Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano da ke arewacin Nigeria ta cafke wata Amarya da ake zargi ta kashe mijinta ta hanyar sanya masa guba cikin abinci.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Magaji Majiya ya shaida wa manema labarai cewa 'yan uwan mijinta ne suka kai rahoto ofishin 'yan sanda da ke Kofar Wambai a birnin Kano.
- An kai wadda ake zargi ta kashe mijin nata a gidan yari dake abuja
- Ana zargin wata ma ta soka wa mijinta kwalba a gusau
- Ya ce ana zargin Amaryar da sanyawa mijinta guba ne ranar alhamis 4 ga watan Janairun 2018 kuma ya rasu ne bayan kwana guda da sanya masa gubar.Kakakin rundunar ya ce a lokaci da 'yan sanda suka isa gidan sun tarar cewa Amaryar ta tsere kafin daga bisani aka cafke ta ranar Litinin.Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce an yi wa Amaryar auren dole ne.A 'yan kwanakin baya bayan nan an sha samun rahotanni wasu mata da ake zargi da kashe mazajen su.
- Sai dai masana ilimin zamantakewa na ganin akwai bukatar ma'aurata su kai zuciya nesa a lokacin da suka yi fushi domin gujewa nadama.
No comments:
Post a Comment