake shirin fitowa daga
gareki nake ba. Ki yiwa girman Allah kir ki bari
wannan magana ta zama gaskiyya, ba ke kadai
za'a zaga ba har damu iyayenki. Na mu ma zai fi
yawa saboda mune muka isa dake. Yanxun
abinda na rokonki shine, ki share hawayen ki ki
gaya min, laifin me Al-ameen yayi miki kike son
ki katse masa rayuwa? Gaya min daga ni sai ke
ce a dakin nan kuma share hwayenki, muddin shi
ne baida gaskiyya. Ta shre hawayneta wasu suka
xubo mata, kalaman ummanta masu taushi ne
dashiga xuciya, amma kash Danliti ya riga ya
gama da ruhinta. Allah ya bashi sa'a ya kamata
ahannu, idanuwanta ba sa ganin kowa sai shi,
kunnuwanta ba sa sauraron kowa face kalaman
yaudarsa da izgilanci. Dalilin da yasa kenan
kalma daya bata tasiri a hrt dinta, a duk tsahon
jawabin da Umma tayi, da ka dubi fuskarta, zaka
gane bata yarda bane kawai. Murya cunkushe
tace, ni babu abinda Al'ameen yayi min Umma,
kawai raina yafi kwanciya da Danliti kuma shi
nake so na aura. Haushi kamar ya kashe Umma
ta mike tsaye. Tace, to baki isa ba! Mu dan Liti
baiyi mana ba, idan kina da wasu iyayen da za
su dauta miki auran to bismillah!
Ya ci gaba da fadin, ai kuwa bata isa ba,
ni zanje in dauko ta kuma dole ta auri wannan
yaron tunda itace tace tana so tun farko! Yace,
Yaya duk yadda kake tunanin al'amarin nan ya
wuce nan, amma ka gwada ka gani, kilan kai tafi
jin tsoronka, sai dai kafin nan xance Al-ameen
din ya kira ka, kuyi magana, don ni gaskiyya ban
san me xance masa ba. Yace ba wani abu xan
rarrasheshi, ya kwantar da hankalinsa, kaima
yaunxun nan ka kama hanya kaje ka yiwa
Hajiyansa bayani, kace kar su damu ba wata
matsala bace babba. Ya numfasa ya amsa da to
kawai. Lallai babban yaya yana dau kara abin
wasa ne. Suna aje waya Aunty amina ta nufo shi,
me ya faru ne wai? Nan take ya labarta mata
abinda ke faruwa. Tun kafin ya kare idanunwanta
ke waje, wai kana nufin Mama ta fasa auran Dr?
Yace gara da kikace wai, don bata ida ba. Ni xan
je na dauko ta, cikin gidan nan zata zauna sai ya
dawo. Ta kada kai cikin damuwa, tace amma
mama ta ban mamaki, me Dr? Yayi mata? Babu
abinda yayi mata, wani ta hango saboda rashin
hankali irin naku na mata da butulci! Tace wlh na
yadda sai dai matsalar banyi zaton haka ba daga
wajen Mama ba ganin yadda take nunwa Dr. So
mai tsanani, duk yaudara ce, kai gani kuma a
zahiri ai ta nuna. Amma ai tayi kuskure ni zan
gyara mata zama, don bata isa ta zubda mana
mutunci ba! Tace gaskiyya ne. Allah yasa ta
gane. Ya wuce tebur don cin abinci. Shi kuwa
abdulkareem, bai sami zaman cin abincin ba
gidansu Al-ameen ya nufa ba tare daya san wane
irin bayani xai iya yi masu ba, don hankalinsu ya
kwanta. A haka ya isa gidan. Nan da nan aka
tarbe shi da girmamawa da abubuwan kusa da
baka, marafa baya gari, saboda haka mami ce ke
tare da shi, ina fatan dai kaci abinci? Yayi dan
yake yace, Alhmdlh Hajiya, nagode. Tace amma
dai ko Juice kasha ko? Haba, kamar wani bako?
Yanata murmushin rashin nayi, yana kallo ta
xuba masa ta mika masa, Ungo sha don Allah.
Kuma maimakon kazo min da surukartwa, yau in
riketa cikin gidan nan sai tayi min sati. Ya aje
kofin lemo ya kara gyara zama, Yace Hajiya, hkr
na zo in baki, domin ban sami dawowa da Mama
ba,... Saboda me? Kodai maganar Al-ameen
gaskiyya ce, sakeena na cikin wani hali? Bata da
lfya ko? Ya karkada kai.... Tace karka bote min
komai Baban ameer, duk tsananin da sakeena ke
ciki, nasan yadda xan rarrashi Al-ameen don
hankalinsa ya kwanta. Gaya min me ya faru da
ita? Jikinsa ya kara sanyi, cikin taushin murya,
yace Matsala ce babba Hajiya, wacce ni kaina
ban da ita ba, sai da naje daxun. Ashe tun
komawar ta gida, wani yaro ya hure mata kunne,
shi ya hana ta dawowa. Su abba na ta fama da
ita kuma suna kan kokarin su don ganin raba ta
da shi. Na yi nayi ta biyo ni, taki hajiya, shine
Abba yace in zo in baku hkr kafin yazo. Insha
Allahu za'ayi maganin abin. Gaba daya hankulan
mu atashe suke, al'amarin yana daure mana kai.
Idanuwanta xuru akansa, hannunta bisa kunci.
Tace, wyyo Allah! Wayyo Allah! Me xanji yau mai
kama da almara? Ta goce da sallalami, yanxun
baban ameera kana nufin sakeena tace amanar
Al-ameen kenan? Idanuwanta suka cika da
kwalla, yayi da yaya Abdul ya kara kasa da
kansa. Yace, kiyi hkr Hajiya, a gaskiyya ban san
yadda xan fassara wannan al'amarin ba, amma
abinda nake so ki gane Abba ba xao rungume
hannayensa ya sanya mata ido ba. Haka muma
'yan uwanta. Muddin kuwa tana son albarka dole
tabi umarnin mahaifinta. Shi yasa ya fara turo ni
kafin ya zo da kansa ya ga alhaji. Haka kuma ku
rarrashi Al-ameen ya kwnatar da hankalinsa
komai zai daidaita cikin hukuncin Allah da
yardarsa. Ta cire tagumi. Tace, a gaskiyya ba
zan iya fuskantar Al-ameen da wannan maganar
ba, in katsa masa karatu. Na san ya damu kwarai
ya san halin da sakeena ke ciki, amma ba xan iya
gaya masa wannan mummunan labarin ba, kuma
na rokr ku don Allah ku kyaleshi kawai. Gara abar
shi cikin duhun da agaya masa sakeena ta sauke
alkawarin da ta daukara masa. Na tabbata komai
nasa zai tsaya jarabawar su gab take da xuwa.
Ni da kaina xan iya xuwa na roketa, ta tausaya
wa Al-ameen karta kashe masa zuciya. Kwalla
masu zafi suka xubo bisa kuncinta bata re da
saninta ba. Hankalin Abdul ya kara tashi, BAKIN
CIKI ya dada lulluba shi. Don girman Allah Hajia
karki xubda hawayenki akan maganar nan. Da
yardar Allah komai zai gyaru. Kamar yadda kika
ce kar agaya masa ba, ba za'a gaya masa ba.
Gara ace masa bata da lfiya ne, xuwa lokacin da
xa'a shawo kanta. Ta goge kwallah, tace ina
ganin hakan zai fi sauki iyaka dai yayi tunanin
jikinta, mu kuma nan mu rinka gaya masa tana
samun sauki. Yace, to shkienan, Allah yasa
mudace. Don girman Allah hajiya kuyi hkr,
sakarci ne kawai irin na yara. Tace, ya za muyi
baban ameer? Dole mu rungumi kaddara. Ya mike
babu isasshen laka a jikinsa, yayi mata sallama
ya fice, batare da hajiyar ta kara ko motsi ba.
Wucewar awa daya da rabi tana zaune xuciyarta
cike da sake-sake iri-iri. Ji take kamar a mafarki
abdul yaxo mata da wannan mummunan labari,
wanda take ganin zai iya salwantar fa rayuwar
dant tilon danta da takeji da shi. Duk fadin
duniyar nan bata hada shi da kowa.
Yaya marafa zaiji, idan wannan labari
yake kunnen sa? Tabbas xai fita shga damuwa,
domin yafi ta sanya Al-ameen ransa, ko alama
baya son yaga ya nemi abu. Waya ta dau ruri a
falon, ita ta katse tunaninta tare da haddasa
mata faduwar gaba mai tsanani. Ta mika hannu
ta dauka ba tare da tayi hasashen mai kiran ba.
Tayi sallama cikin raunin murya. A raunane taji
muryar Al-ameen ya amsa mata kafin yaci gaba
da cewa, mami na, ashe sakeen ba ta da lfiya
shine aka boye min? Ni ban ma yarda bata da
lfiya bane Mami, kawai ku gaya min idan mutuwa
tayi, xan hana Allah ikonsa ne? Ai nasan yafi ni
sonta, kuma ta shi ce ban isa in hana shi amsat
kayansa ba.... Tace saurareni Al-ameen, kar
hankalinka ya gushe.idan baka yarda ba da
maganar yayun sakeena ba, ai ni mahaifiyar
kace, ba xan rufe maka komai ba, ka yarda ko
baka yarda ba? Murya na rawa ya amsa, Na
yarda mami, tace to sakeena bata mutu ba,
rashin lfya ce ta sameta aka maida ta gida. Bana
so ka damu da yawa, domin sosai take samun
sauki, gobe ma xan sake xuwa in dubo ta, kaji?
Ya numfasa yace, amma Mami me yasa za'a
ajiyeta gida? Akaita asibiti mana, ko can xariya
xanyi magana da abokina, na tabbata xai kula da
ita tamkar ni. Pls mamy ki basu shawara idan
kinje goben. Tace ba ciwon asibiti bane, shedanu
ne suka tabata, kuma su iyayen nata suna tsye
neman magani. Kai ma kasan xa su xauna ba. Ni
dai rokona gareka shine ka nutsu ka kwantar da
hankalinka, ka fuskanci jarabawar ki mai xuwa.
Ka zama mai imani da Allah, shi xai sa ya karbi
addu'ar ka idan kayi mata. Ka jini? Ya goge
kwalla, yace naji mami don Allah idan kinje ki
dafa kanta ki karanta mata ayatul kursiyu, falaki
da nasi. Idan har gane ki ko da baxa ta iya miki
magana ba, ki gaya mata Al-ameen dinta na
gasheta, kuma xan ciga ba da yi mata addu'a har
xuwa lokacin da xanji muryar ta a waya.
Idanunwanta suka tara kwalla. Tace, Insha Allahu
xan gaya mata, tare da dukkan abinda kace,
muddin kayi min alkawarin zaka kwantar da
hankalinka. Da sauri ya amsa, Allah nai miki
alkawari mami, kinsan bani da wani buri daya
wuce in faranta maku rai. Tace, Allah yasa dalilin
alkawarin da kayi min Ubangiji ya yayewa
sakeena abinda ya sameta! Yace, ameen Mami
na! Dadina bai dawo ba ko? Bai dawo ba sai
zuwa jibi. Yace Allah ya dawo da shi lfya. Ta
amsa da ameen. Yace ki gayawa su iya su taya
mu da addu'a, Allah ya taimake mu. Tace, xan
gaya musu. Al-ameen, karka damu kaji? Murya
raunane ya amsa, to mami sai kinsake jina. Bata
iya kara komai ba ta aje wayar, domin muryarsa
kawai ta isa jefa mutun cikin damuwa. Taci gaba
da xama dauke da tagumi tunani na cin xuciyarta
fiye da tunanin mai kallonta. Haka al-amarin yake
wajen Al-ameen, domin dai rayuwa tayi masa
tsauri kuma hasashen rashin lfiyar Mam yafi
koma zama cikin ransa. Ba don yayi wa mamy
alkawari ba, da babu makwa zai iya baro abinda
yakeyi ya dawo ya ganewa idon sa Mama, tana
cikin mummunan hali. Kafin kace kwabo, kowa
ya fahimci samun sauyin sa, domin ya yamutse
ya wayi garim duk kuzarin da nutsuwar sa basu
jikinsa. Yana zaune addu'a yana tafe addu'a,
haka acikin aji, hankalinsa yafi rinjayea ga
addu'o'in da yakewa mama cikin ransa. 12pm
washegari lokacin ne motar Mami ke fakin kofar
gidan Uban dawaki. Yayin da mama ke kwance
rankas ciwon jiki, sakamakon fadowar da tayi
daga mota. Can da nan bata iya motsawa,
Baraka ke tare da ita tana zazzaga mata
nasihohi, duk da ta san bata sauraron ta, sai dai
ya zama wajibi gareta, ta kara gaya mata
gaskiyya. Mami tayo sallama falon ta shigo,
gaban Umma ya yanke ya fadi. Ta amsa tana
fitowa daga dakinta. Yake baki kawai takeyi,
amma zuciyarta ta shake take da takaici tare da
BAKIN CIKI mai tarin yawa. Ga wata kunya da ta
yo wa idanuwanta dirar mikiya, mai alaka da
ciwon dundumi. Sannu da xuwa Hajiya! Ta amsa
mata da fara'ar karfin hali. Ta nuna mata kujera
ta xauna, tana kara yi mata sannu da xuwa.
Sannan ta debo mata abubuwan sanyi masu
ruwa. Ruwan ta fara xuba mata, ta mika mata ta
sha. Suka gaisa cikin girmama juna. Ta kara
gyara xama, tace, sai kika ganni da rana tsaka
ko? Fuska kunshe da tashin hankali. Tace ke dai
bari, nasan kin sami sako maras dadin ji. Ta kada
kai dauke da damuwa. Tace naji sakon da ya
hani barci jiya, wanda ya sanya ni rama kafin
safiya. Ina jajantawa shi kansa Al-ameen da ya
sallama rayuwarsa kaf kan sakeena. Nayi kuka
da wadannan idanuwan nawa, don na tabbatar da
amsata ba alkhairi bace a gareni, domin komai
zai iya faruwa ga tilon da na, farin ciki na kuma
sanyi idona. Shi ya sa nace xama bai ganni ba,
tilas inxo in rarrashi sakeena, ta tausaya min kar
in rasa Al-ameen. Wadannan kalami sosai suka
sanya hawayen Umma suka tsinke nan take, ta
rasa me zata ce wa Mami ta sanyaya mata rai?
Dole tayi kuma domin dai bata da kwakkwarar
mafada, mama na nan akan bakanta babu sauyi.
Da kunnunwata ta, taji lokacin da take gaywa
Baraka tabbas zata iya kashe kanta, saboda
Danliti. Mami ta cigaba da fadin ki daina kuka
Hajiya, Baban ameer ya gaya min tashin hankalin
da kuke ciki, kukan bashi da alfanu.......
[11/01 19:35] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***4(TRUE LIFE STORY)
umma ta hare kwalla ta katse ta Tabbas
mama bata da lafia ciwon daya kamata mai
tsanani ne maganin Allah, dole kuwa in yi kuka ,
don mama ta dasa mana BAKIN CIKIN da ban
taba tunani ko mafarkin irinsa ba daga ni har
Abban ta mu na cikin rudu tare da mamakin
yadda wannan alamari ya kasanze haka, hakuri
zakuyi hajia sannan ku taya mu addua mama
kam ko ta so ko taki doke ta auri Alamin, tunda
zabin ta ne na farko bamu muka cusa mata shi
ba. Hasali ma bamu san lokacin da suka hadu
ba. tsabat rashin kunya ce irin t yayan zamani da
rashin sanin mutuncin mutane. saboda. haja hajia
karki damu kuma dabarar da kikayi wa alamin
tayi daidai sai dai akwai sauran rina akaba domin
fadar kalmar ciwon ma ba zai bar shi yayi sukuni
ba. Tace zaifi sauki akan a gaya masa gaskiar
magana ni na dauki dawainiyar kwantar masa da
hankali kullun ya kira waya. Tace to shikenan
Allah yasa mu dace ta ce ina sakinar take mu
gaisa Ta mike tana fadin Taso muje in kaiki
kwance ma take bata iya tashi. Ah me ya faru?
ina fatan ba dukanta kukayi ba, ta ce Baban
Amira bai gaya maki bude mota tayi ta diro kasa
ba? ido waje ta dafe kirji ta diro daga mota? tace
ya wuce wai! zo muje ki ganta ta tashi dauke da
mamakin tana fadin naga abinda ya ishe ni ni
yasu, sakina da gaske take bata son Alamin.
suka cusa kai dakin, baraka dake zaune bakin
gado ta mike tana gaishe su. umma ta nuna wa
mami wurin zama a bakin gadon tace zauyna
hajia kinga idanuwan maras kunya ta juya kan
mama taci gaba ga hajia nan tazo da kanta
inkinga dama ki bude ido
ta kudundune kai cikin pilli mami ta dube su
tace ku bamu wuri hajia ita baraka suka bar
dakin mami ta karasa matsowa tasa hannu ta
birkito ta kuka taga tanayi tasa hannu biyu ta
tallafo kuncin ta ta sanyaya murya tace sakina
dan dubeni kinji? ta dago idanuwa jajur ta dube
ta hawaye suka wuce bisa kuncinta. mami ta
kara goge su . ta ce na san ba'a siyan so mama
da yau nayi cinikin sa ko nawa ne na siya wa
alamin, koda zai kasance zani daya zai rage min
a fadin duniya. amma kash hakan ba zai taba
yuwuwa ba, sai nayi imanin ko dan yaya ne kin
san mahimamcin rike alqawari me yasa kika
dauki alqawarin da ba zaki iya cikawa ba? me
yasa kika yaudari shi kika bari tsananin son ki ya
zauna a zuciyarsa? kina so ki kashe shi ne
sakina? ki tausaya min ana gaya masa sakon nan
zuciyar sa zata iya bugawa ya mutu mama. shi
kenan na rasa shi kuma ban da wani alamin na
sonki mama sai dai ayi zancen dan adam
ssaboda haka ki gaya mani abubuwan da yake
miki wadanda baki so har suka sanya ki tunanin
fasa aurensa. wallahi nayi maki alqawarin zan
masa fada tare da lallashi in kuma. gargade shi
kinji? gaya man matsalarki da alamin. hawaye
suka ci gaba da ambaliya bisa fuskar mama
domin ko sunan alamin bata son ana ambatowa
tsawon lokaci bata tanka ba sai kwarara ruwan
idonta kamar zai kare mami ta sake fadin da
alama alamin dai bai maki komai ba sakina
tsuntsun son sa ne kawai ya tashi daga kansa ya
koma wa wani ko?
ta kara aje ido kasa mami tai wawan ajiyar
zuciya idanuwanta suka kawo kwalla baki man
halacci ba sakina a iya tunani na mutuwa ce
kawai zata raba ki da alamin shi yasa gaba
dayan mu muka dora burin mu a kanki. bamu da
wami buri face Allah ya nuna mana ranar da zki
zama mata danmu sai gashi dare daya kin juya
mana baya. A tunani ki kinyi daidai? baki gudun
kar amana ta ci ki sakina? kiyi tinani cikin
natsuwa duk wanda ya ha'inci wani Allah ba zai
kyale shi ba. zan barki kiyi tunani kan magana ta.
idan kin canza ra'ayi ki koma minna zuwa gobe
Alamin yaji ki hankalinsa ya kwanta kinji? yace in
gaishe ki kuma yace inyi maki addu'a. Ta
taimaka mata ta kwanta a hankali idanuwanta
rufe suke yayin da mami ta dafa kanta tayi mata
addu'oi da alamin yace tayi sannan ta kirata ta
bude ido. nizan koma sai najiki a minna karki bari
shaidan ya rinjayeki ki bar mai tsananin sonki
cikin kunan zuciya nakasa zaiyi kinji? ta lumshe
idon a natse mami ta wuce ta bar dakin umma ta
shiga tare da sallama ta nemi wuri ta zauna
yayin da baraka ta fice. ta basu wuri ta
saurareki? tace to! bata dai tanka ba sai kuka da
zan fito. ma nayi mata addua' kallo na ta dinga
yi. da alamun za'a dace tace kwarai da gaske
bari in lallaba hajia zan shiga wajen gwaggo
sannan mu wuce . to a gaishe ta da kyau Allah
ya kiyaye hanya
Suka wuce suna fadin"Amin"har kofar gida
tayi mata rakiya,motarsu ta daga ita kuma ta
dawo gida dakin mama a koma suka taru da
baraka suka ci gaba da yi mata nasihohi tana
kudundune bata tanka ba,balle su gane me take
nufi,Awa guda bayan tafiya mami yaya. Abdul-
kadeer ya iso gidan daidai lokacin kuwa Abba ya
dawo gidan,yayan tare yake da dakarun sojoji
guda uku,duk suka fito,suka toge suna sarawa
abba,sannan suka gaishe shi tare da yayan suka
rankayo yana ruwan masifa, maganar banza
yarinyar nan take yi,mu makace ta kawo shi ko
mu muka hadasu wannan ai iskanci ne yanzun
nan zan wuce da ita shiya na dauko kuratan nan
su yi min gadinta a mota na ga ta inda zata
fito,Nonsense kawai"
Abba yace kayi daidai domin ni mama ta ginsheni
ko ganinta bana sonyi cikin gidan nan,saboda
"BAKIN CIKI",abu kamar al'mara yana so ya
zama gaske yarinya ta bamu kunya ta zubar
mana da mutunci basu ma san sun shigo falon
ba sai da umma tace maraba da babban yaya
yace sannu umma bamuyi sallama ba ko?raina
bace yake ina mama?tana daki ina fatan tafiya
kazo yi da ita sosai kuwa umma akwai kurata
uku nazo dasu wadanda zasu gyara mata zama
muddin tayi yunkurin bata mana lokaci tace yayi
kyau wallhi yanzu ma hajiyar al-amin ta bar
gidan nan bakaga uwar kunyar da ta lullubeniba
na rasa inda zansa kaina
Abba yace tazo kikace"tana ma cikin garin
nan bata wuce ba"Abba ya nemi waje ya zauna
ya kama kai,shi kuwa yaya babba dakin ya nufa
kina jina baza ki fito ba"umma tace da wace
kafar zata fito bayan ta kusan kashe kanta,yace
kadan ta gani amma yau sai kin bar garin nan ko
za ki mutu!Useless girl!kina nufin ki zubar mana
da mutunci ko,baki. Kai wannan matsayinba,I
swear,kin ji na rantse"yasa hannu ya fisgo ta da
karfin sa yana fadin"stand up my friend"ta
tsandara kara mai garfin gaske saboda gaba
gabobain ta suka amsa suka kaiwa kwakwalwar
ta zuwa falon dole gabobin suka loma aiki ashe
dama wuri suka samu.
Ya dankwafar da ita bisa kujera tace wayyo
na shiga uku yace"No lokacin bai zoba tukuna sai
kin ci gaba da bijire wasu umma I'am telling you!
yau abuja zamu wuce ki zauna can, sai lazy
doktan ki ya dawo ai ke ki ka zabe shi tun farko
so now you have no reason ki ce kin fasa bayan
kun kusa aure ya dubi umma yaci gaba karki ji
tausayinta ta umma ki fidda ta a ranki har sai
tayi biyayya a gareku,
Ta kada kai tace tuni mama ta fice min a rai
balle tausayinta ko alama babashi cikin raina ka
tafi da ita duk abinda ya dace kuyi mata don ta
gane kuskuranta yace wannan dole ne Abba bari
mu wuce umma ta fara magana bari in hado
mata kaya yayin da abba da babban yaya kamar
zasu cinye mama a falo kuka take tamkar za a
zare mata rayuwa umma ta fito da jakar kayan ta
wurga mata gyale bisa jiki,yaya soja ya mike
tashi karki bata min lokaci taki mikewa yasa
hannu ya maketa
sannan ya cafko. ta yana fadin zan iya
karya ki u know dat! gara ki shiga hankalinki bai
sake taba har kofar gida ita kuwa umma cikin
sasa ta shiga ta gayo masu za a wuce da mama
don haka suka yo waje ganin yadda za a yi
saboda suji dadin karaars wa. A gaban su ya
cilla wa kuratan daya zo da su ya ce kusa min
ita a mota! kan kace kwabo mama na cikin mota,
suka sanya ta tsakiya yayanta na gaba sanda ya
jefa jakarta a but yaya ya juya da sauri ya zauna
matsayin driver babu bata lokaci ya murza
mukulli mota ta tashi ya bar wajen, idanuwan
baraka suka cika da kwalla nan da nan ta fasa
kuka ta koma cikin gida da gudu. sauran matan
na ta fadin Allah ya kiyaye hanya ubangiji yasa a
dace. umma ta juya ta shiga gida su suka biyo
bayanta . ganin hankalin umma yayi mummunan
tashi yasa hajia gaje ta janye hajia hajo cikin
gida ta mika hannu suka tafa sannan ta tallafe
haba ido waje tace Ashe abin har ya girman
haka? wanan sojoji kamar an zo kama gagararren
barawo? ta ce ai kamar hakan ne tunda ta gagari
iyayenta. zamuga ikon Allah yarinya na neman
tayi wa iyayenta bakin cikin daula, sun ga samu
zasu ga rashi ai kinga haj halima kamar ranta zai
fita sai kace dole suka sake tafawa haj hajo tace
Hakki ne nake gaya miki kadan ma suka gani
badai danliti ta jajibo masu ba? Allah dai ya
kiyaye lalacewa! ta tabe baki Nayaushe kuma?
wai ance wa kuturu Allah ya laance ka!
shagonsa fa take zuwa tsinancewa ai ba sai an
tambaya ba! hajia hajo tace Allah shi kyauta haj
gaje ta amsa na gaba domin dai wannan ya riga
ya faru anyi abin kunya maga yadda za ayi! sun
jima suna yada labaran banza da karairayi kai
duniya ina zaki da mu? rayuwa kenan uban
dawaki da umma suna kallon ikon Allah suna
fama da BAKIN CIKI sai fatan Allah ya musanya
masu alkhairi
Mama kuwa tun isowarsu Abuja take kudundune
cikin daki duk hargagin yaya soja baisa ta dauki
lomar abinci tasa wa bakinta ba,al'amari ya
daure wa anti amina kai ta zauna ta siga yayyafa
mata nasihohi da rarrashi ko Allah yasa ta gane
amma ina Alla bai nufa ba tukuna shi kuwa soja
babu abinda ya dame shi cewa yayi zai fi kyau
da zata bari yunwa ta kasheta a yau hakan kuma
shi zai tabbatar masa ta cika mai kunnen
kashi,yasa kai ya bar gidan amma kuratan
sojojinsa na nan tsare da gidan bayan masu gadi
mutun biyu ke nan yanzu sun zama su biyar,kafin
yamma mama taci kukan daya fidda ta daga
hayyacinta bama ta jin tarin yunwar da ke cikin
ta saboda tsananin tashin hankalin da take ciki
domin ita kanta ta san ta shigo kurkuku zai yi
wuya ta kara ganin dan liti sai dai tunanin ta bai
yanke ba duk tsananin da zata shiga baza ta
taba auren wani ba dan liti ba.
[12/01 17:26] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***5(TRUE LIFE STORY)
Saboda haka taci gaba da zama cikin kunci da
yunwa har bayan sallar isha'I yayanta ya shigo
gida kamar shi alamin ke kira wayar sa ta hau
bugawa falon kai tsaye kan wayar ya nufa ya
dauka yayain da malami ya sheko da gudu don yi
masa oyoyo.anti Amina ta biyo bayansa daga jin
muryar al'ameen kasa yana cikin farin ciki da
doki cike da zuciyarsa ina yini yaya,yace lazy
dokta ya karatu?"Yana yar dariya ya amsa
Alhamdulillahi ai na kira can minna don in
tambayi jikin mutunniyar sai aka ce min ta sami
sauki harma ka taho da ita, yace haka ne amma
kasan yana yin rashin lafiyar sai a hankali cikin
dan kankanin lokaci sai ta birkice bari in turo
maka ita,koda kaji sauyi daga gare ta kar ka
damu haka yanayinta ya sauya,jikin sa yayi
mugun sanyi duk a lokaci guda gabansa ya ci
gaba da faduwa murya dishe yace to yaya Allah
dai ya bata lfy,ya amsa da amin ya aje kan wayar
gefe ya amsa gaisuwar iyalinsa sannan ya haye
sama ya fada dakin mama yana shiga ta kara
kudundinewa cikin bargo yasa hannu ya kwashe
bargon ya watsar gefr yace tashi zaune sai ga
antin ta shigo ta matsa bisa shimfidar ta birkito
ta tana fadin yi mata a hankali ke mama tashi
kinji! Ta ciccibo ta ta tashi zaune kamar wacce
ta shekara tana ciwo saboda tsabar fita hayyacin
da tayi Tausayi ya lullube antyn a hankali tace
kinaji na?
Ga alamin cen ya kira waya don Allah ki fidda
mu kunya ki tashi ki je ki saurare shi badon mu
ba sai don girman Alkawarin da kika daukar masa
kafin ya tafi tashi kije kudinsa na bin iska kinji?
Tamkar antyn na magana da dutse don ko motsi
batayi ba sai idanuwa ta ke ambaliyar ruwan
hawaye . Haushi da takaici suka rufe yayanta ya
daka mata tsawa mai tsanani sai ta zabura
bazaki tashi ba? Alamarin ya kara kure su cikin
mamaki sukaji wannan kalmar ta fito bakinta
Nifa yaya ba zanyi magana da kowa ba Gaba
daya suka ware ido baki sake sai dai shi
soja baya tsayawa yana kallon raini don haka ya
cira hannu ya tsnke ta da wawan marin da yayi
sanadiyyar daukewar numfashinta karkaf,ta zube
sumammiya ya nuna cikin zafi yace ni zakiyi wa
rashin kunya ba na wasa da ke ni zan iya karya
ki wallhy anti amina da tuni take kwasar salati
tace ai maganar karyawa ta kare tafa suma
yallabai yanzu me za a cewa Al'ameen din
Yace ta mutu ni tayiwa rashin kunya bata isa ba
wallahi!Mtsw"ya ja dogon tsaki ya bar dakin
falon ya sauka ya dauki kan wayar ya kanga wa
kunnensa hello al'ameen naji na ya amsa ina
kinka yaya yace kayi hakuri da mama al'ameen
ya katse shi me ya faru yaya ina take yace ta
suma al'ameen kayi hakuri da ita domin mama ta
riga ta sami matsala....". Ya sauke salati ya
katse shi yaya bazan iya hakura da sakeena ba
kowane irin hali ta shi ina son ta haka koda kuwa
ciwon hauka ne ya kamata,Roko na gare ku shine
ku taimake ni ku kai ta asibiti don Allah ko
nawane zan kashe yaya please ku taimake ni ya
goge hawayen dake zuba bisa kuncinsa yayin da
jikin yaya soja yayi mugun la a sar cikin taushin
murya yace kar ka damu al'ameen zamu kaita
kar ka damu kaji sai da safe. Ko kamin ya gama
amsawa ya kife kan wayar
al'ameen sai da ya lalubi wuri don baya gani
yadda ya kamata sauran abinda ke zuciyar sa
kuwa biro na ba zai iya rubuce shi ba domin
al'amarin gagarumi ne maras misaltuwa sai dai
muce Allah ka kiyashemu sharrin masu sharri
amin summa amin Anti amina keta faman neman
ran mama shi
kuwa yayanta bai sake komawa ta kanta ba
dakin sa ya shige don yin abubuwan da yake
ganin suna da muhimmanci a gare shi ita kuwa
mama zafin. Mari da tsananin yunwa tare da
tarin damuwa su suka taru suka jefa ta cikin
doguwar suma awa daya da rabi ta kwashe babu
motsin rai sannan ta dawo duniya,ta fasa kuka
tana fadin wayyo Allah na zan mutu wayyo Allah!
wayyo!" Nan da nan hawaye suka tsunkewa anti
amina saboda tausayin da ya kamata murya na
rawa ta tarairayo ta tana fadin mama ki tausaya
wa kanki wannan mugun halin da kika jefa kanki
kin kuwa ga yadda kamannin ki suka sauya wane
irin masifar so ne wannan na bala'I. Akan da
namiji kike wahalar da kanki a banza a
wofi ki mutu ya nemi wata ya aura,wannan
sakarci ne mama kiyi wa kanki fada tun dare bai
miki ba sannan ki sani idan kika ci amanar
al'ameen Allah ba zai kyale ki ba,ta fizge jikin ta
ta sake faduwa bisa shimfida ta kara fasa kuka,
malami ya budo kofa ya shigo cikin sanyin jiki ya
karasa gun su yace mami uncle al'ameen ya
bugo waya, kafin anti amina tace wani abu tuni
mama tayi wuf ta tashi zaune cikin sababi take
fadin ba za a zo ba kaje ka gaya masa bazan
dauki wayar ba dole ne sai na aure shi nace. Ba
zan aure shi ba duk ku taru ku kashe ni kowa ya
huta ta sake komawa ta dase ciki anti amina da
malami suka saki baki suna kallon ikon Allah.
Jimawa kadan ta dube shi tace,Mu je falon."
suka fice jiki babu kwari,musamman Malami da
sababin ya bashi tsoro ba kadan ba.Anti Amina
ta dauki wayar tayi sallama,suka gaisa kafin
yace, Ya jikin sakeenar? Ta farfado kuwa? 'Ta
farfado Al-Ameen, har ta samu barci. Ya sauke
numfashi,'Allah ya kara mata lfy. To amin.yace
Anti,don Allah ki taimaka ki tuna wa yaya tafiya
asibitin.Ni ina ganin babu abinda zai gagari asibiti
koda matsalar junnu din ne, akwai ta su irin
gudumawar da zasu iya badawa. Please Anti a
kai ta asibitin a gwada." Idanuwan ta suka kara
tara kwalla,jin yadda muryar sa ke rawa,ta
tabbata hawaye ne ke zuba bisa kuncin sa.Ta
numfasa tace "karka damu Al-Ameen,duk wani
iya kokari ana yinsa.inshaAllahu Allah zai dube
mu ya yaye mata wannan lalura.ka kwantar da
hankalinka kaji? Ya amsa,Hankalina ba zai
kwanta ba Anti,har sai
naji muryar sakeena da bakinta ta gaya min
tabbacin samun saukin.Ban san halin da sakeena
ke ciki ba Anti,kowa cewa yake tana samun
sauki,amma ni ban ji alamun ba a jiki na.zuciya
ta tana min sake-sake iri-iri akan sakeena kuma
tana nuna min ita acikin mummunan hali.jin
muryar ta ne kadai zata warware min rudun dana
fada.....Anti Amina ta amshe,komai yayi zafi
mgnin sa Allah Dokta.ka tsaya wa addu'a kawai
ita ce kadai zata taimake mu.shi kenan
Anti,ngd.Idan Allah ya kaimu gobe zan sake kira
ko na dace jin muryar ta.Tace To Allah ya yasa
a dace.ameen
Sukayi sallama ta aje waya ta koma bisa kujera
ta kama kai hannu biyu ta matse kwallan ta tace
wannan masifa Allah ka yaye mana,muryar mai
gidan taji yana fadin kema zai zauna kina bata
lokacinki yau mu ma bazamu ci abinci ba ke nan
Ta share fuska ta dube shi yallabai ba ka ki
kalaman dokta bane su suka kara dafani wallahi
ya ya zamuyi da yarinyar nan ne yace oho!ni kizo
ki ban abinci ina jin yunwa ta mike ta nufi kicin
shi kuma ya wuce ebur yana kiran malami ya
sauko da gudu yana amsawa gani dadi kaima yau
baza kaci abinci. Bane yace ai na ci dadi to
koma daki kayi barci sai da safe,ya juya ya haye
saman yayin da anti amina ta fito da jerin kayan
abinci bisa tire ta jera bisa tebur sannan ta zuba
masa taja kujera ita ma ta zauna yana ci tana
maida masa kalaman al'ameen sai da ta kare ya
kurbi ruwa ya dube ta, Yace ni kinga duk wannan
shiriritar ina yi ne
kawai saboda hajiyar sa ta roki a rufe masa
amma ni ban ga dalilin yawo da hankali ba yanzu
ina fa'idar yin shirun tunda hankalin sa da ake so
ya kwanta bai kwanta ba?mama ko zata mutu
shi
zata aura to me ne ne abin jin tsoron gaya masa
matsalar da ake ciki banda shiriritarku ta mata,ta
ce ai ba haka bane yallabai kaga kuma shi kansa
marafa ya goyi bayan hakan"shi ke nan sai ki yi
ta rarrashinta kafin gobe idan ta amince yin
maga da shi shi ke nan idan kuma taki kya nemi
wata karyar ki shirya masa kinga sharo karya ya
same mu ke nan sai abinda Allah yayi ina
amfanin sa
Ta numfasa tace al'amarin hakuri zamuyi tayi
rokona gare ka don Allah ka daina dukanta
wallahi taurin kai zai kara mata ido waje yake
magana muddin tayi min rashin kunya zan
tabbatar da na hukunta ta yadda ya kamata don
ni ba sa'an ta bane,you know that so ba zan
dauki iskanci ba kina iya hawa sama idan kin
kare maganar,tace ran maza ya huce yallabai ba
ina nufin wani abu bane yaci gaba da cin
abincinsa bai tanka ba ta zura masa ido tana dan
murmushi ta san halin yan kayan ta idan kayi
magana kaji yayi shiru to kaima ka tsuke dan
bakin ka ka kama kanka shi zai fi zama alkairi.
Garin Allah ya waye,baya ga sallah babu abinda
Mama ta aikata,ta yada kai bisa kafet tayi lamo
kamar sumammiya.Gaba daya ta rame,fuskar ta
ta tsuke duk ta bushe idanuwanta sun kode sun
firfito waje, sbd tsabar kuka.Malami ya fito
wanka ya tsugunna gabanta yace "ìna kwana
Anti?Tayi banza dashi,ya zura mata ido,Baki da
lafiya ne Anti? Tunda ku ka zo da Daddy baki min
mgna ba. Ta ballo masa harara,sai na tsinka mka
mari ka sake min magana! Ta ja tsaki,ta juya kan
ta wani gefen.Haushi ya kama shi,ya tashi ya ci
gaba da shirin sa. Wannan karon kam bai gane
kan gadon Antinsa ba. Me ke faruwane? Karfe
bakwai daidai Anti Amina ta shigo,tana shigowa
Mama ta rintse ido. Anti Amina ta dauko bisa
kanta,ta dan dafa ta na san ba barci kike yi ba,ki
tashi don girman Allah ga Dokta can ya kira.
Kamar yadda na gaya miki jiya so yake yaji
muryar ki,hankalinsa ya kwanta ko da gaisuwar
sa ki amsa,zai ji dadi Mama.
[12/01 17:32] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***6(TRUE LIFE STORY)
Ku da baku wurin in kun amsa.To Mama ta amsa.
Haushi kamar ya kashe anti Amina.ta mike tsaye
tace, kar ki tashi Mamaa,idan kin sake jin nayi
mikí mgn akan Al-Ameen,duk abinda kika so kiyi
min! Mts....... Ta ja tsaki ta wuce. Mama ta
rakata da nata dogon tsakin anti amina ta waigo
rike da kugu ta zubo mata ido,lallai mama,ni kike
yiwa tsaki? Yayi miki kyau! Taja kofa ta fice.kan
wayar ta duka rai bace. Tace, hello! Yace hello
anti,ta tashi? Bata tashi ba dokta.(nace"dokto ka
fiya nace dolene?) "ba matsala,ai barcin ma yana
da amfani a gareta.zan sake kira,ngd antí. Cike
da tausayinsa ta amsa,kar ka damu sai anjima.
To suka aje waya. Ta haye sama shake da
haushi,amma bata nuna wa yallabai ba,don ta
san ita zai tsatstsage danya. Iyaka tace da shi
bata tashi barci ba Wasa wasa mama fa har ta
sake kai bayan
la'asar batasa kwayar abinci a bakinta ba
hankalin anti amina ya tashi kwarai da gaske
mama kam bata cikin hayyacinta gaba daya ta
galabaita yunwa na neman tayi mata illa koma in
ce tayi matan,shiyasa tana jin waya na ta
bugawa taki dagawa don tasab mai kiran kuma
bata da abinda zata gaya masa a hakikanin
gaskiya ma hankalinta yafi rinjaye akan mama
dake ta zama da yunwa tun safiyar jiya
Tayi fada tayi rarrashi duk a banza misalin karfe
biyar ta hada tea ta shigo da shi dakin wai ko
Allah ya bata sa'a ta dan kurba me zata gani
mama ke ta madedewa tsakar daki wata irin
farar kuffa na hauhawa bisa bakin ta,tasaki kofin
tea ta tarairayo ta tana sallalami kinga irinta ko
mama nayi nayi dake kice abinci kin ki kina so ki
kashe kanki a banza a rude ta sake bazamowa
falo ta dauki waya ta kira wayar ofishin yaya
abdul kadeea ta shaida masa halin da mama ta
shiga
Amma yanzu za a fara wucewa da ita asibiti nan
take ya bata izini yace zai same ta asibitin babu
baa lokaci soja daya ya sakata mota anti amina
na tare da ita a gidan baya tana shafa mata ruwa
a fuska sojan na jan motar an bata gado ga ledar
ruwa na aiki a jikinta, wucewa minti talatin yayan
ya iso ya same su jugum jugum,suna kallon ta
rai bace ya watsa hannaye aljihu yace dama
haka take so ba kuma shi zai taimaketa ba
muddin tana motsin rai al'ameen ne mijinta so
idan ta farfado ki fara gaya mata kafin na dawo
zan koma ofis muna da mitin,tace to adawo
lafiya ya wuce cikin kuzarinsa kuratan sa na biye
da shi har bakin mota suka koma sannan guda
ya bude masa ya shiga direban yaja suka
wuce,anti amina ta ci gaba da zama dauke da
tagumi zuciyar ta na mata saka iri iri haka wayar
al'ameen ke ci gaba da bugawa cikin gidan ba a
dauka ba malami ya shigo gidan dawo war sa ke
nan daga maka ranta,kicin ya wuce kai tsaye
saboda yunwa ce ta koro shi ya debo abinci ya
zauna ya fara ci waya ta sake daukar ruri ya
mike da filet din a hannunsa yana kara lomar
shinkafa da salad ya dauki waya baki cike da
abinci ya ce hello hello malami al'ameen ne ba
kowa ne a gidan yace eh nima yanzu na dawo
school mai gadi ya gaya min sun tafi kai anti
mama asibiti wai ta suma.
Jikin al ameen Ya kara mutuwa ya ce gaskiya
Uncle duk ta rame kamar ba ita ba bata magana
sai kuka Tunda suka dawo da dadi ba ta ci komai
ba ko ni bata. Yi min magana ba sai yau ta ce za
ta mare ni idan na sake gaishe ta wane irin ciwo
take yi uncle hawaye suka tsunke wa Al Ameen.
Bai san lokacin da ya kife kan wayar ba malami
yabi ta hannunsa da kallo. Bai gane komai ba
dan haka shima ya aje ya dauki abincinsa ya
cigaba da ci yayi sallar magariba dadinsa ya
shigo yayi masa sannu da zuwa ya amsa ya haye
sama ya cire kaki yasa kana nan kaya jaket da
wando ya sauko ya shiga kicin ya hada kayan
abinci cikin dan matsakaicin kwando ya kira
malami yace kai mota ya jirashi can su tafi
asibitin,yace dadi yauwa uncle al'ameen ya kira
waya dazun me kagaya masa na gaya masa anti
ta sume kunje kai ta asibit to ke ka kirani a mota
ya dauki kwando yayi waje jim kadan dadinsa ya
fito suka tafi har zuwa lokacin mama bata gane
kowa yayan ta ya zauna nan zuwa goman dare
sannan suka koma gida da malami
Anti amina ta kwana tare da ita kiran asubahin
farko ta dawo hayyacinta ido ta zurawa anti
amina kafin ta fasa kuka anti amina ta matsa
gare ta ta dafa ta saman goshinta tace me yasa
kike wahalar da kanki bayan ki na sane da cewa
aure tsakaninki da al'ameen babu fashi,ta goge
hawaye wallahi wallahi anti bazan. Taba cin
abinci ba har sai yaya ya maida ni inda ya dauko
ni kinji kuma na rantse bazan kaffara ba,baki
sake take kallonta tama rasa ta cewa mama ke
ci gaba da fadin na gwammace na mutu da a
raba ni da dan liti sabo da haka mu zuba nida
yaya idan jan idonsa zai sa in daina son dan'liti
anti amina tace gadkiya ne kuma yanzu kika
tabbatar min kinyi nisa ka kya jin kira
To abinda zan gaya miki shine ki guji bacin ran
iyaye rayuwa ki ba zatayi kyau ba muddin kika
bar mahaifanki da BAKIN CIKI sannan dole ki
fuskanci kalubale tunda kika ci amanar dokta
bazan rufe miki ba mama koda nan gaba in ta
Allah ta kasance zaki tuna dani kice na gaya miki
a asibitin nan wallahi yadda kika sanya al'ameen
kuka da radadin zuciya kema sai dan liti ya
dandana miki fiye da hakan
Da namiji ne fa ki bari ya gama shanye romon da
yake hange a jikin ki kisha mamaki daidaiku ke
da rikon amana su ajiye ki ke kadai suna
girmamaki a matsayin matar sunna mai tsananin
kamanta gaskiya shi ne zai ce kik zai kara aur
amma sauran shagalinsu suke sha a waje su
barki hoto a gida balle wannan Dan'liti daya sami
shaidar banza don haka kibi a hankali mama so
ba hauka bane tace na ji kin fada amman yarda
ba dole bane ko ashe kin gane domin ni duk
abinda mutun zai fadi akan Dan'liti ina daukar sa
a matsayin hassada ina abin hassadar ga Dan'liti
koda ban san shiba labarinsa ya gamsar dani
kuma na tsane shi idan kin tsane shi ki daina
maganar sa don zai sanima in tsane ki
Ta ware ido sosai tana kallon ta ban yi mamakin
jin kalamanki ba tunda kika iya shafawa
idanuwanki toka ba kya ganin mahaifanki ki balle
ki saurari nasihohinsu gareki kin ban kunya
mama ban taba zaton wata rana mai kamar
wannan zata zoba in sha Allahu zan rarrashin
dadin malami ya kyale ki duniya ta koya miki
hankali,ido cikin ido ta bata amsa zaifi kyau idan
kika yimin wannan kokarin haushi yasa anti
amina ta mikie ta fito babban falon asibitin tayi
zaune har aka kira asalatu tayi alwala tayi sallah
ta je ro addu'o'I tare da rokon Allah ya sanya wa
al'ameen dangana idan har ya rasa mama
Cikin shigar kakinsa tsaf ya shigo asibitin tare da
malami shi ma sanye da kayan makaranta
kuratan sojoji biyu na take masa baya dauke da
kwandon kayan karin kumallon safe a babban
falo ya same ta zaune bisa dardumar
sallah,malami ya fara isa gun ta ya gaisheta ta
amsa sojojin dake biye suka kwashi gaishuwa
yayin da ta miki ta tarbi yallabai amma fuskarta
babu walwala sannu da zuwa tace dashi ya amsa
yauwa ya dai jikin na ta, tana ciki shiga ka ganta
ai ta farfado tun asuba,ko?suka jera zuwa dakin
tana gaishe shi jin muryarsa yasa mama ta
runtse ido ya tsaya kanta yace ki daina matsr ido
nasan kina ji na ina fatan amina ta gaya miki
sako na saboda haka ina son ki gane wannan
sakarcin bazai firgitani ba abinda na sani kawai
al'ameen ya dawo a daura maku aure middin kina
numfashi sauran shawara ta rage gare ki,
Anti amina dake ta kallon ledar ruwa tasa
hannu ta dago igiyar tabbas abinda take zato
shine din. Ruwan ba a jikin mama yake ba cirewa
kikayi mama, ta juya kan yallabai tayi masa kuri
ka gani ko ta cire ruwan yaya ya kawo iya wuya
kamar ya nannausheta yake. Ji cikin fushi ya
juya ya fita anti amina tace da kanki ki ka kama
drip din ki ka tuge,sau dubu aka samin sau dubu
zan cire me ruwanku dani tunda baku kauna ta
tana rufe baki yayan na shigowa da wasu nosis
biyu amma abin karin haushin mama taki yarda
su mai da mata ledar ruwan nan basu san
lokacin da yayanta ya cire hannu ya tsinka mata
mari ba,sai da bakinta ya tsatso jini saboda
haushi da takaici kafin ayi haka ya bar dakin anti
amina ta biyo bayan sa ta bar nosis na rarrashin
mama yana shiga mota ita ma ta fada ciki tace
kayi wa girman Allah yallabai karkayi fushi ka
tsaya ka saurareni kar ki min magana akan
wannan wawayar yarinya," I have finish with her,
dama munyi waya da abdul-kareem sun ce za su
zo harda abdul-rahman so suna zuwa zasu wuce
da ita daga can su bata kudin mota ta wuce
fandogari zan iya kashe yarinyar nan idan ina
ganinta,
tace wallahi ni ma shawarar dana ke son in ba
ka ke nan idan kaji maganganun da mama ke
fadi zaka tabbatar da tayi nisa bata jin kira sai
addu'a kawai zamu zauna ne tana bamu wahala
koda yaushe mu ma asibiti a aikin banza?ba zai
yuwu ba a irin take taken ta tana gab da fara
sufa mana zagi ku kyale ta da dan-litin shi ne zai
koya mata hankali,yace ai an gama dokta zuwa
kice ya sallame ku kawai zan sake kiran abdul-
kareem din in ce su dame mi gida ta numfasa
don murna kafin tace,"!58,naji dadi yallabai Allah
shi taimake ka ita kuma ya shiryar da ita amin
ga break fast can kije kici ki kyale ta bari mu kai
malami school gada can zan shiga ofis to a dawo
lafiya amin,ta fito sannan sojojin suka taso daga.
Inda suke tsaye tare da malami suna jiran su
babu bata lokaci suka bar harabar asibitin anti
amina ta koma ciki tace wa nosis su kyale ta su
tafi abinsu guda tace oga zaiyi fada madam idan
ya shigo.
ni nace ku tafi kawai abin ku ba mu muka
kawota ba,kuma mu zamu biya bill ku wuce kwai
ba wani abu"nosis suka wuce da mamaki anti
amina ta hada abin kari ta hau ci bata sake
komawa ta kan mama ba har likita ya shigo
misalin takwas da rabi na safiya anti amina ta
maida masa bayanini yallabai likita yace a'a baza
ayi haka ba nan ya ja kujera yayi ta rarrashin
mama,tayi shiru kamar da gaske sauraronsa
takeyi da kansa ya nemo jijiya ya maida mata
ruwan amman me yana gamawa bai ko bar dakin
ba ta sa hannu ta zare ta aje masa robobin sa
haushi ya shake likita ya jima yana kallon ta
sannan ya dauki (file)din ta yayi rubutu,ya dubi
anti amina yace kuna iya tafiya gida madam da
alama ba zamu shirya da sakeena ba tace ai
dama na gaya maka kayi hakuri dokta kan ta tayi
mawa tace ba wani abu shawa ta kawai ia ce ku
kyale ta ta auri wanda ta zaba may be rabon
wahala ke kiranta,tace sosai kuwa dokta mun
gode ji suka yi mama taja wani shegen tsaki duk
suka bita da kallo likita yace I'am sorry for yau,a
tunaninki kinyi abu
Mai kyau ke-nan? NO,ba hk rayuwa take ba.
Ya kamata ki rinka kulaw. Ya sa kai ya
fice.Nosis din sa suka take masa baya,kowanne
su babu wanda bai shakì taikacin Mama ba. Tana
hada kaya direba na shigowa, yaya ya turo
shi,idan anyi sallamar ya kaisu gida. Shi ke nan
kaya sun tsunke karkashin kaba. Ya kwashe
kaya,ta dubi Mama tace, ki na iya tasowa muje
gida,idan kin so.Ta yunkura ta tashi,Anti Amina
bata saurareta ba ta wuce abin ta. Da kyar ta
sauko daga gadon,wani mugun jiri yayi tafiyar
ruwa da ita,ta koma dabas! Ta zauna.(maganin
mara jin magana,yarinyar nan tana ban haushì!
Mts!) Tafi minti uku dafe da kai,sannan ta sake
mikewa ta daddafa bango ta fito tana layi. Kowa
kallon ta yakeyi,musamman Noisis din da komai
ya faru a gaban su,ai nan take aka shiga maida
labari. A mota ta same su. Anti Amina na gidan
baya,duk ta kulle sakatun kofofin biyu,saboda
haka dole Mama ta bude murfin gaba ta zauna
tare da direba. Ko a cikin gidan ma,babu mai
kula wani,hasalima Anti Amina kwanciyar ta tayi
tasha barci,bayan ta yi wanka ta sauya kaya.Ita
kuwa Mama taci gaba da sanya tsananin kunci
cikin ranta,ji take kamar ana hura wa zuciya ta
wuta.Tsananin son ganin Dan-Lati da kewarsa
suka hana ta sukuni. A yadda jiri ke dibar ta,sau
uku tana fitowa waje ta tsaya wai ko zata ga
lakwa-lakwa ta sulale ta gudu.Amma ina,ko
fuska babu a wajen kuratan nan,balle ta sami
hanyar fita.Don haka ta kifa ciki tsakar falo,tayi
ta sharara kuka har azahar,bata san lokacin da
barcin wuya ya sace ta ba.
Anti Amina ta sauko tayi girki ta gama bata
farka ba.Dawowar Malami ya kwarara
sallama',shi ya tashe ta,tayi doguwar mika tare
da hamma mai kunshi da yunwa da wahalar
duniya. Ta tashi zaune taja jikin ta,ta zauna ta
jingina da kujera,wucewar 'yan mintoci.sannan
idanuwan ta suka kwalli agogo.karfe daya hard a
rabi. Da kyar ta yunkura ta tashi ta haye sama a
wahale,tana shiga dakin ta zube a kasa,sbd babu
karfi a jikinta.Malami da ke cire kayan
makaranta,ya zubo mata ido.yana so ya gaisheta
yana jin tsoran mari. Ya sauya kaya,ya fice daga
dakin,wajen Momin sa ya shiga idanuwan sa cike
da damuwa. Ya zauna kusa da ita,tana kallon
yadda ran sa ke bace,don hk ta rungumo
kafadun sa tace, "Yaya dai,yunwa akeji? Ya kada
kai yace, Momi Anti fa zaa mutu,ku maida ta
asibiti.Allah bata warke ba. Ta zura masa
ido,tace,Ba laifin mu bane Malami,a gaban ka ai
kana kallo taki yarda asa mata Drip. To ya take
so muyi?" Yace, kawai ku kira mata abba yayi
mata fada. Wlh bana son Antí ta mutu. Ina son ta
Momì,me yasa take ta wannan ciwon ne? Ta
kara rungume shi tace, kowa ma nason Antin ka
Malami,kuma babu mai son mutuwar ta,Matsalar
taki cin abinci ne,shi yasa ka ganta haka. To sbd
me? Tace kaga ka yi shiru da bakin ka,kai yaro
ne ba ruwanka da maganar manya.kai daì idan
ka yi sallah ka roki Allah ya bata lafiya. Yace, To
Momi,tace. Maza kicin ka zuba abincin ka.'ya
fice tana kallon sa.
Zuwa karfe biyar Mama ta sake fadawa cikin
mummunan hali,bata gane kowa. Anti Amina ta
rasa inda zata sa ranta,domin ta rasa yadda zata
yi da Mama don ta ceto ran ta. Ta sauko falo da
nufin kiran wayar ofishin yallabai. Shigowar mota
harabar gidan,shi ya dauki hnklnta ta zage
labulan taga ta daga.Motar Abdulkareem ke fakin
a harabar aje motoci,ta dawo da sauri ta nufi
kofa cike da farin ciki da baya misaltuwa. Ta
bude kofar tayi waje,farin cikin ta ya karu,ganin
har da Abba acikin su. Sannun ku da zuwa! Ta
isa wajen tana fadi. Duk suka amsa,sannan suka
rankayo cikin gida. Malami ya rugo ya rungume
Abba. Bayan gaishe gaishe suka tambayi Mama.
Tace,tana daki babu kyan gani,nama fito ne,in
kira dadin Malami ko za mu sake komawa
asibitin ne,sai gaku. Wlhy Abba taki cin komai
tunda suka zo garin. Ban jin tasa ruwa a
bakinta,wannan masifa dame tayi kama? Duk
suka yi shiru sbd takaici,babu wanda ya tanka
har Anti Amina ta mike ta kawo musu abincin da
ababen sha. Ruwa kawai suka sha Abba. Ya-ce,
muje mu ganta. Duk suka rankaya saman.
Yanayin da suka riski Mama,ba karamin daga
hankulan su yayi ba. Abba ya zura mata ido,idan
da zai hadu da ita a hanya,ba zai shaida ta
ba,sbd sauya kamannin da tayi,sbd tsananin son
cikawa al-ameen alkawari ko alama bai barì
tausayinta ya rinjaye shi ba. Don hk ya dubi
sauran yace,wannan ba shi zaisa mutuncin mu
ya zube a idon duniya ba.sbd hk zamu koma da
ita asibiti,ta farfado.sannan mu wuce da ita
fandogari. Farin ciki na Mama ta mutu a dakin
nauran al-ameen wanan shne kwanciyar hnkli na.
Ku dauko ta mu tafi.
[12/01 18:20] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***7
.Yayay abdul-kareem yace gaskiya ne abba shi
kuwa yaya abdul-rahman abin ne ya zame masa
banbarakwai don bai taba zaton labarin da yakeji
abin ya kai haka ba duk da yana jin zafin abinda
mama tayi ,halin da idanuwansa suka gane masa
mama a halin yanzu kwarai tausayinta ya kwanta
a zuciyar sa shi ne ya fara kai hannu ya ciccubo
ta suka taimaka suka sauko da ita kasa kamat
matacciya,da kyar likita ya karbe ta sai da yan
uwanta suka yita rarrshinsa sannan ya bata gado
yayi mata duk abinda ya dace. Acan yaya abdul-
kadeer ya same su bayan sallar magariba kafin
ayi issha'I suka rankaya gida akabar anti amina
tare da ita,kusan kwana sukayi shawarwari akan
al'amarin,kwana daya da wuni mama na kwance
magashiyan ledar ruwa goma sha tara ta
shanye,ana shirin daura mata na ashirin sannan
idanuwanta suka fara washewa ta gane inda take
hada ido da abba tare da karkaf yan'uwanta bai
haifar mata da wata nadama ba illa kuka da ta
fasa wai don su tausaya mata babu wanda ya
tanka mata wannan itace shawarar da suka
yanke babu wanda zai sake bata bakinsa don yi
mata fada amma zata sha mamaki ranar da Allah
ya yasa al'ameen ya dawo kasar nan,babu wanda
yace cikanki har ta gaji da shashekar kukanta. A
zaton ta shirun na su alamma ce ta saduda
ma'ana sun rasa yadda zasuyi da ita dole suu sa
mata ido anti amina ta fara bata ruwan lipton
tana kurba da kyar take iya hadiye shi gaba daya
Makogwaronta ya farfashe kafin gari ya sake
wayewa mama ta samo kanta misalin goma da
rabi kawai ganin su tayi sun shigo suna gaya wa
anti amina an sallame ta zasu wuce yanzu bata
yi mamakin jin haka ba don haka ta amsa da
to,Allah kara lafiya ita kuwa yar gigalar murna ce
fal cikin ta jin za a wuce da ita fandogari nan da
nan suka kwashe kaya,yaya abdul-kadeer ya
dauki matarsa,mama kuma tabi ayarin komawa
gida a minna suka yada zango suka ci abinci tare
da yin sallolin azahar da la'asr in banda su
ameera babu wanda mama tayi magana dashi
domin anti rabi ma ta sauya fuska al'ameen
dintama bai sami kulawa ba suna idar da la'asar
yaya abdul-rahman ya jawo matarsa daga inda
ya aje ta aka maida jakar mama ciki ita ma ta
fito ta shige gidan baya abba na tare da karamin
yaya a gaba
Shi ya jasu a hankali xuwa fandagori. tun
daga kan kwana hankalin mama ya soma
kwantawa, domin dai idanuwan ta sun hango
wanda take son gani. yana zaune bisa benci a
kofar shagonsa, yayi murmushi itama ta sakar
masa nata. har motar ta wuce, ba su daina leken
juna ba. sai da ta daina hangensa, sannan ta
zauna sosai kirjibta nata bugawa, ji take kamar
ta balle murfin motar ta fice taje gunsa. ya
mikawa ayuba hannu suka tafa. yace baka da
kyau! Yace karya kak don ubanka, kalle ni sama
da kasa! ba kyawun sura ba, ina nufin.... ya kai
masa naushi a kafada, shi ya katse shi. zan
ci..... kai! ka kiyaye ni fa wlh! me na gaya maka?
yadda suka dauke ya ahaka za su dawo min da
ita. wahalar banza sukeyi sakeena mallaka tace.
yace ranar da Allah kuma zai kama. ayuba baya
wajen, duk ka gama iskancin ka. ya ballo masa
harara yace, to ko ka na wajen me zakyi? kai ma
ka ji da naka, don ubanka. Menayi? ni nakai ka
iskanci a garin nan? dama wane kai, amma
sannu a habkali xzaka biyo ni mujera hanya
watakila ma ka xarta ni. ya tabe baki yace Allah
ya sawwake, kai din ma so nake na janyo ka
baya. ka auri yarinyara nan, ka manta da
kudinrinka na wulakantata. ya dafa shi yace ka
dan kula da shagon, bari na je nemo gasasshiyar
kaza. kasan dole anjima ta zo£ ya xuba masa
ido kawai, bai ce masa komai ba. yayi dan
saurayin murmushin. ya mike ya fada motar sa
yayi birnin gwarin tsinke. kai tsaye mama dakinta
ta shige. umma bata gasganta idonta ba, irin
yanayin da taga mama saboda haka tatashi tabi
bayanta.
Kallo daya tayi mata taji kanta ya ci gaba
da sarawa, wani kululu ya daure xuciyarta,
idanuwanta suka tara kwalla, saboda tsabar
BAKIN CIKI. Ta jima kafin tace, Mama kina da
hankali da tunani kuwa? Ji tayi an dafata ta biyu,
muryar Yaya abdul rahma ke fadin, baki da lfya
Umma, karki daga hankalinki, abba yace ki fito ki
kyale ta. Ya kamo ta suka fito, jiri na dibarta, shi
ya sa tace yawuce da ita dakinta. Abba ya taso
ya biyo su, yayin da take kwanciya a gado.
Gefen gadon ya xauna yace, bai kamata ki bar
ciwon ki ya tashi ba halima, kin ji dai abinda Dr.
Ya fada, jininki ne ke hawa saboda damuwar da
kika sanya a ranki. Ki hrk kawai. Tace, ba
alamun yin nadama a wajen Mama, ni kaina,
nasan haka,amma shawarar da mu ka yanke da
'yan uwanta shine mu sanya mata ido tayi
shirmen ta, sai ranar da Al-ameen ya dawo xata
gane mu ma ba muyi nadama ba. Abdul yace
saboda haka ki kwantar da hankalinki, ISA sai dai
mama ta mutu a dakin Al-ameen, ba zamu ji
kunya ba. Su Yaya babba da Iyalnsu duk sunce
gaishe ki, sai sun xo. Tace ina amsawa, Allah ya
taimake mu, suka amsa ameen. Abba ya dube
shi ya cigaba, kai ma ya kamata ka hanxarta
wucewa yamma tayi sosai. Umma ta amshe, ba
xai bari xuwa gobe ba? Yace, akwai aiki Umma,
yanxun nake so na lallaba. Ta dan kada kai.
Tace, to Allah ya Tsare agaida min safiyya da
kyau. Zata ji, ki daina damuwa Umma, komai xai
wuce da yardar Allah. Ta amsa da kai, tana fadin
shikenan abdul, Allah yayi maka albarka. Yace
amin. Ya wuce cikin hanzari. A tsakar gida ya
hadu da su Haj.Hajjo. Ashe da gaske ne kun
dawo? Yara ke fada mana yanxun. Yace eh, nima
xan wuce kd kenan. Gaba daya suke to Allah ya
tsare! Ya amsa yayi gaba abinda, su kuwa ciki
suka kutsa kai dakin mama. Kwakwazon surutun
su ya sa Abba ya ta so fito. Sannuku da dawowa
Yaya. Yace yauwa, ga haliman can a dakin ta.
Haj. Hajjo tace, muna nan mun ganin ikon Allah.
Mama ta dawo kashi ba rai? Yace haka take so,
ai ku daina bata bakinku, kowa ya sa mata ido.
Haj. Gaje tace, lallai kam wannan al'amarin sai
ido. Allah ya kyauta. Ameen. Suka fice tare suka
koma dakin Umma, suka isheta da surutu. Duk
iya kokarin mama na son fita a wannan daren
abin ya faskara, domin dai Abba ya kasa ya tsare
a falo har goman dare ya garkame kofar ya shige
dakinsa barcinsa. Allah da ikon sa, abba bai xare
mukulin ba, domin bai taba tunanin Mama xata
iya aikata wani abu a wannan tym din ba lallai
abba bai san Mama ta wuce tunaninsa ba. Yana
bada baya, taji motsin rufe kofarsa ta yi wuf ta
mike, takalmanta a hannu tare da mayafinta.
Tayo sanda ta fito jim, tsakar falon bata ji mtsin
kowa ba, sannan ta karasa kofar ta bude ta cikin
nutsuwa ta sulale ta fice. Can ma kofar sassan
hka ta bude ta, ta wuce zaurukan gidan, ta zare
sakatun ta bude ta fita ta maida kofar ta sakaya.
In bakayi bani wuri! Ta callah da gudu bata ko jin
rashin karfin jikinta, sai da tayi rabin tafiya,
sannan ta tsaya ta sa takalmanta ta yafa gyalen
tana ta xuba haki, ta dau hanya babu jama'a
sosai. Gata nan ga ta nan har kofar shagon dan
gogan. Ya tare da dije a kofar shagon bisa banci,
ta cukuikuye shi kamar na goye fadi yake, wai
dan Ubanki dole ne? Kin fa matsa min da yawa,
xan ci ubanki a daren nan, in ga mai kwatar ki!
Kawai ganin mama yayi akan su. Ya banbare dije
ya ture gefe, bai bata lokacin ya daga kanta ya
shige, shagon yana jan tsaki. Mama ta daga
itama ta bishi. Dije kuwa mikewa tayi ta kakkabe
jikinta ta wuce tana kwafa. Ya hade rai a kujera,
bai ko kalle ta ba. Ta matsa gare shi murya
sanyaye tace, fushi kayi danliti? Ni ban yi fushi
ba sai kai? Ina can naki ci na ki sha saboda kai.
Ashe ka na nan ka tare da wata? Dubi yadda na
rame na sauya kamanni, saboda tunanin ka
Danliti. Bai kamata ka yi min haka ba. Ya dago
idanuwansa farare sol! Sunji kwalli ya dubeta, ko
mai nai miki ai kekika jawo, kinbi 'yan uwanki ki
manta da ni, ba dole in sami wata ba! Tun
yaushe kuka shigo garin nan? Nayi ta xuba ido,
amma ban ganki ba, me kike tunanin xan dauka?
Kafin tace wani abu ya fizgo hannunta xuwa
daki, yana kara fadin, idan karya nake yi, xo muje
ki gani! Ayuba dake kwance bisa katifa yayi
firgigi ya tashi yana kallon ikon Allah. Ledar kaji
ya janyo ya xaxxage su. Yace me kika gani nan?
Saboda ke na tafi har birnin gwari na siyo miki
gashin xamani kajin turawa.
Dubi nan juice ne kala-kala har sanyi su ya
fita, baki xo ba. Ba dole in yi fushi ba, in saurari
mai so na! Ta sauke numfashi, idanuwan ta taf!
Da kwallah, ba laifina bane Danliti, baka san irin
bakar wahalar da na sha ba, don kawai su dawo
da ni. Sau biyu ina kwanciya a ascibiti, dube ni
da kyau, kai kanka kasan ba haka nake ba.
Amma kayi hkr, tunda kana ganin kamar da
gangan nayi, ka hkr? Ya xura mata ido jim,
sannan yayi dan murmushi ya ware hannayensa
yace, to oyoyo! Ta sa hannaeyanta ta rufe fuska.
Yace kunya? Ashe baki so na, lallai na yarda ni
kadai nake haukan sonki. Yana rufe baki ta
matso da sauri ta rungunme shi. Ayuba, yayi
gyaran murya. Mama tayi wuf ta rabu da jikinsa.
Ya dubi Ayuba, yace malam ka fita ka bamu
wuri! Yace, ai ku ya kamata ku koma daga waje
anan nake so mu xauna, fita ka bamu wuri don
Allah, shago fah abude yake, ya yankura ya tashi
yana fadin, gaskiyya kuyi sauri ku gamacin
kazaraku, barci nakeji. Ba ruwanka wannan. Ya
fice yana waigen Danliti yana masa ishara da
idanuwansa dauke da gargadu, wanda shi kansa
ya gane nufinsa, shi yasa yake wani irin
mur0ushin na iya shege. Yana fita ya dubi Mama
suka hada ido dukkan su sukayi murmushi,
sannan ya kamo kafadunta yace, gashi dare yayi,
amma dole ki xauna ki cinye kajin nan, domin
saboda ke na siyo su. Ba tace komai bam ya
xaunar da ita gefen katifa, ya jawo kayan
kwalama, ya baje mata kajin, yana bata abaki,
tun tana jin kunya har ta saki jikinta, tana amssa
sosai tana ci, suka ci suka sha suna hirar bayan
rabuwa. Bayan sun kare. Danliti ya dubi
agogonsa ya ce shadaya da kwata yanxu, ya
kamata kije gida ko? Sai gobe, ina fatan xaki rika
cin abinci don ki gyagije kyanki ya dawo kamar
da. Kinji ni? Tace, naji kuma xan kiyaye, amma
don Allah ka daina bari 'yan mata na xuwa
gunka, watarana xamuyi dambe da su wlh, kaji
na rantse. Ya kyalkyale da dariya son ransa kafin
yace, xaki kuwa sha duka, don dai nasan sunfi
karfinki. Wannan jikin naki rugu-rugu babu kwari.
Ya fadi yana mammatsa hannayenta da
kafafuwanta. Ta yankura ta tashi tana cewa,
haka kake gani, ka maida abin wasa, zaka sha
mamaki. Shima ya mike ya kamo yatsunta, yace
karki damu, ke kadai nake so, ko da damben ya
kama kuyi, xan shigar miki balle ma banda
lokacinsu. Ke me xai dameki? Tayi murmushi,
tace, to shikenan sai da safe. Ya sumbaceta
yace, muje na rakaki. Suka fito yana rike da
hannunta, tayi wa ayuba sallama suka wuce. A
kofar gida suka fuskanci juna, tallafo kuncinta ya
xura mata ido, yace karfa ki damu da ganin Dije
tare da ni, wlh ba sonta nake ba, kawai ta matsa
min ne dole muyi soyayya, amma xan dauki
mataki akanta, tinda ta fara bata miki rai. Tayi
murmushi, tace, nayarda da kai, ina fatam Allah
ya yarda mana, ya bamu nasara abinda muka sa
gaba. Da sauri ya amsa amin sakeena. To sai da
safe nagode, wannan karon abin ya cigaba akan
labbanta ya sumbace ta. Ta juya da sauri, ta
tura gida ta shige ta maida sakatu. Danliti ya
runtse ido ya jinjina hannayensa, shege ni! Ya
juya yana takawa dda+dai kamar wani
kasaitaccen basarake. Mama kuwa sanda takeyi,
kamar barauniya ta turo kofar fa'aar dshigo ta
mayar d hankali ta kuleta, ta fada gado. Tana jan
mayafi, taji a; ttay bude kofa, tayi tsaye jim,
sannan ya mayar ya rufe. Muryar umma taji tana
fadin, menene alh.? Yace kamar motsin naji ana
taba mukulli.. Tace Innalillahi an shi ne? Yace
amma ban ga kowa ba. Ya dubi agogo, karfe sha
biyu saura kwata, dare ma bai yi ba sosai, to
Allah yai mana tsari da sharrin masu sharri. Yace
amin, je ki kwanta. Cikin fargaba suka bar falon.
Mama ta gyara kwanciya tana gyatsar naman
kaxa. Dan kanta tace kwanta naman kaza. Tayi
tunani Danliti har barci ya kwashe ta, shi take
marfi yana sa mata naman kaza abaki. Da safe
tayi wanka, duk 'yan ciwukan da suka rage ba su
warke ba, ta goga musu mai, ta shafa hoda ta sa
atamfah riga da xani, nan da nan ta dan yi fasali,
duk da cewa akwai rama sosai a jikinta. Yau kam
tayi dan kyan gani, ta fito falo wajen Umma cikin
kicin inda take aikace aikacenta, tace sannu
Umma ina kwna? Ta juyo da sauri ta dubeta
sama da kasa, tace kalau na kwana. Ta kara
matsowa tace, bari in gaida Abba, sai in xo in
tayaki aikin. Bata amsa ba ta fice, ta bita da
kallo sannan ta kada kai tace, Allah ya shirya.
Dakin Abban tayi sallama, ya amsa ya bita da
kallo, ta karaso gunsa ta tsugunna, ina kwana
Abba?
Yace Kalau, ta dan dube shi, amma bata
kara komai ba, ta mike tayi waje ta koma kicin:
Umma me xan tayaki? Tace ban so, koma dakinki
kawai. Saboda me Umma? Ai ban isa na fadi ko
saboda mene ba, tunda kin xama shafaffiya da
mai. Je ki kawai ki sha xamanki. Kai tsaye kuwa
ta wuce daki abinta. Tana fadi cikin ranta, kya
gama girkawa, mu zo mu jajja (hmmm mama tayi
nisa walle). Kan Umma ya sara ganin yadda
mama ta wuce ko ajikinta, bata damu ba.
Mamaki bai gama kashe Umma ba sai da ta
hange ta kicin din tana diban abinda take son ci.
Tana kallo ta koma dakinta ta cinye, ta maida
kayan kitchen ta fito. Haushi ya kume Umma
bata san tym din da tace, Uban wa kika ajewa
kayan ya wanke miki? Tabbatacciya! Ta dan bata
rai ta juya ta kwaso kayna ta wanke. Karfe 9
abba ya fita harkokinsa. 9:30 mama figi gyale
tayi waje, Umma nace na wanka. Ta sha hirarta
wajen Danliti har 12pm sannan ta tsallaka ta
gangara wajen Baraka. Sosai taga sauyin fuska
wajen Inna saude. Sam abin be dame ta ba.
Suna kebewa da Baraka tace. Kawata ban gane
ba, sai da nayi miki kallon kurulla. Yanxun
saboda Allah dawowa kikayi? Tace ga ni kuma
kina ganina. Matsala tace, babu ruwan kowa.
Mutane masharanta ne kawai, saboda Allah yayi
wa Danliti kyau da farin jini, ga shi ya Rufa masa
asiri, shi ya sa ake masa hassada.... Ta katse ta,
idan hassada ce, ai kuwa kem kinyi masa da.
Menen baki fada ba akansa? Tace, Rashin sani
ne, duk surutan da akeyi wai dan Iska ne dan
guguwa. Dan wata tsiyace, ni har yanxun Danliti
bai taba furta min maganar banxa ba balle ya
nemi aikata wani shashanci. Rashin fahimta ne
kawai yasa ake masa zargi, kisan mutum mai
farin jinin 'yammata (Kuji fa wai bai taba mata
komai ba?) baki ganin ko mace ce ta fiye samari
sai arinka mata wani irin kallo? Baraka ta sauke
fuska, tayi guntun tsaki, baki jin kira Mama. Allah
ya shirye ki. Ameen, ni bari in koma gida, dama
lekowa nayi mu gaisa kisan na dawo. Tabita da
kallo, ki na san kin dawo wajenki xano? Menene
anfani kawancen mu? Bayan ko na gaya miki
gaskiyya bakyaji. Allah ko? To Allah ya bamu
alkhairi ki gaida mohd dinki, in yazo. Yaushe
xasu kawo gaisuwane? Ko bai shirya aure bane?
Wlh ban masa zargin komai ba, amma sonsa bai
rufe min ido ba, ina bukatar in gama sanin ko shi
waye tunda ba gari daya muke ba. Ta tabe baki,
Baraka ke nan, Miss kakale! Ba kakale bane,
gaskiyya ce kawai, daga kinta sai bata. Shi ya sa
nake nuna mikita, don banson ki bata. Ta mike
hannu daya kame da kugu, tace, nagode, ni nayi
gida, kar Umma ta neme ni. Tasa kai tafice.
Baraka ta biyota, ta sallami Inna ta rako ta iya
zaure ta juya. Ta shige gida, tabar mama dauke
da mamaki. Tai kwafa tace, kiyi da gwana
yarinya. Ta kama hanya ta koma wajen Danliti,
wasa-wasa sai da ta bata mini talatin anan,
sannan ta karasa gida. Umma na zaune tskar
falo ta sha tagumi, ta gaji Mama ta shigo babu
ko tsoro ko fargaba tace, sannu da gida Umma.
Inna saude na gaisheki. Ta zura mata ido ba tare
da cire tagumin ba, jima kafin tace, da izinin wa
ki ka bar gidan nan Mama? Ta mimmike kafa
sosai akujera. Tace ai kinshifa wanka ne Umma
shi yasa banyi miki magana ba. Umma ta
numfasa, tayi hucin BAKIN CIKi tace, lallai kin
isa mama, duk son danliti ne yasa kika zama
maras kunya? To kibi a hankali, duniya zata koya
miki hankali, muddin kika dauke ta kika goya. Ta
figi gyalenta, ta mike cikin sauri tana fadin,
Uhm.....! Ta wuce ta fada dakinta, tayi
kwanciyarta. Umma ta kada kai, kwallah suka
xubo mata, ta share tace, Allah kana kallo, munyi
iya yinmu, amma shiriya na wajenka, kayi mana
gaji Ya Allah. Nan Umma taci gaba da zama tana
shan BAKIN CIKI tare da takaici mai tarin yawa
har aka kira azhar, ta tashi tayi sallah. Abba ya
dawo ta labarta masa, hannaye biyi ya kama kai,
takaici kamar ya kashe shi, bai niyyara kara yiwa
Mama wata magana ba akan Danliti, amma dole
tasa ya kira tazo dakinsa ta xauna. Yayi mata
kaca-kaca, sannan ya sa mata dokar fita ko'ina,
duk da yasan ba dole bane tabi umarninsa.
Tabbas hakan ne, yadda Mama ta fito dakin bakin
nan nata ya kai wani gari wai shi ZUNTU. Shi
kasna ya san rashin kunyta Mama ta kai wani
mataki na kololuwa kwatance, ta xauna bakin
gadon ta tana fadin a fili, wannan shine bature
ke kira Impossible! Tunda kuka hana shi xuwa
guna, dole inje gunsa mu ga juna. Ta saki wani
lafiyayyen tsaki, ta yada kai bisa filo.........
Maganar mama dutse. 7days
kenan babu abinda ta fasa, muna iya cewa
al'amarin kara haukata yayi. Domin a halin
yanxun Mama bata shayi, agaban Umma zata
dauki mayafinta, ta fice. Umma na kira, tana
fadin tana xuwa yanxu xata dawo. Sau uku
Umma na xuwa da kanta kofar shagon Danlinti,
tana taso keyarta. Jama'a na kallon su, gwanin
ban kunya. Sai da Abba ya hanata xuwa. Yace
tasa mata ido, tunda ta zama gagararriya.
Wannan abin kunya ya zama abin yayatawa
awajen su hajjo, duk inda suka xauna xancan
kenan. Babu abinda bai dawowa kunnen Umma
ba, sai dai tayi kuka ta share hawayenta ta
barwa Allah komai. Mama fa ta gagari kowa,
suna ji suna gani mummunan labari na ta
yaduwa har gidan Gwaggo Hausi. Daga can
labarin ya mika gidan Marafa. Nana take mami
ta tsani auran mama da Al-ameen. Shi kuwa
Marafa nuna mata yake su daina kama jita-jita.
Aure dai nufi ne na Allah, idan sakeena matar Al-
ameen ce, bbu makawa xai aureta, idan kuwa ba
matar sa bace si barwa Allah yayi masa zabin
alkhairi. Duk da haka al'amarin yana jefa Mamai
cikin tunani ba kadan ba, kuma da Al-ameen zai
ji shawarar ta, da ta umarace shi daya hakura da
sakeena, tunda shasahnci tasa gaba. Sallar
la'asar ta kammala, amma bata bar sallayar ba,
saboda gabatar da lazimi takeyi. Wata tasi tayi
fakin kofar gidan, direban ya fito ya bude but,
yana fido jakar kaya. Yana rufe but din, idanuwa
na suka nuna min Al-ameen a tsaye ya cusa
hannu gaban riga ya zaro kudi ya mikawa
direban, yace, ka rike chanji. Ya sunkuci jakarsa
ya wuce. Direba na xuba gdoiya. Ya tura karamin
gate ya shiga, bakin mai gida har kunne ya taso
da gudu ya amshi jakar yana fadin Maraba da
oga! Fuskarsa babu walwala sosai, yace ya
kuke? Lafiya lau oga. Ya shige masa da kaya
falo. Al-ameen yayi sallama, muryar sa ta dauki
hankalin duk wanda ke cikin gidan. Iya ta riga
kowa fitowa, wa nakehi kamar dan Iya? Ya nufo
ta fuska sake, ni ne iya, surprise ko? Ya dan
rungumo tana fadin, ai kaki koya min turancin
nan, da yanxun na gane nufinka. Yana murmushi
ya rabu da jikinta, ya dubi Ladi, Hajiya Ladi ina
fatan kunje kun duba min jikin sakeena ta? Tace
muna dai shirin tafiya da hada tsaraba. Ya ce,
baku da tsraaba? Gaskiyya kunyi min babban
laifi. Tace, mun san hakan amma tuba muke. Ta
ya kuke? Ta amsa lfya lau ya hanya? Yace,
Alhmdlh. Yana juyo wa sukayi ido hudu da mami
tana masa kallon mamaki. Ya nufe ta da sauri ya
rungumeta, Mami na! Idanuwanta suka tara
kwalla, ta kasa cewa komai har ya dago ya
dubeta, yayi dan murmushi. Yace, nayi muku laifi
Mami, kuyi min hkr na kasa daurewa ne. Tace
nagode Allah da ya kawo ka lfya. Amma banji
dadin xuwanka ba Al-ameen. Yace, na tuba
Mami, ki duba halin da nake ciki, kiyi min uzuri.
Ta dan kada kai. Tace, muje ciki ka sha ruwa ka
yi sallah. Suka wuce yana tambayar Dadinda.
Tace, xai dawo anjima daga kd. Yana xama Ladi
ta shigo masa da ababen sha masu sanyi. Bayan
ya jika makoshi, ya dubi Mami yace, ya jikin
sakeena? Na daina kiran waya, don kunnuwa na
ba za su jure jin mummunan labari ba, koda
yaushe. Dalilin da yasa kenan, nace ya xama
wajibi in xo inga halin da take ciki da idanuwa
na. Dan hutu muka samu na sati daya, shine na
yi anfani da wannan damar. Yaya yanayin jikin
nata yake? Ta numfasa sosai kafin tace, jikin ta
har yanxun a rikice yake, xan so ace Allah ya
saka maka hkr, da dangana akan sakeena, domin
kwakwalwarta ta jirkita Al-ameen..... Hauka
Mami? Kina nufin sakeena ta haukace? Inna-
lillahi wa Inna-illaihiri Raji-un! Idanuwansa suka
tara kwalla, ba xan iya hkr da ita ba Mami, ko ba
zata taba warkewa ba, sai na aureya. Alkawari
ne wannan Insha Allahu ba xan karya wa sakeena
ba. Tana ina ne yanxu? Ita ma nata idanuwan
suka kawo kwalla. Ta ce, tana Fandagori, kuma
ni ma xan so hakan Al-ameen, domin duk abinda
kake so, nima shi xuciyata take matukat so da
kauna. Amma al-amarin ya sauya salo, ka dauki
kaddara kayi hkr da ita, hankalina zaifi kwanciya
Al-ameen. Da gudu hawayen sa suka wuce bisa
kyakkyawar fuskarsa, ya matso ta a hankali, ya
dauko hannayenta biyu ya matse, ya dubeta ido
cikin ido. Yace, har abada bana fatan in saba
umarnin ku mama, amma ina rokon alfarma ki
ban izini in cikawa sakeena alkawarin da daukar
mata. Zan tafi samun nutsuwa, idan ina kallonta
a matsayin mata ta kowane irin yanayin take. Ina
rokon ki Mami ki taimaka min. Ya jingina
goshinsa bisa kafadar ta, ya matse hawayensa
tare da ajiyar zuciya mai karfin gaske. Haka
maminsa ke cikin irin wannan yanain. Ta jima
shiru tana tunanin zuci, tana son gaya masa
gaskiyya, amma bakinta ba xai iya furtawa ba,
saboda tausayin dan tilon dan ta. Ta yi ajiyar
zuciya. Tace, nayi maka Umarni akan duk abinda
yafi xama alkhairi Al-ameen. Mike ka je kayi
sallah kaci abinci. Ya dubeta yana share kwalla.
Yace, nagode Mami. Ta danyi murmushin dole.
Jeka yi sallah. Ya tashi da sauri ya dauki jakarsa,
ya fice. Mami ta raka shi da kallo, hannunta a
kunci. Ta nunfasa kafin tace, Allah gamu gareka.
Yana shiga, bangarensa ya isa ya yar da jakar
hannunsa ya xauna gefen gado
Ya kama kai hannayensa 2 yana yiwa
Allah tasbihi. Jim kdan ya tura hannu aljihunsa,
ya xao wallet dinsa ya bude ya xurawa dan
karamin hoton Mama ido, nan da nan hwaye suka
goce masa, bai ma san tsaninin kukan da yake
ba har da shassheka, kamar xuciyarsa zata tsago
kirjinsa. Allah da ikonsa, tamkar mami na da
masaniya ta taso ta biyo shi dakin, don ganin a
wane yanayin yake? Da sauri ta karaso ta zauna
kusa ta shi ta rungumo abinta, idanuwan na tara
kwalla. Komai ya sami bawa daga Allah ne Al-
ameen, bai kamata ka xauna ka rinka kuka ba!
Jin muryarta yasa hankalinsa ya dawo jikinsa,
sannu-sannu hawayensa ya tsane. Ya dago ido
jajur! Ya dubi Mami, yace mami ki amince min
inje in dubo sakeena Yanxun. Ta goge masa
guntun kwallan dake bisa kuncinsa. Tace, na
baka izini Al-ameen, fargaba na kawai dare.
Yace, kar ki damu Mami. Allah xai tsare.
Shikenan, Ubangiji Allah ya sa ganinka ya xama
waraka gareta, hankalin kowa yakwanta. Yace,
Ameen Mami. Tace , To kayi sallah Maza-maza,
don Allah kar ka zauna dogon tunani. Yanxun xan
fito Insha Allahu. Ta mike ta bar dakin. Al-ameen
Ya sauke numfashi, shima ya mike ya fada bayi,
nan da nan ya watso ruwa ya dauro alwala ya
fito. Bayan yayi sallah ya kimtsa, ya fito Mama
ta matsa yaci wani abu, amma bai iya zama ba,
gaba daya hankalimsa ya koma Fandogari. Sai
dai ya sha Mamaki daya ga Mami ta nace dole
ya tafi da direbanya, bai yi musu ba. Kai tsaye ya
shiga mota direba ya ja shi suka dauki hanya
suka bar Mami cike da damuwa tare da tunanin
yaya al'amarin zai kasance idan Mama ta juya
wa Al-ameen Baya?
[12/01 18:24] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2*** 8
Ba su ido Fandogari ba, sai
karfe 8pm, babu bata tym gidan Uban dawaki
suka dosa. Ya shige sassan sa tare da sallama.
Umma ta amsa ba tare da ankara da mai muryar
ba. Sannu Umma. Ta dube shi da kyau, gaban ta
yayi mugun faduwa, ta mike tsaye tana fadin, Al-
ameen! Saukar yaushe? Yace, yau din nan
Umma. Ikon Allah. Sannu da xuwa! Zauna mana,
ya zauna yana amsawa. Kafin yace, ina yini
Umma? Ta amsa, lfya lau ya karatu? Mun gode
Allah, ya jikin sakeena? Tayi dan shiru, kafin tace
wani abu. Abba yayi sallama ya shigo, duk suka
amsa amsa Abba! Yace, ah! Al-ameen! Saukan
yaushe? Yace daxun da la'asar Abba. Ya xauna
suka gaisa, sannan ya sake tambayar jikin
mama. Abba yace ciwo na nan Al-ameen. Halima
kawo masa abinci ya ci, kafin muyi magana.
Abba bana jin yunwa, domin na riga na saba da
ita, tun tym din na sami labarin tashin hankalin
da kuke ciki. Abin daya hana ni jurewa kenan,
nace dole in xo inga halin da Mama take ciki.
Abba yace, gaskiyya ne. Mama na nan cikin
lularar da ta sameta sai dai al'amuran zai ba ka
mamaki idan na gaya maka alabari ya sha
bambam Al-ameen, nasan an boye maka komai
coz of karatunka, amma yanxun dole ka sani,
tunda ka zo. Jikinsa ya kara sanyi, yayi xuru
yana sauraron abba, al-ameen rayuwa ta
sauyawa mama, wanda muke ganin sa tamkar a
mafarki, daga ni har 'yan uwanta kaf! Babu
wanda ba shi ckin alhinin wannan abu. Balle
kuma kai da soyayyah ta hada ka Mama, kuma
ita da kanta takwo mana kai cikin gidan nan. Shi
yasa nayi rantsuwa, idan mama xata mutu, sai
dai ta mutu a dakin ka tunda tun farko ita ta
kawo ka. Ashe kuwa babu wani dalili ko uzuuri
da xata kawo mana mu saurare ta. Nasan har
yanxun kana jina a hagunce ne, baka gane inda
na dosa ba. To bari na fito maka a mutum kada
ka wahalar da kanka, Magana daya ce, mama ta
gano wani kuma idanuwanta sun rufe ta manta
cewar tayi xafin farko kuma na karshe a
swajena. Ka fahimce ni? Gaba daya kansa ya
kunce, daga yadda yayi kuri idanuwan sa kafe
yana kallon Abba, suka gane bai fahimci su ba.
Saboda haka yace, dole ka shiga rudu fiye da
wanda ka shuga a baya, amma ina so ka sani,
mu muna tare da kai, ba mu san kowa ba face
kai, ba don komai ba sai don tun farko kai tafara
kawo mana. Abinda nake son ka gane shi ne,
xuwanka ya sanya ni farin ciki. Domin kai kadai
nake jira in tabbatar wa Mama cewa lallai ni ba
tsohon banxa bane, kuma bana magana 2.
Ina mai tabbatar maka ba xaka koma ba
sai na daura auranka da sakeena da yardan
Allah. Na gama magana ta, ka tashi hankalinka
kwance, kashiga wajenta tana nan cikin dakinta.
Ya mike ya bar falon. Umma ta dube shi tace,
Al-ameen! Murya dishe ya amsa, na'am Umma
tace kayi hkr, ka kwantar da hankalinka. Mama
bata isa ta xubar mana da mtunci ba. Kai zata
aura da yardar Allah, domin da kai ne akayi mata
baiko. Tashi ka shiga wajenta ku fahimci juna. Ta
mike tabashi guri, don yaji dadin tashi......... Me
kunnuwan Al-ameen ke ji yau? Ya runtse ido
tamau! Ya girgiza kai wai ko barci yakeyi ne?
Abba ya xo masa a mafarki. Ya bude idanuwan
ya ware su sosai, tabbas zaune yake cikin falon
su Mama. Kenan dagaske ne maganganun da
Abba ya gaya masa? Kirjinsa ya soma bugawa ji
yake kiris! Yarage ya zare masa rai, saboda wani
gagarumin ciwo da yaji cikin xuciyarsa, nan take
ya kama shi. Motsin kirki ya kasa yi har Umma
ta sake fitowa da nufin dauko wa Abba
abincinsa. Ta danyi jim, tana masa kallon tausayi,
sannan ta matso tayi kiransa, ya dubeta firgigi
idanuwa sun juye jajur! Tace, ka na xaune, baka
shiga ba? Tashi ka shiga mana, ka kwantar da
hankalinka, komai xai wuce Insha Allah, ya mike
a kasale, ya nufi dakin ba tare da yasan me xai
je yayi ba. Tana zaune tsakar daki ba ta hade kai
da guiwa, tsiyayar hawaye kawai takeyi, domin
tana jin duk kalaman da Abba ke fadi. Daf! Da ita
ya tsugnna, bai san lokacin da yasa hannu ya
dago fuskarta ba. Sukayi wa juna xuru tsawon
lokaci kafin yace, kin ganeni sakeena? Al-ameen
ne, kin gane ni? Ta kau da kai abinta. Da sauri ya
kara juyo da ita, kiyi min magana sakeena ko na
sami nutsuwa saboda ke na dawo kasar nan, don
na duba jikin ki. Ina can tunani da xulimmi sun
addabe ni, idan kin gane ni, ki amsa min, ya jikin
ki? Ta watso masa harara, hawaye na kwarara.
Tace waya gaya maka banda lfya? Yace, haka
kowa ke gaya min tun tym din da na daina jin
muryarki a waya, komai nawa ya tsaya sakeena,
radadin ciwon daya sameki, ya hanani sukuni. Ina
fatan gani na ya zama sanadin samun saukin ki.
Ta goge kwalla. Tace duk wanda ya gaya maka
banda lfya, ya maka karya, kalau nake, gani kuma
kana kallo na xaune, sai dai na tabbata dawowar
ka zata iya zame min cuta! Ya kara xura mata
ido , kina nufin abinda Abba ya gaya min yanxun
gaskiyya ne? Tace ka daina kokwanto. Ya
langwabe kai gwanin ban tausayi. Yace dole nai
kokwanto sakeena, don nasan akwai alkawarin a
tsakanin mu, kuma bana tunanin zaki yaudare ni,
wannan ya tabbatar min da tsantsan son da kike
min. Ban taba kallonki da xuciya 2 ba sakeena.
Shiyasa har halin yanxun da nake magana dake
ban yarda kin karya alkawarin mu ba. Ta kalle
shi a dage, ta watsar tace, ya kamata ka amince,
tunda gashi da bakina ina gaya maka, tsutsun
soyayyarka yayi fiffike yayi dogon tashi. Ya dafe
kirjinsa a natse idanuwansa tam! Da wahaye,
yace, bai tashi ba sakeena, nayi rantsuwa kina so
na. Akwai miskhila dai a wani wuri, ki gaya min
laifin da nayi miki. Wlh da kaina xan hukunta
kaina, koda da jinin jikina ne xuba, idan har zai
zama fansar tarin laifin da nayi miki. Gaya min
da sauri inji. Ta ya mutsa fuska, hawayen ta ya
bushe tace, Al-ameen ka farka daga barcin da
kakeyi ka saurareni, ni sakeena na gaya maka a
da naso ka, amma yanxun ban son ka, ba kuma
zan aure ka ba, idan sama da kasa za su hade!
Kaji ni ko? Sai na maimaita? Ya matse ido,
kwalla
masu zafi suka yo waje da gudu, ya dan kada kai
murya shke yace, kin xuba min dafi, kin xuba min
dafi sakeena. Baki tunanin amana? Yasa hannu
ya kamo yatsunta, ya kura wa zobensa ido, ya
ciga, baki kallon zoben alkawarin mu? Me yasa
kika mance da dimbin kalaman da kika sha gaya
min? Wadanda suka jaddada imani na akan son
da kike min? Ta kwace yatsunta a hankali ta zare
xoben, ta jefa masa, ga tsiyarka nan, idan shi
kake kallo a matsayin alkawari, ni ma cire min
nawa ka bani. Yaci gaba da kallonta, kafin ya
dauko zoben yace, kiyiwa Girman Allah ki maida
zoben nan sakeena.... Bazan karba ba! Idan ma
ka aje shi, zan jefa shi masai! Kuma nima dole
ka ban nawa! Yace sai dai ki kashe ni, sannan ki
zare shi, wannan din ma zan ciga da boye shi,
har xuwa tym din zaki sami nutsuwa dakin
auranmu. Ta kwada masa harara, sannan tayi
wani dan murmushi na kaico, ta kauda fuska, y
mika hannu ya kamo habarta, ta sa nata da karfi
ta doke nasa, kafin tace, karka sake tabani, idan
ba haka ba kuma sai na kurma maka ihun dan
iska! Ta mike da sauri ta bar wajen, kai tsaye
bayi ta shige, ta maida mukulli ta kulle.
Yayin da Al-ameen ke cigaba da kiranta.
Ya tashi ya tsaya kofar bayin yana fadin, ki fito ki
saurare ni sakeena, ya kamata mu fuskanci juna,
mu gane inda matsalar mu take. A zatona har
duniya ta nade ba zaki taba juya min baya ba!
Tana daga ciki ta amsa, bazan fito ba. Daman
kasan inda dare yayi maka, yace ki tuna alkawari
sakeena, don Allah karki bari ayi min dariya. Idan
na rasaki zan iya rasa komai nawa, ki tausaya
min sakeena, kar damuwa ta kasheni. Tace, kan
ka akeji! Ni na gama magana da kai. Ko za'a
kashe ni ba xan sauya ba, dama ka kama
gabanka zai fiye maka alkhairi. Ya tsaya jim,
shiru goshin sa jingine da kofar ya rasa inda zai
tsoma ransa yaji dadi. A hankali ya soma
karannto Innalillahi Wa inna ilaihir Rajiu'un. Ya fi
10mins tsaye. Sannan ya juyo da sauri ya fito
yana share fuska da hankaci. Kawai arba yayi da
su Abba zaune falon. Ya rage sauri ya nufi gunsu
ya tsugunna, abba zan koma. Gab dayan su ido
suka xuba masa, jim Abba yace, amma dai ba
minna zaka nufa ba yanxu ko? Ya dan kada yace,
kuma ka kwantar da hankalinka Insha Allahu
Mama matar kace. Kar ma ka bata tym din
wajen xuwa goben, kai tsaye ka wuce gida, ka
gayawa Marafa ina tafe da kaina, muyi magana.
Yace to, Abba na barku lfya. Ya mike ya fice
suka raka shi da kallo. Ummma kam bata sami
cewa komai ba, saboda tsabar tausayinsa. Yana
fitowa Gambo direba ya balle murfin mota ya fito,
ya tarbe shi ganin ogansa na ta share fuska,
yaya jikin nata? Ya dube shi ido jajur yace ba
sauki Gambo. Mu shiga mota, ka maidani gida.
Yace yallabai ai dare yayi sosai, nayi zaton gidan
gwaggo xamu kwana. Ya miko hannu yace bani
keys, kai ka wuce gidan Gwaggon ka kwana! Ya
dan sunkuyar da kai, yace yi hkr yallabai Allah ya
sauke mu lfya. Shi tuni ya bude gidan gaba ya
fada. Gambo ya xauna mazauninsa da sunan
Allah ya murza mukulli yaja suka wuce, a tym din
agogon motar yana nuna 09:45pm. A daren nan
nake son ganin Dady na. Gambo yace Allah ya
yarda mana, ita kuma Allah ya bata lfya. Ya
kama kai ya runtse ido, ya jingina sosai da kujera
yana fadin amin Gambo. Direba na ta tsula gudu
cikin dare. Shi kuwa Al-ameen kurwarsa na can
cikin tunanin baya. Itin tsantsan son da Mama ke
masa, shi yake gani cikin idanuwansa, har xuwa
ranar da ya xo sallama da ita a sch, kawai
gambo ji yayi Al-ameen na sambatu, sosai kikace
kina sona sakeena, dama yaudara ce? Me yasa
sakeena? Me yasa? Hnkalin Gambo ya koma
gunsa yayi kiransa sau uku, kafin yaji kiran. Ya
xuba masa ido yayi da direba ke fadin, kayi hkr
yallabai, yace sakeena ta yaudareni Gambo, ta
xuba min dafin da xai wuya na sami maganinsa.
Xan iya mutuwa Gambo, domin gaba daya na
sallama kaina gareta. Ko kasan inda nake da
mishkila ka gaya min in gyara? Gaba daya
tausayin sa ya lullube gambo, ya kada kai da
sauri, yace babu inda kake da mishkila Yallabai,
sai dai ko ajizanci na dan adam. Ni kaina ban
yarda sakeena bata sonka ba, watakila ciwo ne
rudata yace, kai ma ka yarda bata da lfya ko?
Amma kowa yace kalau take, ni nasan sakeena
bazata ki ni haka kawai ba, zuciya na wasi-wasi.
Gambo yace , kar ka damu Yallabai, Allah zai
warware komai, sakeena zata zama matarka. Ya
sauke numfashi mai karfi yace, wannan shine
babban burina a duniya, komai Allah ya bani na
gode masa, saura wannan burin ya rage min.
Shima zaka sameshi Insha Allahu. Yayi dan shiru,
sannan ya kada kai yace, laifi nane, rashin
kasancewa ta kusa da sakeena, shi ya jawo
shaidani ya shiga tsakanin mu. Lallai mata na da
rauni Gambo, ba taba tunanin sakeena zata iya
hango wani har ya rikita ta amince dukkan
amanar da muka damka ma juna. Al'amarin na
daure min kai, na rasa yadda xan fassara shi.
Yace, haka ne yallabai, amma idan ka barwa
Allah komi na tabbata xai maka zabin alkhairi. Ka
sani ko wata jarabawa ce Ubangiji yake yi ma
don ya gwada imanin ka. Kar ka damu Yallabai,
Allah ba zai hana ka sakeena ba, idan har kayi
imani shine mai hanawa da badawa. Ya sake
jingina da kujera, ya runtse ido ka fadi gaskiyya
Gambo, na gode. Bai sake tankaea ba haka kuma
bai daina tunanin xuci ba, ma'ana sakeena bata
daina xuwa cikin idanuwan sa dauke da lallausan
murmushinta mai sanyaya masa rai, tana tura
hularasa gaban goshi bakinta na fadin, so much!
Shi ya sa baya aikin komai face ajiya xuciya.
Gambo na jinsa tausayinsa nakara zama cikin
ransa. Karfe daya dai-dai na dare motarsu na
tsayuwa kofar gate din gidansu. Gambo yayi hon,
nan da nan Mai gadi ya shaida hon din motar
mami ne, ya taso a guje ya bude kofar, motar ta
shige kai tsaye kofar shiga ya tsaya. Al-ameen
ya fito, sannan ya wuce ma'ajiya motaci. Tun
kafin ya kwankwasa, yaji ana kokarin budewa,
don haka ya dakata hannayensa biyu cikin aljihu.
Marafa ne da kansa ya bude kofar, suka zuba
juna ido, daga bisani ne mami ta bayyana wajen
har ta riga marafa magana, Al-ameen .
Idanuwansa suka yi tam da kwalla, ta yi azama
ta jawo shi ciki, daddynsa ya maida kofar ya
rufe. Don me ka iyo daren nan Al-ameen? Sai
kace babu inda zaka raba ka kwana! Ya zauna
dabas! Ya kama hannaye biyu, Marafa ya xauna
kusa shi.
Ya rungumo kafadunsa, yace baka kyauta
min ba Al-ameen, da ka dauko hanya cikin daren
nan dan kuskure kadan za'asamu, shikenan ka
ajwo mana tashin hankali, karfa ka manta, kai ke
nan guda daya muke kallo zukatan mu na
wankewa daga radadin rashin da. Ya dube shi ido
jajur! Yayin da Mami itama ta xauna daya gefen
suka sanya shi tsakiya. Yace, na kosa in ganka
Dady, sakon Abba xan gaya maka, yace gobe
yana nan tafe maganar aure na sakeena, kafin in
koma yake so a daura shi. Mami tace, kun
daidaita da sakeenar ne? Ya dan kada kai yace,
sakeena ba warke ba Mami, hasalima bata gane
ni ba, shiyasa tun farko nace a kaita asibiti, kowa
yaki amincea da ni, ga shi nan kwakwalwarta ta
tabu. Sakeena ta kasa ganeni Mami, ni kuma
bazan fasa auran ta ba, domin shine babban buri
na a duniya. Su abba sun goya min baya, kuma
ku taimaka min buri na ya cika don girman Allah.
Gaba daya ya kara daga musu hankali babu
kamar Marafa da ko alama baya kaunar yaga
dansa na kukan neman wani abu, shi yasa nan
take ya ji ko ana ba maza ha mata, sai Al-ameen
ya auri mama. Amma ita Mami bata an ta dosa
ba, don haka tace. Al-ameen bania ron hankalin
kanan, na ga alama baka yarda Sakeena lfy lau
take ba.... Ku kuka gaya min ai Mami... Yanxun
kuma ni na gaya maka lfya, kawai cin amanar ka
tayi, tunda kaje bata saurare ka ba, kai ma ka
manta da ita kawai, ka roki Allah ya musanya
maka da mafi alkahiri. Bafa sakeena kadai ce ta
yalwatu da dukkan abubuwan da kake so ba.
Saboda haka ka kama kanka, ka nutsu ka gane
cewa ko an daura auran, ba zaku zauna lfya ba,
tunda idon ta ya bude, tana takamar tana da
kyau, kowa na kallonta, kajini? Ya girgiza kai,
idonsa xuru yana kallonta, tace au baka ji ni ba?
Menene nufinka? Marafa ya amshe don Allah,
don Annabi ki kyale shi, ba yace Uban dawaki na
taf ba? Allah ya kaimu goben lfya, shi aure ai
nufi ne na Allah. Yanun kaje ka kwanta mu
saurari goben, kaji? Yace naji dady, don Allah ku
tayni da addu'a sakeena kadai nake so. Yace na
sani, addua kuwa kullum munayi, kayi alwala ka
sami koda raka'a 2 ne kafin ka kwanta, na
tabbata zaka sami nutsuwa ok? Ya amsa da kai
ya dan bubbuga kafadarsa yace, yau dan Dady,
Allah ya bamu alkhairi. Bai dai tanka ba, ya mike
ya bar falon. Mami ta cire tagumi tace, sai Allah
yayi wa yaron nan sakayya! Yadda tai masa haka
Allah zai mata. In banda idon Al-ameen ya rufe a
kanta, me zaici da ita? Yarinyar da gwaggo tace
shagon saurayi take su raba dare suna.... Marafa
ya katse ta, don son Annabi, ki bar wannan
magana haba. Ki yi masa fatan alkkhairi kawai.
Cikin bacin rai ta mike ta koma daki. BAKIN CIKI
kamar ya kasheta. Shi kuwa Al-ameen yana can
yana nafilfili kamar yadda dadinsa ya umarce shi.
Da safe ya fito gaba daya ya zabge, kallo daya
za kai masa ka tabbatar da hakan. Gaban mami
ya fadi ta kwala wa Ladi kira ta zo a gigice.
Tace, to hajiya. Ta juya da sauri ta fice. Mami ta
dube shi tace, matso nan kusa da ni. Ya kara
matsowa yace, ina kwana? Ta amsa tana shafar
kansa. Ina dadina, bai tashi bane? Tace, kwana
yayi baiyi barci ba, sai bayan sallahr asuba
barcin ya sace shi. Tana rufe baki ladi na
sallama da tiran abinci ta dire gabansu. Tace ga
shi hajiya dr, Iya tace in gaida ka, yanxun xata
shigo. Yace ina amsawa. Ta fita ta bar dakin.
Mami ta jawo tiren ta hada masu shayi ta mika
masa, ungo nan dan iya. Daute ka sha kaji karfin
jikinka. Ya sanya kofi a baki ya kurba kadan. Wlh
daci mami ba xan iya sha ba. Tace don me? Ka
cigaba da sha za kaji bakin ya washe. Ga kuma
farfesun, bude bakin in xuba maka. Ya bude 'yar
kular ta debo a cokali ta mika masa, karbi ka
gani mana. Ya bude bakin ta xuba masa tace,
yauwa ko kai fah? Yanxun idan Abba ya zo
maganar auranta kankama, haka za'a ga ango a
rame? Dadi ya lullubeshi yayi wani lallausan
murmushi yace, mami na rame ko? Kai baka ji
ajikin ka ba? Bana so kayi angwanci a rame, don
haka ma za ka kama abinci ka ci. Nan da nan ta
ga ya gyara zama ya hau shan farfesu yana
kurban shayi, kinsan wani abu Mami? Sai ka fadi,
shayin nan ya daian min daci. To yi sauri ka
shannye. Ya kuraba ya sake kallonta, yanxu
Mami idan aka daura auran anan xan barta? Eh
mana, ko ba xan iya kula da ita bane? Yayi dan
murmushi, a'a mami na, amma ni na fison mu tafi
tare can, kin ga kafin mu dawo ta mance da
sakaran Yaron da ya hure mata kunne. Ko ma
muyi xaman mu can tana karatunta ina aiki na,
ko kuwa? Ta dafa kafadarsa, gaskiyya ne, ina
goyan bayanka, sai dai in ta haihu ka kawo min
maigida ko kishiya. Ya kyalkyale da dariya, kwalla
suka cika idanuwan mami ta bisi da kallo tana
gyada kai. Yayi gyatsa kafin yace, ina son twins
mami, ko? Sai dai an mai son su baya samun
su?
Da sauki ya katse ta, no duk canfi ne Mami, ni
dai ina so kuma Allah xai bani ameer da ameera.
Tayi 'yar dariya tace, duk naji, idan ma 'yan hudu
ne Allah ya kawo masu albarka, yanxun tunda ka
koshi, kaje ka yi wanka kafin dadin ka ya tashi.
Xai ji dadi idan ya ga ango shar! Yace haka ne
mamina. Ina xuwa, ya tashi da sauri ya fice.
Mami ta ta tallafe kunci ta ce nikam tawa....
Nikam tawa ta sameni, ni Ya su, Allah ka
duba mana. A bakin kofa suka hadu da iya suka
gaisa. Sannan ya wuce bangarens, ya fada bayi
ya sheko wanka, ya kimtsa jikinsa da wani
lafiyayyen farin boyel mai taushin gaske. Ya fesa
turare, ya dawo dakin Mami, ita ma wanka yi ta
sauya kaya. Ta dube shi tana fara'a tace, haba
yanxu na ga daidai. Ina ganin ma dai daga yau
aka angwancin nan. Ya xauna kusa da ita yana
dariya. Tsokanata kike sonyi Mami, me kika gani
yanxun? Sai ma ranar kenan. Ki gane Mamina,
ranar ba zaki shaida ni ba. Ta ware ido tana 'yar
dariya zai hana? Sai dai ko amarya ta kasa
shaida kai, amma ina mami zata mance da dan
tilon dan ta. Dadi ya kara lullube shi, ya rungumo
ta yana fadin Allah sarki mamina, Allah ya bar
min ke tare da Dady na. Dadin ne kansa ya
amsa, amin amin. Ya kara sa shigowa suna
masuayar fara'a. Dadyna ya tashi lfya? Na tashi
lfy Doktna. Suka gaishe shi cikin annushuwa, duk
da bai san sirrin ba, xuciyarsa tayi masa dadi.
Don haka ya xauna aka kawo masa abincinsa su
ka fara ci tare suna kara kwantar masa da
hankalin. Sosai kuwa hankalinsa ya kwanta, yana
ganin tamkar an daura auransa da mama, tunda
yana da magoya baya ta kowanne bangare
[12/01 18:24] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***9
Abba bai ga ta zama ba, 7:30 suka
kama hanyar minna shida Alh. Adamu tare da
Umma, domin ita tana bukatar ganin likita.
Saboda ha ane aka tafi da Inna saude don ta
rinka taimaka mata. Basu iske abdulkareem a
gida ba, ya riga ya fita aiki. Hankalin Aunty Rabi
ya dugunxuma nan da nan ta dauki waya ta kita
wayar ofis dince, Yaya abdul yaji kamar zai mutu,
saboda tsabar bacin rai, amma ba yadda zaiyi ya
fito saboda tsarin aiki irin na banki. Daga nana
aunty amina ta kira, itama ta shaida mata, kafin
ayi haka labari ya gauraye ko'ina. Asibiti suka
fara aje Umma tare da inna saude. Aunty Rabi
itace jagora domin asibitin da banki ke da reg da
su ne. Daga can da Abba da alh. Adamu suka
dumfari gidan marafa. Da ganin su, gaban Mami
ya fadi, fara'ar karfin hali kawai takeyi. Bayan su
natsu a falo. Abba ya tambayi marafa? Tace, ai
kuwa yayi sammako ya tafi Lafai, don shaidawa
mutannan gida maganar daurin auren, shi kuwa
ango na san ya ma kai zariya yanxun Insha
Allahu. Kasan a can yawancin abokansa suke
saboda can yayi krt. Ina fatan lfya? Ya sauke
numfashi idanuwan sa suka kara juyewa yace,
babu lfya Hjya, Ki Innalillahi Wa inna ilaihir
raji'un! Alh. Adamu ya gaya mata. Ya gayara
xama, yace hajiya wannnan al'amari babu dadin
ji, a takaice dai sakeena ta gudu tun jiya har
yanxu ba mu san inda take ba. Tsaye ta mike
dafe da kirji, ta yi me? Ta kame a hakan bata iya
kara komai ba. Abba yace, nayi iya yina Hajiya,
amma mama ta nuna min ta karfina, hanyar da
zabarwa kanta ta wuce da sani nan. Kuyi hkr
hajiya, ni ban ma san da kalmar da xan gaya
maku ba. Ta koma a hankali ta zauna cikin
kasala tace, ai shikenan, duk abinda Allah yayi
daidai ne, mu mun hkr, Allah ya musanya wa Al-
ameen da mafi alkhairi, sukayi ji. Shiru kafin
Abba yace mu na nan garin nasan har Alhji ya
dawo. Itama hajiya tana nan na kawo ta asibiti
tun jiya ciwon ta ya tashi abin sai yadda Allah
yayi. Ta maida tagumi tace, dole Umma tayi
ciwo, ubangiji Allah ya bata sauki ya kuma shirya
mana zuri'a, suka amsa amin. Suka mike sukayi
mata sallama suka tafi. Hawaye suka kubcewa
mami, hannunta a kunci tace, ta faru ta kare
kowa sai ya hkr! Tab, wannan yarinya ta daure
min kai. Allah kayiwa Al-ameen sakayya! Iya da
ladi suka jiyo hajiya na sambatu, suka fito suka
taushi xuciyarta, babu bata tym ta sa driver ya
kaita Lafai. Gado aka ba Umma, saboda yanayin
jikin nata, yana bukatar kulawar likita sosai domin
jininta ya hau, har ya haye yadda ko alama ba 'a
so. Anan su abba suka ci gaba da zama har
karfe 4. Yaya abdulkrm ya samu ya baro ofis. Kai
tsayr asibitin ya nufa a sukwane. Da ka dube shi,
kasan ransa a nbace yake, yana ganin Umma
kuma al'amarin ya kara gigita shi. Ya dubi Abba
ido jajur! Yace, yanxun wane mataki aka dauka?
Abba yace, ni na sallama mama, tunda ta iya
toazarta ni haka. Na kuma je gidan su Al-ameen,
matslar kawai ban same su bam duk sun tafi
raba goron gayyata, sai hajiya na samu shaida
mata. Alh. Adamu yace amma ni ina ganin zai fi
kyau abada cigiyar a gidajen Radio da Tv. Abba
ya amshe, da kudin wa? Saceta akayi? Ba xan
kara asara ba, yadda ta sa kafa ta bar gidana, ta
tozarta ni, ta wulaknata ni, ta nuna min ban isa
da ita ba. Wlh ni ma na hkr da ita. Ba xan yi
mata baki ba, dan ko bance wani abu, tabbas ita
da kanta ta kai kanta mkrntar koyo hankali. Za
ku ce na gaya maku. Taje duniya cem ta ishi
kowa riga da wando har da mayafin yafawa. Ya
abdulkrm ya numfasa, yace ta yiwa knata, Allah
ya shiryar da ita, yasa ta gane, suka amsa da
amin. Jimawa kadan ya ba Aunty Rabi mukullin
mota ta wuce dauko su Ameera daga sch. Kai
tsaye ta wuce da su gida. Ta kama hidimar
shirya abinci. Tana gamawa ta kwashe gaba
daya da yaran suka koma asibiti. Ta iske kofar
dkin da Umma take dankam! Da Jam'a, ashe
bayan tafiyarta kadan su ya Abdul kadir da
abdulrhmn suka iso. Can kuma sai ga dady da
mami. Al-ameen ne kadai bai dawo ba. Duk
tabisu ta gaida su. Dady kam yama rasa yadda
xai fassara al'amarin Allah ya sa bai riga ya
yayyada xancen ba ko 'ina, iyakar sa cikin
babban gidansu. Allah ya kawo Mami tayi masa
birki. Shi kansa yadda yakeji a tym din, idan xa'a
gwada jininsa dole ace ya hau, amma daya iso
ya dubi halin da iyayen Mama ke ciki sai yaga
ashe shi nafila ne, tashin hankali na inda yake.
Shi yasa ya nutsu sukayi magana ta fahimta da
abba......
Ya Dubi halin da Iyayen Mama ke ciki
sai ya ga ashe shi nafila ne, tashin hankali na
inda yake. Shi yasa ya nutsu sukayi magana ta
fahimta da Abba. Suka dauki komai suka barwa
Allah tare da rokon Abba daya amince ya bawa
mama wanda ta sake xaba. Abba bai ce komai
ba anan. Don baya jin zai iya ba Danliti 'yarsa su
hada zuri'a da mutuncin sa da komai a gari.
Yanxun tunaninsu dan gogan. Yaya al'amarain
zai
kasance? Bayan abba ya kauda masa duk wani
shakku, ya bashi tabbacin babu wani face shi, shi
ya kara karfafa masa gwiuwa har ya sami kafar
tafiya gayyato abokan taya shi murnar angwanci?
Wannan amsa sai wanda ya gani da idanuwansa.
Gab! Da kiran sallah magriba duk suka bar
asibitin, aka bar Inna saude ita kadai tare da
Umman, wacce har yanxun barci takeyi, domin
allurar da akayi mata mai karfi ce sosai, saboda
ana son ta samu hutu kwarai da gaske. Su dady
na isa gida, kamar tare suke da Al-ameen. Bai
fhimci komai a fuskokinsu ba, don basu yarda
yaga sauyi ba ya baje a kujera yace, wsh! Ai fah
an fara kenanm kinji yadda naga ji Mami? Ta
danyi murmushi tace, dan Iya kena, to abinda ya
kamata ka hanzarta yin wanke ne, don gab ake
da kiran magriba. Haka za'ayi Mami na, dadi ya
aka baro mutanan Lafai? Ina fatan zaka jaddada
musu su taso da wuri? Wannan ai dole ne, kama
san kawunka ba shi da wasa. Yana ta far'a
gaskiyya ne ni ma frnds dina ne ce masu kai
tsaye su wuce Fandagori, ai gidan Uban dawaki
ba boyayye bane, suna tambaya za'a nunna
masu. Dadi yace, kayi daidai, yanxun tashi ka
shiga wankan nnima shi xanyi aga wanda xai riga
fitowa cin abinci. Ya mike xumbur! Yana dariya ni
ne xan riga Dadi, to shikenan, mami ki na ji ko?
Idan kuma na riga shi bulala tara, tace ni kuma
xan cikashe dayar, su zama goma. Na yada. Bai
jira komai ba ya kwasa da gudu, ya shige
bangarensa. Mami ta bishi da kallo. Dadi ya sa
hannu ya cire mata tagumi yace, ke ma tashi ki
daina damuwa. Ta sauke numfashi, amma ba
tace komai ba, ta yunkura ya taimaka mata ta
tashi suka wuce. Kowa ya shige dakinsa. Al-
ameen ya fara fitowa falon, ya nufi gefen tebur
inda ya hangi ladi na jera abinci. Ya isa wajen
yana fadin, angaida Maman abinci. Tayi dan
murmushi. Tace ni ma na gaida dr. Yace na kusa
dina cin abincinki Ladi, ina ganin daga yau nai
masa bye bye. Tayi 'yar dariya, to aci gaba ne
dr.
Amma ina ganin akwai gobe kafin amaryar ta iso
ko? Ya gyada kai, yana dan murmushi, wa ya
gaya miki xan dawo ni kadai? Tana 'yar dariya ta
amsa, au can xaka zauna? Kafata, kafarta, zata
sake magana, ya dakatar da ita, shisshhh... Tayi
tsit! Tana kallon sa yana boyewa bayan kujeru.
Dadi ya fito mami na biye dashi, madalla, kinga
bulala ta hau kan danki, kira shi na tsatstsala
masa. Tace, yanxunn nan ma xaka ganshi a
sukwane, kwai ganin sa sukayi yana gyara xaman
kujera xai xauna. Gaba daya suka kwashe da
dariya. Ladi na tasya su sannan ta bar wajen.
Dady yace, gaskiyya ba haka ake yi ba, ai dai sai
ya bari mu fito tare ko mami? Dariyar Al-ameen
ta karu, yayin da Mami ke fadun, kaji wayau! Ta
xuba wa kowa abinci yaci, suka kashi suna ta
biye masa, suna labarin biki. Bukatarsu ya cika
cikinsa, kuma ya ci sosai. Bayan su kammala
Dady ne ya fara barin tebur din Al-ameen ya byi
shi xasu yi wata magana, nan da nan ya mike ya
bi bayansa. Mami ta kwala wa Ladi kira tace ta
gyara kan tebur din, ita ma kai tsaye ta wuce, ta
iske su xaune bisa kafet. Dayan gefen ta xauna,
suka sanya shi tsakiya. Dadi yayi gyarn murya
yace, wasu 'yan tamnbayoyi xan yi maka Al-
ameen, ina fatan xaka nutsu ka bani amsa
shakikiya. Da farko dai shin Al-ameen wa yake
badawa, wa yake hanawa? Yace, Allah. To idan
ya baka, sannan ya dawo ya karba, me yakamata
kayi? Ya amsa, nayi masa gdya, watakila ya
musanya min da alkhairi, ko Mami? Tace,
Gaskiyya ne! Dadi yace, Madalla, abinda nake ka
sanya wa ranka kenan. Idan har ka tabbata
tsakanin ka da Allah ka amsa min tambayoyi na.
Ka kuma san imani shine cikar dan musulmi, ko
ba haka ba? A salube yace, sosai dady. Yauwa,
to kayi hkr maganar da xan gaya maka. Nasan ka
na son sakeena, sannan kayi imani Allah ne ya
hadu ku ya sanya maka sonta, a da mu na ganin
kamar itama tana sonka, kamar yarda kake
sonta. Amma yanxun ta nuna yaudara ce kawai,
saboda haka ka hkr da ita. Kamar yadda kace
Allah xai musanya maka alkhairi. Ya dubi Mami,
ya juya ya dube shi, Dady ban fahimce ka ba, ai
sakeena na so na, xuga ce kawai kuma na
tabbata da xarar aka daura auranmu, ni masan
yadda xan da hankalinta gareni. Dady ya ka kada
kai, maganar ka dawo da hankalinta gareka duk
ya kau. Al-ameen sakeena ta gudu tun jiya babu
wanda yasan inda take saboda haka nake
rokonka arziki da ka kwantar da hankalinka, kayi
imani da furucin da kayi daxu, Allah ba xai bari
kasha wuya ba.
Ya Dubi Mami fuska kunshe da tashin
hakali yace mami ban fahimci ta gudu ba? Me
dady yake nufi? Tace iyakar kiyayya sakeena ta
nuna maka, tunda ta xabi ta dauki akwatinta ta
bar gidan iyayen ta ada ace ta aure ka. Ta xabi
ta ci mutuncin mahaifanta akan auranka.
Wulakanci ya kai makura Al-ameen, ya kamata
ka nuna mana ka haihu dan halas, kace kai ma
ka hkr da sakeena. Ya xura mata ido, du sun
kadu, mami kina nufin an fasa daura auran gobe?
Tace abinda Abbanta yayi sammakon xuwa
shaida mana kenan, ia ske ba ku nan kun riga
kun tafi gayyata, ni na bi dadynka Lafai na
dakatar da shi. Kai ma ina so ka dauki waya ka
kira abokin ka dr. Lawal ka gaya masa an fasa,
don ya gaya wa saura kar su yi wahala. Ya kada
kai yace, baxan iya ba mami, na rantse da Allah
sakeena na so na, ina xata gudu taje? Ban yarda
ba mami sace min ita kayi, don a raba mu....
Rufe min baki! Mami ta daka masa tasawa mai
karfi, daga nan ta balle da masifa, kar ka yarda
Al-ameen, amma ina son ka sani, babu maganar
auranka gobe da sakeena! Idan kuma ka sake tak
a wurin nan sai na tsinka mata mari, don ka gane
ba wasa muke yi da kai ba! Yaya ana rarrashinka
ana numaka gaskiyyar magana ka naso ka akrya
ta mu? Sakeenar banxa sakeenan wofi? Ita
kadaice mace a duniya? In sake jin xancen ta
abakin ka sai na saba maka! Ku ma ka sani,
daga daren yau ka fara shiri gobe xuwa jibi xaka
koma sch! Kaji ko baka ji ni ba? Ya aje kai kasa.
Dadi yasa hannu ya dago fuskarsa. Tuni hawaye
suka wanke masa kunci, shi ya fara fadin, me
yasa zata gudu ta barni Dady? Ko baxan hkr da
ita ba, ai bai kamata ta gudu ba, hatsari ne
babba ga diya mace, wa ya san hannu da take
yanxun? Mami tayi caraf? Ta cafke, tana hannun
wanda take so. Dama ka daina bata hawayenka
a banxa. Sannan kama kunnunwanka da kyau ka
ji ni, tun daga ranar da ka daina jin muryar
sakeena awaya ta daina sonka, ta mance da kai,
ta share ka a rayuwarta. Saboda kin da ta ke
ma. Sakeena ta diro daga mota, da abin ya zo da
karar kwana da yanxun an kusa mata sadakar
arba'in. Sakeena tayi kwana da kwanaki tana
yajin cin abinci, tayi ta suma ana mata karin
ruwa a asibiti. Kai saboda kiyayyar ka, gabada
dabi'iun sakeena suka sauya, bata gannin kowa
da daraja, nballe ta saurari fada, da iayeynta da
'yanuwanta ke mata ba dare ba rana. A karshe
sakeena ta aikata abinda yafi komi muni akan
diya mace. Duk saboda bata sonka, ashe ya
kamata ka hankalta kasan halin da kake ciki, don
kai ba yaro bane, kuma ba alfahari ba, ilimi
muhammadiya da boko sai dai a yiwa wani gori
ba dai kai ba Al-ameen, duk kuma wanda yayi
imani da kaddara, baya tabewa Al-ameen. Ka
maida al-amarin ka wajen Allah shi xai maka
magani. Ya dube su daidai tamkar karamin yaro,
murya na rawa yace, gaskiyya ne Mami, duk
abinda ki ka fadi na yarda, kuma na hkr da
sakeena, sai dai son ta ba xan iya cire shi cikin
raina ba, saboda ba ni na aje shi ba, kuyi hkr, ku
yafe ni, idan furuncin danayi ya muku xafi,
sannan ina rokon ku don Allah da son Manxonsa,
kar ku kullaci sakeena cikin xukatan ku akan
wannan maganar. Wlh har yanxu ina ji ajikna
sakeenna tawace. Dady ya rungumo kafadunsa
yace, shikenan,ya Isa, munji rokonka mun amsa.
Zamu cigaba da taya ka addu'. Yanxun abinda
nake sonka da shi shine, ka kira Dr. Lawal ka
gaya masa, don su sani. Sai dai in baka lambobin
ka kira shi dady, bakina ba xai iya furta
mummunan labarin nan ba. Ya mike ya jao
durowar dadi ya dauki biro da paper ya rubuta ya
bashi, ya mike xai fice, ya kusan kaiwa kofa
mamy ta kira shi, ya juyo tace kayi nafilfilu cikn
dare. Allah zai saurareka, ya nisa kafin yace
xanyi mami. Ya sa kai ya fice. Mami ta dubi
dady ta hadiye hawayenta, tace gobe in Allah ya
kaimu xan koma Lafai wajen baba liman in samo
masa ruwan addu'a ya sha ya sami sanyi cikin
ransa. Yace hakan ma yayi, Allah ya sa mu
dace. Tace amin. Ta jawo wa dady kan waya ya
nemi Dr. Lawal, ya sanar masa. Yace an fasa?
Subhanallahi? Wannan abu baiyi dadi ba. Don
girman Allah dady a samu a daidaita, wlh Al-
ameen yana son yarinyar nan ba kadan ba. Ya ce
ba sai ka rantse ba Lawal, ni kaina nasan hakan,
amma fadan da ya fi karfinka dole ka maida shi
wasa. Mu nan muna ta addu'a Allah ya zaba
mafi alkhairi. Ya numfasa, yace amin. Ina Dr.
Yake? Ai sai da ka neme shi xuwa gobe, yanxun
kam babu sukuni yana dakinsa. Yayi dan jim,
kafin yace Allah shi kyauta, amma ayi kokari Dadi
idan xai yuwu a sasanta. Ba komai mun gode a
gaida Iyali. Zasuji, ya aje wayar tare da tsananin
mamakin wannan abu? Me ya faru haka da xafi?
Haka ya kwana da tambayar kansa, don babu
alamar wata mishkila a tattare da soyayyar
abokinsa da sakeena, ko daya zo sanar da
xancen auran ma babu alamat akwai matsala
babba. Labarin barci dai babu shi a wajen Al-
ameen kuma xuciyarsa bata daina karyata masa
xancan ba. Ko alama ta ki amsar sakon, saboda
tsabar shakkun da yake ciki, wai sakeena taci
amanarsa? Har 8am yana kan sallaya, ba don wai
yana sallah ba, a'a kasala ce ta hana masa tashi.
Mami tayi sallama ta shigo da tiran kayan karin
safe. Ya xubo mata ido.
Mami tayi sallama ta shigo da tiran
abinci, ya xubo mata ido, ta aje a agbnsa, ta
xauna gefe, sannan yace, ina kwana mami? Lfya
lau, ina fatan ba ka tsananta wa kan tunani ba?
Ya kada kai, ya xanyi mami? Kin san ba yin kaina
bane? Ta dafa shi a sanyaye, kllm ina kara gaya
maka Al-ameen, kai kadai ne garemu, kuma ka
zama tamkar dubu, ba gare mu kadai ba,
gabadaya al'umma za su so rayuwarka ta daure
cikin fciki da walwala, saboda muhimmancinta,
ina so ka san wani abu yau. Wlh na yi maka
rantsuwar da ba kaffara da rayuwarka ta
salwanta, gara ni in mutu, don na..... Ya rufe
bakinta, a hankali, idanuwansa taf, da hawaye
yace, kiyi shiru mamina! Da ni dake zamu rayu da
yardar Allah cikin farinciki da kwanciyar hankali.
Har ga Allah na hkra da sakeena mami, kawai
ciwon fitar son ta ke azabtar da ni. Ka kwantar
da hankalinki mamina, a hankali zaki gan ni
yadda kike so. Tayi dan murmushi tace, Allah
yayi ma albarka! Da sauri ya kwanta a kafadarta
yana fadin amin mamina. Zauna da kyau na hada
maka brkfst. Kaga masa na sa iya ta shirya
maka da sassafe, na san kana so kuma kana
kewarta, don ba'a samu a Rasha. Ya bita da kallo
dauke da tausayi. Yace nagode mamina, amma
tare xamu ci ko? Ta jawo fileta tana fadi ah! Me
zai hana? Bari ka gani. Ta loda waina a plate
tana xuba miya ya ware ido, yace mami kin cika
abincin nan! Ita ma ta ware idon tace injiwa? Ni
da kaine fa? Sa hannu ka gani ko asa man
shanu? Ya kada kai, a'a kinsa banso kayan karni.
Ka bar dadi yaro. Yayi 'yar dariya yace Allah ko?
Ta tura masa a baki tace, haba ai ba sai na fadi
ba. Dady yai sallama dakin ya karaso da sauri
yana cewa iye! Masa kuke ci kuka nuna min 'yan
ubanci? Gaskiya ba ha akeyi ba, ai sai ku kira ni
ko? Ya tambaya yana kallon al-ameen cikin ido.
Ya gayara masa wwuri, yace laifin mami ne,
xauna abinka Dadyna. Ya xauna yasa hannu ciki,
yace ai mami akwai rowa, Allah dai ya tsaga da
rabona. Suna dariya ta bashi amsa, ka san kuwa
da na kawai, na aka yi ma. Kaji ko? Tafi son ka
akaina. Yayi wuf ya rike hannu da yake kokarin
kai loma yace, ba xaka ci ba sai ka fadi! Gaya
min, mami ta hau dariya shima ita yake yi. Dady
na ga dai da ta rikice kanka. Tace babu wani sai
kai, sannan aka sameni, ko ba haka bane mami?
Tace ni xaka tambaya? Dady ya karbe yanki
wainar daga hannunsa ya tura masa baki, yace
cinye dana, ka bani amsa daidai. Bai gama
cinyewa ba ya dauko cinyar kaza ya tura msa, ka
ra da wannan kayi brush! Duk suka sa dariya,
ganin al-ameen na neman kwarewa, kan kace
kwabo sun yaudari Al-ameen ya cinye wainar da
mami ta zo da ita, domin dai shi suka yi ta
turawa da wasa da dariya ya take cikinsa. Bayan
sun kare, mami ta dube shi tace yanxun ka tashi
ka shiga wanka ka kimtsa, muje asibiti ka gaida
Umma.... Umma? Me ya sameta? Tashin hankali
ya sa ta sami hawan jini tuntuni, maganar jiya
kuma ta kara birkita ta jininta yayi mugun hawa.
Tana nan asibitin sun bata gado. Jiyan abba ya
taho da ita. Ya marairaice yace, Umma na asibiti
tun jiya baku gaya min ba? Ban dadin hakan ba,
dady yace kayi hrk, ganin kai ma baka da sukuni
ya sa muka kyaleka, kaji da guda 1. Ya mike
yace ba sai nayi wanka ba, yanxun xan tafi, idan
na dawo nayi, bai saurara ba ya wuce ya jawo
dirowa ya dauko key ya fice. Mami ta biyo shi
tace Al-ameen, ya tsaya cak! yana dubanta, ta
matsi sosai ta dafa shi, ka tafi a hankali, idan
kaje kace ina gaishe ta, ni ma xan biyo in na
dawo daga Lafai, ya dan lumshi ido, ya bude
yace xan kula mami, amma me xaki je yi Lafai?
Tace uzurina xai kaini. Allah ya kiyaye hanya, ta
amsa amin. Ya daga kai dubi dady dake tsaye
yace, sai na dawo dady, to ina jin ma xan
sameka asibitin. Yace shikenan sai kazo. Ya juya
yayi waje, su iya na kokarin fitowa su gaisa.
Amma ina saurin da yakeyi, ya hana su su same
shi falon, tuni ya kai ma'ajiyar motocin, ya murza
ya bar gidan. Umma na xaune an jera mata filo,
ruwan lipton kawai ta iya kurba, ya xuna cikinta.
Likitan ne yace ta dan jingina kadan ta huta. Duk
'ya'yan sun kewayeta, abba na xaune gabanta
bisa kujera. Gaba daya tausar xuciyarta suke yi
don ta fidda abin a aranta. Sallamar al-ameen
cikin dakin ita ta dauki hankalin kowa, suka amsa
kona masa duban tausayi, ganin yadda ya xabge
kamar mai ciwo, wai don ma su mami na yin iya
kokarinsa akansa. Ya bisu daidai sukayi
musabaha, sannan ya tsugguna gaban Abba suka
gaisa. Tuni ganinsa ya sa hawayen Umma suka
tsinke, yayi shiru a tsugunne. Abba ya dafa shi,
yace sai ka dawo ka sami labari maras dadi? To
ina so ka kwantar da hankalinka kayi imani da
kaddara, ka sani yau da ace mama na da 'yar
uwa xan baka ita, don in nuna maka iya kaunar
da muke maka. Mama ta zabi ta wulakanta mu,
shi yasa na ke son kowa ya cireta a ransa, mu
manta da ita mu kyaleta duniya ta hora ta. Kayi
hkr kaji? Ya goge kwalla yace naji abba, kuma
nagode akan iya kokarin da kukayi min, amma
abba ina rokon ka, don girman Allah ku ya fe
mata, sannan ku sanya mata albarka, a auran da
xatayi. Duk sukayi shiru, kowa ya xuba masa ido.
Tausayin sa na ratsa su, umma ta goge kwalla.
Tace Mama ba abar tausayi bace Al-
ameen, don haka ka daina rokon ayi mata afuwa
laifin data aikata. Ya kata matsowa gaban gadon
yace, ba haka bane Umma, ki san sharrin
shaidan, sannan xuciya bata da kashi, ba 'a son
ran mama zata aikiata wannan abin ba, xuciya ce
ta saka mata, na tabbata duk ranar da ta nutsu
tayi tunani xata gane lallai bata kyauta ba. Don
Allah Umma ko ina nan ko ba nan, idan Mama ta
dawo ku amshe ta hannu 2, ku samata albarka.
Insha Allahu shaidanin daya rinjaye xuciyarta, xai
kyaleta, ta dawo diya ta gari kamar yadda take
da. Abba ya kara dafa shi, yace idonka ya riga ya
rufe a son mama, shi ya sa baka kallon girman
laifin da ta aikata. Ya juya ya dube shi, ba haka
bane Abba nasan ina son mama kuma har na
mutu ba xan daina son ta ba, amma ku yafe
mata, don rayuwar ta, tayi kyau nan gaba, ba
farin cikin mu bane ace mama ta lalace tabi
duniya, tunda gaba dayan mu nan, muna son ta.
Kun yafe mata ko Umma? Tace kayi hkr Al-
ameen ba xan iya cewa komai ba tukunna, ya
abdulqadeer yace, ko mu bamu goyi bayan su
Umma suyi afuwa gareta ba, har sai ta sauya
zabin da tayi da. Tunda tace ba kai ba, to ka
kawo wani dan mutunci tamkar kai, amma ba
Dan liti ba. Wanna itace shawarar da muka
yanke. Yana rufe baki dadi ya turo kofar ya shigo
tare da gaishe-gaishe. Ya dubi al-ameen yace, dr
na jiranka. Da mamai ya dube shi, dr. Lawal?
Yaushe ya zo? Bai dade ba, muna shirin fitowa,
sai gashi shine nace ya xauna xan biyo na gaya
maka. Ya mike yayi sallama da su ya bar
asibitin. Bai sami mami ba, don itama driver ya
wuce da ita lfya. Dr. Lawal na babban falon
gidansu, ladi sun adana shi da kayan kusa da
baka, amma da ka dube shu kasan baya cikin
sukuni. Yana shigowa ya mike da sauri ya tarbe
shi suka kama juna. Dr. Lafai! Yace banyi xanton
xaka xo ba. Dole na xo, wannnan mummanan
labari ya hanani barci jiya. Yayi dan yake, kai dai
bari, mu xauna aboki na. Suka zauna kujera daya,
dr lawal yace, me yayi zafi likita? Idanuwansa
suka kada yace, bansan me ke faruwa ba dr
sama da sati 4 ina can na daina jin wayar
sakeena, aka ce min bata da lfya ne, dalilin da
yasa na dawo kenan don hankalina yaki kwanciya
ita kawai nake son gani. Ina xuwa na iske labari
ya sha bambam, wai sakeena ta sami wani ya
hure mata kunne, har ta mance da manyan
alkawuran da ta daukat min. Kowa yayi iya
kokarinsa wajen nuna mata gaskiyya, amma sam
tace ba san wannan ba. Abban ta kuwa ya sha
alwashin ni da ta fara kawowa akayi mana baiko,
ya sani ba xai daura mata aure da kowa ba, face
ni don haka yace ba xan koma sai an daura
auran. So da kaunar da nakewa sakeena yasa
bana tunanin komai Illa xumudin a daura mana
auran, shi yasa koda naje jiya bana nuna maka
komai ba.a xato na bai kamata in tona kwanne
sirri na sakeena ba, do kar a zage ta matsayin
maci amana, ina ganin kamar idan muka kebe
matsayin miji da mata, xan iya rinjayar ta. Son da
take take min ya sake dawowa xuciyarta. Ashe
duk abin da nake zato ya wuce nan dr.lawal
kawai na dawo jiyan su dady ke gaya min
sakeena ta gudu cikin dare ba a san inda take
ba. Al-ameen ya jingina da kujera ya runtse ido
sai hawaye shar... Na malala, hankalin dr. Lawal
ya kara tashim ya xura masa ido jim sannan ya
sauke numfashi ya dafa shi, yace, kana cikin
tashin hankali aboki na amma Allah yace duk
inda tsanani yakem to tabbas da akwai sauki. Pls
ka zama jarumi a cikin jarabawar nan, ka bari hkr
ya xama sanadin samun saukin tashin hankalin
nan. Ya bude ido taf da kwalla, yace inason
sakeena Dr. Kai kasan hakan, yace kwarai da na
sani kuma xato na itama tana tsananin sonka. Ya
matso shi sosai yace haka ne, wlh sakeena tana
sona, to me yasa ta kini tym 1? Yace mata
kenan Dr. Lafai. Balle sakeenna na da kyau da
xata iya wasa da hankalin kowane da namiji.
Watakila kuma wancan yafi ka duk abubuwan da
take bukta. Dan wani minister ne a abja? Yace
ban nemi sani ba, a yau ne nake jin sunansa
bakin yaanta wai shi Danliti, danliti? Daga jin
sunan kasan ba wani bane. Da sauri ya amsa ai
kuwa wani ne.... (Hahaha Allah sarki lazy Dr.)
tunda ya sace min sakeena. Ko da kuwa kwara
masai yake yi. Inda ace xan gan shi xan iya
durkuwa gwiuwa 2 in roke shi, ya bar min
sakeena ta. Wlh itace rayuwata dr. Ya kada kai
yace, ka daina fadar haka Dr. Lafao kar fa ka
mance wani hani ga Allah baiwa ne, xa iya
kasancewa sakeena kyan dan miciji gareta.... Ya
dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu....
Yace gaya min kowace kalma dr. Amma kar ka
aibata min sakeena, ba xan taba ganin farinka ba.
Ya xura masa ido, kunshe da mamaki, kafin yace,
ba nufi nake nan ba aboki na, ina so ka gane
cewar bakomai da kake bane yake kasancewa
alkhairi a gareka, shi ya sa kullum ake son bawa
ya roki alkhairi wajen Allah. Yace sakeen alkhairi
ce gareni, tuni mafarkai na suke nuna min hakan,
har xuwa yanxun kuma jiki na yana bani sakeena
tawa ce, mishkila aka samu wani wurin, bana so
musu da su Dady ne kawai, shi ya sa nake nuna
musu na hkr da ita. Yace to idan baka hkr ba,
yaya xakayi yi? Tunda batayi da kai? Babu
abinda
[12/01 18:24] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***10
Amma nan da iya shkrun da xanyia
duniya ba xan daina son ta ba har na koma
Ubangiji. Ya xura masa ido, yace Al-ameen kar
ka manta akwai gagaruminn aiki gabanka wanda
kowa ya xura ido don ganin rawar da xaka taka,
kasancewar kai kadai ake tunanin xaka iya taka
ta kuma mutanenan arewa suna jiran daya
tamakar dubu ya dawo masu da abin alafahrin a
duniya baki daya. Ina ka sami nutsiwa ka
fuskanci abinda ke gabanka ka tare da jadda
imani a cikin ranka, lallai Allah xai iya baka wata.
Ina fatan xuwa na ba xai xama abnxa ba ba,
kuma addu'ar duk masoyanka a zariya ba zata
fadi kasa banxa ba. Kowa yace Allah ya
musanya maka da lakhairi, na tabbata Allah xai
duba ya kawo sauyi na fadi daidai? Ya numfasa
yace ka fadi daidai abokina na, na gode ma kowa
bisa addu'ar da suka yi min. Xan koma rasha da
yardar Allah cikin yardarsa xan dage na fidda
kowa kunya. Sai dai abinda nake so ka sani har
in mutu ina son sakeena. Yace tuni na sani,
sannan ina da ilimin xuciya daya gareka, duk
abinda Allah ya xuba cikin ta, babu me iya dauke
shi. Ya koma ya jingina da kujrea, rungume da
hannayensa, ya dan numfasa ya kada kai, dr.
Lawal ya bubbuga kafadarsa ya sake fadin, ka
manta kawai abokina, ya wuce, ya bishi da kallo
kawai baice komai ba su dade tare. Dr. Lawal na
kara kwantar masa da hanakili tare da nuna
masa mahimmancinsa ga al-aumma. Bayan
azahar suke asibiti ya gaida Umma, daga can ya
wuce zariya, shi kuwa Al-ameen gida ya dawo,
don shima ba ya son yana ganin Umma kwance
tausayinta yana kara karya masa xuciya. Ya rinka
jin kamar su abba ba xa su yafe wa sakeena ba.
Wannan shine babban tashin hankalin sa. La'asar
ta kawo jiki yana xaune shi kadai bisa gadonsa,
tym-tym ya kan dauki hoton da ke bisa kirjinsa
ya duba. Hotonsu ne shi da mama wanda sukayi
a dakin Mami, xuwan ta farko gidan. Karo
barkatai kenan daya daga hoton ya xura masa
ido tsawon lokaci, sannan ya mike ya sake kife
shi. Ya laluba aljihunsa ya dauko xoben da Mama
da dawo masa dashi, ya xare na hannunsa ya
hada su waje daya, ya xura masa ido. Sannan
ahankali yake wasa da su, ya rike kowanne yana
hada su karo. Cikin idanuwansa yake ganin ita ke
rike da wanda ya bata, suke karawa juna.
Wannan karon da karfinsa ya kara mata, na
hannunta ya karye nan da nan ta shagwabe,
gaskiya ba hake ake yi ba! Ba haka ake ba Dr.
Al-
ameen! Al-ameen tsananin kiran ya dawo da shi
tunaninsa duniya. A firgice ya dubi Mami dake
gabansa xaune. Ba xai iya cewa ga tym da ta
shigo ba, don haka yake mata kallon mamaki,
haka itama ta xura masa ido mai dauke da
questions. Mami! Yaushe kika dawo? Ta sauke
numfashi ta kada kai, kafin tace, tsoron na Allah
tsorona kar ka xaunce al-ameen ka dawo cikin
hankalinka mana! Yai sauri ya runtse ido yana
fadin Hasbunnallu wa ni Imal wakil, Allahuma
ajirni fi musibati wa akhlifini khairan minha. Ya
bnude ido jajur ya dubeta, kiyi hrk mami....
Takatshe shi ba xan bari rayuwar ka ta salwanta
ba Al-ameen sai inda karfi na ya kare, Allah na
gani yarinyar nan ta xalunce ni. Kafin yace wani
abu, ta mike da sauri tai waje, ya bita yana kira,
ba su hadu ba sai a dakinta... Mami.... Ta daga
masa hannu. Ban son jin komai, ta mika masa
wani ruwa da ke hannunta tace shnaye shi ka
bani kofi. Yace na menen? Ban son tambaya ni
na umarce ka kashanye, ka bani kofin. Ya daga
kofin da sunan Allah, ya kafa aabki ya
kwankwade. Ta karbi kofin ta aje gefe. Ya sake
tambaya mami ruwan me nasha? Tace baba
liman ya bani taimako na kawo maka, anjima
zaka sake sha, gobe ka kara da safe da yamma.
Jibi in Allah ya kaimu lfya za ka koma sch, domin
fitar da dadin ka yayi bookin ya je maka, ina
fatan kajini? Jikinsa yai sanyi, ya kamo
hannnayenta 2 ya ja suka xauna bisa kujera yace
Allah sarki mamina. Allah bar min ke. Nagode da
karfafa min gwiuwar da kukeyi. Idanuwanta taf
da hawaye tace, hankalina bai taba tashi ba irin
na yau. Ban taba jin faduwar gaba ba irin ta
yaukai da zobuna kake hira kana dariya, Al-
ameen ban same xai faru ba nan gaba.
Kafadunta 2 ya dafa yace sai alkhairi mamina,
kawai xancen xuci ne ya fito fili mami... Tace
daga haka sai tabin hakali al-ameen , yayi dan
murmushi yace Allah ba xai sa ba mamina, ya
san ni kadai ya baki, kuma shi mai tsananin
tausayi ne. Allah sa ruwan da kika bani ba wanda
xai cire min son sakeena bane. Ta xura masa ido
cikin xafi tace, shine Al-ameen Insha Allahu
sakeena ba xata zama ajalinka ba, ya numfasa
yana murmushi da bai kai ciki ba mami kenan,
wa ya gaya miki sakeena xata kashe miki tilon
danki? Kuma wa ya gaya miki danki xai ji dadin
rayuwa ba tare da soayyar sakeena ciknin
xuciyarsa ba? Duka 2 tafiya suke kafada da
kafada mami, Allah yayi hukuncinsa, don haka
ban ji Baba liman xai iya cirewa. Bayin kaina
bane, kiyi hkr mami. Tayi masa xuru duk jikinta
ya mutu a hankali ta ce ko bai fita ba xaka ji
sanyi cikin ranka. Tunaninn ka xai daidaitu da
aikin kwakwalwar ka ta yadda xaka yi mu'amula
kamar sauran mutane. Wannan shine farinciknm.
Yace, Allah ya taimake ku akan burin ku. Nima
ya taimakeni akan nawa.....
Tace xamu ci gaba dayi da fada idan
har kana gaya min irin wadannan kalaman. Ya
kada kai ba xa muyi ba mami. To ka daina. Ya
lumshe ido, ya bude yace na daina, Allah yayi
maka albarka. Ya dora kansa kafadarta ya amsa
da amin. Ta ciga da yi ma nasiha yana
sauraronta sai dai can kasar xuciyarsa cike yake
da xulumi, Allah ya sa ruwan da mami ta ba shi
ya sha ba wanda xai sa ya mance da sakeena
bane. Da wannan xulumin ya tafi yin sallah
la'asar hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya tura
yatsansa ya arce makogwaronsa ya kirkiro wa
kansa aman dole. Bayan sallar magriba dady ya
shigo ya tsare shi yaci abinci. Sannan mami ta
debo ruwan addu'arta ta mika masa, ya shanye.
Allah Allah yake yi tashi ya koma dakinsa ya
jawo aman, amma kmar dady ya sano ya ki
barinsa tashi. Yayi ta jansa da hirarrakin duniya,
wai don ya rage tunanu. Kafin ya bar wajen ya
kwashe awoyi sama da 2 takaice ya ishe shi, don
ya tabbata ruwn nan ya gama bin jininsa.
Wannan karon bai nemi yin aman ba, gado ya
fada ya fara tunanin iska, har bacci ya samuyi,
da alama an fara samun nasara. Shi kansa yayi
mamakin irin barcin da yayi bugu da kari ya rage
jin xugin xuciyarsa ke y, hankali kwance suka yi
karin safe. Mami ta kara bulbuo ruwan addu'ar
ta a gora, ta mika masa. Ya kwankwada duk ba a
son ransa yake sha ba, a yau takardun
komawarsa Rasha xasu kammalu, haka dady ya
gaya masa. Saboda haka ya umarce shi daya
kasance cikin shiri koda yaushe xa'a iya basu
tym din tashi. Jikinsa babu kasala ya koma
bangarensa ya jwo jakar kayansa yayi ta lda
kaya har da wadanda ya dade bai anfani da su
ba. Ya wuce dirowar madubinsa ya jawo ya
kashe takardun cikin kaf, dinsu ya dauko xai
xuba jaka, wata ambula ta fado duk hotuna ciki
suka watse bisa kafet daidadi shigowar mami
dakin. Ya aje takardun gefen gadon yana amsa
sallamarta, sannan ya tsugunna ya kwashe
hotunan, akasarinsa duk na mama ne, sai kalilan
wanda suke tare. Tayi tsye tana kallon katuwar
jakar da yake lodawa kaya, ya akayi mami na?
Tace kamar bada jakar nan ka xo ba? Ya mike
dauke da hotunan a hannunsa yana amsawa, xan
kara wasu kayan ne, shi yasa na sauya jaka. Ya
matsya xai cusa hotunan, tayi wuf ta karbe ina
xaka da dasu? Ai wadannan hotunan wuta ya
kamata ka cinna musu. Wuta mami? Me ya san
xan sa wa sakeena wuta? Saboda nan gaba xata
xama matar wani, ka ga haramun ne gareka
kallon hotonta. Ina fatan ka gamsu? Yayi shiru
na 'yan dakikai kafin ya numfsa, ya dubeta
idanuwan har sun kada, yace kin fadi gaskiyya
mami, amma baxan iya cinna wa jikin sakeena
wuta ba, sai dai ina rokonki dan girman Allah ki
adana min su har xuwa tym din da xata halasta
gareni. Tayi masa xuru tana shakku cikin ranta,
addu'ar Baba liman batayi tasiri bane ko kuwa
bata fara aiki bane tkunna? Ta kada kai ta dubi
hotunan ta sake dubansa, amma shi ya riga ta
magana. Mami pls ki ajeye min su inda ba xa su
salwanta ba. Ta sauke numfashi, xan boye maka
sun tunda kafi son hakan, gwaggo ce ta xo tana
daki na. Ya ware ido sosai. Gwaggo? Da
sasssafen nan? Dole tayo sammako, hankalinta a
tashe yake, ka fito tana daki.Tayi waje da
ambulan din a hannunta, shima ya biyo bayanta.
Tana xaune a shimfida bisa kafet ya xube
gabannta dauke da murmushi, uwargida ran fida,
kuma sai ki bugo min sammako kamar ban aika
da cefane ba? Duban tausayi take masa, ta dafa
kafadarsa tace dole nai sammako, in xo in ga
halin da kake ciki. Ina fatan xaka sanya dangana
cikin ranka. Ka mance da yarinyar nan, domin
dai.... Ya katse ta, ya kamata mu gaisa gwaggo
kinxo lfya? Ya tsufa? Tace tsufa na nan kuma
lfya lau na xo. Amma me yasa ka katse min
magana? Babu komai gani nayi bamu ko gaisa
ba, alhalin ya dace na fara gaisheki. Haka ne to
ina fatan duk shawarwarin da kowa ke ba, kana ji
ka kuma dauka? Ka manta sakeena... Da sauri ya
katse gwaggo tuni na hkr da ita, hasalima yau ko
geb xan koma sch. Ban xan dalilin katseni ba Al-
ameen akwai abinda baka so na fadi. Mami ta
amshe, sosai kuwa kina so ya mance da
sakeena, kunnunwansa ba sa son ji, shi yasa
yake katseki. Tace oho, to wahalar banxa kakeyi,
domin dai labari ya tabbata tare da shashashan
saurayinta suka tafi, kaga kuwa sai abinda Allah
yayi. Gara ka kama kanka ka san inda ke maka
ciwo. 'yan mata dai ga su nan birjik duk wacce
kace kule xata ce cas. Rayuwa kawai sakeena ta
xaba, don na tabbata yaron nan baxai aureta ba,
nawa ya lalata, ya watsar tana gani kuma ta
bishi, inm banda ita ma, rayuwarka ta sha
banban da wacce sakeena ta dauka, kaga kuwa
tafiyarka ba xata xama daidai da tata ba. Ka
fahimce ni? Wasu kwalla masu xafi suka sauka
bisa kuncinsa, hakan ya jawo mamaki ga gwaggo
da Mami suka xuba masa ido baki sake. Xugum
sukayi, daga bisani mami ta numfasa tace ikon
Allah! Gwaggo ta xare tagumi tace, akwai sauran
aiki, kuma ina mai tabbatar maka , bata tym
dinka kakeyi. Ya jawo hankaci ya share fuska,
yace, ko kadan gwaggo, labarin ki tsananin
tausayin sakeena ya cusa min, sakeena ba haka
take ba, nayi rayuwa da ita sosai na fahimci
halayenta, xan iya cewa nafi kowa saninta, na
fahimci halinta.
,Zan iya cewa nafi kowa sanin ta hakika ya
zalunce ta tunda ya sauyamata rayuwa ya bata
tarbiyarta ya gurbata mu'amalarta da iyayenta da
yan uwanta ya datse tasananin soyayyar dake
tsakaninmu ka ALLAH bazai kyale shi ba ta ko
wace hanya ya bi yayi nasa a kanta sai ya ga
sakayya,"ya mike da sauri zai bar dakin gwaggo
ta kwala masa kira ya tsaya bakin kofa yana
goge kwalla tace dawo ka zauna ai ban gama
magana da kai ba yana daga tsaye gaskiya
gwaggo kunnuwa na ba za Su iya sauraron irin
wadannan labarurrukan
akan sakeena ba,tausayin ta bazai barni sukuni
ba gara a bar ni cikin bakin duhu ina laluben inda
ALLAH zai sake hada fuskokin mu har ta zama
mata a gare ni," jikin gwaggo yayi mugun sanyi
tace dawo zauna nan ya dawo ya zauna gefenta
ya hade kai da guiwa ta dafa kansa tace idan
nayi kuskure kayi min afuwa amma ba laifi na
bane ka sani ko wace uwa tana kishin danta
kuma abinda ya faru da kai dole mai kaunarka
yayi bakin ciki balle mu da muka fi kowa kusa da
kai, na san kana son sakeena sai dai ba na son
idon ka ya rufe ka kasa ganin aika aikar da ta
aikata a garemu, ya cire kai ya dube ta ni kuwa
hakan na fi so gwaggo domin na yi imanin ba yin
kanta bane sace min ita akayi hure mata kunne
akayi da kalmomin shaidan addu'a zatayi
maganin abin, da zaki taimake ni da ita ma zan fi
farin ciki akan wadannan labaran da ki ke son
bani," gwaggo " mami ta karbe za a yi maka in
dai addu'a ce ka samu tashi kaje kaci gaba da
shirinka bai tofa komai ba ya yunkura ya bar
dakin,kamar daman can ya kosa ya
barshi,"gwaggo ta dubi mami hankali tashe tace
bai kamata ku kyale yaron nan ya koma haka
kawai ba tare da wani taimako ba tace tun jiya
na je lafai na samo masa wajan baba liman wai
nan yama sha ruwan addu'ar ke nan tafdijan ki
na kallo fa ko laifinta baya son a fadi wannan so
yayi yawa gara ma da auran bai yuwu ba da
muna kallo zai zama mijin ta ce,abin haushi
nama na jan kare, mami tace me ki ka gani
gwaggo?ALLAH dai ya zaba alkairi abin cewa ke
nan anan gwaggo ta wuni,
Shi kuwa Alameen a dakinsa ya wuni don
baya son ana daga masa hankali da labaran
sakkena kazantar da baka gani ba tsafta ce,kai a
yadda yake jin mama cikin ransa koda ya ga
kazantar da idanuwansa zuciyarsa ba za ta
amince masa ba bai fito ba sai da gwaggo zata
koma suka yi sallama daga nan dakin iya ya
shige ya kudundune kamar maraya sama da awa
guda tana tausar zuciyar sa da kalamai masu
dadi,ya kuwa ji dadin cikin ransa saboda kalaman
iya sunfi rinjaye ga. Bashi tabbacin idan sakeena
matarsa ce duk rintsi duk wuya sai ya aure ta
karfe shidda dai dai dady ya dawo masa da
takardun tafiyarsa sun kammalu kuma gobe da
yardar ALLAH sha biyu ranan zasu tashi don
haka yana gama cin abincin dare mami ta ba shi
ruwan addu'a ya kwankwada kai tsaye asibiti ya
wuce don yin sallama dasu abba,kowa yayi masa
nasiha kuma sun jaddada masa ya maida
hankalinsa akan anibda ya kaishi kar ya tsaya
bata lokacinsa. Akan tunanin iska wanda ba zai
fisheshi ba,sai dai abin yana basu mamaki yadda
lafuzzan alameen ke nuni da tsantsan son mama
a zuciyarsa. Wanda ko alama na bayyana har
yanzu bai yarda sakeena. Taci amanarsa ba,
akwai mishkila wani wuri shiyasa yake ta
rokansu dasu taya shi addu'a ALLAH yasa wata
rana sakeena ra zama mata a gare shi,gaba daya
ya kwabe masu guiwa har suka yi masa
alkawarin yin yafiya a gareta idan har ta dawo ta
nemi gafara,kowa ya dubi alameen sai ya ji tarin
kwalla cikin iadanuwansa lokacin da yake barin
asibitin yana gugar fuska shi kansa yaya soja a
yau zuciyarsa ta karaya,tausayi ya kwarara cikin
jikinsa ya nemi haddasa masa abin mamaki
domin kwalla ya ji tam da idanuwansa suna
zubowa da saurinsa ya bar wajan bai gama ganin
wucewar alameen ba
[12/01 18:24] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2*** 11
Karfe 8am suka dauki hanyar abj tare
da mami. Hankalinsu bai gama tashi ba, sai da
tym ya cika aka kira passengers. Al-ameen ya
rungume su, idanuwan sa cike da hawaye,
bakinsa na son yin magana amma kasa, haka su
ma Allah ya doro masu nauyin baki, kallon juna
sukeyi. Da sauri ya juya ya wuce, yana goge
fuska da hankici. Shi yasa suke tafe cikin mota
kowa shiru. Mami dauke da taguminta. Tunaninta
yay rayuwar dan nata xata kasance a kasar da
babu wanda ya damu da wani balle ya sami wata
kulawa ta musamman. Dadi yayi tana share
hawaye ya dan dube ta, kada kai. Amma bai iya
cewa komai ba don ya san mami tana mukatar
zubda hawaye ko ta ji dadi cikin ranta, amma da
ya ga abin yaki karewa, dole ya tanka, ina ganin
bai dace ki ci gaba da bata ranki ba, wanda kika
yi ai ya isa, ko sai ya jefa ki wani hali ni in rasa
da wanda xanji? Ta goge kwalla, tace Alh. Ba
haka bane ganin Al-ameen na da abin fadi, amma
yakasa ya wuce da damuwar cikin ransa? Wa zai
gaya mawa a can? Kai tsaye ya bata amsa, Allah
zai gaya mawa, kin kuwa san ya fini, ya fiki, yafi
duk wanda kike tunani zai ba Al-ameen wanni
taimako, saboda haka ki bar shi da buwayin sarki,
shine xai masa dukkan gudunmawa. Ta zare
tagumi ta numfasa, haka ne, Allah ya taimake
shi, to amin kuma na tabbatar zai taimakeni shin,
tunda kika furta, addu'ar uwar yankan wuka ne,
don haka ki kwantar da hankalinki. Ina fatan kin
ji ni. Tace, naji alh. Allah ya shige mana gaba,
yace amin. Daga nan Mami ta saki jikinta suka ci
gaba da hira. Suna shigowa gari, asibiti suka
wuce gano jikin Umma. Alhmdlh, Umma na
samun sauki, watakila ma xuwa gobe a
sallameta. Ba su iske yaya abdulkadeer da Abdul-
rahman ba, duk sun koma a wannan yammacin.
Sun dan jima asibitin, sannan suka dawo gida.
Mami ta dukufa rokon Allah cikin sallolinta, Allah
ya sanyaya wa Al-ameen xuciyarsa, ya cire masa
wannan makahon so sa ya ke wa Mama. Haka ta
kwana tunaninsa har barci tayi mafarkinsa xaune
yana wasa da xobunan guda 2. Shiyasa da ta
fara tayi ta da na sanin da ta raba shi da
zobunan kafin ya tafi. Suna karin safe karfe 8:30,
waya ta dauki kuka, mami ta baro tebur ta zo
duka tayi sallama. Muryar dan lelenta taji ya
amsa. Farin ciki ya lallube ta tace, Allah sarki Dr.
An sauka lfya? Yace lfya lau Mami, ina dadina?
Ga shi nan, ya taso ya ji kaini, ina fatan ba
matsala? Babu mami, na ma iske time table din
jarabawar mu ya fito, karatu kawai xa mu
fuskanta, ni da abokan karatuna. Dadi ya tsaya
wajen tana fadin, kai naji dadi sosai, to Allah ya
baku sa'a baki daya. Ga dadinka. Ya ce, to
nagode Mami. Dadi ya amsa suka gaisa. Dady
time table ya fito a taya mu addu'a. Yace kullum
a cikinta muke, amma xa mu kara kaimi. Ubangiji
Allah ya taimako. Yace amin. To xan wuce cikin
sch, sai kun sake jina. Yace, yayi kyau, all d bst!
Cike da fara'a ya amsa. Nagode Dadina. Ya aje
waya ya dubi mami yace hankalinki ya kwanta?
Bakinta har kunne ta amsa. Kai bari Allah ya
kara masa hkr. Yace amin, muje muci abinci ko?
Suka koma tebur. Mami tace abinci hankalinta
kwance.
Ba Haka al'amarin yake
wajensu Umma ba, domin yau sun koma
Fandagori sun iske da kuara da suka bari baya.
Hankulansu su kara tashi yadda xance ke ta
yamadidi a agari. Zagi iri-iri babi irn wanda ba'ayi
ba wasu suna ba iyayen Mama laifi, amma da
dama sunfi zargin mama akan rashin hankali da
ta aikata. Wani abinda yafi daga wa Ubandawaki
hankali shine, wai gaba daya gundarin labarin
daga bakin 'yan uwansa da matayensu ya fara
fitowa. Bayan gaskiyya ga tarin karya da
karairayin da suka yiwa labarin kawanya, don
haka ya tara su falon sa bayan sallar isha'i.
Wannan shine karo na 2 da na tara ku akan wasu
maganganu na batanci da suke fitowa daga
gareku. A zatona ku masu rufa min asiri ne ko
bayan raina a matsayin ku na 'yan uwana da
muka fito ciki daya. Amma bansan abinda nayi
muku ba kuke min bita da kulli, ko kuma ince
kuke farinciki don wannan abin ya sameni. To
abinda nake so ku gane shine, da frko dai bamu
mukayi kanmu ba. Allah ne yayi mu, mu kuma shi
ya rubuta duk abinda zai faru da mu. Babu
wanda yasan kaddarar mu2m bnalle ya share
masa mummuna kafin tazo. Da anayi da na
gogewa Mama, don na duk fadin duniyar babu
wanda zai kaini BAKIN CIKI, sai kuwa mahaifyar
ta. Idan kuwa hakane, bai kamata ace ku da
matayenku, ku dauki wannan al'amarin ya zamar
maku abin hira a gari ba. Kaddara na kowa, idan
baku duba kusancin mu ba, ya kamata ku duba
wannan. Allah yai sani ban zalunci kowa ba cikin
ku ba, haka ban xalunci mama ba, kamar yadda
kuke yadawa cewar mu ne muka dage sai mai
kudi xata aura, alhalin kun san komai a game da
alkawarin auran ta da Al-ameen. Kun fi kowa
sanin gaskiyya, amma kuka boye ta, saboda son
rai to na bar kowa da Allah, yayi min sakayya, Da
yardar Allah BAKIN CIKIN Mama bazai kashe mu
ba, haka zalika ina mata fatana shiriyar koda
yaushe. Mai surutu da dariya kuma Allah ya
bashi sa'ar yi. Amma kar ya mance kaddara bata
fatan shiryar kowa! Yana sa aya, ya mike ya bar
falon ba tare da wani yayi magana ba, ita ma
umma tashi tayi ta bi bayansa, yayi sauran ke
mazuran rashin gaskiya. Haj. Gaje ta buga tsaki,
ta bar falon. Daga bisani Haj. Hajjo ta lallaba ta
sulale, Alh. Basiru ya dubi Alh. Adamu. Yace
mutane munafukai ne, wai daga dawowarsa, an
sami wani kusugurmin ya feshe shi, don neman
fada. Alh. Adam yace, wai me akace? Au ya faru
ba za'a maida yadda akayi ba? Me za'a baoye
bayan ta gudun kowa kuma ya sani tare da
shegen yaron nan suka tafi! Ai ko ba 'a fada ba,
amsar a bayyane take. Tace, bata so, ba sai a
kyale ta ba, ta auri dan iskan da ake ganin ba shi
da asali ba, ba ita zata zauna da shi ba? Wahalar
tace tunda tasan halinsa. Tace sai shi. Wai kuma
mu ake ganin laifin mu, don fin karfi! Mts.... Ya
ja tsaki yayi waje abin sa. Alh. Basiru ya mike
yana kada kai, shi ma ya fice. Zaman doya da
maja yaci gaba da yaduwa cikin gidan, duk da ba
gaba daya sukeyi ba, amma babu wata
kyakkaywar fahimta atsakninsu. Shi uban dawaki
yana ganin ya kamata su ba shi hkr a matsayinsa
na babban su, sannan yana gani sun yi masa
laifi, don sun bada labarin yadda akayi mama ta
gudu, tunda ba su suka xuga ta ba, komai ya
kwana gidan sauki saboda haka basu ga dalilin
da xai sa Uban dawaki Ya dauki dalan laifi ya
dora masu ba har ya rinka jiran kalaman tubansu.
Su ma fah yanxun ba yara bane, girman 'ya'yan
su ya kai, ya gane shekarun su sun cika daidai
matsayin masu 'yanci. Zuwan Ali da Ya saed don
duba jikin Umma da kuma jin labarin Mama ko ta
bayyana, Al-amarin bai yi musu dadi ba, ganin
Yadda iyayen su suka ware ubandawaki suna
masa yankar baya. Musamman Ya ali, hankalinsa
yayi mummunan tashi, babu bata tym ya gurfana
gaban abba yana bashi hkr. Daga bisani Ya
saeed ya shigo falon. Ya ali Yayi rantsuwa da
ace mama zata dawo ta amince da auransa,
maimakon Danliti, a shirye yake a daura masu
aure. Ko a gaban iyayen sa haka ya maida
zancansa. Haj. Hajjo ta rufe shi da bala'i Allah
wadarn wannan so kuwa, tunda yake hana ka
kishin kanka. To idan ma mafarki kake yi, ka
wanke idon ka, ka saurareni, idan har ni na
haifeka, ba xaka auri ragowar Danliti ba. Wannan
kalma tayi masa ciwo, bai san tym daya tasshi
ya tabbatar wa su Haj. Hajo cewa kashe miciji
sukeyi basa sare kansa. Domin ko banza sun
kwana da mamakin Ya ali da yayi tafiyarsa, daga
magana, shima ya gudun kenan? Ko mene
nufinsa? Muna iya cewa matsalarsu ce, ko dama
abba ya fadi kaddara na kan kowa.......
Inna saude ke xaune gefen gadon tana
mata fifita. Kallo daya zakayi mata, ka gane
cewa ta jima tana fama da ciwon tsananin
damuwa, domin dai ta fyade ta fita kamanninta.
Amma hakan bai hana ragargazar shagalin bikin
da akeyi cikin gidan ba. Nasan xakuyi mamaki,
idan na gaya musu cewar bikin yaya Ali da Ya
Sa'ed akeyi. Iyayeyn sun hur masu wuta, tun tym
din da suka lura da take taken shi Ya alin, sam
hankalinsa ba shi akan abinda zai fishshe shi. Shi
yasa suka matsa kwarai da gaske akn ya fiddo
matar aure ko su su fidda masa, ya kuwa
tabbatar da mahaifiya sa xata ita. Gudun kar ta
manna masa alakakai ya sa ya fito da yarinyar
da ta dade tana sonsa a birnin gwari. Amina
sunanta, kuma makwabtansa ne a gidan daya ke
xaune. Sa'ed tuni yake tare da Hassana a kd. A
yau ne maza suka daura auran 11am. Daga can
suka wuce kd, inda xa'a daura na sa'ed bayan
azahar. 8pm wannan rana motocin amare ke
shigowa layin gidan angwayensu, haka daidai
wannan tym motar Danliti parkn a kofar shagon
sa dauke da tasa amaryar. Cike da mamki ayuba
ya taso, ya bude kofar yana fadin, wa nake gani
kamar amafarki? Wai dama kuna tunanin gida?
Dan liti ya fito yayi doguwar miki, yana dariya,
yace ah gamu kuma mun dawo, ya juya cikin
mota ya cigaba da fadin, ya Gimbiya anan zaki
sauko ko na karasa dae gida? Ta kada kai, tace,
naji tsoro ya kamani Danliti, bansan yadda xanyi
ba? Yayi 'yar dariya. Yace tsoro kuma? To me xa
suyi miki? Ta kada kai bari dai na sauka nan,
canm ajima na karasa gidan. Ya kace da dariya.
Amma ke shirmen ki yayi yawa, to fito ki shiga
ciki. Ta ballo murfin ta fito, kai! Anya kuwa
Mama ce? Tayi wata shegiyar kiba ta kara ja, ina
ganin shi yasa Ayuba ya xura mata ido, tym din
da take mika masa gaisuwa. Danliti ya bude but
suka ciro manyan jakunkuna guda 2 da kit, sai
manya ledoji guda 3. Ayuba ya taimaka suke
shige da su cikin shago. Kai tsaye dakinta shige
ta xube a katifa. Duk suka biyo bayanta. Danliti
ya xauna kusa da ita. Yace kin gaji ko? Tace kai
dai bari, kamar in kwanta inyi ta barci wlh. To ki
kwanta mana, ai ba kya jin yunwa ko kinaji? Ta
kada kai, banji, to ki kwnta ki huta ne, xuwa karfe
goma sai in tashe ki, ki koma gida. Haka za'ayi,
ta jawo filo ta yada kai, suna kallon juna suna
musayar murmushi. Ya lukuce mata hanci, yace
baby na kenan. Ta juya gefe tana 'ya dariya. Ya
mike ya dubi ayuba yace, to muje dogari. Ya juya
yana murmushi, ina tsarabata? Yace yauwa ka
tuna min, ya suri jakar leda suka fice da ita. Ya
xauna bisa kujera ayuba na kan tabarma, ya
zazzzage kayan kedar a gabansa. Gaba daya
kayan sawa ne. Na gayu ya siyo masa, ya dube
shi suka hada ido, yace ga tsarabar legos nan.
Baki sake yace babu wai, har ma ga tsaraba nan
duka naka ne. Ya washe baki m amma na gode,
watau shi ya sana kunyi jajur abinku, ashe kuna
bakin teku. Yace, hutu ba karya bane ayuba, ga
kuma lafiyayyar bebi na, nake gaya ma. Yayi
shiru yana kallon sa, fuskarsa gaba daya
tabayyana babu abinda bai faru ba. Ya numfas
duk jikinsa ya mutu yace, bakaji Danliti. Me nayi
ma tukunna? Ko kaji surutu ne a gari? Ya gyara
zama yace ba'a tonawa Danliti, abinda nake son
ka da shi, ku sasanta ka aureta kawai, ka ba
masu surutu kunya, donn sunce ba auranta
zakayi ba, tayi saki reshe ne, ta kama ganye, ya
shafa habarasa yace, ko? To ai ba suyi karya ba,
shagali kuma basu ga komai ba daga nan ma illa
masha Allah ba za mu daina ba. Ya kada kai
yace, meye nawa a ciki? Idan ka huta ko xuwa
gobe mayi lissafi. Yace ina fatan akwai kudi
sosai, don wanda na tafi da su naci uabansu, ya
amsa ciniki na na ba laifi, sati biyu ma da suka
wuce na je kno na karo kaya da cinikin yafi haka.
Da kyau mutumina, shi yasa nke sonka wlh. Yayi
'yar dariya yana daga kayan da aka kawo masa,
ni kuma ina sonka da nutsuwa ba amma kakiji.
Ya mike ya nufi daki yana cewa, kai ka fiye
surutu, bari in baka wuri. Ya shige dakin ya bar
ayuba da kallonsa. Ya kada kai yace aransa,
Allah ka shiryemu. Shi kuwa Danliti komawa yayi
ya hana mama barcin. Karfe 10 ta dan gota, dan
liti ya umarci Mama da ta koma gidan iyayenta,
su san ta dawo, dan su san matakin karshe da
zau dauka. Watakila hakan su ta cimma ruwa.
Watau su amince da auransu cewarsa madugu
uban tafiyar. Ya hado mata kayanta taf! Da
katuwar jaka, tana xaune tana kallonsa, kafin
tace gaskiyya ba xan dauki jakar nan ba, guda
uku kawai dauka cikin kit, in tafi dasu. Ido waje
ya tambaya, sabda me? Ka sani ko su koroni? Ka
bari tukunna mu gani, idan suka kyale ni, sai in
dawo in kwashe sauran. Idan basu kyaleki ba
fah? Sai na dawo nan ka yanke hukunci duk da
zaka yanke. Ya xura mata do, ai iyayenki na san
ba su ki karbarki ba, hasalima ai laifin su ne, na
tabbata yanxun sun gane kuskurensu, dole su
lallabaki. Ta doke kafadarsa tana dariya, har ma
kasan dole su lallabani? Kai dai ka yi fatan su
amince da auranmu. Yace shikenan, yanxun ki
dauki abinda xaki dauka na rakaki, dare nakara
yi. Ta bude kit ta xuba kaya kala 3, yasa hannu
ya dauko wata 'yar karamar doguwar riga
yace.....
Yace ba xaki dauki wannan rigar ba?
Tace wannan shegiyar rigar? Shegiya? Lallai ba
ki san yadda take mi ki kyau bane, a'a ka dai
barta anan, sanin kanka ne, su Abba bna za su
barni na sanya taba cikin gidansu. An wuce
wurin, ki barta kyasa a gidana. Ta yada kai kan
kafadarsa tace ashe ka gane. Ya tsikare ta, ta
mike xumbur! Ban fa so Danliti banso! Ta figi kit
dinta, tayi waje baki a ture. Ya kwaso mata gyale
da takalmi ya biyota yana fadin sorry 'yar bebi
na! Taja ta tsya tana haraarsa, ya yafa mata
gyalen, ya aje takalmin gabanta ya jawo
kafufuwanta, sa abinki mu tafi. Ta xura kafar
tace wa Ayuba, sai da safe. Yake yayi ya amsa,
Allah ya kaimu. Suka fice, Danliti na cewa, har
kin tabbatar da xamanki a gidan ne kike ce masa
sai da safe? Tace gane min hanya wai, makaho
ya so gulma. Ya ci gaba da dariya, suna tafe
suna hira. Gab da gidan, ya tsaya sukayi sallama,
idan kuma ya gan ta ta dawo shikenan. Y koma
ita kuma taci gaba da tafiya hankalinta kwance
yake, don bata saka komai illa in su koroto, ta
koma inda ta fito. Daga bisani ma wata dabara
ta fado mata. Tana dosowa kofar gidan, ta hangi
kamar ana hada hadar jama'a, duk da dare ya
fara yi, kana iya gane wa ana sha'ani a gidan.
Bata yi wa kowa magana ba,a haka suma babu
wanda ya shaidata. Sai da ta shige xauran
karshe ta aje kit dinta, ta xauna akai ta hade kai
da guiwa ta kirkiro kukan dole ta shiga yinsa har
da shesheka, sannan hankulan masu wucewa ya
fara xuwa gunta kuma, Ya ali shine mutum na
farko daya fara dosar ta da tambaya, wai wacece
xaune? Gida kike son komawa? A zata son cikin
'yan kawo amare ne, yayi dan murmushi, don ta
bashi dariya. Da girmanki da komai kike
kauyanci? Dan Allah tashi ki koma cikin gida tun
kafain yara su fara miki dariya. Ko an yi miki
wani abu ne? Daga ji ta gane mai magana, shi
yasa ta dago sosai ta dube shi, kawai batare da
tayi magana ba. Gabansa ya tsinke ya fadi
xuciyarsa ke ambato sunan, mama? Sannan ya
tsugunna gabanta ya furta a hankali, mama!
Hawayenta suka kara tsunkewa, ta sadda kai,
tana gogewa da bayan hannu. Innalillahi wa Inna
illaihir raju'un! Ya waiwaiga babu mai kallonsa
yayi sauri ya ja mayafinta ya rufe fuskarta, yace,
taso muje, kar ki bari kowa ya ganki. Ya ja
hannunta suka sulale dakinsy Danlami. Babu
kowa cikinsa, duk suna can wajen fatin da sukeyi
da abokansa. Ya xaunar da ita gefen gado ya
tsugguna. Yace, yaushe kika dawo mama? Baki
na rawa ta amsa, yanxun, idanuwansa suka kawo
kwalla a raunane. Yace abinda kikayi kin kyauta
kenan mama? Da mtuncin ki da komai? Iyayen
mu masu girma da daraja a gurin jama'a, kika
tozarta su? Haba mama, kamar baki sami tarbiya
ba? Ta goge kwalla. Tace, ba haka bane, Ya ali
me yasa zaku rinka ganin laifi na ni kadai? Nace
ga wanda nake so, ba sai a ba ni shi ba. Ina
ruwan kowa da rashin asalinsa? Ai dai ba daga
sama ya fado ba, da uwarsa da ubansa. Yace,
Maganar banza ce wannan mama, don na
tabbata Daliti bai fi miki iyayenki ba. Kin kuwa
san halin da umma ke ciki tun ranar da kika sa
kafa kika bar gidan nan? Kin daure min kai, ban
taba xataon zaki aikata irin wanan mummuna aiki
ba. Tace hakan kadai xai memin mafita kuma
akan bakana na dawo ko Danliti, ko su rasa ni
baki daya. Ya xura mata ido, yana kada kai.
Afuwa ya kamata ki nema ku sulhunta da
iyayenki, su sa miki albarka, ko kin ga rayuwa
mai kyau da anfani nan gaba. Saboda haka ki
xauna anan ki jirani, xan shiga wajensu in
kwantar musu da hankali tukina, gaskiyya bana
so ayi miki taratsi cikin jama'a, kuma gidan cike
yake da baki. Baki? Me akeyi a gidan? Ya amsa,
biki na akeyi dana seed. Kana nufin kunyi aure?
To Ya xanyi, tunda kinki ni Mama? Akan
dole na yi auaran nan, su Baba sun matsa min.
Ina muku murna, nima Allah yasa ni a danshinku.
Ya xura mata ido gwanin tausayi. Yace, nasan ba
xaki ji komai a ranki ba, tunda ba so na kike ba,
amma ni har kwanan gobe ina sonki, shi ya sa
abinda ke faruwa da ke ya xame min ciwon cikin
raina, ki yiwa girman Allah mama ki sanya
tunanin ki dawo sak! Yadda kowa ya sanki. Karka
damu dani Ya Ali, ko da yaushe ina gaya ma kai
dan uwana ne, kauanar mu ta jini ce mai asali.
Kwanciyar hnakalina kuwa Danliti ya zama
mijina. Ina fatan iyayen Al-ameen sunyi xuciya
su fasa? Ko baka ji komai akai ba? Ya xuba mata
ido yana mamakinta, ya jima bai amsa ba, kafin
yace, Al-ameen ya koma Rasha da ciwon xuciya
Mama..... Ta katse shi ido rufe ta dafe kirji.
Tace, nagode Allah! Har naji sanyi cikin raina. Ya
kada kai yana kallonta. Yace, baki masa adalci
ba, baki tsoron amanarsa ta ciki? Akan me? Bafa
dole bane na aure shi, ina son kowa ya gane
wannan, kawai kaje ka gaya masu na dawo din,
kaji me xasu ce? Yace ni ne nayi niyyar yin
hakan, ba sai kin bani umarni ba. Yi hkr Yaya, bai
tanka ba, ya tashi ya five, ta bi bayansa da kallo
tana fadin cikin ranta, je ka dawo, duk na kosa in
san babin da nake. Cikin dakin yayi sallama, abba
ya amsa masa yana kokarin hadawa Umma shayi
ta samu ta dan sha, ya akayi Ali? Ya xauna gefe
kusa da shi, yace babu komai abba, wata alfarma
naxo nema wajenku. Hankalin abba ya dawo gare
shi, yace ina jinka. Allah ya sa batafi karfi na ba.
Ya kada kai ya amsa, bata fi ba Abba, duk mai
laifi idan ya nemi afuwa, me yakamata ayi masa?
Ya dube shi da kyau da mamaki yace, ayi masa
afuwar, domin Allah yana son masu yafiya ga
bayinsa. Su kuma masu laifin su yi alakwarin ba
xasu sake komawa ga wancanm laifin ba. Laifin
me kayi? Ya amsa, laifin mai girma ne Abba, a
misali Mama ta dawo ta nemi gafara, abba xa ka
karbi tubanta? Ba abba kadai ba harda Umma
dake kwance ta xubo masa ido, abba ya jima
kafin ya numfasa. Yace Bansan dalilin da yasa
ka min tambayar nan ba, amma ina so ka sani,
mama ta aikata laifi mafi muni a shafin tarihin
gidan nan, da mu karbeta da kar mu karbeta,
bakin fentin da ta shafa mana yana nan baxai
goge ba, ina so ka sani Ali, xaiyi wuya a fadin
gari na Mama ta sami wani mijin, face katon
daya dauke ta ya boye wani wuri tsowon watanni
3. Abu na karshe da nake so ka snai, shine bai
kai kadai ka rokeni ba. Al-ameen ma ya rokar
mata gafara kuma nayi masa tare da alakwarin
ba xanki karbarta ba. Saboda haka ka kwantar da
hankalinka, muddin Mamma ta dawo gidan nan,
ba xan ce ta koma ba, haka xalika idan bata
sauya ra'ayinta ba, ba xan ce mata a'a ba, Allah
na kallo, nayi kokarin na, don nuna mata hanyar
kwarai da samun abokin zama na kirki mai kyan
asali. Ko duniya ta zageni, alhakin Na suka duka
kuma zamuyi shari'a da su gobe kiyama. Kawai ji
yayi kwallah na xubo masa, saboda tausayin
Abba, yasa hannu ya goge, abba ya riga shi sake
magana, ka daina kuka Ali, kaddara ce, tashin
hankalina daya, mahaifiyarta da ta kasa samun
nutsuwa. Ina jin tsoron kar ciwon xuciya ya
kamata kamar yadda likitocin da ke duba ta suke
gargadin ta kullum. Dalilin da yasa kenan nake
fatan Allah ya sa mama ta dawo, watakila ya
zama waraka ga mahaifiyarta. Na tabbata
hankalinta xaifi kwanciya idan tana ganin ta koda
a dakin auran Danliti ne. Ya Ali ya gyara xama
yace, gaskiyya ne abba, kuma naji dadin bayanan
ka. Saboda haka ina mai farin cikin shaida maku
cewar mama na nan ta dawo. Abba ya xura
masa ido. Umma kuwa ciccibawa tayi ta tashi
xaune. Ba fahimce ka ba Ali? Inji Abba, yace
Mama na nan a cikin gidan nan, idan kun ban
izini, zan shigo da ita ta roki gafararku. Suka dubi
juna shi da Umma baki sake, tuni hawaye suka
tsinke mata, tana kada kai tare da salatin Manzo.
Abba ya dube shi yace, je ka ashigo da ita Ali.
Har ya mike ya sake komawa ya xauana, yace
Abba ina fatan ba xaku daga mata murya ba,
kasan gidan na cike yake da baki. Yace Insha
Allahu, ba xan daga mata ba. Yace nagde abba.
Ya mike ya wuce, abba ya bishi da kallon,
sannan ya dubi Umma, ashe haka Ali ke da
hankali? Nayi kuskuran hana masa auran Mama
tunda farko. Umma ta goge hwaye tace, hakika
mama tayi asara masoya 2. Haka Allah ya so, ba
mu da abinyi, dai yi masa godiya, abba ya sauke
numfashi, sukayi xugum suna sauraron ta yadda
mama xata bayyana garesu. Jimawa kadan suka
tsinkayi muryar Ya Ali yana fadin ki shigo mana!
Na gaya miki komai ya wuce, ki shigo kawai.
Make-maken munafurci takeyi ba wai ainihin
tsoron bane cikin ranta, da su abba xa suyi
kuskuran cewa ta juya, fes! Zata juya babu
waiwaye sukayi sallama dakin. Ya ali na dauke
da kit dinta. Ta toge bakin kofa, yasa hannun ya
janyo ta har gabansu abba dake sake da baki
suna kallon abin al-ajabi. Gata abba, umma ga
Mama, ku mance da abinda ya faru, ku amince
da xabanta, ku sa musu albarka, sai kuka ga
Allah ya basu zuri'a abin alfahari. Mama ki
durkusa ki roke su gafara. Ko dama a durkushen
take kuma tuni hawayen suka tsunke mata,
murya na rawa, tace..
[12/01 19:16] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***12
Abba kuyi hrk, Umma ki yafe min. Abba
ya numfasa yana kada kai. Ya ce a rayuwata
gaba daya Mama ba tba xataon xaki min irin
wannan mugun butulcin ba. Na dauke ki 'yar da
na dauki burin duniya na dora a kanki. Kece kika
bambamta da kowa cikin xuciyata, kuma na nuna
miki dukkan gata amma dare daya, kika numa
mana akwai wanda ya fi mu muhimmaci a
rayuwarki. Tabbas na yarda da hakan, don a
tunani na xan ga kin dawo kin bushe a lalace
saboda tunanin kin barmu cin BAKIN CIKI sai
gaki Fes! Kinyi kiba. Ban miki baki ba, ba kuma
xan miki ba, amma ina mai tabbatar miki in rasa
masoyi, kin rasa mai tsanin kaunar ki tsakani da
Allah, kuma a yau na kara nadamar hana Ali
auaranki tun farko. Maganata karshe itace, tunda
kin nace sai Danliti to ki gaya masa ya turo
magabatansa, muyi magana, sannan kiyi wa
Yayanki Ali godiya, domin yayi miki dukkan
taimako. Zaciyarta fara sol! Jin Abba ya ambato
Danliti ya turo. Ta kara dukawa tana goge
kwalla. Tace, ngde abba, kuma ina kara baku hkr,
don Allah ku yafe min. Ta rarrafa gun Umma ta
cusa kanta jikinta, umma kiyi hkr! Ta share
hwaye tace ai ya wuce Mama, kinci albarkacin
al-ameen da ali. Amma gyara kayanka, ai baya
zama sauke mu raba ba. Ki bi duniya a sannu,
domin ita duniya budurwa ce mai kyale-kyale da
yawa, da zarar ka biye mata, to ka bace ka kuma
shiga uku ka lalace. Ban da abin kari a gareki,
don nasiha anyi miki, amma kin rushe saboda
batan basira. Allah ya ganar da ke, ya sa ki a
hanya madaidaiciya. Ya ali ya amsa da amin,
yayin da mama ke ci gaba da gugar hawaye. Alin
ne ya cigaba da cewa, don Allah abba karku
nuna kowa ta dawo har tym din bakin nan xasu
koma. Ko su Baba a kyale su tukuna. Ke mama
ina son ki cigaba da xama cikin dakinku dan
Allah, na san xuwa gobe da yamma kowa xai
watse, sai a kam magana ta gaba, kinji? Ta amsa
da kai, Abba yace shikenan Ali, kana son ka
rufawa 'yar uwarka asiri, asirin kuwa da ya riga
ya tonu. Yace kayi hkr dai abba, yace babu
komai, ta tashi ta koma dakinta, idan tana jin
yunwa, akwai abinci, yace xaki ci abinci ne? Ta
kada kai, to taso na raka ki dakinki. Umma mun
gode, tace Allah yayi albarka, ya amsa da amin.
Tare suka mike suka bar dakin. Umma ta tafa
hannu tana salati, sannan ta buga tagumi.
Yanxun alh. Danliti xata aura? Yace, t ya xamuyi,
wa kike ganin xai fito neman auranta, bayan ya
san wannan kwamacala? Haka nan xamu hkr da
abinda Allah ya kaddaro, yanxun dai bana ce ya
turo ba? Sai mu sa ido mu ga wadanda xai turo
din. Ta numfasa, tace Allah shi kyauta yace
amin. Ke dai ki kwantar da hankalinki, ki daina xa
damuwa a ranki don Allah. Tace naji alh. Ya ciga
ba hada mata shayin suna tattaunawa. Kamar
yadda ake tattaunaea da mama da Ya Ali.
Shawarwari kawai yake bata, tana sauraronsa
kamar gaske. Har kusan sha daya da rabi suna
tare. Dagab bisani yayi mata sallama ya barya
cike da farin ciki da baya misaltuwa. Nan da nan
ta fada bayi tayi wanka, ta kintsa jikinta ta
kwanta. Kewar Danliti ta lullube ta, fadi take
cikin ranta, ba dan dare yayi ba da naje yiwa
sweety Na albishir. Da kyar barci ya sace ta
saboda murna. Washe gari hidima taci gaba,
mama na cikin dakin na kulle babu wanda ya san
ta dawo, daga Ya Ali sai su Umma. Kuma anyi
sa'a taji maganar Ya Ali batayi marmarin fitowa
ba, sai shi ne ma ya kan saci jiki ya shiga
wajenta, ya ganta yaji dan ji sanyi aransa. Allah
sarki! Garin dadi na newa, iska na ta wahalar da
mai kayan kara, bayan sallahr la'asar baki suka
koma muhallin su aka bar amare da angwayensu.
Shi kuwa Ubandawaki 'yan uwansa ya tara falon
baki yace, naki ku ne a matsayin ku na kannena
na in shaida muku cewar Mama ta dawo daren
jiya, kuma har na yanke hukuncin ta gayawa
Danlitin ya turo magabatansa, muyi maganar
aure. Ban san yadda zaku karbi abin ba, ko da
mahimmanci ko ya zama abin dariya a gareku,
duk daya ne, ni dai na fita hakkinku. Suka dubi
juna cikin sigar tsarguwa, sannan Alh.basir yace,
ai shikenan yaya, amma banji dadin yadda kayi
mana fassara ba, ya kamata kayi mana uxuri
tunda mun ce maganar nan bada wata manufa
muka fadeta ba. Amma ace mama ta dawo tun
jiya, sai yanxun mukeji? Ba komai. Alh. Adam ya
cage, tabbas naga Danliti a shagonsa, sai dain
banyi tunani tare suka dawo ba, tunda banji
labarin ba a cikin gida. Sai dai Yaya a gaskiyya
muna so mu ganar da kai cewa ba farinciki
mukeyi da abinda ya sami mama ba, mutuncin
gidan nan, ai duk namune, me zai sa muyi murna
da rugujewarsa? Abba yace duk naji, magana ta
gaskiyya, Allah kadai yasanta, don shine masanin
sirrin xukata. Abinda ya sa bau san Mama ta
dawo ba, sai yanxun. Ali ne ya fara ganinta kuma
ya xo ya sameni guiwa 2 ya roke ni da kyale
mama kar in daga murya, saboda baki fa ke cikin
gidan nan. Idan sun tafi ayi su wacce xa ayi. To
maga ma ta kare, nacewa Danliti ya fito a daura
musu auran, su karata. Allah dai ya gani ba da
son raina bane. Fuska Ya mutse Alh. Basir ke
cewa, Dan liti xata aura? Yace bamu da abinyi,
haka Allah ya so, sai dai muyi mata fatan
alkhairi. Saboda haka bana son abin yayi tsawo,
yana turo sai aure.
Ya turowa za'a sa rana kuma ba zata
wuce sati 3-4 ba duk abinda Allah ya hore min
shi xa'a kai mata. Ita kenan maganara, kowa na
iya tafiya harkokinsa, mu saurari xuwan
magabatan nasa shikenan, Allah ya nuna mana.
Haka suka fadi baki dayansu. Abba ya amsa da
amin, suka bar falon ba yabo ba fallasa, cikin
xukatansu, ma'ana intayi ruwa rijiya in ba tai ba
masai. Suna shuga sasan su, suka bajewa
iyalensu babu bata tym suka fara xuba sharhi.
Haj. Gake kuwa har da guda. Daga bisani suka
baxama sassan Uban dawaki, don gain Mama
tare da yiwa Umma murna dawowar Mama fida,
amma a zahiri a cikin xukantasu yanayin Maman
suke son gani. Suka kwarara sallama, umma ta
amsa, sai mukaji daddadan labari! Ina maman?
Inji Haj. Hajjo, tana dakinta, gaba daya sukace
Allah shi kyauta na gaba. Yanxun da Danliti
xa'ayi auran? Tace, nufi ne Allah, duk abinda ya
rubuta bamu isa mu goge Ba. Haj. Hajjo tace
gaskiyya ba haka muka so ba. Sai dai hkr kwai.
Haj. Gaje ta tabe baki tace, ya xama dole, amma
a hakikanin gaskiyya mama ta bamu kunya. Ajin
ai ba daya bane in banda batan basira. Koda
yake ance so mako ne. Allah ya sanya alkhairi.
Sukayi dan shiru, kafin suka nufi dakin Mama, ina
kike? Kina jin mu amma ba xaki fito ki gaishemu
ba? Tana xaune gefen gado, ta fesa ado kyanta
ya kara bayanna, banda haka da ibar da ta kara
suka kalli juna sabe da haba, kafin Haj. Gaje ta
soma xuba, lallai Mama, watau hankalinki a
kwnace kika je, ki ka dawo! Wannan kiba haka?
To Allah yasa ki sami irin wannan a gidansa. Haj.
Hajjo ta amshe amin dai, kin dai riga kinsan
halinsa, komai yayi miki sai ki hadiyewa cikinki,
kar ki doshi kowa, tunda kin nace shi kike so! Ko
kuwa gaje? Tace haka yake yaya, ai kowa ya
sayi rariya yasan zata xubda ruwa. Mayafinta
dake bisa filo ta figo ta mike tsaye ta xura
takalmanta tayo waje tana yafa gyelenta, ta
barsu anan sake da baki, suna kallon juna. Ko
kinga dibar albarka? Inji Haj. Hajjo, Haj. Gaje
tace, mamaki kikeyi Yaya? Karfa ki manta
watanni 3 ta shafe a bariki, an kuwa ce xama da
madaukin kanwa, shike kawo farin kai. Mu meye
namu? Ta malam ai bata wuce amin. Can suka
sameta dakin Umma tana neman izinin zuwa
wajen Danliti, don ta shaida masa sakon abba,
suna isowa, umm ana fadin bance kije ki xauna
ba, mutunciki shine ya biyo ki nan kofar gidanku.
Saboda haka daga yau kar na sake jin kin koma
shagonsa. Tace, to Umma, insha Allah yanxun
xan dawo. Ta sa kai ta fice, ba tare da Umma ta
kara wani abu ba. Nan su Haj. Hajjo suka xauna
suka cigaba da kwasar tsegumi, ita kuwa tana
fitowa xauran farko, angwaye ta ci karo dasu,
saeed Ya maka mata harara, ya wuce abinsa
cikin gida. Ta dubi ya Ali, tace me nayi masa?
Yace kin fi kowa sani. Taja dogon tsaki, aikin
banxa, to shinme me? Don ya ki min magana?
Yace, kin baci da Rashin K mama, me yasa? Da
ba haka kike ba. Ta dan tabne baki tace, ni ina
da wurin xauwa, ba na fito magana da Ya Saeed
bane. Yace amma ba kije kinga amare ba. Xanje
ai, so nake in sauke wannan nauyin ko ni,a na
kama dahir. Yayi dan murmushi yana kllonta,
mama kenan, to a dawo lfya, nasan sakon bai
wuce na Danliti ba. Tayi 'yar dariya. Shi ysa nake
sonka Yayana, bari dai in dawo amaryarka ka xan
fara xuwa na in gani. Ta wuce tana cigaba da
dariya, ganin yadda yayi tsaye duk jikinsa ya
mutu. Ya bita da kallo, sannan ya kada kai, yace,
ni ma ina mutuwar sonki Mama. Ina ma ace
hankalinki xai dawo gareni? Ya sauke numfashi
ya shige wajen amaryarsa. Bakinta har kunne
take sallama kofar shagon, ayuba ta gani xaune
ckin shagon ya amsa mata cike da fara'a
amaryarmu kenan, ya gajiyar tfya? Tace tabi lfya,
ina mutumin? Ya amsa yana ciki tun azahar yake
barci saboda ragwanci. Ta fara dariya, lallai
kuwa ragwanci, barin inshiga dole ya tashi ya
bani goron albshiri. Ta wuce ciki, ayuba na fadin,
ya dai kamata ya tashi ko salla ya samuyi. Kan
tsaye bisa katifar ta fada, ta dada masa duka
cinya, don Allah tashi rago! Ka wani baje kana
gugar barci, ni ina can ina tunaninka. Ya bude ido
firgigi yana kallon ta jim, sannan yayi dan gajeran
tsaki. Yace kash! Wlh ba don ke bace, marin
Mutum zanyi. Kin ji dadin barcin kuwa? Tayi far
da ido, tace ko? To ka tashi, na tabbata dadin
barcin bai kai albishir din baki na ba. Ya xuba
mata ido yace fadi ina jinki. Idan kuma bai fi ba,
kinsan Allah sai na sanya ki kuka, ai kin san
gamuwar mu babu tausayi. Tayi 'yar dariya, tace,
haba duk wannan kukan wasa nakeyi, kama
daina hura hanci. Yayi murmushi, haka kikace?
To shiknen, fadi ina jinki. Ta gyara xama
albishirnka? Yamasa goro. Xaka bani Ah! Me xai
hana? Ke dai gaya min inji. Abba yace in fada
maka ka turo, ranar auren mu za a sanya. Ya
xuba mata ido, ya kasa ko motsi, kayi shiru? Ya
sa hannu 2 ya mutsutsuke idanuwansa yace, dan
Allah karki xalayeni! Ta ware ido, kana nufin baka
yarda ba? Gaskiyya ban yarda ba, yaushe Abba
xai yarda ya bani ke, bayan ya san bani da kowa
a garin nan? Sannan suna min kallon dan... Tayi
wuf ta rufe bakinsa, sau nawa xan gaya maka ka
daina dorawa kanka maraici? Ina sonka
Danliti.....
su abba kuma sun amince ka turo asa mana
rana da gaske na ke gaya maka maganar nan ba
wasa ba da sauri ya figo ta jikinsa yayi wani irin
ihu wai shi murna ayuba ya kwaso a guje ya fado
dakin ya same si kankame da juna dan haka. Bai
tsaya tambayar komai ba ya juya ya fita yana
kada kai cikin ransa yana fadin "Danliti akwai
dan iska"ya jima bai kyale mama taci gaba dayi
masa bayani ba yanzu yaushe. Zaka turo? Ya
yunkura ya tashi zaune yace bashine matsalar ba
wadanda zan turar sune matsalar ta dan bata
fuska tace ai ba za ka rasaba "Danliti ko yan
dattijan daku ke gaisawa sun isa su wakilce ka
ko kuwa? Ya zura mata ido duk sun juye, yace
haka ne sai ki baru in gan su mudaidaita tukunna
sannan in gaya miki ranar daza su zo ko" tace
shi ke nan bari in kwashe sauran kayana in koma
gida ya kara matsarta haba tun yanzu ?" Umma
ta ce kar na dade kuma tunda sun amince da kai
ai zaka rinka zuwa ne kan ka tsaye,"ya
kankameta ya na fadin haka ne amma ban so ki
tafi yanzu sonki kawai ke azabtar da ni ina
kewarki da yawa jiya da kyar nayi barci kinji
yadda ki ke tashin kamshi?gaya min dame dame
ki ka shafa in karo miki irinsu?"Bata iya bashi
amsa ba don tun tafiyar su yake koya mata irin
wannan renon ya gama da rayuwar ta gaba daya
kai ALLAH ka raba mu da sharrin masu
sharri,magariba ta wuce wadan da sukaje
masallaci ma sun koma gida yayin da mama ta
fito daga shagon Danliti jaye da katuwar jakar
kayanta.
-yar tafiya kadan ya taka mata ya dawo
abinsa bata sami dan dakon da zai daukar mata
kayanba ba don haka da kanta tayi ta ja har gida
abba da umma na zaune a falo dauke da bakin
ciki maras misaltuwa mama ta turo kofa ta shigo
sa sallamar ta dauke da uwar jakar kaya babu
wanda ya amsa mata ta wuce ta gabansu ta
tsugunna tace sannu abba, wani irin kallo yayi
mata mai isar da sakon haushi da takaici kafin
yace daa ina kike?ta dan sunkuyar da kai tace
naje gaya wa Danliti sakon ka ne ai na gayawa
umma kafin na fita ko um..."Ya daka mata tsawa
rufe min baki don ALLaH shine zakije ki zauna
har bayan magariba kiji tsoran ALLAH mama ki
sani cewar mutuncinki ki ke zubarwa wannan
uwar jakar da kika shigo da ita tawace tukuna?
idanuwanta suka kawo kwalla ta fara rawar
murya na...nawa ne.. Kayan da...Danliti ya siya
min ne yace to ba a gidan nan ba idan yazo ki
maida masa kayansa ya baki can gidan sa,ai kinji
ni ko,?ta amsa da kai umma ta cire tagumi ta
kare mata kallo sannan tace Alhaji ya kamata a
tuhumi yarinyar nan idan idan tabada kanta
gareshi kasan istibira'i ya kamata, kafin a daura
auransu domin ni banyarda da mama ba a yadda
suke tare da yaron nan,ya numfasa ciki da bacin
rai yace ki na da gaskiya don ni ma wallhy ina
wasi wasi cikin raina ke mama ki gaya min
tsakaninki da ALLAH ki fi jin tsoran sa akan
komai na duniya ki gaya min gasjiyar abinda ke
tsakanin ki da Daliti kar kisa muyi kuskure da
gangan idan kin san da wani abu to ki gaya
mana mubi tsarin da ALLAH ya shimfida.
-sosai ta goce da kuka murya na rawa tace
ALLAH abba babu abinda ya shiga tsakanina da
shi duk sukayi shiru suna dubanta kamar sun
gaskanta ta kamar basu yarda ba amma dolensu
yarda tunda basu da wata hujjar kama ta don
haka abba ya daka mata tsawa ya isa don
ALLAH tana wani bare baki kamar mummuna
tashi kiba mu wuri kuma na gaya miki yana zuwa
ki maida masa jakar kayansa,ta goge hawaye ta
dan sunkuyar da kai tace yace ya gode insha
ALLAH zai turo din suka yi banza da ita shiyasa
da dago ido ta dube su uwar hararar da ta yi
arba da ita tilas tasa tayi saurin maida kanta
kasa jim sun kikara cewa komai yasa ta mike
simi simi ta janye jakar ta, ta wuce daki bakin
nan tamkar na agwagwa kai tsaye bayi tashige
tayi wanka ta dauro alwala ta fito ana ta kiran
issha'i,don haka tana yin magariba ta dora
issha'i
bayan ta kammala ta fito neman abinci nan falo
sukayi kicibis da yaya ali wai me ki ke nufi baza
kizo kiga amarya ba?ta kama kugu hannu biyu
tace wannan amarya an damu nazo na ganta
hala tafini kyau ne ya kama dariya kafin yace
soosai kuwa tafi ki kyau muje ki ganta tace haka
yake amma duk kyanta dai ni aka fara so kifin ita
saboda haka a daga min kafa inci abinci
tukuna"kalamanta sun ruruta wutar zuciyarsa ba
kadan ba koda ganin yadda jikinsa ya saki kasan
ya fada wani yanayi ya zura mata ido
hannayensa rungume a kirjinsa murya sanyaye
ace zancan ki dutse yar uwata,.
[12/01 21:52] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***13
hasalima rashinki yasa na aure ta koda
yaushe ki kace da ni kule da sauri xan ce cas
mama don son ki ya zauna a raina, tayi yar
dariya tace yaya ali ke nan kar kasa amaryar ka
ta tsane. Ni daga wasa sai ka hau jera zance!ba
haks nake nufi ba yaya ali muje kawai naga
amarya in na dawo na ci abincin bata jira yace
wani abuba ta yi gaba abinta tilas ya biyo
bayanta yana kada kai!Amare kam masha ALLAH
suna dauke da tasu baiwar da ALLAH yayi masu
musamman aminar yaya ali har mama na masa
tsiya wai ya kamata ya maida sunan sa aminu
dan su kara dacewa da juna kallon ta kawai yake
yi cikin ransa shi yasan babu wacce tafi dacewa
dashi face ita kanta maman,bata wani dade ba ta
dawo sasan su ta dauko leda cike da kayan
garar amare bayan ta gama cin abinci ta zauna
gaban madubi tayi wa fuskar ta kwaskwarima
tayi zaman jiran Danliti har barci ya fara dibarta
bataji aiken yaro ba,ta kwana zullumi da juyayin
abinda ya hana Danliti zuwa alhalin ya sami
izinin yin hakan ko har yanzu bai amince wa
ransa bane?ya gudun kar yazo ya fuskanci
wulakanci!wannan tambayar taso ta hana ta
barci domin ta kai sama da karfe dayan dare
bata sami barci ba,Da sassafe ta tashi da ciwon
kai wanda ya haddasa mata jiri akai akai duk da
haka ko karyawa bata yiba karfe bakwai da rabi
tasa kai ta fice babu wanda ya sani ta nufi
wajen Danliti dauke da ledar kayan garar amaren
da aka bata jiya ita ta tashe shi barci ya tashi a
gigice yana tambaya lafiya kika bugo sammako
haka?tace nayi zaton zaka zo jiya hira me ya
hana ka zuwa.
ya ja dogon tsaki ya kauda kai jim sannan ya
juyo ya dubeta wai me ke damun kine?ba kinzo
nan ba sai bayan magariba kika tafiba?to kuma
me zanje in yi maki saboda ALLAH ta zura masa
ido ya kare mata kwakwazo nan take idanuwanta
suka tara kwalla murya na rawa ta ba haba
Danliti laifi ne don ban gan kaba na biyo in duba
ko lafiya?ya bita da kallo tana ta gugar kwalla ya
kece da dariya kamar mahaukaci hakan yasa ta
daina hawaye ta zuba masa ido yayi dariya mai
isar sa sannan ya natsu shima ya bita da kallo to
meye abin kuka ni ina can ina ta billayin neman
mana waliyai ai banga ta zaman fira ba
sakeena"nan da nan ta hadiye tashin hankalinta
ta fara murmushi duk kin wani daga hankalinki
don baki ganni ba jiya kawai " kawai ne? In gaya
maka dai dai da sakwan daya bana son zama
babu kai,yayi wata budurwar dariya yace ko to
na kara baki tukuicin kaina ta kwanto masa tana
dariya kasan ALLAH da ciwon kai na tashi ga
wani jiri na diba na amma na kasa daurewa na
fito ko karyawa banyi ba, yace ai ya bebi na
sannu ko ya kamata mu karya ki sha magani bari
inzo. Ya fice ya bar ta kwance bisa katifar
wucewar minti ashirin ya dawo da soyayyun kwai
da naman kaza da doya itama hade da kwai ta
hada masu shayi suka batse cikinsu harda ayuba
anan ta yada kafada daga fira barci ya kwasheta
Danliti ya dawo shago ya zauna tare da ayuba ya
zura masa ido yace don ALLAH ka tasheta ta
koma gidan su yayi banza dashi ya fito yana
zuba fito kamar katon arne.
-Ayuba ya kada kai yace karshen alewa kasa
Danliti idan an ciza a rinka hurawa ya ballo masa
harara ya ce ba ruwanka malam ka kyale ni in ci
lokacina ya tabe baki yace na barka zaifi kyau
suka yi shiru kowa na harkan gabansa, a gida
kuwa tunda suka shafa babu mama a dakin ta
suke ta kwasar BAKIN CIKI don sun tabbata tana
can shagon Danliti karfe tara uban dawaki ya
gama shirin sa zai fita ko karyawa bai yi ba
saboda tsabar takaici yasa umma ta fito masa da
jakar kayan da mama ta shigo dasu ya sunkuta
yayi waje da ita kalla ya tarbe shi da sauri ya
amsa ya bude but ya saka Abba yace minna
zasu tafi amma zasu tsaya shagon Danliti, kalla
yaja mota suka wuce yayi fakin kofar shagon
abba ya umarci daya fito masa da jakar nan kai
tsaye ya wuce shagon lokacin da su Danliti ke ta
harkokinsu yayi tsaye babu sallama har
hankulansu suka juyo gareshi Danliti ya matso
yana fadin sannu alhaji ina kwana yace nasan
mama na nan tare da kai ina take baki sake yace
tazo amma ta tafi yayi jim yana kallonsa kafin
yace ba shi ya dame ni ba wannan ya rage kuda
ubangiji ina fatan. Ta gaya maka yace ta gaya
min kokarin da nakeyi ke nan na samu na turo
yace kar ka bata lokaci domin na kosa na kauda
kazantar da nake gani ya dan sunkuyar da kai
yana murmushin izgilanci naji abba in ALLAH ya
yarda zuwa anjima ko gobe zan turo yace shike
nan ina sauraronka amma ga kayan ka nan ka
aje idan ta tare gidanka sai ka bata ba na
bukatar komai daga gareka sai sadakin da
ALLAH ya wajabta ga jakar nan bai saurari wani
abu ba yasa kai ya bar shagon ya fada motarsa
kalla ya ja suka dauki hanya
Ayuba ya matso gare shi yace, Allah na
tabaka dama, don ka gyara kuskuran ka Danliti,
kar ka bari ta subuce maka, ka dawo kana cizo
yatsa. Ya watsa masa harara yace bana bukatar
wa'azinka alaramma karfa ka manta da ni da kai
duk daya ne. Na ma dai san abinyi, ayuba ya
xuba masa ido ya rasa ta cewa babu abinda ya
sami Danliti, yasa hannu ya dauki jaka ya shige
da ita. Hannu 2 ya rike kugu, yana kallon mama
xucyarsa na masa sake-sake. Kusan 5mins yana
tsaye, sannan ta tsugunna ya bubbugata. Ta
farka tana yamutsa fuska, menene? Tashi kiji? Ta
yunkura ta tashi xaune, yasa hannu ya kara janyo
jakarta, don ta ganta sosai. Cike da mamaki tace
waya kawo ta? Yace, abbanki mana! Wannan
kadai ya tabbatar min baya sona, baya kaunta.
Bai dameni ba, amma me yasa zai uzzura min
dole sai na turo magabata na yanxu-yanxu?
Hankalinta ya tashi, ta matso a hankali ta dafa
kafadarsa. Don girman Allah kar hankalinka
yatashi Danliti.... Cikin sababi. Yace ki daina
gaya min wannan maganar! Kora da hali abba ke
min, saboda haka ki hkr, kije su baki wanda suke
so! Tashi ki bar dakin nan, kar kuma ki sake
xuwa, ni babu ruwana! Ta narke da kuka, murya
na rawa tace, karka yi min haka Danliti, ina mai
tabbatar maka xan kashe kaina idan ka juya min
baya. (Kuji banza mtsw ). Ya cire hannunta
daga jikinsa yace, ni ban aikeki ba ya kamata ki
gane ki gane ba dole bane na aureki. Don me xa
a daga min hankali akan magabata? Banda su,
uban wa xanje na tura idan ban nema ba? Kinga
ki tshi kije ki gaya musu na fasa. Ta marairaice
kamar ranta xai fita ni ina sonka Danliti ba xan
iya rabuwa da kai ba, ai dai ni xa'a daurawa
aurenko? Xan gaya musu su kyaleka, sai ka
shirya. Shikenan? Ya kara murtue fuska, yana
kallonta bai tanka ba. Takara matsarsa sosai taci
gaba da fadin, muddin suka ki yarda da uxurinka
wlh na yi rantsuwa xasu sha mamaki dan wlh
nan xan dawo na tare..... Ok, ki sa a daureni
kenan? Tace wa xai daureka? Don Allah ki
kyaleni ni bana son surutu, tashi ki tafi kawai, sai
na nemeki! Dan..... Ya daga mata hannu, idan
baki so raina ya baci to ki tashi kawai ki bar
dakin nan! Ta cigaba da share hawaye, ta xura
takalmi ta dauki mayafi ta mike xata wuce,
amma ta kasa, tayi tsaye tana kallonsa, don
Allah kayi hkr Danliti. Ya dago ido ya dubeta,
hawaye keta ambaliya, yayi dan jim, kafin yace
nayi hkr, amma kije tukunna xan nemeki. Xaka xo
gidanmu? Eh xan xo ki share hawayen, ba wani
abu. Ta share da sauri ta duro bayansa, Nagode
Danliti na! To kayi dan murmushi mana ko naji
dadi mana. (mayya ) Ya banbare hannayen ta
ya mike tsaye, karki damu da murmushina, muje
in rakaki, kafin tace wani abu, ya fice, dole ta
biyo bayansa, bakin shagon kawai ya tsaya, yace
sai nazo ko? Tace, daga nan xaka tsaya? Xan
wuce neman wadanda xan turo din ne. Nan da
nan sanyi ya ratsa mata xuciya, baki har kunne.
Tace, Allah sarki nawan, to sai mun hadu anjima.
Ya daga gira yana fadin, sai mun hadun, yana
sakin tsaki. Tana shigowa dakinta, ta shige,
motsinta kawai Umma ta jiyo ta biyo ta dakin,
tana kokarin cire kaya, don shiga wanka. Umma
ta kare mata kallo, ta kada kai, tace don girman
Allah mama ki rinka xama a gida. Tunda Danliti
na sonki kuma abbanki ya bashi dama ai shi xai
biyoki. Kullum inaga ya miki babu mutunci ga 'ya
mace ta rinka bin saurayi har makwancinsa. Ko
bai aikata miki komai ba jama'a ba za su dube ki
da mutunci ba. Me yasa Danlit ya sauya miki
tarbiya.? Tayi shiru tana ciccika tana batsewa,
Umma tacigaba ni rokonki nakeyi, ki taimakemu
ki taimaki kanki, don mu tsira da 'yar martabar
da tareg mana a idon jama'a. Kinji? Ta amsa da
ka, kafin tace, Umma idan abba ya dawo ki fada
masa ya daina matsawa Danliti akan turo
magabatansa...... Ta katseta kamar ya? To
umma tunda an gayama sa kuma ya amsa xai
turo din, ba sai asa masa ido ba? Ta mako mata
harara, bangane asa masa ido ba? Shi daman
can bai shirya auran ba, ya hanaki sauraron
wandan ya shirya? To baku isa ba, mu ba wasa
mukeyi ba, tunda ya hure miki kunne dole ya
gaugauta turowa, ya raba da mu da bakin ciki da
muke gani, kinji nagaya miki. Tayi ta tashi tana
fadin, to shikenan ai matsa masa ba shine xaisa
ya turo din ba. Me kikace? Ta shige bayi da sauri
ta rufe kofa. Mama ni kike wa rashin kunya?
Lallai kin rika, kina gab da tsinka min mari akan
Danliti.
Sallamar da jiyo, shi yasa tayi shiru. Ta
mike ta fito tana amsawa. Inna saude ce da
Baraka, saude sannunku da xuwa. Duk suka
amsa, yayin da Baraka ta tsugunna ta cigaba da
gaisawa. Bayan sun nutsa a falon, inna saude
tace, tun jiya naso fitowa, wani axababben ciwon
kai ya addabeni. Tace ayya ina fatan yayi sauki.
A'a da sauki, ina maman? Tana ciki ta shiga
wanka.... Wai dama saboda ita kika zo? Ai da kin
yi kwanciyar ki kin huta, domin al'amarin Mama
ya zama jiki. Tace, ya xama dole in taso yaya.
BAKIN CIKI kuwa baya taba zama jiki sai dai
imani. Allah dai ya bamu ikon cinye jarabawar, ta
nisa tace amin. Tace, yanxun me kuke ciki? Ta
fada mata yadda al-amarin yake, ta cire tagumi.
Tace haka shi yafi dacewa, in ma banda sakarci
ba ita xata taimaka mana ya turo da wurin a huta
ba. Tace ina fa, ai ina mai tabbatar miki tafi son
shi akan mu. Allah dai shi kyauta. Ta amsa da
amin. Suka ci gaba da hira har suka ji motsin
fitowar Baraka ta tashi ta shige dakin. Ba suyi
wata hirar kirki ba, domin ra'ayinsu yasha
bambam yanxun. Duk mai zagin Danliti Mama
bata ganinsa da kima haka ta fada ma baraka,
shiyasa ta shiga taitayinta, tafito daga dakin tace
xata ganin amare. Mama dataga shirinta can ta
sameta dakin amaryar Ya Ali, nan suka shantake,
sama da 2hrs sai da Inna saude ta shiryo tafiya
tasameta can, ita ma bata yi ma Mama maganar
komai ba akan abinda ta aikata. Domin a
tunaninta babu wata bakuwar kalmar da xa
agaya mata wacce bata sani ba. A wannan daren
mama tasa ido taga xuwan Danliti shiru kakeji
yasa ta jin haushin rashin dawowar abba. Al-
amarin nata cizon ta taga ba xata daure ba, karfe
goma harta goa, ta fito ta bude kofar ta fice
abinta. Ko kafin Umma ta fito taga wanda ya
bude kofar mama har ta kai kofar gidan, ganin
bata a dakin ya tabbatarma da Umma ita ta fita.
Ta nemi kujera ta xauna hannunta a kunci BAKIN
CIKI ykamar ya kasheta. Take nan taji xuciyarta
na ciwo, wani abu dum! Cikin kanta kamar xai
makantar da ita, tasbihi ta shiga jerawa ko ta
samu saukin kan. Ita kuwa mama Tunda ta
kwashi sauri bata sausauta ba sai da taje shagon
mutumin nata ta ja birki. Ayuba na xaune daga
ciki, taga kanta ta shiga tare da sallama. Ya
amsa mata ta wuce tana fadin sweetyna naciki
ne? Da sauri ya amsa mata ai bayana nan bai
gaya miki bane? Ta tsaya cak dauke mamaki, ina
yaje? Ya amsa gaskiya bai gaya min ba, cewa
yayi xaiyi tafiya kawai. Na xaci ya gaya miki
daxun. Ta kada kai, bai gaya min ba wlh, amma
xai dawo gobe ko? Yace watakila, ta danyi shiru
sannan tace to shikenan sai goben. Allah ya
kaimu. Taga kanta ta fice, ya bita da kallo. Duk
tasuayinta ya lullbe shi, aransa yace Allah ya
kubutar dake daga sharrin Danliti. To nima nace
AMEEN! Da babbar murya. Tana tafe tana sakar
xuci, wai duk fushin ne yasa Danliti yatfi ba
sallama? Ina xansa kaina idan kalaman Abba
suka korar min Danliti? Bata samo amsa ba taji
ann fige mayafinta, 'yammata ji mana! Firgigi ta
waigo hankalinta ta dubi gungun samarin da suka
kai kusan shida, kowanne su dauke yake da tabar
wiwi. Ta dora hannu bisa kai wayyo nashiga uku,
duk suka fashe da dariya, ina kika nufa mu
rakaki? Ta durkusa kuyi hkr dan Allah, dariya
kwai suke kyakyatawa, 2 daga cikinsu suka kawo
mata cafka. Ta xabura ta mike, Allah ya
taimaketa ta kutsa ta cikinsu ta xura aguje, dawa
Allah ya hada su ba da ita ba, ta watsar da
takalma, ko daman gyalen yana hannunsu, taci
gudun fitar rai, ta rufta cikin gida, yayin da alh.
Adamu, ke kokarin rufe gidan, bakara min figita
yayi ba, amma yayi axama ya maida kofar ya
jefa sakata. Mama kuwa tuni tana sassansu, ta
fadi warwas! Tana maida numfashi tamkar xata
mutu, Alh. Adamu ya biyota, ya isketa daidai
kasa, ya xura mata ido kafin yace, wai daman
mama ce kartin Maxan nan suka biyota? Me kike
a waje har 11pm? Umma tayo waje tana sallami,
ganin mama a kasa yasa ta dafe kirji lfy? Ya
dubeta ido waje, yace, yanxun saboda Allah me
yarinyar nan take a waje cikn duhu? Kinga kartin
da suka biyo sunyi su 10, wannan ai diban
albarka ne da iskanci. Jiri ya soma dibar Umma
tana fadin me? Innalillahi Wainna ilaihir raju'un
kasan Allah, Alh. Adamu har na rufe kofa naji
motsin fitarta, xaune nake kawai narasa inda
xansa kaina dan BAKIN CIKI! Ban san yadda
mama ta maida rayuwarta ba.........
Tana rufe baki, tayi kasa da dafe kirji,
saboda ciwon da yake tsananin yi mata. A
hankali hawayenta ke fita tana fadin, BAKIN
CIKIN ki zai kashe ni Mama.... Alh. Adamu ya
daga murya yana masifa, kin shiga 3 mama! Kin
maida kanki 'yar iska da karfi da yaji, to ki bi a
hankali, muddin kika bari BAKIN CIKI ya kashe
mahaifanki, kin buga babbar asara, tashi ki ba
mutane wuri, kafin in taka ruwan cikinki. Ta
yunkura ta tashi da kyar, amma ta kasa mikewa
tsaye, a duddauke ta shige falo a tym din har
mutanen gidan sun fara taruwa, don ji me ya
faru, Alh Adamu ke daga murya cikin dare? Nan
take ya maida yadda akayi har ya dora karya,
wai kartin har sun turmusheta, tsawat da yayi
masu, yasa suka gudu. Kowa tafa hannu yakeyi
yana salati, kusan 12am suna xuba magana.
Sannan kowa ya koma sasansu, aka bar Umma
kwance da ciwon abubuwa barkatai. Ya ali ne
kadai bai tanka ba, don BAKIN CIKIN sa na gaske
ne, tamkar yadda UMMa takeji cikin xuciyarta.
Dakin amaryarsa ya koma yana kuka da
hawayensa. Amina tayi rarrashinsa tana nuna
masa addu'a Mama tafi bukata ba kuka ba.
Mts!.... Amina ba zata gane ba, BAKIN CIKIN
dake cin angonta ba xai iya jurewa ba, tilas sai
ya matse shi. Hasalima ba zai iya zama yana
kallon irin wadannan abubuwan ba, gara ya koma
bakin aiki ko ya kauracewa idanuwansa ganin
abinda ya fi komai daga masa ciwon xuciya.
Saboda haka yacewa amina ta shirya kayansu
gobe zasu koma birnin gwari da yardar Allah.
Al'amarin ya daure mata kai, kuma tayi
tambayoyin da bata sami amsarsu ba. Washe
gari da suke shirin tafiya, taji fashin baki na
bakin Haj. Hajjo. Eh lallai biri yayi kama da
mutum. Nan take kumallon mata ya taso mata,
ya dasa mata kyamar Mama cikin ranta har tafi
Ya ali kosawa su bar garin. 12pm kuwa ya samo
shatan mota suka damki hanya. Mama bata ma
san anayi ba, tana can tana murkususun ciwon
ciki ita kadai a daki. Don ko daya shigo yin
sallama da umma bai shiga wajenta ba. Sai
wajen azahar barci mai nauyi gaske ya dauke ta.
Haka ita ma Umma ke ta gyangyadin takaici bisa
kujera. Rabonta da abincin kirki tun jiya da
daddare motsi taji a falo ana shigowa da kaya, ta
taso da sauri ta leko falon. Kalla ta gani da tsirin
kwalaye ya aje gefe yana gaisheta. Ta amsa da
fara'a ta karfin hali. Bai karasa ficewa ba, abba
ya kawo ka falon tilas ya rabe gefe ya bashi wuri
ya shigo, sannan ya fice. Alhajin yana fadin,
agaida Iyali, yace xasu ji. Kallo daya yayi wa
Umma gabansa ya fadi, ya amsa sannu da
xuwan da tayi masa. Ya xauna falo. Yayi da ta
shiga kitchen dauko masa ruwa ta kawo masa ta
xauna gefe tana kara masa sannu da xuwa.
Bayan yasha ruwa ya numfasa. Tace an dawo
lfy? Ya amsa lfya lau, duk suna gaisheki, ni ne
har abuja, daga can na xarce kd yau da safe.
Tace, wai kunsha hanya, ina fatan duk lfya ka
baro su? Yace kalau, amma sai naga kamar kin
rame, ina fatan ba ciwo ne ya tashi ba? Ta kada
kai. Kai dai bari Alhaji, ciwo na ba zai taba
warkewa ba, idan ban ga yarinyar nan dakin miji
ba. Kaci abinci tukunna, kaji abinda ya faru jiya.
Yayi dan shiru har ta mike xata dauko abinci kafi,
yace ki gaya min kawai Halima, nasan babu
bacin ran da xanji wanda ya wuce na baya. Ta
dawo ta xauna ta fede masa abinda ya faru. Ya
kada kai. Yace ya rage nata, ba burinta ta fita
duk tym da ta ga dama ba? Jikinta xai gaya
mata, xata gane akwai wadanda suka fita
iskannci. Yanxun tana ina? Tana daki, ni yau ko
kalarta ban gani ba. Bata xo ta gaisheki ba ke
nan? Tace ni a suwa? Bana ma bukatar
gaisuwarta, amma tun jiyan na gaya mata idan
na mutu, ta sani BAKIN CIKIN tane ya kasheni.
Yace, ba xaki mutu ba Halima da Yarda Allah
mama ba zata salwantar min da rayuwarki ba.
Karki manta, su hudu kika haifa, kuma Allah ya
albarkace su dubi tsibin kwalayen nan, duk
sakonki ne, kowa na da sa nau'in tsarabar, zabi
kalar abubuwan da kika fiso. Bayan haka, jibi
asabar duk zasu hadu anan, don su share mana
hawayen kukan da Mama ta samu. Don kuwa zau
tsaya tsayin daka dole Danliti ya turo wakilnsa a
daura masu aure a cikin satin nan. Saboda haka
ki kwantar da hankalinki, ki na dasauran 'yal3an
da suke bukatar ki kusa da su a koda yaushe.
Kinji ni da kyau? Ta goge 'yar kwallan da suka
xubo mata, tace naji alhji, Allah yayi musu
albarka baki dayansu. Yayi murmushi yana fadin,
amin kina iya dauko abincin yanxun. Ta tashi da
saurinta, ta wuce, ya raka da ido tausayinta ya
kwarara cikn ransa. Ya numfasa yace, mun gode
maka Allah da wannan jarabci. Ta fito masa da
abin, ya gaugauta ci, domin gab ake da kiran
la'asar. Ya kammalawa kuwa tym yayi, ya mike
yana fadin, ki shiga ki tasheta tayi sallah. Ta
amsa da to, ya wuce dakinsa. Umma ta kwashe
kayan ta maida kicin, sannan ta nufi dakin
Mama, don tashinta. Tana kife ruf da ciki, Umma
ta dada mata duka ta tashi a firgice. Umma ta
xura mata ido, tace, in kin ga dama ki tashi kiyi
sallah! Tayi waje ta bata wuri. Da kyar ta mike
zaune, kanta ya sara mata, ta dafe shi hannu
biyu, gaba daya miyan bakinta ya kafe. Makoshin
ta ya bushe. Tana daga xaune, amma jiri ne ke
dibar ta....
Idanuwanta na ganin duhu, don haka ta
runtse su tamau! Tana maida numfashi, ta wuce
minti sama da goma ahaka, sannan ta iya tashi a
daddafe ta shiga bayin. Tunaninta kawai tayi
wanka ko tafi jin dadin jikinta. Nan da nan ta
kwashi ruwa a bokiti ta fara wanka. Kamshin
sabulun( Joy) Ya gauraye bayin, ba xato ba
tsammani taji xuciyarta ta tsani kamshin, kan ka
ce kwabo ta goce da amai. Ta kwarara mai
isarta, wai don ma babu komi cikin nata. Tana
gamawa ta dauki bojitin ta juye ruwan ajikinta,
tun daga kai. Ta jefar da shi ta yayo xani ta
daura, ta banko kofa ta dawo daki, ta bar bayin
face face da amai. Ruf da ciki ta sake fadwa
gado fadi take, wash! Wayyo Allah xan mutu! Tun
daga tym din al'amura suka kwance mata, ta
rasa kanta ta rasa meke damunta tana rashin
son abinci da yawan tashin xuciya, ga wani cikin
safe da jiri wani tym din jikinta yayi xafi, don
kansa kuma ya sauka ba tare da tasha magani
ba.
Duk ba wannan bace babbar Matsalarta
ba, Ina Danliti ya shiga kwana 2 babu labarinsa?
Me kuma yake nufi da tafiyarsa? Duk da cewar
tasan dole ya dawo, idanuwanta da xuciyarta sun
gaza jure rashin sa na 'yan kwanakin 2. Shi yasa
koda yaushe tana kunshe a dakin matsalolinta
masu yawa na neman xautar da ita. Umma da
kanta bata gane kanta ba, musamman rashin
xuwanta neman abinda xat ci. Amma yawan
xaman daki umma ta jingina da rashin ganin
Danliti da ta rataywa xuciyarta, balle ayi maganar
jingina shi da wanccan Matsalar. Ta kan kada
kai, tace, kaico! Abincin wani, gubar wani! Allah
ka raba mu da muguwar kaddara... A yau asabar
ake sa ran xuwan yayyin Mamma, ga shi babu
magana mai kwari ko kuma muce uban gayyar
baya gari, shi da kansa abba xaune yake shiru
dakin ta same shi, ta xauna gefensa tace, kana
xaune baka shiga wanka ba? Yayi gajeran tsaki,
yace maganar nan ke damuna, da yarinyar nan
xata gane da ta amince cewar Dalinti ba xai turo
kowa ba. Banda aikin rashin gaskiyya, menene na
kama hanya kabar gari, kai da aka ba damar ka
aiko a baka mallakar abinda kake so. Wane bata
tym xakayi saboda Allah? Ta numfasa, tace
yaushe xata fusknaci hakan yadda ta makance
gaba daya, bata ganin kowa sai shi? Ai na gaya
maka ko abinci bata ci, duk ta fige saboda bala'i,
ni yaran nan ma dasu wahala suke nake
tausayawa ba su gama warware gajiyar biki ba,
ga aikinsa mai dan banxan wahala, da da halin da
xa'a ce da su dakata, wlh da ance suyi xamansu.
Ya gyara xama kyale su suzo ko hira mukayi, ai
maji dadi, ko ba haka ba? Haka ne, Allah ya kawo
su lfya. Amin ke ki kira min Mama ta zo yaushe,
dan liti xai dawo? Ta mike ta nufi daki Mama ta
tura kofa kakarin amai ya fara dibar hankalinta,
cikin fargaba ta nufi kofar bayin ta murda ta
bude, Mama! Tana durkushe kame da ciki, kamar
xata mutu. Kan Umma ya kara daurewa, domin
bata taba ganin Mama na kwarara amai haka ba.
Ko rashin lfya takeyi, bata amai, sai dai xafin
xaxxabi. Don haka ta nufe da sauri ta dafe ta, me
xan gani haka Mama, baki da lfya ne ko yaya ne?
Bata iya amsa mata ba, tana tsaye kame da
haba, tagama kakarinta, ta kuskure baki hade da
fuska, tayo waje abinta, ba tare da kula Umma
ba. Bisa gado ta fada ta datse ciki tana
numfarfashi. Umma ta biyo a fusace tasa hannu
ta birkito ta, ba kyajin ina magana ne? Nace lfya
kike sheka amai? Ido jajur! Cike da kwalla tace,
cikina ke min ciwo, tun yaushe? Yau 3days. Ta
jawo ta waje cikin haske sosai, ta kama
hannayenta ta dudduba, sannan ta gwale
idanuwanta, ta duba cikinsu, a tsorace ta
tambayeta ke, kina yi al'ada kuwa? Tayi shiru
tana xaxxare ido, baki na rawa tace, nima ban
sani ba Umma. Ba ki sani ba? Ke xaki gaya min
ko sai na farfasa bakinki? Ta goce da kuka, don
ita ma ta kideme, ta mance rabonta da a'alada.
Umma ta xura mata ido, jinin ta na kara
hauhawa, da sauri ta wuce ta bar mama tsaye.
Dakin abba ta koma ta xauna, ta rike kai tana
maida salati. Me akayi? Tace alh. Magana takare
ka dauki mama ka kaita asibiti ayi mata
gwajegwaje! Gabansa ya fadi gwajegwaje? Name
kuma? Na komai Alh. Ina shiga na sameta tana
sheka amai a bayi, wai cikinta ke ciwo, amma
alamu a bayyane sun nuna Mama juna 2
gareta........ Tsaye ya mike tare da fadin me?
Hawaye suka kara tsunke mata, ya koma a
hankali ya xauna bakin sa na karanto salatin
Manxon rahma. Gaba dayansu tsit! Sukayi
tsawon lokaci sai Umma ke shatatar hawaye,
baiyi aune ba kawai ya ga ta dungura ta fadi a
sume. Ya xabura ya tarairayota, yana kiran
Halima! Halima!! Don girman Allah karki kara min
tsahin hankali akan wanda nake ciki, ya jawo
goran ruwa ya xuba a hannunsa, ya yarfa mata,
ya cigaba da shafa mata ruwan bisa fuska,
ahankali har ta dawo hayyacinta. Ta bude ido,
jim tana kallonsa, sannan ta sake fashewa da
kuka, nan take tausayinta, yasa kwallan
Ubandawaki suka fara sauka bisa kuncinsa.
BAKIN CIKI kamar ya aika shi barxahu. Kiyi hkr,
ki kwantar da hankalin ki Halima, wannan
jarabawa daga Allah Ubangiji take, babu wanda
ya isa ya kankare mana ita, bana son tsanin
damuwar nan da kikeyi, tana jefa ni mummunan
matsayi, ko dogara da Allah Halima shine xai
magance mana komai. Ta goge hawayenta tayi,
iyayinta don ta tashi xaune amma ta kasa. Yace
kar ki damu da sai kin tashi yanxu kiyi
kwanciyarki ki huta, bari in kwaso magungunan ki
in duba wanda ya dace kisha. Ya mike da sauri
wani duhu ya rufe masa idanuwansa, bai ganin
komai face wasu miliyoyin taurari kanana, tilas
ya dawo ya xauna ya fadin Hasbinallahu wa
nimal wakil. Yayi ta maxa ya sake mikewa.
Umma tace ka xauna Alhaji kar kaje ka fadi ka
nakasa. Bai tanka ba, ya fice. Jimawa kadan ya
dawo da kwanndon magungunan ta ya xauan
yana bincikawa, jikinsa na rawa saboda bacin rai.
Sallama sukayi daga falo kuma babu tantama
muryar Ya abdurahman ce, abba Ya amsa, ya
kara da fadin gamu nan, ku karaso ciki. Ganinsu
jugun2, Yaya take ya rasa kuzarinsa. Yaya dai
Abba? Jikin nata ne ya tashi? Yace shine
abdulrahman, nan da nan ya xube gabanta, da
dauko kanta ya dora bisa cinyoyinsa, sannu
Umma! Sannu!
Ta matse kwalla, ta dube shi, kaxo lfya?
Ina safiyya? Ya amsa lfya lau take, tace in
gaisheki. Ina amsawa, me yasa baka xo da ita
ba? Ya goge mata kwalla, tayi nauyi ne Umma
bata jin dadi, idan tayi doguwar tafiya, koda muka
koma, bayan daura aure sai da tayi xaxxabi. Ta
dan kada kai, tace Allah sarki, Allah ya raba su
lfya. Amin. Ya amsa sannan ya dubi Abba suka
gaisa. Kafin su kama wata maganar, muryar
Manyan yayin ta gauraye cikin falonm. Abba ya
gaya musu suna ciki, kowa ya shigo da kuzarinsa,
ya ga Umma a kwance sai yayi turus! Bayan sun
gaisa tasha magani. Abba ya kwashe abinda ke
faruwa kaf, ya gaya musu, kowa yayi shiru,
kawunansu sunkuye tsawon tym kafin Ya soja,
yace, yanxun Ina Maman take? Oho inji Abba,
gaba daya sukace oho? Ta bar gidan nne, Umma
tace tsakar gida na barya tsaye, ban sani ba ko
ta koma daki ko ta fice don ba sani xamuyi ba.
Duk tym din ta so fitarta, ficewa ta takeyi.
[12/01 21:55] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***14
Ya soja ya dubi Ya abdulrahman, yace
je ka kawo mana ita nan! Ya miki cikin hanxari,
ya nufi dakinta, tana kife bisa gado aikin kuka
kawai takeyi. Ya sa hannu ya fisgota, ba karamin
tsoro ya bata ba, ta kwala ihu, wani BAKIN CIKI
ya kara turnuke shi, bai san tymda yasa hannu
ya doke bakinta ba, yace rufe mana baki
shashasha. Da sauri ta kame baki, wanda take
kyautata xaton hakoranta xasu iya xaxxagow
idan bata dafe shi ba. Ahaka ya ciga da jan ta
har dakin abba. Gaban babban ya direta, ta xube
har tana karo da guiwarsa. Ya xuro mata ido
kamar zasu fado kasa. Yace matsa kdaga kusa
dani, xan iya tokarinki, ki mutu idan baki matsa
ba. Ta janye jikinta baya, ahankali hawaye na
ambaliya, sunfi minti 5 babu wanda tanka saboda
takaici, kafin Ya abdulkrm yace, gaba daya kin
rusa rayuwarki Mama kin lalata cikar asalinki da
martabar iyayenmu. Yanxu wa ya isa ya kankare
bakin fetin da kika shafawa kanki? Wa ai daura
miki aure da ciki? Wa kuma xai jagoranci kisan
kai? Wannan cikin dole ki haife shi, domin
yunkurin xubda shi, ya fi yinsa barna da tarin
xunubi. Kin ga tun daga nan idan kinyi tunani
cikin hankalinki, xaki gane babu soyayysa
tsankaninki da Danliti. Burinsa dama ya ruguxa
rayuwarki, burinsa kuma ya cika tare da hadin
kanki. Saboda haka dabara ta rage wa mai shiga
rijiya, sannan karki xargi Danliti, idan ya tsallake
auranki, gaba daya abinda yake bukata ya samu,
abinda yai saura shine ki haife masa wannan
ckin, in ya ga dama ya karbi dan, idan bai yarda
ba ya kyaleki da shi, ku wulaknta. Dama wannan
shine karshen son xuciya. Babu uwar kudi balle
riba ga mai cinikin son xuciya. Kuma duk wanda
ya hau motar kwadayi da son xuciya, babu
tantama tashar kunya da nadama xata kaishi ta
aje. A koda yaushe karshen danasani, ina fatan
wannan xai xama darasi gareki, ki gane cewa
abinda Babba ya hango, yaro ko ya hau gwauron
dutse ba xai hango ba. Ya goge 'ya kwallan da
suka xubo bisa kuncinsa sannan ya sauke
numfashi ya dubi sauran, yace yanxun mene
abinyi? Abba yace abinyi babu shi abdulkrm,
tunda maganar aure ta rushe a halin yanxun. Ya
Soja yace duk da haka, dole ya san tana dauke
da cikinsa, bayan ta haihu xa a daura musu aure,
su tare da yaronsu! Su karata can da abin
kunyarsu! Ya abdul rahman ya kara sanyaya
muryarsa mai taushi, yace wannan dole ne,
amma abu na farko shine, ina xata xauna? Ta
kula da kanta? Umma dai ba xata jure ganinta a
wannan yanayin ba, ya soja ya gyara zama yace,
gaskiya ne, kuma waje na ya kamata ta xauna,
sai dai ba xan iya daukarta ba saboda xan iya yi
mata dukan mutuwa yadda nake jin na tsani
ganinya. So a cikinku, wanda yake ganin xai iya
hkr da ita, yana iya tafiya da ita Allah ya
shiryeta, mu kuma kullum addu'a muke mata,
idan ta dauki wannan mtsayin darasi a gareta,
xamu fi kowa farin ciki. Ya Abdulrahman, yace ni
xan tafi da ita, no ka bari ni in wuce da ita
Minna. In ji Ya abdulkrm. Abba yace ba xata biki
ba nan da xata xauna...
ban ce mata yin ku za su yadda ta ba
amman yau da gobe sai Allah. gara ta zauna
anan, domin anan ne suke aikata abin kunyar u
kun ga ganinta da juna biyu ba zai girgiza kowa
ba sanin cewar daman can sakamkon da zai biyo
baya kenan. in ba wani gyaran Allah ba. saboda
haka ku kwantar da hankalinku kuci gaba da yi
mata addua sannan ku kwantar da hankalinku ku
tallafa wa mahaifiyar ku ta kowace fuska don
ganin ciwon BAKIN CIKIN bai tagayyara ta ba,
dukkan su suka jinjina kai alaman uban dawaki
gaskia ne. yaya soja yace da yardar Allah umma
ba za ta tagayyara ba, idan mama bata son ki mu
bamu da wacce ta fi ki. bamu da wani buri. da
ya wuce mu rayu tare da ke. kar bacin ran mama
yasa mu dakatar da dukkan farin cikin mu. mu
ukkun nan mun ishe ki kallo ki samu sanyi a
ranki ko umma? hawaye na suka malalo mata
yaya abdul yayi maza ya rungumota ya na share
mata hawayen ki daina kuka umma in kina kuka
mama ba zata taba ganin haske ba, duk adduar
da zamu mata tace ba komai wallahi bana
jayayya da ikon Allah amman ku sani BAKIN
CIKIN ba zai goge cikin raina ba, domin FARin
ciki da bakin ciki duk halitta ce cdaga Allah fata
na kawai Allah ya bamu ikon cinye jarabawarnan
Allah yayi maku albarka
Kowa ya numfasa, yace amin, abba ya
dubi mama da hawayenta yaki yankewa yace, ina
fatan kin ji abubuwan da 'yan uwanki suka fadi,
idan kinyi anfani da su, ki ga daidai, idan kuma
kin ce ba haka ba, mu babu abinda xamu iya yi,
sai mu kyale ki, ki ci gaba da rayuwar da kika
xaba. Ko dama kin riga kin ruguza ta, karashe ne
kawai. Allah ya shiryeki, ki na iya bamu wuri mu
sha iska, ki jira dawowar Danliti, amma ki sani
auran ku ba shi yuwuwa, sai bayan kin haihu.
Tashi ki bamu wuri. Ta kara makurewa, kukanta
ya karu, duk suka xubo mata ido. Ya soja yace
wa yace kiyi kuka? Cewa akayi mun gaji da
ganinki, ki koma dakinki. Ta yunkura kamar xata
tashi, amma ta kasa, da sauri ta rarrafa jikin Ya
abdulrahman, ta kudundune ta rushe da kuka.
Nan da nan ta karya masa xuciya, ko dama shi
akwai sanyi da saurin jin tausayin mutum.
Idanuwansa suka cika taf da kwalla, tun baya
son kulata har ya kai hannunsa, bisa knta
muryarsa na rawa yake fadin, imani kawai xai sa
akalleki Mama, amma ke ba abar tausayi bace,
tunda baki tausaywa kanki ba...... Ya soja ya
katse shi, pls abdulrahman, fita da ita, Umma
tace sai ma ya fita da ita? Gata kenan, ya
kyaleta, ta tashi da kanta ta wuce. Ya tarairayo
ta suka mike tare, ya janyo ta xuwa dakinta ya
xaunar da ita bakin gado. Ya tsugunna gabanta
yace, dube ni Mama. Da kyar ta dube shi,
hawayen ta na xuba, yace kukanki bai da wani
anfani, muddin ba nayin nadama bane. Nadamar
ma ta gaskiyya, tsakani da Allah. Saboda haka
ina shwaratar ki da ki kama kanki, wannan ya
xama na farko kuma na karshe. Ba soyyaya vace
wannan, ki dauki jikinki ki ba da ga namiji, daga
ranar da ya sanki a waje. Wlh kin gama yawo,
duk wulaknci da ya ga dama xaiyi miki, ko da
kinyi sa'a ya aureki, abanxa xai rika kallonki,
sannan wulakanci ba xai daina shi ba, a karshe ki
ga auran ya bantale, tun ba aje koina ba. Kuskure
ne, kin riga kin yi Mama, irin wanda bamu taba
xato ba, babu yadda xa muyi mu gyara shi, sai
dai kiyi tuba wajen Allah, sannan ki nemi
afuwarsu Abba, kin jini? Ta xura masa ido,
hawaye na ta bulbula ta kasa fadin komai, domin
ita kanta bata san ainihin abinda ke damunta ba,
cikin ranta agame da samun ciki ba tare da aure
ba. Saboda haka, sake fado masa tayi, ta
kankame shi, kukan ta kamar xai fasa xuciyarta.
Ba karamin rikita shi tayi ba, domin nan take ya
goce da kukan shi ma. Da kyar ya banbare ta ya
mike da sauri ya bar dakin, ya dawo falo ya
cigaba da gugar kwalla, xuciyarsa na masa ciwo.
Kai! Sun dandani BAKINCIKI, da akwai yadda
xasuyi su goge wa Mama wannan bakin fentin da
sun goge mata shi, ko da shi xasu rasa komai
nasu. Sai dai kash! Babu hali, shi ya sa ko abinci
tsakurarsa sukayi suka ci, ba don yayi musu dadi
a baki ba. Haka suka juya bayan sallar la'asar
makare da BAKIN CIKIN da baya misaltuwa.
Haka zalika sun bar Mama cikin wani yanayi na
kunci rayuwa, wanda ya wanxar mata da
cututtuka masu dama ajikinta. Kafin yamma ta
fadi, kamar ba ita ta dawo Legos dambasheshiya
ba. Sati 2 kenan yau babu labarin Danliti, yayin
da rashin lfyar mama ke cigaba da yaduwa
tamkar yadda labarin samun cikinta ya gama
baza gari, ta bakin Hajiya Gaje. Amma don tsabar
yaudara su suka matsawa Mazajensu su akan su
kai ta asibiti ko ta sami dan taimakon da xai rage
mata larurar jikinta. Da kyar abba ya amince.
Alh. Basir ya kaita babban asibiti da garin
Kagara. Suka ga likita, yayi gwaje gwajen sa ya
gano, lalurar shigar ciki ne ke wahalar da ita.
Saboda haka ya bata 'yan taimakon da xasu rage
abubuwan da take ji a jikinta, sauka dawo gida.
Sun wuce kofar shagon Danliti shi kuma yana
karasowa wajen. Yayi fakin ya fito tare da yin
daguwar mika mai isar da sakon gajiya. Ayuba ya
fito ya tarbe shi, sai dai fuskar sa babu fara'a ko
alama. Yaya dai mutumina? Naga kamar kana
ciwo? Ya numfasa, amma bai tanka ba har suka
shige shagon. Ya dube shi da kyau, yace ina
magana ka kyaleni, lfya nace? Ya kara sauke
numfashi. Yace ina fa lfya, magana ta cika
gari..... Ya katseshi Mama na da ciki ko?
Gabansa ya fadi ya saki baki yana masa kallon
Mamaki, Dan liti ya kece da dariya, kwalla na
gangara bisa kuncinsa kafin yace, shiege ni, dan
buzu mai shayi. Raina kama gaiyya, ka tabani ka
ga tsiya. Watau labari har ya bazu ko? Kaga
burina na farko ya cika, amma har yanxun akwai
saura, don na san dan xagin kalilan za'ayi mata.
Ido jajur! Ayuba yace, kaji tsoron Allah Danliti, ka
kyale yarinyar nan haka. Tunda ba xaka aureta
ba, ka barta taji da wannan bala'in! Ai ka gama
ruguzamata rayuwa, babu sauran wulakanci da
yafi wannan.....
Ya ja Kujera ya xauna, yace haka kake
gani, nasan akwai saura, sai dai ba xan shanye
maka dadin labarin ba, idon ka nake son ka gani
kamar yadda ka ga wannnan. Ya bishi da kallo,
yana kada kai. Murmushin keta Danliti yayi, ya
sake fadin, babu wani abu mutumina, kai kanka
kasa ramuwar gayya, tafi gayya xafi. Dadin abin
a gabanka mama ta xageni, ta xagi Mahaifina, ka
manta kawai! Yace wannan ba hujja bace Danliti,
ina gaya maka barnar da kakeyi tayi yawa. Allah
ba xai kyaleka ba. Ya ja dogon tsaki ya mike
tsaye, kai wannan ya dameka, ni yanxun gidan
ma xani kuma lfy lau xaka ga na dawo, see you!
Ya juya ya daga kanta ya fice abinsa, ayuba ya
koma a hankali, ya xauna ya dora tagumin
mamaki da takaici. Danliti ya sake gani ya dire
masa bakar leda tare da kwalin juice kato bisa
kanta. Yace ga sauran kazar da na ci a mota
nan, idan ka gama laulayin, ka ci. Ya juya ya
wuce mota, yayi tafiya sa ya bar shi da tagumi.
Kansa tsaye yayi fakin kofar gidan Uban dawaki,
akwai yara gidan suna wasa, don haka bai yi
wahalat neman yaro ba, take nan ya aika yana
kiran Mama. Yarinyar ta shiga, jim kadan ta fito
ta gaya masa tana xuwa. Yana nan jingine da
mota yana kada makullai. Abba ya fito. Nan da
nan ya tsuguna kai sunkuye, mummunin kare
kenan. Yace, ah! Sannu abba, ina yini? Abba ya
bishi da kallo, amma kash, ya kasa ganin bakinsa
balle ya gaya masa bakaken maganganu. Ya
amsa gaisuwasa, sannan yace mike ka biyoni. Ya
wuce kofar falon bakinsa, ya murda ta bude suka
shiga, xauna, ya nemi waje ya tankwashe
kafafuwa. Abba ya xauna ya dube shi da kyau
yace, yanxun saboda Allah Danliti abinda kayi, ka
kyauta kenan? Me ya sa duk abinda xakuyi baku
sa tsoron Allah a xukatanku? Ya xa kace kana
son yarinya da aure, sannan ka aikata mata
abinda ba shine ba? Danliti ya kara sunkuyar da
kai, kamar xai tsaga kafet din falon ya shige don
gulma, abba ya ciga da cewa, to ta faru takare,
ahalin Yanuxn Mama juna 2 gareta, kaga xancen
auranku ya rushe kenan dole tayi zaman istibra'i
xuwa tym da xata haihu. Wannan abu ya bani
kunya kuma kun xubar min da mutunci da kima a
garin nan. Hannaye 2 Danliti ysa ya rufe fuskarsa
yayi xugum, ko mtsi ba yayi. Abba ya numfasa
ya kada kai ya cigaba, ni bani da abinda da xan
iyayi, tunda kaddara ta riga fata, abinda kawai
nake soka sni, shari'a ce ta tsara haka, saboda
haka dole ku kauracewa juna, don gudun karku
kara maida hannun agogo baya. Ina fatan kaji?
Sai ka koma jira ranar da xata haifamaka danka,
kaga kun sami dan aike, ba sai kun nema ba.
Kana iya tfiya, mu jira abinda Allah xaiyi.
Shawara da xan baka kawai, ka nemi tuba wajen
Allah, domin ka saba masa, ka keta rigar
mutuncin yarainya. Shiru yayi ya kasa tashi, abba
yace tashi mana, ni nakare magana, ya dago kai
da kyar, amma bai kalli fuskar abba ba, cikin
sanyin murya yace, abba kayi hkr ka yafe min?
Wlh sharrin shaidan ne. Ya goge kwalla, abba na
kallonsa kafin yace, haka ne, amma wani tym har
da son xuciya. Si yasa nace ka nemi tuba wajen
Allah, don ta ni mai sauki ne. Ya kara
rankwafawa yace, je ka kawai. Ya tashi simi simi
ya fice babu ko waige. Abba ya raka shi da ido,
sannan ya numfasa ya kada kai, yace Allah ya
shirya mana. Shi kuwa Danliti yana fita yayiwata
'yar girgiza ta jin dadi, ya wuce motarsa cike da
farin ciki ya koma shagonsa. Ledar kazar da ya
ajewa ayuba suna nan bisa kantar bai taba ba.
Wai don ya ba ayuba haushi sai ya dage kantar
kayan suka watse kasa. Ayuba ya bishi da kallon
kafin ya ce ni baka ban haushi ba don ka xubar
kudinka ne, ba nwa ba, gaskiyya ce dai ba xan
daina gaya maka ba, watakila ma baiji shi ba,
domin bai tsaya ya saurare shi ba, cikin daki ya
shigr. Yayi kwance yana tunanin shirinsa na gaba
akan mama. Abba kuwa ys jima falon xaune yana
tunani rayuwa kawai. Sannan ya mike da kyar ya
koma cikin gida, ya maida wa Umma yadda
sukayi da Danliti ta kada kai tace , shikenan,
Allah yasa ta nutsu ta xauna gidan. Yace amin,
amma ina mai tabbatar miki muddin tace ba xata
nutsu cikin gida ba, xan bata mamaki, domin,
dole ta xaba ko mu ko shi. Umma tace gaskiyya
ne, ace wannan abu ya sameka, baka yi nadama,
ai kuwa sai a sallama mutum asa masa ido. Allah
yasa mu dace. Ya amsa da amin. Tunanin uwar
gayyar ba anan yake ba, domin kuwa jin ga
Danliti yana kiranta, ya tabbatar mata da cewar
ya dawo kuma taso ta ganshi, su Abba suka taka
mata birki. Duk da haka taji karfi a jikinta kwarai
da gaske, har wasu daga cikin cuttuttukan da ke
damunta suka yaye nan take. Sai dai tana ganin
babu adalci a hukuncin dasu abba suka yanke. A
zaton su zan iya zama tsahon tym banga
masoyina ba????????
Ta tabe baki tana daga kwancw tace,
ba xan iya ba gaskiyya, sai dai suyi hkr wlh. Ai
dai maga juna, ya san halin da nake ciki, ya
tausaya min. Ta goge kwalla ta cigaba da sakar
xuci. Ana ta sallar magriba, tym ne da ita mama
ta sami damar satar jiki ta sulale ta isa shagon
danliti. Shi kuma kaida ke xaune cikin shagon.
Ayuba ya shiga sallah. Yana ganinta ya dafe kirji
ya wani lumshe ido. Yace wayyo Allah na gode
maka! Ta daga kanta ta shiga, ta nemi t barma
ta zauna, saboda bata jure tsayuwa. Tana xama
ta hade kai da guiwa ta fasa kuka ya kare mata
kallo, a dage yana dan murmushi, sannan ya taso
ya dawo gunta yace haba bebina! Meye abin
kuka? Ya xauna gefenta ya rungumota jikinsa,
bana son kukan hakan nan....... Ta cira kai da
sauri ta dube shi, ba xanyi kuka ba? Ciki fah
gareni, kowa ya tsaneni ana ta zagina. Shine
xaka ce ba xanyi kuka ba? Yayi dan murmushi
yace, bebi kenan, to don kowa ya tsaneki shine
me? Bayanni ina son ki kuma ina son ciki na!
Kina so yi kukan ne, wata kila kuma na dadi ne
yayi miki yawa. Ta mako masa harara tace, jin
dadi? A zageni, a tsaneni shine jin dadi? Son ka
ne kawai yake sawa bana damuwa, amma kai ina
ganin abin baya damunka, daya dame ka, da
baka wanke kafarka ka bar garin ba, tsawon sati
2, alhalin an ce ka turo a daura mana aure. Da ka
maida hankali ka turo din, ai da duk hakan bata
kasance ba, koda cikin xai bayyana adakinka xai
fito. Tunda ni ban ma taba nuna wa akwai wani
abu tskanin mu ba. Sannann.... Ya da ka mata
tsawa, ya ida don Allah! Haba! Wannan maida
xancen na menene? Ko kuwa turo ki akayi ki zo
ki batan rai? Ko dan kinga ina ta rarrashinki?
Babu fah dole, kin ganne? Abban ki cewa yayi ba
dole bane ya bani ke, ko bayan kin haihu. So pls
ki daina damu na da irin wadannnan surutun
banxan, ban son jinsu, idan har kin son mu
shirya! Kin gane? Ta xura masa ido hawaye na
xuba, ta ma rasa me zata ce? Ayuba yayo
sallama ya shigo ya riske su cikin wannan halin.
Shi ma yayi tsaye yana kallon su, jim kadan
Danliti ya buga tsaki ya tashi ya shige daki ta
goge hawayen itama ta tashi ta bishi, ayuba yaa
kada kai ya ja kujera ya xauna yana fadin Allah
ya kwaci yarinyar nan. Tana shiga ido ya xubo
mata. Yace au biyo ni kikayi? To ranki xai baci
kuwa, gara ki koma. Ta marairaice tace, kayi hrk
Danliti, ba don ranka ya baci bane ya sa na gaya
maka abinda ke damuna. A xatona xaka tausaya
min a halin da nake ciki. Bani da wani gata wajen
iyayena. Tun ranar da na nuna kainake so Danliti,
ka tausaya min. Yayi lum da ido ya bude, ya
cigaba da kallonta tana tsiyayar hawaye kusan
3mins sannnan ya yafito ta da hannu, yace xo
nan! Da sauri ta isa gunsa, ta fada jikinsa ta kara
fashe da kuka. A'a, kinga ni fa kukan ne bana so.
Yanxu menene damuwarki? Ta goge hawaye,
tace kullum in rinka samun kulawarka, hakan shi
xai tabbatar min da kana sona kana son abinda
ke cikina. Yayi dan murmushin nan nasa, ya kara
janyo ta jikinsa, yace, kin samu bebi, karewa ma
da kewarki na dawo. Kin ci abinci? Ta kada kai,
saboda me? Bana iyawa ne, jikina gaba daya ya
canza, sai amai kamar xai kasheni. Yace ayya
sorry ko? Amma duk da haka ba za a rasa abinda
kike sha-awa ba, gaya min in nemo shi, na kosa
in kore kishirwata. Ta mako masa harara, ya
kyalkyale da dariya, meye na harara ta? Ko ke
ma xaki min BAKIN CIKI ne, irin na 'yan sa ido?
Masu shiga tsakanin masoya suna son suga
bayansu. Haushi su nake ji wlh. Tace ai ko ni din
ma haushin su nake ji, ah haba? Wlh kaji na
rantse. Ya cacume ta tana dariya tana fadin, ban
da lfya Danliti, bai saurare ta balle ya tuna ya
nemo mata abinda take son ci. Karfe 8 ya fito ya
barta can kwance tana murkukusun ciwon ciki,
ya wuce waje wani mai suyan nama, ya karbi
danyan naman da yasa ya aje masa. Ya dawo ya
bade shi da magani, ya maida cikin leda ya
nade. Yana xaune bakin shgo bisa benci, yana
tunanin tafiya yayi wanka ko ya samu yayi
sallah. Mama ta fito tana yafa mayafinta, ya bita
da kallo yana murmushin keta, ya cikin? Tace
yayi sauki ni xan koma gida sai gobe. Haba haka
da wuri? Yanxun fa 8 ta wuce? Kar a neme ni ne.
Wa xai neme ki? Don Allah xaumna muyi hira, ba
wanda xai nemeki, bayan sun san kina nan. Bata
da xabi, don haka ta xauna kusa dashi, ya shiga
bata labaran banxa. Jimawa kadan wani kare ya
xo gilmawa nan take ya hau kiransa, tace me
xakayi da kare kake kiransa. Kasan karen
okundiri fada gareshi ko?
Yace bai sami nama bane don ubansa
okundiiri, ya kece da dariya, okundirin ne ubansa?
Lallai ka samo shi. Yacee to da waye ubansa?
Kinga bude ledar nan nama aciki dauko ki ba shi.
Yana magana yana shafar kan karen. Tace, taf
ya cafke min hannu? Kai dai ka bashi kai da ka
siyo masa,don raka asara. Yace karki bani kunya
mana, me xai sa ya cije ki, bayan yasan ke
bebina ce, ko kare? Ai ka santa ko? Sweetheart
dina ce kar ka cije min ita. Tuni kanta ya fasu,
ya jawo leda ya bude ta dauko katon yanka ta
mika masa tana fadin, abin har da yaji? Sangarta!
Ya kwashe da dariya, yace ina ruwanki? Ke dai
mika masa gudan. Ta dauko ta mika masa, ya
cafke, Dan liti ya runtse ido yace yes! Ya xarce
da dairya. Ta xuba masa ido tace, menene abin
dariya har da wani cije labe? Yace ji nayi kamar
ya hade da hannunki ya gartse. Takai masa bugu
a kirji tace amma kai mugu ne! Yace sosai ma
ashe baki sani ba yarinya, to tashi kije gida an
gama hirar, kinga karen yayi tafiyarsa. Ka gaida
okundiri kaji? Ta ci da kyakyata dariya. Yace, ah!
Tashi karki sa yarona ya fito yana fito yana
kyakyatawa kamar dolo. Ta shi kije gida sai safe.
Don Allah kiyi hkr, so nake nayi wanka inyi
sallah. Ta fido lah nima har ka tuna min banyi ko
magriba ba. Ta juya da sauri tana cewa, sai da
safe! Yace Allah ya kaimu. Ya bita da kallo, yace
yarinya kin gama yawo kin shiga 3 kin lalace, ya
daga murya ki fa sami abinci ki ci. Ta juyo ta
amsa, kar ka damu xanci. Suka ja hankalin
mutane, don haka yama didi ya biyo baya, masu
tsinuwa nayi, masu addu'ae shiriya nayi. A tsakar
gida ta iske su Abba na jiran dawowar ta, shi da
su Alh. Basiru. Tana shigowa tasha jinin jikinta,
ta shiga bin bango, tana so ta shige falo. Alh.
Basiru ya daka mata tsawa, ke dawo nan! Simi
simi ta matso gun su ta durkusa guiwa 2, batayi
aune ba, taji saukar wani wawan mari. Gaba
daya ya ratsa kanta, ya gigita ta, ta dunkule ta
fasa kuka. A cikin ba tace ga wanda ya xabga
mata wannan marin mai tsanannin xafi ba. Sai
dai taji muryar Abba na fadin wannan shine
gargadi na karshe da xanyi miki, shi ya sa na
tara kowa su xama shaida! Idan har ba xaki bi
umarni na, ki xauna a gida ba, to wlh sai dai ki
xaba, ko mu ko Danliti! BAKIN CIKIn nan ya ishe
mu mama. Gara in sallama ki, in tabbatar da kinfi
karfina xaman kanki kikeyi. Saboda haka daga
yau kika kara sa kafarki kika fita kikaje gun yaron
nan, to kar ki dawo, ki yi zaman ki can wajensa
ku sha shagalinku yadda kuke so. Duniya ce
Mama, mai dauke da axuxuwa babu adadi! Ina
fatan kinji kuma kowa ya shaida! Alh. Basir ya
karbe karuwa kike so ki xama ko? To Allah ya
baki sa'a, mu dai ba xa mu hana shi ba, duk
ranar da koreki. Alh. Adamu yace dama saboda
me xamu hana shi? Cikin shege ne fah ajikinki,
amma bai sa kinyi nadama ba, to me xai sanya ki
kuwa? Karkiji da wai, mun tsame hannun a kanki,
haka xuri'ar gidan nan kaf! Kar ki ce kin san daya
daga cikinsu, duk ranar da wuya ta koro ki! Ta
shi ki bace mana da gani shashasha sakarya. Ta
mike da gudu ta fada dakinta, ta dasa kukanta, a
fusace abba ya bar wajen kowa ya kama
gabanmsa, suka cigaba da yada xancan a sasan
su. Daren nan su ma Umma basuyi barci ba,
musamman Umma da tabbatar wa kanta ciwon
xuciya ya kamata. Da safe ta atashi xuru-xuru
baki daya idanuwanta sun xurma, shi kansa Abba
ya rame ta maxa kawai yakeyi yana wa Umma
fada kar ta salwantar da rayuwarta akan Mama.
Ita Mama ba wannan ta aje ranta ba, kawau
burinta kasance tare da Danliti, don haka take
ganin kowa ya tsangwame ta saboda kiyayya.
Kafin safiya ma ta mance duk kalaman su Abba
da kawunninta. Allah Allah takyi ta sami saukin
laulayin safe dake damunta ta lababa taje ta
gano Danlitin ta. Xuwa 12noon ta iya shiga kicin,
ta dan tsiyayi ruwan lipton, ta dawo ta shanye.
Xufa ta keto mata, danji dadi ajikinta, kana ta
shiga bayi tayi wanka da sabulun wanki maras
kamshi. Ta kimtsa, tsaf, duk da tayi haske sosai,
ta kuma rame kwarai, kana iya gane kyanta na
asali mai daukar hankali. Ta koma ta kwanta
yana kllon agogo 1:00 ta tashi tayo alwala tayi
sallah, ta dauko gyalemnta ta xura takalma ta
leko falo bataji motsin kowa ba, ta kwahi sauri ta
fice abinta. Yara suna ce mata sai kin dawo
aunty Mama! Jin haka yasa Umma yanke sallah,
ta fito da sauri ta tambayi yaran ina maman?
Sukace yanxun ta fita. Tabi xauran, yaran suka
biyota ta tura su tace, ku kira min ita. Yara suka
fice da gudu suna kwala mata kira, Aunty Mama,
ki zo Umma na kira! Haka suke ta gudu suna fadi
har suka isketa, ta dube su tace, sai na ci
ubanku in kuna kwala min kira haka! Ni sa'ar
kuce don Ubanku? Ku tafi ku ban wuri kafin in
fallawa yaro mari! Mts..... Taja tsaki, ta wuce
abinta, yara suka dawo a guje suka iske Umma a
xaure sukace, wai sai ta ci ubanmu idan muka
sake kiranta! Ta dafe kirji tace, ta kyauta, kuje
wasan ku. Ta dawo cikin gida a salube tare da
mamakin taurin kai irin na Mama, me take nufi
kenan? Ta xauna a falo tana juyayi. Da kyar ta
sake mikewa ta shiga dakin Abba, ta tashe shi
barcin ramakon da yakeyi. Ya farka yana
kallonta......
Yace, azahar tayi ko? Tace tayi alhaji.
Ya yankura ya tashi yace menene na ganki a
salube? Tace tasake fita, wa? Mama mana. Cike
da mamaki yace ta fita? Yanxun nan kuwa,
kamar fako na takeyi, har yaran nasa su kirata,
ta dinga kunduma musu xagi, taki dawowa. Ita
Maman ta zage su? Tayi murmushin takaici, tace
kana mamaki ne? Bai kamata kayi ba alhji. Ta
kuwa tafi kenan, kinsa Allah ba zata dawo ckin
gidan nan ba. Kiyi hkr, duk abinda ke ranki na so
da kaunar Mama, ki cire ki dangana da ita, nima
na hkr da ita. Umma ta fasa kuka, ta tashi da
asauri ta bar dakin. Hankalin Abba ya kara tashi,
ya taso ya biyota dakinta, tana xaune bakin gado
kukan kawai takeyi. Ya tsaya kanta, yace saboda
Allah ya kike so nayi Halima? Ta cira kai murya
na rawa. Tace har ga Allah ba korar Mama ke
sanya ni kuka ba, tausayin rayuwarta ke bani,
yadda ta ka sa gane cewar mu ba tsangwamarta
mukeyi ba, saboda tana son Danliti. Yanxun
shikenan ba xata gane cewar alabarkar mu itace
kwanciyar hankalinta ba, duk tsananin son da
Danliti ke mata, shikenan ta xabi cigaba da
xaman shashanci akan ta nutsu, dn tym kankani
a daura masu aure? Wannan rayuawar tana cike
da tausayi da ban Mamaki, kamar Ya asirce
Mama? Ta kada kai ta ciga, ba haka Mamar mu
take ba alhji, ta sauya saboda soyayya, kenan ta
fi son shi a kanmu? Ina xan samo amsoshin nan
Alhji? Ina xan..... Ya rufe bakin da sauri, ya ace
ya isa haka! Kar ki jefa kanki damuwar da xata
tada miki ciwo, ki kauda kanki ki akan komai,
sannan ki nisanta xuciyarki ga irin wadannan
tambayoyin da kike wa kanki. Xaki xautu saboda
yarinyar da bata damu da lfyarki ba, xamani ne
Allah ya kawo mu da yara ke rufe idanuwan su
akan abinda suke so. Suyi ta fada da iyeyensu
har xuciyoyin iyayen su fara xargin asirce su
akayi. Xan ji dadi da farin ciki idan xa'a ce, duk
wannan abubuwan da suke faruwa, ki dauke shi
amatsayin mafarki mai wucewa, tamkar baki
taba haihuwar wata mai suna sakeena ba. Ta
dube shi xai yuwu ko? Mai hana? Idan har zaki
dage da adduoi, ubangiji ba xai barki haka ba, ta
goge hawayenta ta sauke gwauran numfashi
tace, xan yi iya kokarina Alhji. Ya jinjina kai.
Yace haka nafiso sadiya, kin san ina jin dadin
xama dake, kuma tun ina saurayi ban taba son
wat 'ya mace ba sai ke. Ban fatan abinda xai
salwantar min da rayuwarki, ya kasance wata
kaddara tasa kin fara barina cikin duniyar nan.
Kullum nayi sallah, sai na roki Allah ya fara
daukar raina saboda ba xan iya ganin gawarki ba
halima. Idanuwanta suka kara tara hawaye. Tace
ka daina fadar maganar nan Alhji..... Ya katse ta,
ni ma ba ason raina na fadi ba, domin sirri nane
wanda nake xaton shi kdai ne ban taba gaya miki
ba, sai yau, dole ce ta sanyani, don ina son ki
sami nutsuwa sadiya. Ta matse ido kwallatana
suka kwararo ya mika hannu ya goge mata yace,
sha kurkuminki Maman abdul 3, gwarazan
samarin nan masu takama da baiwar Allah. Ta
numfasa tace, Allah yayi masu albarka baki
dayansu. Kina nufin har da sakeena ko? Ta amsa
da kai, kafin tace, ai mu na mata fatan shiriya
ko? Yace haka ne, toh Allah ya shiryta. Amin ta
amsa. Haka yayi ta rarrashinta, ta samu
nutsuwa, sannan sukayi sallah suma mika kukan
su ga Allah. Na san kilan kuyi musu ko mamaki
idan nagaya muku Mama bata dawo gida ba, sai
bayan sallar magriba. Abu na farko da ta fara cin
karo da shi a kofar sasansu dake kulle, shine
akwatin kayanta. Taja cak! Ta tsya ta xura masa
ido tsawon tym, kana ta matsa ta tura kofar taji
ga,! A kulle. Ta tabe baki tare da jan tsaki, ta figi
akwatin ta juya tana fadin a ranta, sai aga na
kwana a titi. Kai tsaye Danliti ta dosa, yana
xaune kofar shagonsa, inda ta basa. Yana
hangota da akwati, ya mike ya shige daga ciki
yana gayawa Ayuba ga mutuniyar can tafe da
akwati, ko maganarta tace ta tabbata? Ayuba ya
murtuke fuska yace ni xaka tambaya? Au haushi
kaji? Amma dai kana ji na gaya mata kar ta
kuskura ta bari su koreta, don bani da wurin
ajeta, ko ban gaya mata ba? Yace oho! Wai kai
wani irin banxa ne? Yace Ni banxa bane, ai rainin
wayau yasa ka gaya mata hakan. Wa ke jan
ragamar rayuawarta, in ba kai ba? Ai sanin bata
da xabi shi yasa ka raina mata hankali. To ya isa
malam, sai gata tsaye gaban kanta, tana kokarin
dagawa, duk suka xubo mata ido, ta karasa
shigowa, ido waje ya dubi shirgegen akwatin, ya
ce ya dai? Bata saurare shi ba, kofar dakin ta
tasarmawa xata shige. Yayi azama ya shawo
gabanta, magana fa nake yi, kona kokarin
shigewa kamar gidanku? Ta xubo masa ido a
marairaice tace, me na gaya maka? Ni kuma me
na gaya miki? To yaya xanyi? Ina komawa na
iske akwatina akofar gida sun kulle gidansu. Ya
gayara tsayuwa, da yake kuma ke sakarya ce sai
kaka kamo hanya kika taho baki tsaya kika nemi
sulhu ba! Yanxun menene nufinki? Anan xaki
xauna? Cikin shago? Lallai kin cika dakikiya,
Jaka! Kuka sosai ya kwace mata, ta tsugunna ta
rungumi kafafwansa, murya na rawa tana fadin,
karkayi min Haka Danliti! Saboda kai suka koreni,
ina kake so naje, idan ba nan ba?
[12/01 21:58] +234 818 701 7363: BAKIN CIKI 2***15
Ayuba ya daga kanta, ya fice
hankalinsa tashe, shi kuwa ko gezau beji ba
ajikinsa, a dage yake kallonta, tsawan tym
sannan ya fizge kafarsa ya kama hanya xai fita,
da sauri ta mike ta cukuikuyo rigarsa, fadi take,
kayi hrk don girman Allah. Wasu samari 2 suka
iso wajen siyen taba sigari, ai sai suka buge da
shari'a, kaya-kaya hayaniya har waje Danliti na
daga murya shi ba xai aje ta cikin shagonwa ba,
ta koma ta nemi sulhu da iayeynta. Kan ka ce
kwabo jama'a sun cika makil a gun. Kai Mama ta
sha zagi da la'anta, Allah shi kara kwando-
kwando. Kalilan ke cewa Allah ya shiryeta, Dan
liti ya gacciye banci kofar shagoin ya xauna yace
yaga uban da ya tsaya mata agarin nan, wnada
xai sashi ya ajeta. Baiwar Allah kuwa na tsugene
gaban akwatinta, tana ruasar kuka har karfe
10pm. 'yan ganin kwakwaf suka gaji suka koma
gidajen su dauke da labari mai ban al'ajabi. Wasu
suna ganin bai kamata Uban dawaki ya koreta ba
a matsayin sa na Uba, kuma babban mutum mai
sarauta, wasu kuwa suna ganin hakan shine
daidai, imna xai sa BAKIN CIKI? Idan bai sallame
ta ba, tunda ta tara masa, ya cika masa xuciya,
tana neman fashewa ta hallakashi? Ai gara da ya
sallamata duniya ta koya mata hankali. Ga darasi
na farko nan ta fara gani, duk iskancin Danlitim
yace baxai aje taba. Alhalin saboda shi aka
koreta. Wannnan ya nuna a fili ita ta nace masa
kamar sauran 'yan mata marasa xuciya. Mutane
na mamaki abinda Danliti yake da shi wanda
yake tsonewa 'yan Mata ido. Su mutu cikin
soyayyar sa. In bata ga kyau me yake da shi? Shi
babu hali babu kwakkwaran asali. Amma duk
wacce ta fada tarkonsa sai gagari iyayenta. Ko
don kudi da ya ke kashe mus ne? Shiya sa suka
dauki laifi kacokan suka dorawa 'yan Matan masu
biye masa don kwadayi da kyalekyalen jikinsa.
Wayyi, kai bai san dawan garin ba, dai bai yi
tunanin kutsa kansa ciki ba. Tun ciki dare surutai
kala-kala suka fara baza gari. Shi kuwa gogan da
ya ga kowa ya watse sai ya matso ya xunguri
Mama da kafa, ta dago kai da sauri ta dube shi,
matso mana nan kiji, ta matsa gareshi, tana
hawaye. Ya dubeta da kyau yace, ke banxa ce
wlh, shi ya sa kika bani haushi. Nace ba xaki
xauna anan ba. In banda hauka irin naki, ya
xa'ayi ki xauna tare da mu cikin shago? To ina
sane da abinda nakeyi, kin gane? Saboda haka ki
koma ki nemi wani wurin ki xauna, ki bani nan da
sati xan san abinyi. Murya dushe tace, ni bansan
inda xani ba, a'a ko gidan 'yanwanku ba xaki je
ba? Ko baku da su ne? Sai dai inje gidan su
Baraka, yace ko gidan su Mubarak xaki, sai kinm
dawo matsalar kice. Amma ba xaki kwana
shagon nan ba. Yauwa, tashi ki sungumi
akwatinki, ki wace kar su kulle gidansu. Tace to
nagode, sai da safe, Allah ya kaimu 'ya bebine.
Muyi fada mu shirya ko? Kar ki damu xan ganki
goben. Tayi murmushi, dadi ya rufeta, ta mike
tana kara masa godiya, taja akwatinta ta nufi
gidansu Baraka. Ya mike janye da benci yana
kyalkyala dariya, ya shige shago. Kai mugu dan
gidan buzu mai shayi! Yayi wa kansa kirari ya
shige daki. Ayuba na kallonsa yana kada kai.
Gidan su Bara akulle yake, saboda sha dayan
dare tayi ma. Ta shiga bugawa har aka xo aka
bude mahaifin Baraka ke tsaye cikin xauran, ya
dubeta da kyau yace, Mama ce? Daga ina haka?
Ta fara kuka yace shigo shigo ciki! Ta wuce da
uban akwati ya maida kofa ya rufe. Tana gaba
yana biye da ita yana fadin, subhanalillahi! Dakin
Inna saude suka shiga tana tsaye tsakar daki,
lfya? Ta xube sharaf! Cikin kuka tace, abba ne ya
koreni..... Ina saude ta nemi waje ta xauna, yayin
da malam kasim ke fadin, me ya sa Uban dawaki
xaiyi hak? Inna saude tace BAKIN CIKIN ta ne ya
ishesu. Ace kamar Mama ta gagari kowa duk
abinda ya sameta da abinda ake gaya mata ba
su isheta nadama ba, idan ba su koreta ba me
kike so suyi miki? Ba shashanci kike sha'awar yi
ba? To sun baki hanya, meye kuma na kuka?
Mal. Kasim yace hakan ba hujja bace, duk abinda
xatayi, gara tana gabansu suna tsawata mata,
yau da gobe ana hada mata da addu'a, sai Allah
ya taimaketa ta gane illar abinda take aikatawa.
Saboda haka ta xauna, gobe Allah ya kaimu lfya,
xanje in ganshi. Ke kuma je ki kwanta kiyi tunani,
meye amfanin lalata rayuwarki da kikeyi? Har
jikokinki sai an yi musu gori, wannnan abinda
kika aikata! Kina da babban laifi mama, sai kin
tuba kin bi Allah kin bi iyayenki sannnan xaki ga
daidai a rayuwarki, kinji ni? Ta amsa da kai, yace
ta shi ki shiga wajen 'yar uwarji kafin Allah ya
kaimu goben. Ta mike simi-simi ta ja akwatinta,
inna saude ta xuba mata ido tana mamakinta. Ta
kada kai, taca baka ce xata aikata ba, yarinya
kyakkyawa, ta lalata rayuwarta. Allah ya shirya
mana, yace amin albarkar annabi. Atsakar gida
taga Baraka tsaye tana share hwaye, ta matso ta
kama mata akwatin suka shiga dakin, kowacce ta
nemi wuri ta xauna bakin katifa. Baraka ta
dubeta.........
Tace anya mama abubuwa da kike yi
kanki kalau? Ke bakijin kinya? Baki tunanin gaba
daya idanuwan garin nan sun dawo bisa kanki?
Baki da martaba da darajar Abba agarin nan?
Haba Mama, kamar ba tare muka taso ba?
Tarbiyarmu iri daya, nutsuwa da kamun kai, kowa
na yabon mu. Mutane na rububin mu, da son
hada xuri'a tagari. Ta daga kai sama, idanuwa
cike da hawaye ta cigaba, Allah ya isa
tsakaninmu da Danliti! Ta dube ta sukayi ma juna
xuru kafin Mama tace kar ki sake xagin Danliti
Baraka, alhakin sa xai kamaki, laifin mune? Tun
tym din da mukace muna son juna, ya kamata su
Abba su rungume mu hannu 2 amma suka ki,
suka gwammace in kwashe kayana in bishi. A
tunanin ki wane sakamako ya kamata su gani?
Bayan wannan dake jikina? Baki sake take
kallonta, kafin tace, maganar Banza ce, idan duka
jina kunnuwa ne xai taba sauraronki ba, wa kika
burge don kin aikiata wannnan sakarcin? Shi
kansa Danlitin adage yke kallonki. Kin dawo an yi
miki afuwa, cikin nman ya bayyana, duk sun hkr,
sun shanye, amma ki ntsu xuwa tym din da xaki
haihu, a daura maki aure, kar fa ki manta xaman
nan naki agida ibadane tunda Allah ya shifida
hakan, sai ki ga dalilin xaman, duk xunubunku
sun kankare, auran ku yayi karko tare da xuria
masu albarka. Ki kwanta kiyi tunani mama, ko
asiri Dan liti yayi miki, xakewar taki tayi yawa. Ta
sualala kafita ta kwanta, tace, na kwanta shekiya
Baraka, sai da safe ko? Ta bita da kallo ta
numfasa, tace Allah ya sa ki gane. Amin, ta
amsa da gatse ta juya baya abinta. Baraka ta
mike ta rufe daki ta dawo ta kwnta. Ta jima bata
sami barci ba, saboda juyayin halin da 'yar
uwarta ta shiga. Da farar safiya M.kasim ya usa
gidan Ubban dawaki yasa aka yi masa sallama da
shi, jin cewa shine ke sallam ya sa yace ya shigo
cikin gida. Bayan su gaisa. Umma ta fito suka
gaisa. Sannan ya maida jawabinsa, a karshe
yace, alhaji kar bacin rai yasa ka yanke wannan
hukunci, ni ina ganin gara yarinyar nan ta xauna
agaban ku, kuna tsawata mata, sai Allah ya
taimakemu ya shiryar da ita. Don girman Allah ka
yafe mata dawo gida, tunda tayi tunani taxo
wajenmu, ta kawo mana kukanta. Abba ya gyara
xama yace, a tunanin ka a kashin kanta, ta yanke
shawara taje wajen ku? To ba haka xancen yake
ba, kila ba xaka sani ba ne, saboda kuan cikin
lungu. Amma ni tun jiya na sami labarin
wulakancin da yaron nan yayi mata, ya tara mata
jama'a, ya tozarta ta, ya kuma ce ba xata xauna
masa a shago ba, kaji dalilin nemanku, amma ba
nadama tayi ba. Yace, duk da haka ina son ka
duba girman da martabar ka agarin nan. Kayi hkri
ka amshi rokona, ba don ni ba, sai don girman
Allah da darajar iyaye. Ya sunkuar da kai yana
kadawa, kafin yace, M.kasim ban ki ta taka ba,
amma ba xan iya xama da yarinyar da ban isa in
bata umarni ta bi ba. Ta fita tayo shashancinta,
ta dawo min gida ta wanke najasa ta kwanta.
Mts! Ban jin idanuwana xa su iya jure gainin
wannan kaxanta. Gara ta tafu su cikashe. Wlh na
hkr da ita, kuma ina rokon Allah ya sanya mana
dangani nida Mahaifiyarta, ba kuma xamu gaza
ba wajen yi mata addu-ar shiriya. Watakila wata
rana taga uwar bari, ta dawo da kanta ta neme
mu. Kaga a tym din xan tabbatar da tayi nadama.
M. Kasim yayi shiru, jawabin Uban dawaki na
cike da tausayi, ya numfasa, yace, na yarda da
kai Alh. Sai dai har yanxun ina rokonka, da ka
sake bata dama ta karshe, mu gani.idan bata
daina ba, to muma sai mu tsame hannayen mu.
M. Kasim ya cikwa Abba ido kwarai da gaske, ya
jima kafin ya numfasa, yace, shikenan ba komai
nagode. Yace nima nagode, Hajiya akara hkr, a
bata damar karshe, tace babu komai M. Kasim,
Allah saka da alkhairi. Yace amin, barin in koma
in turo saude ta dawo ita. Tace to ka tsaya kaga
abin kari akawo maka mana, ya mike cike da
fara'a, yana fadin alhmdlh, kar ki damu nagode,
to nabr ku lfya, Allah ya shige mana gaba, suka
amsa amin. Yaka hanya fice. Bayan tafiyarsa
kamar da hadin baki, jama'a sukayi ta xuwa suna
ba uban dawaki hrk tare da rokonsa ya daure ya
maida 'yarda gabasa xai fi kyau agareshi. A cikin
su har da abokansa da yaron gidansa, watau
kalla. Duk ya karbi rokonsu, kuma yaji dadin
kulawar jama'a gareshi tare da tausaya masa
akan kaddarar da ta fada wa iyalinsa. Karfe Tara
saura, Inna saude ta taso Mama xuwa gida. Bata
ma biyo da ita ta shagon Danliti ba, balle ya
gansu, haka suka taru da matan gidan kamar
zasu cinye ta danya, sannan matza suka shigo
suka dasa nasu. A gaban kowa suka tilasta, ta
dauki alkawarin ba xata sake xuwa ko ina ba,
kidan kuwa ta saba, to a yanke mata hkunci da
yafi wannan. Kwana 2 hatsaniyar nan ta kwnata,
mama na xaune cikin gida bata fita daidai da
tsakar gidan sasansu. Muna iya cewa Danliti bai
murda kambunsa bane haka? Saboda haka
xuciyar Mama ta sami 'ya nutsuwa. Bata ita
kadai ba, su abba ma sun sami 'ya nutsuwa har
tana debo 'ya'yan itatuwan da Abba ya ka siyo ta
kawo mata, tace ta sha saboda rashin cin abinci
da take fama da shi.....
***************** A wannan
asabar din ma abdulkrm ya xo daiyalinsa duka.
Su ameera nata murnar ganin auntynsum domin
sun jima basu ganta ba. Dr. Na ta dabo, yana son
ya taka, sai 'yar banxar kuiyam shi ya sa yaki
yarda Mama ta daukeshi. Aunty Rabi ta tasa ta
da nasihohi, ayoyi, hadisan Manxo SAW akan ta
dage ta yaki xuciyarta ta dawo kan kanya,
sannan ta nuna mata wannan ba shine soyayya
ba, duka saurayin da ya nemi lalacewa da
yarinyar da yake so, a hakikanin gaskiyya ba son
gaskiyya yake mata ba. Sha'awar sassan jikinta
kawai yakeyi. Haka yayanta ta tsatsagge mata
gaskiyya, har yayi mata alkawarin idan ta nutsu
ta xauna gida kamar yadda aka umarceta, to
bayan ta haohu za'ayi bikinta, duk abinda take
so, shi xai sayo mata. Mama ta wani kuka tana
ba su ameera tausayi. Anann suka kwana,
washegari lhadi karfe 12noon suka juya. Su
ameera nata tambayar antyn su yaushe xata xo?
Tace kar su damu tana nan xuwa nan bada
dadewa ba, suna isa gida, yayan ya kira 'yan
uwansa, ya labarta musu abinda ya gani game
da Mama, idan har ya dore a hakan, alhmdlh! Ana
iya cewa an fara samun nasara. Kowa yayi farin
ciki jin wannan labarin da fatan Allah ya shige
mus gaba. Allah, da ikonsa a yammacin yau din,
tun bayan sallar la'asar mama ke cike da kewar
Danliti, kafin 5pm ra mance kaf! Da alkawuran da
dauka, babu abinda take so face gain Danliti,
kewarsa ta gigita kwakwalwarta, ta birkita ta.
Kamar an tsikare, kawai ta tashi ta suri gyale da
takalmi ta fito kanta tsaye ta fice abinta. Dan
gogan ta samun cikin dakin barcinsu, tana
shigowa yana xubawa wani kaskon rushi ruwa,
ya dago ido ya dubeta, yace ba xan miki sannu
da xuwa ba. Ta xaune gefensa tana murmushi,
saboda me? Ya xubo mata harara, yace kwanaki
nawa rabon ki da nan? Sabo da nayi miki fada
ko? Ta rungomoshi tana dariya, ayya nawan ba
haka bane, kowa yasa min ido, sai surutai sukeyi
kamar ni kadai na fara soyayya agarin nan.
Amma kana cikin raina, kaima ka sani, bani da
burin da wuce in kasanxe tare da kai, ta bae baki
yace tsarani, au baka yarda ba? T yanxun ba ni
na xo ba? Dana kiraki ba? Ka kirani? Kamar ya?
Ya ture kaskon ba xaki gane. Sai dai na yarda
kina sona, tunda kika amsa kiran. Ta xura masa
ido tace ngode, tunda kasan hakan, me kake yi
da kasko? Ke duk xamanki a dakin nan baki taba
ganinsa ba? Da shi fah muke turaren daki. Kai
amma wannan bai hadu ba, kauri gare shi, kin
kuwa san tsadarsa? Ai ku maza ba gwabe bakin
ku ake wajen siyayya? Kabari xan kawo maka
mai kyau, idan ka sanya shi sai makwabta sun
tambayeka ina ka samo. Ko? To sai kin kawo din.
Yanxun mu ake maganar turare, ina kuka kwana
da su Abba? Ta tabe baki, me ma? Wai an bashi
hkr ya kyaleni, amma idan na sake xuwa nan,
dole in tafi. To kice kin karya doka, tunda gaki
kin sake xuwa, ni kuma da har nayi cinikin wani
gida can bayan tasha, ina fasa kenan? Bakinta
har kunne, tace ka fasa kuma? Ai xai mana
anfani idan munyi aure ko? Ya shafa kai,
gaskiyya ne, xan biya kudin in sa a gyara shi, ai
sau muje ma ki ganshi ko? Ya xama dole, yaushe
xamu? Duk tym din da kika shirya. Ko yanxumn a
shirye nake, mu tafi kenan? Bismillah. Ta
sumbace ta yace, amarya ta kenan, maman bebi!
Ta rausaya da kai tana dariya. Tare suka fito
yana rike da hannunta, har gaban motarsa. Ya
bude mata ta shige, ta dawo maxauninsa yaka
suka tafi. Gidan ginin kasa ne mai dauke da
dakuna 2 kicin da bayi, tsakar gidan turbayar
kasa ce, haka ginin babu digon siminti ko kadan,
zallar kasar ce kawai, illah iyaka cikin dakunan
anyi masu dabe, suna tsaye kafada da kafada, ya
dubeta yace, kinga gidan, ina fatan yayi miki? Ta
yake baki ta makalo wuyansa tace, ya fiye min
kowannne irin gida muddin da kai xan xauna
cikinsa. Kar wani abu ya dameka,a hankali na
gyara shi, kyau xaiyi fa, yayi dan murmushim ya
falla ido sannan yace, toh shikenan, tunda yayi
maki, yau din xan nemi dillalin in bashi kudin. Ta
kara kankame shi tace, ina tayaka murna. Ya
xubo mata ido yace ni xaki taya murna, ko ke xan
taya murna, gidan ki ne fa? Tayi dariya sosai. To
dukkan mu Congratulations! Ya sumbaci labbata,
tace thnk U! Sun jima cikin gidan suna
sharholiyar su, ana kiran magriba, suka fito, ya
kulle kwadaon gidan suka koma shago, maimako
ta koma gida sai ta rashe nan, tana nishadantar
da shi, kamar yadda ya bukata, ya siyo mata
abubuwan da take so, tace, tayi hani'an, kai barci
sace ta mana, ta yada kai bisa filo tai tayi
kuwa......
11pm za su kulle hsago, ayuba yayi
juyin duniyan na Danliti ta tashe ta, ta tafi gida
amma yaki, ya kuma hana Ayuba ya tasheta. Da
ita suka kulle shago, ayuba ya kwana tsakar
shagon, shi kuwa dan gogan yana tare da
gimbiyar. Tsakar dare ta farka da ganta tare da
mutum. Ta tashi xaune ta bubbuga shi ya tashi,
menene? Tace dama ban tafi gida ba? Yace ga
shi nan kin gani, ai da ka sani ka tasheni Danliti.
Yace waya gaya miki ana tashin mai ciki barci?
Kiyi kwanciyarki kawai da safe kin koma, Abba
xai koro ni Danliti, yace akwai gida na biya
kudinsa, baki da haushin wannan. Idan kina
kwanciyarki, ki kwanta ida kuma yanxun xaki fita
2am ga hanya nan babu ruwana. Bebi na kawai
nake ji. Ta watso masa harara ni banda ni ko?
To! Na ga kin wani hakikance ne, meye sabo idan
kin kwana anan? In banda gulma! Ta dare ruwan
cikinsa ta kai masa duka, ni ce magulmaciya?
Kai din fa? Todama mai neman kuka ne aka jefa
shi da kashi awaki, sai yaya? Washegari, yadda
bata sallaci magriba da isha ba haka batayi
asuba ba, karfe 7am ta dauko hanya. Gata nan
ga nan har gida, salalau-salalau ta karaso ciki, ta
iske duk sammakonta Abba ya riga ta tara
jama'am don haka tana xuwa tsakar falo, tayi
sanrada. Gwiuwa 2 ta xbe ta fara kuka. Kowa ya
saki baki yana kallonta, M.kasin ya fara magana,
yanxun saboda Allah Mama duk maganganun da
aka gaya miki ta bayan kunnunwaki suka wuce?
Ashe haka kike da taurin kai? To mu babu ruwan
mu, dama rokonsa mukayi, ya ga girman mu ya
hkr, tunda ke baki gani ba. Shikenan ga hanya
na, ki bi duk wacce kika xaba. Abu yaya kamari
har da kwana? Ke Mama kiji tsoron Allah ki
tausayawa iyayenki. Ba xata suka ji tana
magana, wlh Baba bada niyyara kwana ba na fita,
Danliti ne ya sayi gida, yace muje na gani, mun
dawo ina hutawa, ban tym din da barci ya
kwasheni ba, abba ya xaburo yana fadin, kunaji
Maganar Banxan da take fadi ko? Kun tabbatar
da cewa abinda nake fadi gaskiyya ne? To ya
isheni haka! Ya isheni haka!! BAKIN CIKI ba xai
akshe mu ba. Daga nan ki juya ko koma, idan har
ki na son kanki da arxiki, wlh! Wlh!! Babu wanda
ya ya sake roko na in kyaleki cikin gidan nan!
Duniya ce da fadi, karki saurara wajen bin ta
kwararo-kwararo har ki gano iyakar ta! Tashi ki
bace min da gani, kafin in kusa kashe ki da duka.
Gaba daya falon yayi tsit, sai shasheshekar
kukan Mama, jim kadan muryar abba ta kara
gauraye falon, kai Jama'a! Ina xan kai takaici da
BAKIN CIKI? Me nxan yi wa yarinyar nan a dniya
na huce, banda in sallama ta, tamkar ban taba
haihuwarta ba? Ki tashi fice min nace, in daina
ganinki a gabana..... Ki ta... Kawai sai ya yanke
jiki ya fadi, gaba daya suka mike da sallalami
sukayi kansa......
Toh masu karatu, wannan fa shine
wasa farin girki. Nayi iya kar kokarina ace nayi
muku sallama anan. Amma ina abin ya faskara,
kuyi min hkr karshen badakalar wannan littafi
yana cikin 3, ku biyo ni, kada ku gajiya nayi
gaba....................THE END!!!
Download Book Here Part 2
No comments:
Post a Comment